Showing 42001 words to 45000 words out of 139785 words
Chapter 15 - Albi Book Complete document by Hajjace.txt
ɗaya ga wani irin sanyi da yaji yana hurowa ta ko'ina ta cikin falon. Da sassarfa ya nufeta ya ɗagata cak! ya nufi stairs har ya buɗe ƙofar ta fara mutsu-mutsu cikin hannunsa, a hankali kuma ta shiga buɗe idonta tayi arba da fuskarsa, tana so ya sauketa bai sauketa ba har ya kaita kan bed. Da sauri ta mike zaune tana wani haɗe rai yasan laifinsa, kama kunne yayi yana wani langaɓe mata kai, make kafaɗa tayi ta sauka daga kan bed gamida shigewarta toilet, Shima ɗakin ya bari ya nufi nasa ɗakin. Har kusan karfe 6:00 na safe tayi wanka sanye take cikin wata Dubai a baya baƙa mai bakin lace a duka hannayen rigar, tayi rolling da veil ɗin abayar tayi wani irin kyau. Shida da mintuna ya turo ƙofar room ɗin da take ciki, ta ɗaga kai tana kallon ƙofar lokaci ɗaya ta haɗe rai gamida turo baki. Shima lokacin yayi wanka cikin yadin filtex ashcolour sai kamshi yake xubawa. Ta mike tsaye rataye da handbag nata burinta kawai Imran ya sauketa a makaranta, taje zata wucesa ya dawo da ita zuwa gabansa yana yi mata wani irin kallo da idonsa masu cike da soyayyarta. Kallon shigarta yake tun daga sama har ƙasa yadda yaga tayi wani shigen kyau. Itama kallansa tai yayi mata kyau, sai dai shi yaji tsoron kyan nata, Ya shafa sumar kansa cikin husky voice ɗinsa yake faɗin "Hijab." Tasha toka tamkar xata fashe masa da kuka take faɗin. "Tare fa zamu fita Imran, kuma a mota ne dan Allah kabarni a haka zafin zai yi min yawa wallahi, haba ga xafin doguwar riga ga dogon hijab." Shima cikin tsagwaran kishi yake faɗin. "Makaranta xaki shiga fa R... Are You mad?" Ya karasa maganar a ɗan hasale. Ɗaga kai tayi tana kallonsa meye kuma abun ɓacin rai a ciki? Ta girgiza kai tana faɗin, "Hhmm bani da traditional kaya, Imran tare muka kaisu ɗinki taya xan saka doguwar riga na kawo hijab har ƙasa na saka? kayi hakuri dan Allah muje Ihsan na jirana." Ta faɗa tana ƙoƙarin kama hannunsa ya fisge hannun yayi gaba. Binsa tayi tana girgiza kai yau ƴan rigimar sun motsa kenan. Yana tuki ba tare da ya kalleta ba yake tambayarta mexataci, tace Ihsan xata shirya mana breakfast da haka ya mai da hankalinsa kan tuki. Yana gama parking ya ciro 5k ya damka mata acikin tafin hannunta yana faɗin "Idan kun tashi ki kirani naxo mu koma gida." Kallonsa tayi tana girgiza kai, "Nafa dawo hostel Imran." Ko kallonta baiyi ba har ta fice daga motar. Zama tayi gefen bed tana kallon Ihsan, itama Ihsan ɗin kallon Rahama takeyi wadda taga duk tabi ta canja mata tamkar wacce tayi shekara bata ganta ba. Ihsan ta girgiza kai tana faɗin. "Wannan tsare gida haka fa? yau kuma da fushinwa aka baro gida Abba, Ummi ko Imraan?." Ta faɗa tana maida kallonta kan Rahama. Girgiza kai kawai tayi ta amshi mug ɗin hannun Ihsan wanda yake cike da damammen kunun gyada. "Ga naki can a flask na xuba maki." Rahama ta girgiza kai tana faɗin, "Wannan nake so kin san ni bana shiri da duk wani abu mai xafi." Hira sukayi sama-sama suka ƙara duba karatun gwajin da xasuyi sannan suka fice. Basu suka dawo hostel ba sai ƙarfe biyu na rana ko wace agajiye take wanka kurum Rahama tayi gamida sallar azahar tana kwance kan bed bacci ne sosai acikin idanunta, daman sun riga da sunci abinci a cafeteria kafin su shigo hostel, kuma suna fitowa ta kunna wayarta dan kiran Imran sai dai wayar a kashe bata kawo komai aranta ba tasan maybe yana busy..
**********************
Wani irin kallo Mummy ta shiga aikawa Hajiya Azizah tana faɗin. "Yanzu saboda bakin ciki anga Imran ya fara kula Humaida shine xaki zo kice ayi maganar aurensa da Ilham? Ni dai wallahi daga sama kikazo da wannan xancen dan ban taɓa jiba." Cike da mugun jin zafinta Hajiya Azizah ke faɗin. "Auh ashe har Humaidah wannan yarinyyar da xata zo sa'ar Imran ɗin ita kika ƙirƙirar xai aura? tsohuwar macce ragin wasu maxan ita kike yiwa Imran fatan aura?!" "Ya isheku?" Matawalle ya faɗa yana daka masu tsawa, "Dukanku bance kuxo kuyi min zaune kuna kara ɓatamin rai ba, idan har babu wacce xata bani shawarar yarda yarona xai fitar harkar yarinyyar nan ba ku tashi ku fita, kuma ni baxan tilasta Imran lallai dole sai ya auri xabin ɗaya daga cikin kuba, kun sani duk abunda yarona keso shi nakeso, ko wannan yarinyyar da ya kawo sabida tana jinin Abubakar Galadanci shi yasa kawai bana son auren." Baki buɗe Azizah ke kallonsa ta girgiza kai aranta tana faɗin. "inhar tana raye Imran Matawalle bashida wata matar aure sai yarta ilham." Amma a fili cewa tayi. "Kayi hakuri Yaya ga shawara tunda kasa an ɗauko maka Imran Itama yarinyyar kasa a ɗauko maka ita ka kaita wani gidan na daban a boye maka ita. Kaga idan Imran yaci nema ya gaji maybe ya hakura da ita. Sai ka daukesa zuwa wani ƙasar na wani lokaci." Wani irin murmushi Matawalle ya saki yana faɗin "Shawara mai kyau Azizah, dan haka watarana nake son hangen nesanki." Wani kallo ta shiga yiwa Mommy tana juya ido. A fusace Mommy tabar parlorn bayan fitar ta Azizah ta ƙara karya murya tana faɗin. "Da izinin Allah plan ɗin nan xaiyi aiki Yaya, idan har Allah yasa an dace kawai a haɗa aurensa da Ilham a tura su wata ƙasar na wani lokaci." Matawalle ya shiga girgiza kai yana cewa. "Aziza kina manta Imran ne, kina nuna tamkar baki san taurin kansa ba, arabasa da wannan yarinyyar da ina jin ta kusa kamo soyayyata a xuciyar Imran a rabasu kina tunanin zai yarda ya auri Ilham ɗin ne? kedai mu cigaba da lallaɓa shi idan ya amince zai aureta ba shikenan ba. Ai abun farin ciki ne wajan mu.." Mai yiwa Imran hidima Matawalle ya baiwa motar Imran ɗin yace yaje b.u.k ya dauko masa Rahama su haɗu a guest house ɗinshi. Sannan da tashiga motar ya shaƙa mata abunda xai gusar mata da hankalinta na ɗan wani lokaci.
Har kusan 3:00pm bata samu lambar Imran ba jikinta yana bata tabbas babu lafiya dan baya taɓa kaiwa haka ba su yi waya ba dan ko sunyi faɗa xai kira yaji lafiyarta. A bangaren Al'ameen kuwa yace mata duk yau basu haɗu ba sannan bai wani daga hankalinsa ba yasan kila Imran ɗin a buge yake can wani wajan. Haka ya kwantarwa da rahama hankali yace yasan Imran yana lafiya, da haka sukayi sallama har kusan 5:00pm Rahama ta fito daga hostel riqe da waya a hannunta, wannan karon tayi wanka ta canja kaya, Fitowa tayi daga cikin hostel tana son shakar iska na daban, haka hankalinta gaba ɗaya bai natsu da kashe wayar da Imran yayi ba, tana ta tunanin ko ta shiga adaidaita taje gidan ko ta kira Al'ameen ya maidata har tayi dialling lambar Al'ameen tayi saurin katse kiran hango motar Imran da tayi, cike da mamaki take bin motar da kallo. Misbahu yana hangota ya sauke ajiyar xuciya dan kusan awarsa biyu anan ko mai kama da ita bai gani ba, gashi daman Matawalle yayi masa gargaɗi akan ko mai xai faru ya tsaya ya jirata dan an tabbatar da tana cikin makarantar. Da mamaki take bin wanda ya fito daga cikin motar da kallo, tunani take ina ta san wannan fuskar? da ladabi Misbahu ya ƙarasa inda take yana gaisheta da respect. Ta amsa tana kallon sa anan ya shiga yi mata bayanin shi yaron Imran ne bashida lafiya zuwa yayi ma ya tafi da ita. Hankali tashe take faɗin "Meya sami Imran din?" Dama ta fito da wayarta dan haka kasa komawa tayiwa Ihsan sallama kawai ta faɗa front side, gaba ɗaya tunaninta ya tafi akan meya samu Imran? Gudu kawai Misbahu keyi da motar ganin hankalinta tamkar baya jikinta yasa yayi amfani da wannan damar ya hura mata wata powder a fuska, Rahama xatayi magana taji kanta na wani irin juyawa daga nan bata sake sanin abinda ke faruwa ba. Har bayan magrib Ihsan ta kasa samun natsuwa toh ina Rahama ta shiga ne? Dan bata taɓa fita ba batareda ta sanar mata ba ta gashi ta buga wayarta yafi sau goma a kashe. Gaba ɗaya sabbin dabi'un da Rahama ta tsiro dasu a kwanan nan suna daure mata kai. Haka ta hakura ta xubawa sarautar Allah ido ko a ina take tasan ita ba yarinyya bace xata iya tsare mutuncin ta duk da yau da gobe baxaka iya shaidar halin dan Adam ba. Manyan sojojin dake zagaye dashi kawai yake bi da kallo kowane fuskarsa babu cikakkar fara'a ya dubi ɗakin da yake kwance akan bed xuciyarsa na tafasa cikin harshen turanci yake faɗin "Ku su wanene? a ina ne nan?" Ya faɗa yana daka masu wata irin tsawa dan gaba ɗaya a ruɗe yake bai san a inda yake ba. Jin sunyi masa shiru yasa yaji ransa ya kara ɓaci sauka yayi daga kan bed ɗin ya nufi ƙofa ya buɗe. Bin parlorn kawai yake da kallo ya runtse ido gamida dafe kansa yana sauke wani irin numfashi, kara buɗe idonsa yayi yana bin manyyan hotonan Matawalle dake manne a bangon falon, sai yanxu ya fahimci a inda yake wato a guest house ɗin Matawalle, but ya akayi yaxo nan? sai lokacin ya tuna ya shiga wani restaurant xaici abinci, wasu kattin mutane yaga sun xagayesa sun rufe masa fuska, Kenan duka aikin Daddyn shi ne? ya buɗe idonsa cike da wani sabon ɓacin rai, yana shiga cikin parlorn yayi arba da mahaifinsa zaune a ɗaya daga cikin manyyan kujerun alfarmar da suka kawata falon. Da fara'a mai girma Matawalle ke faɗin. "Ka tashi kenan?" Ya karaso cikin falon da wani sabon ɓacin rai yake faɗin, "Daddy ya akayi naxo nan?" Murmushi Matawalle yayi cike da wata irin soyayyar Imran ɗin komai yayi masa baya iya jure fushi dashi. "Zan amsa maka duka tambayoyinka kafin nan kaje kayi wanka ka canja kayan jikinka ka rama sallolin dake bisa kanka sai ka dawo muyi dinner yau tare zamu ci abincin dare, rabon da mu xauna muci abincin dare tare dakai baxan iya tuna kokacin ba." Zaiyi magana Matawalle ya dakatar dashi" Bana son musu Imran idan kuma kayi girman kai xan tafi na barka da mutanen nan acikin gidan nan idan naga dama ko kofar gate kafarka bazata taka ba kasan halina." Matawalle ya ƙarasa maganar yana kallon sa, sanin halin matawalle Imran ya juya da sassarfa yabar falon, salollin duka ya jera su babu wata addu'a tunanin sa kakaf yana ga Rahama Galadanci bai sha wahala wajen canja kaya ba dan ko'ina yana da kayan sakawa Matawalle yana sawa a xuba kayan Imran a duka gidajensa da yake shakatawa acikin su. Hango Matawalle acikin dinning area yasa Imran ɗin ya kara haɗe rai ganin manyyan kuloli wanda kamshin abinci kurum ya tabbatar masa dana mommy ne. Yaja seat ya xauna kusa ga Matawalle falon ya rage daga Imran ɗin sai mahaifinsa, Matawalle da kansa yayi serving ɗin Imran ɗin ya tura abinci gabansa. Sosai Imran yaci abinci Matawalle ya kallesa cike da kulawa yana faɗin. "Hope kabi umurnina ka rabu da yarinyyar na?" Imran ya kalli Matawalle idonsa na kadawa lokaci daya yana girgixa kai yake faɗin. "Rabuwa da Rahama daddy ba abu bane mai sauqi, kayi hakuri kayi hakuri dan Allah baxan iya wannan biyayyar ba." Wani irin kallo Matawalle ya riqa yi masa kafin ya haɗe wani abu da yakeji kasan xuciyarsa. "Kana tunanin idan ban amince da auren naka ba xaiyi albarka ne.?" Matawalle ya faɗa idonsa na canja kala haka ya shiga tari da sauri Imran ya riqesa sabida yasan mahaifinsa nada hawan jini, bottle water ya ɓalle yana faɗin "Daddy kasha ruwa dan Allah." Matawalle ya karɓa yasha, xaiyi magana Imran ya dakatar dashi. "Mubar wannan maganar zuwa wani lokacin, muje gida na duba lafiyar ka, nasan ko maganin naka baka sha kuma gashi ka haɗu da matar da batasan ciwon kanta ba." Har mota Imran yaja Matawalle duk da gaba ɗaya tunaninsa na akan Rahama bari ya gama da lafiyar mahaifinsa tukuna. Shi yake tukin sauran masu kula da senator Matawalle na bayansu. Har cikin master bedroom Imran ya shiga da Matawalle ya kwantar dashi a hankali, Mommy ce ta shigo arikice ta ƙaraso tana wani riqe hannun daddy tana faɗin. "Ciwon ne?" Imran yayi tsaki aransa gamida girgiza kai ya nufi inda maganin Daddynsa yake ya ɗauka ya dawo ya xauna ya ɓalla ya bashi. Mommy na riqe dashi tana yi masa sannu ta girgiza kai tana faɗin. "Ga tafiyar mu marocow jibi ya xamuyi da Maheera Alhaji?" Mommy ta faɗa tana kallon sa. Da kakkausar murya Imran ke faɗin "Me za'a aje ayiwa maheera?" Mommy tayi masa wani kallo tana faɗin "Sun samu hutu xamuje muxo daita." Wani kallo Imran ya shiga yiwa Mommy. "Ita bata da ƙafafuwan shigowa jirgine har sai kunje kunxo da ita? kuma harda Daddy?" Ya faɗa yana kallon daddy. Ya kuma haɗe rai tamkar shine daddyn yana cewa "Babu wanda xaije a cikin ku xan yi mata booking flight jibi ta taho." Da wani irin kallo Mommy ke binsa xatayi magana ya dakatar da ita "Daddy na bukatar huta please kin san ciwonsa baya son hayaniya." A fusace Mommy tabar ɗakin ya shafa sumar kansa aransa yake faɗin foolish women. Sai da mahaifinsa ya samu bacci sosai yabar part ɗinsa. Wayarsa ya fidda da mamaki ya ganta a kashe, da sauri ya kunna wayar ya ɗauki motar Matawalle guda ɗaya da sauri maigadi ya buɗe masa gate da wani irin speed yabar gidan..
#Asmy b Aliyu
#Hajja ce
#imran Matawalle
#Rahama galadanci#
Haske Writer's Association
[11/12, 9:34 AM] Asmy B Aliyu😘: *ALBI....*
(My Heart❤️)
NA
*ASMY B ALIYU*
DA
*HAJJA CE*
PAID BOOK..#(500)
*Account Details*
0004157137
*Jaiz Bank*
*Asma'u Buhari Aliyu*
Shaidar biya ta
08086207764
*Katin waya na MTN ta 07043079282 shaidar biya ta 07065283730 view WhatsApp*
21.....
Kai tsaye B.U.K ya nufa, yana tuki yana kiranta amma baya samu. Yana shiga ya dinga ware eye's ko zai hangota amman ya kasa ganin komai kama da ita, dole tasa shi karya duk wani girman kansa ya tari wata ɗaliba da yaga zata shiga cikin hostel ɗin su, da wani irin taku budurwar nan ta ƙarasa wajansa Imran Matawalle wani irin farin ciki yana ratsata ganin handsome guy yana tsaida ita, idanunsa akan gate ɗin hostel ɗin yake cewa dan Allah idan ta shiga ta kira masa Rahama Galadanci ko Ihsan, cikin ƙasa da murya tace. "Waza'a ce musu?" Sai da ya furzar da iska daga cikin bakinsa sannan ya ɗora manyan idanunsa masu narka zuciyar ƴan mata yace. "Imran Matawalle." Cikin mamaki tare da zaro ido tana dafe kirji tace. "Wai senator Matawalle kake nufi?" Kallan da yai mata ne yasa ta saurin juyawa da gudu tana jin wani irin farin ciki yau tayi magana da ɗan gidan senator. Kwance ta tarar da Ihsan tana game a wayarta, zama tayi da yake department ɗaya suke tace da ita. "Kinsan Imran Matawalle?" Da sauri Ihsan ta kalleta tana mamakin jin sunan a bakin Zainab. "Nasan shi meya faru?" Duka Zainab ta kaiwa Ihsan a saman cinyarta sai wani tsalleta takeyi. "Yana bakin gate ya kirani yace dan Allah na kira masa Rahama ko ke, meye alaƙarku dashi?" Jin haka yasa Ihsan saurin sakkowa daga bed tana neman hijab take bawa Zainab amsa. "Imran shine wanda zai auri Rahama." Zainab ta buɗe baki da ido saboda mamaki, Ihsan ta kalleta tana rike handle ɗin ƙofa. "Ki fito zan rufe room ɗin." Zainab ta miƙe zuciyarta cike da al'ajabi. Tunda ya hango Ihsan yaji zuciyarsa ta shiga shakko, me hakan yake nufi? Rahama bazata zo gareshi ba ko bata da lafiya shine ta turo masa Ihsan? "Barka da yamma I Matawalle." Kasa amsawa yai sai tambaya da ya jefa mata. "Ina Rahama take?" Da mamaki Ihsan tace. "Ni wallahi na ɗauka kuna tare, tun ɗazu nima nake nemanta a waya amma bana samu, handbag ɗin da tazo da ita tana ɗaki bata ɗauka ba." Hankalin Imran yai matuƙar tashi, ina Rahama zataje? Ko sallama kasa yiwa Ihsan yai kawai ya shiga mota yaja, direct gidansa ya nufa kota koma can, yai duban duniya beganta ba dama kuma mai gadi ya sanar dashi bata dawo ba. Hannunsa biyu yasa a cikin lallausar sumar kanshi yajata tare da cije baki yana "Rahma where are you?" Da sauri ya sake fitowa ya shiga mota zuciyarsa na zafi, Al-Amin ya kira yana tambayarsa, nan Al-Amin ya tabbatar masa da cewar ta kirashi tana tambaya ko ya ganshi yace a'a daga nan bata sake kiransa ba. Hankalinsa ya kuma tashi zuciyarsa ta shiga cikin tashin hankali yana jin tamkar ya kurma ihu. Da wani irin speed ya shiga Matawalle link, yana zuwa yai parking motar a ƙofar gidan Abubakar Galadanci, yana zuwa ya tura ƙaramar ƙofar ya shiga, mai gadi ya tashi da sauri yana tambayarsa. "Lafiya?" Cikin ƙanƙanta idanuwa Imran yai masa wani kallo zuciyarsa kamar zata tsinko daga ma'ajiyarta yace. "Rahama tazo?" Baki buɗe maigadi ke faɗin. "Ka saketa ne?" Imran yaji zafin kalmar hakan yasa shi shaƙo masa wuya zai kashe shi Hajja ta fito daga sashenta taga ana faɗa. "Subahanalillahi suwaye haka? Meya faru?" Tana magana tana tafiya gurinsa, maganarta kuma tasa mai wankinsu fitowa daga loundry, wajan ya isa da gudu ya fara janye maigadin, Hajja kuma ta fara jan Imran tana salati. Ummi dake cikin ɗaki ta upstairs ta leƙo, hango harda Hajja a wajan yasa ta sakkowa da sauri. Lokacin anyi nasarar raba maigadi da Imran da yake Hajja batasan Imran ba hakan yasa taja hannunsa tana faɗin. "Haba kai kuwa bawan Allah, kaga a haka mai hankali amma kawai ka samu mutum a bakin aiki kana shirin kaishi lahira? Saboda me?" Kafin yai magana Ummy ta ƙaraso cike da mamaki take kallansa kafin tace. "Imran! Meya kawo ka cikin gidan nan ?" Da sauri ya kalli Ummy tare da kawar da idanunsa yace. "Rahama..." da Ummy