Header Ads
Showing 81001 words to 84000 words out of 139785 words

Chapter 28 - Albi Book Complete document by Hajjace.txt

Ads the beginning of article before Image

11 Jun 2024

1020

Ads at the middle of Article

masa kamar zai fito daga jikinsa ya yo ƙasa. Sosai Imran yake kallansa yana kuma nazartar yanayinsa yaga kamar akwai tashin hankali a cikin lamarin Khaleefa Turaki. "Leefa tell me abinda yake damunka, Ammie ta tabbatar cewa kana cikin damuwa. How can I help you?" Khaleefa Turaki ya kuma rintsa ido yana jin tamkar ya fashe da kuka, ya zamana a yanzu dole ya kyale Rahama ya cireta daga cikin zuciyarsa tunda tana matsayin matar aure, sai dai kuma tayaya? Wani irin mugun so yana yiwa yarinyar har yanajin idan bai furta mata ba tabbas zuciyarsa zata iya fashewa har ta kaishi ga rasa rayuwarsa gabaki ɗaya. "Kayi shiru Leefa, meye a xuciyarka dan Allah ?" Khaleefa Turaki ya girgiza kai, idanunsa jawur yake kallan Imran Matawalle daya kafeshi da kyawawan idanunsa, cikin dauriya yace. "Kasha wahala a soyayya kuwa Imran?" Tambayar ta yi matuƙar bawa Imran dariya dan haka dole sai da ya ɗan dara yana sake lasar saman leɓansa. Kallan Khaleefa yai yana cewa. "Har yanzu ina cikinsa Khaleefa, kasan abinda kake so yafi baka wahala." Da sauri Khaleefa yace. "Kana santa tana sanka taya kake shan wahalar soyayya Imran?" Imran ya gyara zama yana sauke numfashi yake faɗin. "Tana da kishi, mugun kishin ne yasa har yanzu muke wahala a cikin soyayyar mu." Khaleefa ya shiga girgiza kai. "Kace wannan yarinyar matarka ce, amman kuma ba ita muka gani jikin pictures na auran kuba duk da matawalle ya tabbatarwa da Ammi aure na biyu ne kayi ." Imran ya ɗan haɗe rai tare da zaro wayarsa yana yi mata wani irin riƙo mai cike da takaici. "Nida Rahama munyi aure muna san juna iyayen mu basa so. Khaleefa saboda kaunar da Rahama keyi min yasa ranar da za'a daura auranta da ɗan uwanta ta gudo wajena, kowa na family nata ya juya mata baya saboda ta zaɓeni." Cikin madaukakin mamaki Khaleefa Turaki yake faɗin. "And?" "Na ɗauketa mukaje Uncle ɗina ya daura mana aure." Wani irin ɓacin rai ne ya bayyana cikin fuskar Khaleefa Turaki, sosai ransa yai mugun ɓaci cikin yarda reaction din Khalifa ya nuna yasa Imran buɗe baki yana kallansa. "So how dare you zaka yi mata kishiya Imran? Kodan ka ganta yarinya shine zakai ta gwara kanta kana abinda kakeso da ita? Banda wulakanci daga yin auranku shine zaka sake yin wani saboda kaine kafi kowa san yin aure zaka jibgowa yarinya shirgegiyar mace a matsayin kishiyarta? Da gaske har a zuciyarka kana son Rahama ko tausayinta kake keyi?." Da wani irin fushi Imran ya miƙe, hannunsa zube cikin aljihun wandonsa yake faɗin. "Kai kasan idan ina son abu ban iya sonsa ba, haka idan ina ƙin abu ma hakan, ina sonta da dukkan zuciyata da duka gangar jikina." Wani irin rawa zuciyar Khalifa keyi ba abunda yake ambato acikin bakinsa sai sunayen Allah. "Shin meye damuwar Khaleefa Turaki? a sanin da nayi maka ban taba ganin ka ɗauki damuwa ka ɗorawa kanka ba." Khalifa ya girgiza kai yana faɗin. "Kawai dai nima am in love ne akan wata yarinya da bata sona." yadda yayi maganar yasa Imran ya buɗe ido yana kallon sa, bai taɓa ganin Khalifa Turaki ya kula wata macce a duniya ba, haka bai taɓa jin yayi maganar macce ba. Da murmushi acikin fuskar Imran ɗin yake faɗin. "A ina take ita? wacece ita da bazata karbi soyayyar ka ba?" Khalifa Turaki ya girgiza kai yana faɗin "Wannan ba irin matan kan titi bane, zan cigaba da jira idan alkhairi ce acikin rayuwata Allah ya bani, idan kuma babu alkhairi na hakura." Khalifa ya faɗa muryarsa na karyewa. "Amman Rahama tayi ƙanƙanta da kayi mata kishiya, duka-duka nawa take a wannan fannin kayi laifi Imran, ina ganin idan ni ne kai na samu wacce ta sadaukar da kanta irin yadda matarka..." Khaleefa Turaki ya cije lips lokacin da ya furta matarka, yana jin tamkar ransa zai ƙare, da kyar ya iya daurewa ya ƙarasa maganar "Tayi wallahi bazan taɓa kallan wata yarinya har na aura ba." Imran Matawalle ya yatsina fuska tare da bubbuga shoulder ɗin Khaleefa yana faɗin. "Idan second marriage ɗinka ya zo a matsayin umarnin Ammie zakayi?" Khaleefa ya sake cije lips yana datse duka teeth nashi da karfi. "Auran Humaidah umarnin Daddy ne babu yadda zanyi, kuma yarinyar kamar mayya haka take, babu yadda banyi ba akan ta hakura dani zan bata komai takeso amma taki, kasan akwai mata jarababbu da idan suka nace maka sai sunga babu ranka suke kyaleka." Dai -dai lokacin Rahama ta fito tana sakkowa daga stairs gabaki ɗaya suka zuba mata ido, bata kallesu ba har sai da ta gama sakkowa sannan ta kalli Imran cikin turo baki da karya wuya tana cewa. "Kazo mu tafi gida." Imran ya sha toka tare da cewa. "Muna magana ne mai muhimmanci da Khaleefa ki jira mu gama." Rahama ta kalli Khaleefa Turaki dake tsaye ya rintsa ido, jin tamkar tana kallansa ne yasa shi buɗe idon ya zuba mata, da sauri ta janye nata jin tamkar kirjinta zai rabe saboda bugawa. Bata yi magana ba sai hawaye da suka shiga zubowa a idanunta, har ta juya zata koma wajan Ammie sai kuma ta dawo ta isa kusa da shi, hannunsa ta kamo tare da kwantar da kanta a jikinsa tana faɗin. "Please Albi." Yadda take furta Albi ɗin ba Imran ba hatta Khaleefa sai da yaji tsigar jikinsa na wani irin tashi. Imran ya riƙe hannunta yadda yaji jikinta na rawa ne kaɗai yasa gane cewar tana cikin matsala, ya kalli Khaleefa yana faɗin. "Zamu tafi yiwa Ammie magana zamu yi sallama da ita." Cike da takaici Khaleefa ya kalli agogon dake manne a parlorn sannan yana numfashi yana faɗin. "I think yanzu Ammie ta shiga wanka sai dai na gaya mata cewar kun tafi." Cikin rashin damuwa Imran ya ɗaga kafaɗa yaja Rahama dake jikinsa a bangaren jikinsa suka fita. Kasa rakasu yai kawai ya koma cikin soofa tare da riƙe kansa yana sakin wani irin numfashi. Shikenan ya rasa Rahama, shikenan Imran ya shiga tsakanin su, yanzu tayaya zai cireta daga cikin zuciyarsa? Da sauri ya miƙe ya fita dan kar ma Ammie ta fito ta ganshi a wannan yanayin besan me zai ce mata ba.
Suna zuwa wajan mota ta wani juya gabaki ɗayanta tare da faɗawa jikinsa ta fashe masa da kuka, sosai hankalinsa ya tashi ya shiga shafa bayanta yana tafiya da su ya buɗe motar suka shiga back seat ya sake janta jikinsa yana faɗin. "Stop crying please Albi. Ki gaya min menene yasa duk kika shiga tashin hankali?" Rahama ta ɗan dago tare da kallansa tana cewa. "Kawai tunda mukazo naji zuciyata taki yin daɗi ina jin wani irin zafi a cikinta kamar zata ƙone." Ta sake shigewa jikinsa tana kuka sosai, Imran ya fara nazari toh mezai sanyata cikin wannan yanayin bayan bata san kowa a gidan ba sai yau? Basarwa yayi kawai tare da janta sosai zuwa jikinsa yana kwantar da ita ya koma driver seat, kuɗi ya zaro ya bawa maigadi suka bar unguwar asokoro. Kai tsaye gida ya wuce da ita, koda maigadi ya buɗe ya shiga da motar yai parking ya fito, da kanshi ya ɗauketa dan har tayi bacci ya nufi ciki da ita. Kan bed ya kwantar da ita still akwai baccin a cikin idanunta, ya zare mata mayafin tare da danƙwalin dake makale akanta, rigar jikinta ya zuge ya cire mata a hankali ta yadda ba zai tada ita ba, sannan ya zare skirt ɗin ya barta daga ita sai Pant da bra yaja duvert ya rufe ta tare da shafa kanta yana sakin smiling. Fitowa yai ya sake fita daga gidan gabaki ɗaya.
******


Mommy ta kalleta tana girgiza kai kamar zata rufe ta da shegen duka , taja numfashi tare da faɗin. "Humaidah shegen taurin kanki ina jin shine zai dinga hadaki da Imran, haba wannan wace irin jarabace? Kince kina sanshi nayi miki ƙoƙari har gashi an daura muku aure kin zama matarshi, haba yanzu ance ki tashi a kaiki gidan ki kina wani cewa ke sai ya dawo? Toh uban waye yasan randa zai dawo? Ina ji a jikina saboda karma ya ga an kai ki yasa shi barin gidan, ki tashi a kaiki idan yaso ya dawo ya tarar dake a cikin ɗakin ki." Cike da fushi Humaidah ta miƙe tsaye tana turo baki take faɗin. "Aunty wallahi ba za'a kaini ba baya gidan, haba sai kace za'a kai masa hatsi? Wallahi da class ɗina bazan yadda naje gidana babu miji a cikinsa ba, kiyiwa Matawalle magana dan a samu a dawo dashi da wuri, Aunty kin tsumani da yawa taya zan tafi gidan da babu mai kwasar gyaran?" Mommy tai jifa da gyalenta tana faɗin. "Sai kiyi ta zama ai har randa Allah zai dawo dashi tunda ke bakida hankali." Humaidah batace komai ba ta fice wajan kawayenta tana tabbatar musu da cewar Imran yace zai zo da kanshi idan ya dawo ya dauketa. Duk suka saki shewa tare da cewa idan ta tare tayi musu magana zasu zo ganin ɗaki. Suka sake tafawa suna dariya kamar basu da wata matsala ta rayuwar duniya. Wanda sukaje dan yin kwana huɗu sai gasu da sati biyu a garin Abuja suka dawo Kano, shima Imran ɗin baiyi niyar dawowa ba sai ta dalilin jarabawar dasu Rahama zasu farayi, dama tayi ta masa ƙorafi cewar wannan semester ɗin dakyar idan ba'a wullota waje ba, Imran ya hanata karatu kamar yadda ya kamata. Sunji daɗin zuwansu Abuja matuƙa dan sun yawata duk inda suke so, sun sake jefawa junansu so da kaunar kansu ta yadda ɗaya bazai iya wata rayuwa ba sai da ɗan uwansa. Humaidah najin dawowarsu ta takurawa Mommy sai da aka kawota gidan Imran a daran, basu sani ba suna sama abinsu suna bawa junansu kulawa. Sai cikin dare Imran ya sakko dan yasha black tea yaga haske a ɗakin Humaidahn, bebi takanta ba ya wuce kitchen. Gabaki ɗaya haushi ya riga ya gama cika mata zuciya, Imran Matawalle ya mugun raina mata wayo, taya za'ai yasan tana cikin gidan amma ya mai da ita tamkar wata mai gadi? Baya wani kallanta a matsayin mace bare ya ganta matsayi na matarsa. Tun jiya da ya zo be kalli hanyar inuwar da take ba bare yai mata magana. Humaidah ta shiga rintsa ido tana sake matse cinyoyinta sakamakon wani irin mugun zugi da takeji gabanta nayi mata. Duk da tasan baya kaunarta yasha gaya mata hakan amma saboda bala'in san shi da takeyi yasa taji ta gani akan sai ta aure shi a haka, gashi ta danƙari uban magungunan mata sun fara addabarta Imran ɗin kuma baya ta kanta. Sakkowa tai daga kan bed daga ita sai kayan bacci wando da riga masu yauki purple color, tai tsaye a bakin ƙofar room ɗinta tana bin stairs ɗin da suke kallo, tasan yana can maƙale da Rahama a jikinsa ko suna bacci ko kuma suna hira. Da gudu ta koma cikin ɗakin tana ihu tare da furta "Why Imran? Why baka sona menayi?" Kamar daga sama taji kamar ana taɓa ƙwanuka, da sauri ta sakko ta nufi inda take jiyo sautin. Rahama ce keta ƙoƙarin jona coffee kettle saboda zata tafi school Ihsan ta jaddada mata cewar ta shigo da wuri karta makara "Rahama ina mijin mu yake ne? Shin besan nazo gidan bane? Ko kece kika hanashi zuwa bare ya sauke hakkinsa a waje na" Zuciyar Rahama tayi wani irin baki jin a yadda Humaidah tayi maganar tamkar zata kwace mata miji, ko kallanta bata yi ba taje ta ciro bread tayi toasting tasa a toaster, ganin haka yasa Humaidah yin murmushi ta juya kai tsaye up stairs tayi Rahama ta leƙo dan ganin ina ta tafi, ganin tayi sama yasa ta koma kitchen ɗin taci gaba da haɗa breakfast ɗin kirjinta yana bugawa da mugun karfi. Knocking Humaidah tayi, bata bari an bata dama ba kawai ta buɗe ƙofar ta shiga, dai-dai lokacin da Imran Matawalle ya cire duvert ɗin jikinsa yana sakkowa daga kan bed. Kallan ƙofar yai kawai yaga Humaidah wacce gabaki ɗaya ta tsaya tana zuba masa idanuwa a duka sassan jikinsa, da wani mugun ɓacin rai yake kallanta yana faɗin. "How dare you zaki shigo min nan?" Humaidah tayi ƙasa da kanta tana matse ƴan yatsun hannunta. "I'm talking to you Humaidah me ya kawoki nan? Get out of this room ko kisha mamakina." Humaidah tabi ƙafafuwansa da wasu lallausun gashi ya cika su tana lumshe ido, da kyar ta iya buɗe baki tace. "Haba Imran nifa matark...." Taku uku yai zuwa gabanta ya shaƙo mata yuwa, dai-dai lokacin da Rahama ta shigo ɗakin tana bin su da kallo. Humaidah dake zaro ido tayi zaton Rahama zataiwa Imran ɗin magana, ga mamakinta sai taga kawai taje ta dire tray ɗin da ta jero musu kayan breakfast tare da shigewa toilet. "Idan kika sake shigowa room ɗin nan ba tare da izinina ba Humaidah Wallahi sai nayi mugun baki mamaki ." Yana gama magana ya hankaɗata ya juya tare da shigewa toilet ɗin da Rahama take ciki suka bar Humaidah a wajan wacce sauran kiris ta kurma ihu, da gudu ta juya ta fice daga ɗakin........




(Complete documents)
*WAMINAL HUB* #500
*ZO GARENI* #300
*NIDA RAHEEMA* #300
*RAYUWAR AURENAH* #300






#Asmy b Aliyu
#Hajja ce
#Imran Matawalle
#Rahama Galadanci
#Khaleefa Turaki
#Humaida
#Haske Writers Association..
[11/29, 6:05 PM] Asmy B Aliyu😘: *ALBI...*
(my heart❤️)


*ASMY B ALIYU*
DA
*HAJJA CE*👈


PAID BOOK..#(500)


*Account Details*
0004157137
*Jaiz Bank*
*Asma'u Buhari Aliyu*
Shaidar biya ta
08086207764


*Katin waya ta MTN.ta 07043079282 shaidar biya ta 07065283730 view WhatsApp*




37.....


Sai kusan ƙarfe bakwai na safe ta buɗe ƙofar ɗakinta, kai tsaye master bedroom ɗin Imran ta nufa tana tura kofar ta buɗe, tsayawa tayi tana kallon ɗakin da alamar shima Imran ɗin ba cikinsa ya kwana ba. Cikin closet ta nufa ta zabi kayan da zata saka, daman ta riga da tayi wanka, sauri kawai take dan duk atunaninta Imran ɗin a parlor ya kwana. Duk da exam ɗin su sai 9 kuma ɗaya ce zasuyi yau gara tabar masa gidan dan ta tsani koda cin karo da fuskarsa ne. Amman ga mamakinta har ta sauka ƙasan ba kowa a parlorn, ɗakunan Humaidah tabi da kallo lokaci ɗaya xuciyarta na wani irin bugawa, kodai a ɗakin Humaidah ya kwana?" Hawaye taji suna cika mata idonta lokaci ɗaya, sai dai ga mamakinta koda ta fita a harabar gidan babu motar Imran ɗin, samun kanta tayi da ƙarasawa wajen maigadi, har zata tambayeshi ko Imran ɗin ba'a gida ya kwana ba? Sai kuma taga rashin dacewar haka, kawai tayi masa sallama ta fice daga cikin gidan. Tafiya kawai take akan titin unguwarsu tana jin wani irin raɗaɗi a ƙasan ranta, tambayar kanta take a ina Imran ɗin ya kwana? idan yayi laifi maimakon ta hukuntashi sai kanta take hukuntawa? Hawayen da bata san ko na menene ba su suka fara sauka akan fuskarta. Ahankali karo na farko acikin rayuwata da ta tsani wannan soyayyar da take yiwa Imran Matawalle, karo na farko da taji ta tsani kanta na ƙin bin maganar iyayenta. Yadda Ihsaan taga ta shigo mata tasan sunyi halin nasu wato faɗa, soyayyarsu na burge mutane amman ba koda yaushe ba saboda rabinta duk faɗa ne a cikinta. "Ki dinga ɗaukar komai da sauki dan Allah Rahama." Ihsaan ta faɗa mata cikin rarrashi duk da bata san meye damuwar Rahama ɗin ba. Har suka shiga exam suka fito Rahama bata cikin walwala, kwanciyarta tayi a hostel. Sai kusan ƙarfe goma ya shigo gidan ko kallon ɗakin Humaidah bai yi ba ya haye sama. Wanka yayi haka yayi shirin fita office ko kallon ƙofar ɗakin Rahama bai yi ba duk da yasan tana school zai bata fili tayi yadda taga dama da rayuwarta. Ta daɗe da bata haɗiye zuciyarta ba sabida kishi, karo na farko acikin rayuwarsa da ya fara dana sanin yin wannan auren dan shi mutunne wanda baya ɗaukar raini ta kowane fanni, ya tabbatar idan ya biyewa halin Rahama har agaban Humaidah rashin kunya zatayi masa, daga nan itama Humaidah zata ɗauka tayi masa. Tabbas yasan yana son Rahama da dukkanin zuciyarsa, amman bazai ɗauki wulakanci da izgilanci ba. Humaidah matar aurensa ce ta sunna Allah ya halarta masa ya taɓa duk inda yaga dama cikin jikinta. Amman Rahama bata tsaya ta saurari me zai faɗa mata ba ta rufe masa ƙofa, ƙofar da yai ta roƙonta dan ta buɗe masa yayi mata bayani amma taki saurarensa, ya tabbata Humaidah na jinsu, tabbas ta gama saka duka girmansa ya zube a idon Humaidan, bai taɓa jin Rahama ta baƙanta ransa ba irin jiya. Wannan shine karo na karshe da zai ƙara binta, jikinta kuma tayi ta kallo tana ado yasan da ya samu abunda zai kawar da tunaninsa zai manta wani jikinta. Daman shi bawai ya damu da mata bane, shigowarta cikin rayuwarsa soyayyar da yake yi mata yasa ya fara jin sha'awar jikinta. A mota yayi waya da Matawalle, jin muryarsa kurum Matawalle yasan babu lafiya. "Imran kana lafiya kuwa?" Matawalle ya faɗa cike da kulawa, "Lafiya na kalau Daddy, idan na fito clinic zan biyota office ɗinka ko mu haɗu a gida." Matawalle ya amsa, fatan Alkhairi yayi masa ya kashe wayarsa. A wani restaurant ya tsaya yayi breakfast sannan ya nufi clinic. Sai da ya shiga cikin office ɗinsa ya kira Al'ameen a waya, suka gaisa yana yi masa shakiyanci. "kaji sabuwar duniya abokina, mata biyu bisa kanka ka manta kowa da komai ko I Matawalle?" Al'ameen ya faɗa cikin shakiyanci, wani irin abu ya tsaya masa a wuya, wani irin dogon tsaki Imran ɗin yaja, "Bari na katse wayana idan ka gama na sake kira." Da sauri yace "Haba meyayi zafi kuma angon Rahama da Humaidah?. Please na tuba faɗamin meye matsalar?" Al'ameen ya faɗa yana ba duk Imran hankalinsa. "Ina son mu haɗu." Al-Amin yace "yaushe kenan?" Imran yace "Idan ka tashi aiki nima na tashi nawa aikin." Numfashi Al-Amin yaja. "Okay a gida ko a club?" Imran yace "A club ɗin dai zaifi." Al-Amin ya

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads