Header Ads
Showing 36001 words to 39000 words out of 139785 words

Chapter 13 - Albi Book Complete document by Hajjace.txt

Ads the beginning of article before Image

11 Jun 2024

1001

Ads at the middle of Article

school tana da test karfe 9 komai bata karanta ba tana so ta koma hostel taje tayi karatun a can. Tana bacci Imran yabar gidan ba tare da ta sani ba.......




*LITTATTAFIN Albi NA KUƊI NE, KIBIYA 500 KI KARANTA ABINKI CIKIN KWANCIYAR HANKALI. DAN ALLAH KUYI MANA ADALCI KARKUCI AMANAR KASUWANCI MU.*


#Asmy b Aliyu
#Hajja ce
#imran matawalle
#Rahama Galadanci
#Team Albi
#Haske Writer's Association..
[11/12, 9:34 AM] Asmy B Aliyu😘: *ALBI....*
(My Heart❤️)


NA
*ASMY B ALIYU*
DA
*HAJJA CE*


PAID BOOK..#(500)


*Account Details*
0004157137
*Jaiz Bank*
*Asma'u Buhari Aliyu*
Shaidar biya ta
08086207764


*Katin waya na MTN ta 07043079282 shaidar biya ta 07065283730 view WhatsApp*


17....




Da asuba ta rigashi tashi, dubawa tai gefenta taga baya nan, sakkowa tayi daga kan bed ta ɗauki hijab ɗinta tasa ta nufi parlor. Kwance ta ganshi cikin soofa ya takure yana ta bacci, ta sunkuya saitin fuskarsa tana kare mishi kallo. Hannunta ta kai saman sumarsa tana shafawa, cikin magagi Imran ya ɗan yi juyi yana gyara kwanciyarsa. Murmushi tayi ta miƙe tsaye, komawa tai cikin master bedroom ta shiga toilet ta ɗauro alwala tare da komawa parlorn inda Imran yake. Danshin ruwan hannunta ta shafa masa a face nashi, hakan yasa shi buɗe ido a hankali. Rahama ya gani durƙushe a gabansa tana masa fara'a tace. "Katashi kayo alwala muyi sallar asuba." Kallanta ya dinga yi kafin ya maida idanunsa ya rufe. Karan hancinsa taja da ɗan ƙarfi hakan yasa shi sakin wata ƴar ƙaramar ƙara yana sake kallanta. "Ka tashi muyi sallah nace." Wata ajiyar zuciya ya sauke, bazai iya tuna rabonsa da yin sallar asuba a cikin lokacin ta ba. Sake gyara kwanciyarsa yai yana cewa. "Zanyi anjima." Rahama ta ware idanuwa tana kallansa, cikin turo baki tasa hannu tare da yaye lulluɓar da yai tana cewa. "Allah idan baka tashi ba zanyi tafiya ta yanzu." Besan lokacin da ya miƙe zaune ba, kallanta yai tana ta zumɓurar baki fuskarta a matuƙar haɗe. Lallausan gashin da ya zagaye bakinsa ya shafa tare da miƙewa tsaye ya wuce toilet. Zama tayi tana jiransa har ya fito sanye cikin jallabiya brown color. Tun kafin ya fito already ta shimfiɗa musu praymat ɗaya a gaba daya a baya daga gefen dama. Kallan sallayar yai tare da shafa lallausan sumar kanshi yace. "What do you mean.?" Rahama ta hau kan sallayarta tana gyara hijab ɗin ta tace. "You're a Imam, oya kajamu sallar." Kallanta yai tare da lasar lips nashi na sama, kan praymat ɗin ya hau yana jajjan jallabiyarsa kafin ya fara. Tsab suka idar da sallar suna yin sallama ya miƙe tayi saurin kallansa tare da cewa. "Ina zuwa?" Yana tafiya yana cewa. "Wallahi bacci nakeji." Tashi tayi da sauri ta riƙo masa hannu, kallanta yai cikin ido yaga ta haɗe rai, numfashi ya sauke tare da kamo mata face ta kwace, murya cike da fushi take faɗin. "Daga yin sallama a sallah zaka tashi ba wani addu'a?" Cije lips yai yana sake kamo mata fuska, "Mekike so na ce?" Cike da ɓacin rai Rahama tace. "You don't need anything a gurin Allah? Daman idan kayi sallah baka addu'a?" Cikin gaskiyarsa dan bazai mata karya ba yace. "Kina so na ce me R? God gave me a better life, Daddy na yana da kuɗi, nima alhamdulillahi ina dasu, ya barni da rai da lafiya gashi ya saka min sanki a zuciya ta then me zan roƙa? Tell me my beloved R..." Jin abinda ya faɗa ne yasa ta haɗe rai tare da kwace face nata tana kallansa, cikin takaici tace. "Bakasan wannan butulci kayiwa ubangiji ba? Do you think dan ƴa baka duk wannan abubuwan da ka faɗa baya buƙatar kayi wasu addu'o'in? Hakan ya nuna min cewa baka yiwa Mah addu'a ko? Baka cewa Allah yaji ƙanki Mah yasa aljanna makomarki, Allah yasa annabi yasan da zuwanki, you did say ubangiji ya yafe miki zunubanki, why Imraan why? Baka addu'a Allah ya cire maka shan beer? Baka addu'ar Allah ya baka mata ta gari? Shin kana so kenan kaima idan ka haifi ƴaƴa masu shan beer, masu zuwa club da sauransu? Do you think bansan na aikata laifi ba zuwa wajanka da nakeyi? Kasan mene?" Ta faɗa zuciyarta tana tafasa, kafin ya bata amsa ta ci gaba da magana. "Ina sanka Imran I know, ina san kuma naga ka shiryu ka dena shan beer saboda nasan Itace kawai illa a ɗabi'unka. Kana tunanin Allah zai yaye maka shanta ne ba tare da ka roki ya yaye maka ba?" Wasu hawaye yaga suna zirarowa daga cikin idanunta suna bin kumatunta. Jikinsa yai mugun sanyi ya kamo hannunta tare da sanya yatsa ya goge mata, cikin kirjinsa ya kwantar da kanta wanda yake jin tamkar zai faɗo kasa. "Am sorry my R, am very sorry please. Zan dinga yi Insha Allahu, I know kece musabbabin duk wani ragowar mutunci nawa saboda duk duniya kece mai yi min addu'a, na rasa mahaifiyata a lokacin da nake buƙatarta, amman na sameki a lokacin da na rasata. Nasan tun kafin kikai wannan girman kike min addu'a kin ɗauka ban sani ba? But kici gaba da yi min, Insha Allahu zan dena." Ɗagowa tayi tana kallansa, yaja ɗan siririn hancinta ganin har lokacin fuskarta ba walwala yace. "Oya smile." Sai da ta turo baki sannan ta ɗan sakar masa murmushi, wajan sallayar ta maidashi ya zauna tare da ɗaga hannuwa yana addu'a. Murmushi tayi ta miƙe, kitchen ta shiga tana duba abubuwan dake ciki. Ganin babu wani kayan abinci da za'a iya sarrafawa yasa ta dawo ta tarar yana shafa addu'ar da ya gama. "Good morning." Ta faɗa tana daga wajan kujera. Kafaɗa ya maƙe alamar be amshi gaisuwar ba, Rahama tayi murmushi tare da zuwa kusa dashi, har ƙasa ta duƙa tana matsa yatsunta tace. "Barka da safiya." Wani farin ciki ya ratsa zuciyar Imran, kansa yai wani irin girma, sai yake jin tamkar ta zama matarsa. Kin amsawa yai sai da ya riƙo mata hannu ya dawo da ita kusa dashi yace. "Thank you my dear wife, ya jikinki?" Rahama ta sunkuyar da kai tare da zare hannunsa daga cikin nata tana faɗin. "Da sauki sosai." Jinjina kai yai yace. "Mekike son ci for breakfast?" Tace, "Naje kitchen zan dafa naga ba kayan abinci." Jingina bayansa yai da sidetable yana cewa. "Kinsan da yake gidan gwauro ne that's why ba komai." Dariya tayi mai ɗan sauti tace. "Gashi kuma gwauron dama ɗan hutu ne ba iya cooking yai ba." Imran ya riƙe baki, kallanta yai da wani irin yanayi yace. "Who told you ban iya girki ba? Jiya ma fa ni na dafa black tea nasha." Rahama ta saki dariya, tsayawa kawai yai yana kallanta dan be taɓa ganin tayi dariya irin wannan ba, shi kuma iya gaskiyar sa ya gaya mata. "Oh baki yadda ba ko?" Tana riƙe baki tace. "Ahh nidai bance ba, amman dai kadena cewa ka iya dan dafa tea ba girki bane." Tasowa yai tare da riƙota, dariya take masa yace. "When we get married, I promise to you zan miki special cooking, hhhm sai kin dena cin girkin kowa sai nawa am telling you." Rahama tana ƙoƙarin kwace jikinta tace. "Allah ya kaimu, idan ka manta zan tuna maka." Cije lips yai cikin ransa yana cewa dole ya koyi girka wani abun kafin ta kureshi. Hannunta ya riƙe suka koma master bedroom, riƙeta yai yana sake ƙare mata kallo yace. "Bari na fita na samo abinda zakici, yanzu dai ki kwanta kiyi bacci kafin na dawo." Yana magana ya sake mata hannu, kaya yaje ya saka, dawowa yai ya tarar da ita a gaban mirror tana ganinsa tace. "My phone." Girgiza kai yai yana faɗin. "Ba yanzu zan baki ba." Rahama ta turo baki. "Ni kaɗai zan zauna?" Ya ɗaga kai alamar eh. Fita yai ya ba jimawa sai gashi ya shigo riƙe da laptop, ƙarasawa yai ya kamota ya zaunar da ita a gefen bed, film ɗin da bata ƙarasaba jiya ya kunna mata yace. "Sai na dawo." Ya tashi ya fita tana binsa da kallo.


Kai tsaye wani restaurant yaje ya samar mata abinda zataci, yana fitowa ya shiga wani boutique ya siya mata doguwar da zumar zasu fita da yammah ta karasa siyayyar abunda takeso daga pant har kan bra sabida bai san size nata ba. ya dawo gidan. Sai da ta tashi tasa yaga yadda tayi mata sannan ya buɗe mata takeaway ɗin yace taci bari yaje ya dawo. Gidan su ya koma kai tsaye side ɗin sa ya wuce yai wanka sannan ya sakko, apartment ɗin Matawalle ya shiga, yana ganinsa ya fadada murmushi tare da nuna masa kusa dashi ya zauna. Imran ya zauna yana gaishe shi, sai da Matawalle ya fara bashi breakfast ya yi sannan Imran ya sake kallan mahaifinsa yace. "Daddy." Matawalle ya kallesa da kulawa. "My son ya akai." Imran cikin sanyin murya yace. "Daddy maganar nan ta jiya, please Daddy ka duba lamarin, ina san Rahama har cikin zuciyata, ka y...." Cikin tsawa ya katse shi, shaye da toka yace. "Wannan yana nuna cewar har yanzu ƴar iskar yarinyar nan tana wajanka ko?" Imran yai shiru idanunsa a rintsi jin ana kiran Rahama da ƴar iska. "Ashe bakada hankali Imran? Da alama tun kafin takai wannan shekaru ta daɗe a cikin bariki, banda iskanci yarinya ta gudu daga wajan iyayenta shine kai kuma zaka kwasota a matsayin matarka? Meye aibun Humaidah da kaki karɓar soyayyarta? Bari kaji in gaya maka, indai har nine zan karɓar maka aure wallahi ba zan karɓi na jinin Abubakar Galadanci ba, ga mata nan a cikin duniyar mu, kaje daga nan har birnin sin ka zabo mata ni zanje duk nisan guri na dauro maka aure, amman banda jinin Galadanci wallahi." Zuciyar Imran ta shiga harbawa, wani irin bakin ciki ya shiga taso masa ya kalli Matawalle dake sake tsuke fuska yace masa. "Daddy Rahama fa ba ƴar iska bace, hasalima Rahama bata kula kowane ɗa namiji sai ni, idan ma Rahama lalatacciya ce toh tabbas ni na lalatata." A fusace Senator Matawalle ya kalli Imran yana huci yace. "Idan ka sake yi min maganar yarinyar nan sai ranka yayi mummunar ɓace, na gaya maka ban yadda ka auri yarinyar nan ba ko bayan raina, kai ko ita kaɗai ce ta rage mace a duniya ban amince ka aureta ba kaji na gaya maka." Cikin tsananin fushi Imran ya miƙe idanunsa tamkar zasu zubar da kwalla yace. "Am sorry Daddy but bazan iya rabuwa da Rahama ba, Rahama ce farin cikin Imran Matawalle, itace jin daɗin Imran, itace walwalar Imran sannan itace nutsuwar Imran Matawalle, dan h...." Bai bari ya ƙarasa ba yace dashi. "Karya kakeyi Imran, ilimin da na baka da uwar dukiyar da nake narka maka sune duk abubuwan da ka lissafa. Kana tunanin idan ba kuɗi da lafiya ita yarinyar da kake iƙirarin kana so zata kalleka ne? Ya kamata ka dawo cikin hankalinka kasan abinda kake shirin yi ba maiyiwuwa bane ba." Daddy Matawalle ya ƙarasa maganar yana zabgawa ɗan nasa harara. Zuciyar Imran na wani irin suya yace. "Zan auri Rahama Daddy tunda Allah be haramta mana juna ba. Na riƙoƙe ka Daddy kaki bansan me zanyi ka yadda ka aura min ita ba. Amma wallahi Daddy sai na auri Rahama..." Wani gigitaccen mari Matawalle ya sakarwa Imran a fuska, yana hargagi yake faɗin. "Idan har ka auri jinin Abubakar Galadanci Imran kaje ka nemi wani uban amman ba ni ba, kaje kayi auran ka gani."
Ɓacin rai ya ziyarci zuciyar Imran da jin kalaman Daddynsa, taya zai masa haka? Taya zai katse masa hanzari? Saboda kawai siyasa sai ace bazasu auri juna ba? Shi kam indai akan Rahama ne da ta sadaukar da farin cikinta akan shi, wacce tana mace ta hakura da iyayenta saboda ta rayu dashi, dan me shi da yake namiji zai kasa hakura da komai? Kallan mahaifinsa yai jijiyoyin kansa duk sun miƙe ya kalli mahaifinsa tare da cewa. "Shikenan Daddy, kamar yadda mahaifiyata tabar cikin gidan nan bata dawo ba, nima zan tafi nayi rayuwa tare da Rahama. Daddy ba zaka gane muhimmancin Rahama a gareni ba shi yasa kake amfani da rigimar dake tsakaninka da Abbanta ka hanani auranta. Thanks Daddy for everything you did to me, Jazakallahu khairan." Yana gama magana ya juya zai bar masa parlorn Matawalle ya riƙo masa wuyan riga, hannu ya zura cikin aljihun gaban rigarsa ya zaro car key ɗin Imran tare da ciro ATM card da key ɗin hospital ɗinsa ya tureshi yana cewa."Tunda kace itace farin cikinka kuma jin daɗinka sai kaje ta baka waɗannan abubuwan muga idan zaka fi yadda nasanka, and get out of here kafin nasa a karya min wuyanka stupid boy." Wani irin murmushi Imran ya saki tare da juyawa ya kalli mahaifinsa yace. "Bye Daddy." Murmushin ya bawa Matawalle haushi yaji kamar ya rufe Imran da duka, yana kallon ɗan nasa yasa kai ya fice masa daga cikin parlorn, cikin hargagi yai jifa da duka abubuwan da ya karbe a wajen Imran tare da komawa kan kujera ya dafe kai.
Imran kuwa yana fita be tsaya ba ko side ɗinsa bai kallaba ya fice daga gidan. Wayarsa ya zaro ya kira Al-Amin yace yazo ya ɗauke shi a karshen layin gidan Matawalle. Mamaki ya kama Al-Amin jin a yadda abokin nasa yai magana. Cikin ƴan minutes sai ga Al-Amin yana tsayawa Imran ya faɗa cikin motar tare da cewa. "Kaini club." Al-Amin ya karya kwana, sam be taɓa ganin Imran a cikin irin wannan yanayin ba, har suka ƙarasa club babu wanda yai magana. Five bottles of beer Imran yace a bashi, ya buɗe ɗaya ya kafa kai, kafin kace mene ya zuƙeta, ya sake buɗe ta biyu itama ya shanye, ya janyo ta uku yasha rabi tare da kifa kansa yana jin tamkar ya fasa ihu ko zaiji sassauci a ransa. Al-Amin kallansa kawai yakeyi, shi tunda ya karbi ɗaya ma ya kasa shanyewa saboda mamakin halin da yaga Imran a ciki. Ɗagowa yai ya shanye ya buɗe ta hudun, sai da yai tatil dashi kawai ya bingire a wajan yana sambatu. Al-Amin yai saurin tashi yasa aka taimaka masa suka kaishi mota, back seat suka kwantar dashi sannan Al-Amin ya shiga tare da tada motar, kai tsaye ya wuce dashi gidan da Rahama take, dan already Al-Amin yasan suna tare dan Imran ya sanar dashi komai. Mai gadi na ganin motar Al-Amin ya buɗe masa gate, da wani irin speed ya shiga ya ja wani uban birki, fitowa yai da kyar ya janyo Imran suka nufi cikin gidan. Rahama ya shiga kira da karfi, tana zaune tana ta kallan pictures ɗin Imran dake cikin laptop ɗinsa, jin kira yasa ta sakkowa da sauri ta fito. Hango Imran cikin yanayin maye ya mugun ɗaga mata hankali, da gudu ta sakko daga stairs ta riƙoshi tana kallan Al-Amin hankali tashe take cewa. "What happen to him Al-Amin? Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun waye ya ɓata masa rai daga fitanshi?".......






*LITTATTAFIN Albi NA KUƊI NE, KIBIYA 500 KI KARANTA ABINKI CIKIN KWANCIYAR HANKALI. DAN ALLAH KUYI MANA ADALCI KARKUCI AMANAR KASUWANCI MU.*


#Asmy b Aliyu
#Hajja ce👈
#Imran Matawalle
#Rahama Galadanci
#Senator Matawalle
#Haske Writer's Association
[11/12, 9:34 AM] Asmy B Aliyu😘: *ALBI....*
(My Heart❤️)


NA
*ASMY B ALIYU*
DA
*HAJJA CE*


PAID BOOK..#(500)


*Account Details*
0004157137
*Jaiz Bank*
*Asma'u Buhari Aliyu*
Shaidar biya ta
08086207764


*Katin waya na MTN ta 07043079282 shaidar biya ta 07065283730 view WhatsApp*


19.....




A hargitse ya fito daga cikin apartment ɗinshi ya nufo compound, securities ya kalla yace su fita su kirawo masa Imran, kusan su goma suka fito, Matawalle ya koma ciki yana sake cizon yatsa. Sam bazai iya bari wata ƴar ƙaramar yarinya tayi nasarar rabashi da abin sansa ba. Yana san Imran matuƙa, ya kwace duk wani abu nashi ne dan ya tsorata shi, sai dai duk a banza dan Imran ɗin ya nuna masa tabbas jinin Galadanci tafi duk waɗannan abubuwan da ya mallaka masa na jin daɗin duniya. Ya tura a kirasa ne dan suyi magana ta fahimta dan Matawalle ba zai ji daɗi ba ace Imran ya shiga cikin mawuyacin hali. Dan haka yasan duk inda Imran ya tafi beyi nisan da zai ɓacewa securities ba. Gabaki ɗaya ya rasa abinda yake yi masa daɗi a duniya, barin Imran gabansa ba abu ne da zai sa shi kwanciyar hankali ba. Babu inda securities basu duba ba, tun daga kan link ɗin gidan Matawalle har ƙarshensa babu ko mai kama da Imran, basu san mota ya shiga ba, daba dan ya kira Al-Amin ba tabbas zasu iya cimmasa. Komawa sukai suka sanar da senator Matawalle, shaye da toka yake kallan wanda yazo yana tabbatar masa da cewa basu ga Imran ba. Ya miƙe yana bala'i da masifa yace. "Zancen banza zancen wofi kawai, yanzu yaron ya fita a ƙafa amman zaku ce min baku ganshi ba? Yayi maganar da wani irin sabon tashin hankali cikin muryarsa , Imran iska ne da zaku ce baku ganshi ba? Get out of here kafin na huce akan ku." Ya faɗa yana wani irin daka masu tsawa Mommy ce ta shigo parlorn hannunta riƙe da wani tea cup, ganin yananinsa kaɗai yasa tasan ba lafiya, cikin mamaki tace. "Lafiya Daddy ?" Wani dogon tsaki yaja, cike da masifa yake faɗin. " Na fara mafarkin xan cire Imran matawalle daga cikin jerin Ya'yana idan yaki bin umurnina ." Da mamaki mommy ke faɗin."Kamar ya? Kana nufin kace Imran ba...." Dakatar da ita yai cikin fushi, " Ni yaron nan xai toxarta har ya zabi jinin Galadanci akai na, ni yaron nan zai watsawa ƙasa akan ƴar ƙaramar yarinya? Wai har Imran ya amincewa zuciyarsa cewa ya hakura dani?" Wani irin tsoro ne ya kama Mommy, cikin sauri ta koma tambayarsa. "Ni Alhaji ka sani a cikin duhu, wace yarinyar Imran ya zaɓa akan ka.?" Kamar yana jira ta tambayeshi, cikin fushi yake faɗin. "Wata ƴar tasisiyar yarinya ce, tun kafin wannan shekarun na taɓa ganin tazo gidan nan har cikin ɗakinsa, karshen zancen dai saboda ita Imran ya guje ni, kuma abin haushin ma ƴar gidan maƙiyina, wanda yake jin baƙin ciki da ganin mulkin

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads