Showing 111001 words to 114000 words out of 139785 words
Chapter 38 - Albi Book Complete document by Hajjace.txt
HUB*#500
*ZO GARENI*#300
*NIDA RAHEEMA*#300
*RAYUWAR AURENA*#300
#Asmy b Aliyu
#Hajja ce
#Imran matawalle
#Rahama galadanci
#team Albi
#Haske Writers Association
[12/12, 10:02 PM] Asmy B Aliyu😘: *ALBI...*
(my heart❤️)
*ASMY B ALIYU*
DA
*HAJJA CE*👈
PAID BOOK..#(500)
*Account Details*
0004157137
*Jaiz Bank*
*Asma'u Buhari Aliyu*
Shaidar biya ta
08086207764
*Katin waya ta MTN.ta 07043079282 shaidar biya ta 07065283730 view WhatsApp*
47.....
Kallansa Abbie yai sosai ganin yadda ya hau kamar wanda aka shaƙe, numfashi ya ja sosai kafin ya sauke yace. "Kasan girman zunubin daka ɗauka Abubakar? Please kayi tunani saboda akwai ciki a jikinta, a cikin addinin mu laifi ne babba a saki mace cikin jini ko kuma da ciki, idan har so kake ya saketa sai dai ka bari har ta haihu ko a ranar ne idan ta rabu da cikin zaka iya yanke duka igigoyin auran idan kana da buƙatar hakan." Da wani irin tashin hankali Abubakar Galadanci yake kallan ɗan uwan nashi, dayake yana cikin fushi be tsaya ya wani yi nazarin maganar Abbie ba yake cewa. "Kana wani cewa saboda ciki sakin da yayi beyiyuba kenan? Toh ni a wajena ya yi, da ina da hali ma sai nasa an ɓarar dashi dan bana buƙatar jinin Matawalle a cikin ahalina." Abbie ya buɗe idon yana kallansa, cike da takaici yake faɗin. Ya kamata kasan cewa idan hankali ya gushe, still hankali ake sawa ya nemo shi. Maganar aure ne da Farooq Allah beso ba shida Rahama, idan kuma batu ne na, siyasa yanzu akwai damar sake yin wata takarar a gaba idan kana so, kai baka ganin rabon dake tsakaninsu? Babban abin daɗin ma da aure suka samu cikin ba wai a banza yaje ya lalata mana yarinya ba. Ka godewa Allah Abubakar domin yana sanka da rahamarsa kar ka bari ya barka da iyawarka kazo kana dana sani." Gabaki ɗaya Abba ya gaji da surutan da Abbie keyi masa waɗanda suke sake ƙona masa zuciya. "Naji amma Rahama ba zata sake komawa wajan yaron nan ba koda kuwa zata mutu babu aure." Abbie ya girgiza kai ya tabbatar Abba bazai gane abinda yake san ya gano ba, dan haka wayarsa dake ta faman ruri ya zaro daga cikin aljihu yana karawa jikin kunnenshi. Can ɓangaren Hajja kitchen ta shiga da kanta dan yiwa Rahama tuwo saboda tasan masu ciki da dama suna masifar san shi, yayin da Rahama ke kwance cikin bedroom ɗin Hajja, kuka takeyi tana faman rufe baki dan kar ya fito fili. Sosai zuciyarta take wani irin bugawa, tayi mamaki matuƙa da har Imran ya iya rubuta mata takardar rabuwa da ita, cikin zubar da hawaye ta shiga nemo sunansa a wayarta amma ta kasa kiranshi tunawa da tai wannan lokacin mahaifinta ne yake son tayi masa biyayya. Ta sauke wayar tana fashewa da wani irin kuka. Cikinta ta shafa wanda ba zaka taɓa ɗauka cewa an fara yi mata wata halitta a cikinsa ba, ta tuna yadda Imran ɗin yai murna yai farin cikin ganin wannan cikin sai gashi basa tare zasu kula dashi. Ummi ta ɗaga can ƙasan takardunta masu muhimmanci ta sanya takardar a wajan tana bin ta da kallo, ba zata taɓa bari Abba ya gani ba, dan idan har yaga cewar saki ɗayane a ciki sai tsanar Imran ɗin tafi ta baya zafi, dan tsab Abba zai ce ya wulakantashi, ita kuma ba zata sake bari taga an ci gaba da yin gabar nan ba tunda har Allah yasa tsakanin Rahama da Imran ɗin akwai haihuwa tsakaninsu ba. Yanzu zata jira taga me Abban yake nufi, za kuma tasa ido sosai akan lafiyar Rahaman da abinda yake cikinta dan har ta fara murnar samun jikoki. Wani irin danna horn yakeyi wanda yasa maigadin nashi ruɗewa, ko gama buɗe masa ba'ai ba ya kutsa motar har madubin gefen passinger yana karyewa, wani wawan wrong parking yai ya fito a fusace ya nufi cikin gidan. Ko Humaidah dake tsaye ƙofar kitchen be kula da ita ba ya haye sama yana jin tamkar zai faɗi. Ganin ya shige yasa ta saurin fitowa taje ta leƙa parking lot tayi zaton ko Rahaman ce ta tsaya dan indai kaga Imran a hargitse to misunderstanding suka samu shida Rahama. Ta ɗan jima a tsaye ko zataganta amma shiru, ta rufe ƙofar a hankali sannan ta shiga cikin ɗakinta tana sakin wani side smiling, babu abinda yake mata daɗi irin taga saɓani ya shiga tsakanin masoyan nan, takan ji wani farin ciki marar misaltuwa a cikin zuciyarta. A haukace yasa hannu duka biyun ya ture duka kayan dake saman mirror duk suka zubo suka tarwatse a cikin ɗakin. Wani gigitaccen ihu ya saki yana kama kansa idanunsa a runtse yana jin kansa yana barazanar cirewa. Wai yau shi akai wa wayau aka kwace masa mahaɗin zuciyarsa, Rahama na ɗauke da cikin jininsa amma an kwace su duka, yau wa zai kaiwa kukanshi a share masa? Wa zai gayawa damuwarsa ko za'a lallasheshi? Bashi da kowa sai Daddy kuma a wannan yanayin ko ganinsa baya san yi. Da sauri ya fito ya shiga ɗayan ɗakin, ma'adanar beer ɗin shi ya nufa jikinsa yana wani irin rawa ya buɗe sai dai me? Wayam babu komai a cikinsa. A haukace yai wani irin zaman daɓaro yana furta. "No...! No..!! this can't be...." Saboda yasan yana da ragowar guda biyu a ciki ya za'ai ace yanzu babu su? bayan babu wanda yasan inda yake ajiyarsu? "Rahama...! Why Albi? Why...?" Ya faɗa kamar zai fashe da kuka dan yasan tabbas itace ta gansu ta kwashe su kuma yana da tabbacin ta zubar. Cike da tashin hankali ya juya ya fito daga cikin ɗakin dama car key ɗin yana can ko cirowa beyi ba daga motar. Yana zuwa tsakiyar parlorn ya hango beer bottle the same wacce yasha kwanaki kuma irin wacce yaga Humaidah tasha. Gigicewa yai yanajin matuƙar san sha, kallan ɗakin Humaidah yai ganin bata fito ba yasa shi saurin ƙarasawa wajan hannunsa yana rawa ya ɗauki bottle ɗin zuciyarsa tamkar zata tsinko ta fito, yana shirin buɗewa kawai yaji dirar motoci a cikin parking lot yai saurin zuwa ya buɗe labulen window, motocin Matawalle yagani da sauri ya tura bottle ɗin ƙarƙashin kujera yana so yai control ɗin kanshi. Da sallama Matawalle ya murɗa handle ɗin ƙofar bayan yace da masu kula dashi sujira a bakin ƙofar. Hango ɗan nashi a tsaye dafe da kai yasa shi yin saurin ƙarasawa wajan shi ya dafa shoulders ɗin shi cike da kulawa yake yi masa magana. "Dama nasan kana nan cikin damuwa my son, zoka zauna muyi magana." Imran yabi Matawalle suka zauna cikin two seater yana riƙe da hannunshi yake kallan fuskarsa, gaba ɗaya Imran ɗin yaki haɗa ido dashi. "Ban san manufar Abubakar kenan ba da wallahi bazan taɓa zuwa gurin shi ba dan befini zuciya ba, sai dai kawai nasan kaddara ce ta kaimu ina so kayi hakuri Imran." Murmushin takaici kawai ya saki yana haɗiyar wani abu mai zafi yake cewa. "Daddy cikin jikinta nake tunani, bana san damuwar da Rahama take ciki yai affecting baby na. Daddy ina san baby daga wajan Rahama ina san ta haifa min baby's kayi min addu'a Daddy ina jin zuciyata na wani irin zafi." Matawalle ya sake damƙe hannunsa cikin nashi yana jin tausayinsa yace. "Kada ka karaya, indai kuna da ragowar zama tsakaninka da Rahama sai kaga Allah ya sake baka dama, yanzu dai ina so ka kwantar da hankalinka sosai karka nemi Rahama saboda naga alamar har yanzu Abubakar Galadanci zuciyarsa bata sakko ba, ka bari nan da zuwa wani ɗan lokaci sai mu sake jarrabawa ko zai baka ita Allah dai yasa ba duka kai sakin ba?" Kansa kawai ya ɗaga alamar eh bece komai ba. "Kayi sallar magariba?" Imran yai shiru shi gabaki ɗaya ma ya manta da sallar, dama idan Rahama na tare da shi ne baya wuce lokacin yin sai idan akasi aka samu. "Idan baka yi ba ka tashi kayi kasamu kaci wani abun ka shirya gobe zaka rakani Abuja." Da wani irin yanayi ya ɗaga kai ya kalli Matawalle alamar ba zai iya zuwa ba, Matawallen ya dafo shoulder ɗinsa yace. "Please rakani zaka yi." Ɗan turo baki yai saboda baya san zuwa nan da can indai ba a cikin Kano bane. Humaidah ce ta fito cike da farin ciki sanye cikin doguwar riga ta wata atamfa orange da ratsin blue black a jiki, gabaki ɗaya suka juya jin takun takalmi. Matawalle ya faɗaɗa murmushinsa yana faɗin. "Ashe kina ciki?" Tayi ƴar dariya tare da faɗin "Ina wanka naji shigowar motoci, sannu da zuwa Daddy ina yini?" Ta shiga gaisheshi da wani irin respect tana faman wasa da yatsun hannunta. Da fara'a Daddy yake cewa. "Kaga ma kawai sai kuyi tafiyar nan kai da Humaidah tunda ita waccen t...." Da sauri Imran ya katse shi ta hanyar faɗin. "Abar maganar nan please Daddy dan Allah." Matawalle yace, "Shikenan to." Kallonsa ya mayar kan Humaidah yana cewa. "Ki samarwa mijinki abinci zai yi sallah sai yaci." Farin ciki ya cika zuciyarta wai itace yau ake cewa ta yiwa Imran girki harma ana kiransa da mijinta, daɗi kamar ya kasheta haka takeji. Cike da kwarkwasa ta miƙe tare da shiga kitchen ɗin ta tsaya tana raba idanuwa. Muryar Daddy taji yana faɗin. "Humaidah ki barshi ma yace Al-Amin zai kawo masa." Tasan kawai ya gayawa Daddy hakan ne dan karta girka, ta ɗan ɗaga kafaɗa dan ba ƙaramin wahala takeji ba ace tayi girki ko itama sawa take ayo mata takeaway ɗin duk abinda take so, sai ko idan Imran ɗin ya kawo mata. Har mota Imran da Humaidah suka raka Daddy ya tafi su kuma suka koma ciki. Ko kallan inda ya ajiye beer ɗin beyi ba, haka kawai yanzu yaji bazai wani sha ba, ya nufi upstairs har ya fara takawa yaji Humaidah na cewa. "Kana buƙatar wani abun ne?" Imran da ya dan dakata yaci gaba da takawa yana faɗin. "No." Bejira ta koma magana ba ya ƙarasa da sauri ya shige ɗaki. Kai tsaye toilet ya shiga ya ɗauro alwala ya fito, kan praymat ya hau ya tada sallah. Yana idarwa ya sake fitowa dan gaba ɗaya ji yai gidan yai masa wani girma, yayin ɗakin yai masa mugun duhu duk babu daɗi yana jin tamkar zaiga gilmawar Rahama a cikin ɗakin. Gidan ya bari ya ɗauki ɗayar motarshi ya fice, ko kafin Humaidah ta fito mai gadi tuni ya rufe gate ɗin. Ƙaramin tsaki ta saki taje ta ɗauke beer ɗinta da ta ajiye yasha tasamu damar biyawa kanta buƙata, dan tana kallan lokacin da ya ɗauka zai sha su Daddy suka zo ya ɓoyeta ƙarƙashin kujera. Rungume beer ɗin tayi tana sauke ajiyar zuciya, a zahirance take faɗin. "Zakiyi amfani kwananan." Ta shige ɗakinta ta boye, tana son sanin inda Rahama take da kuma abinda yasa bata cikin gidan Imran. Yawo ya dinga yi cikin mota yana so ya rage daren kuma baya son zuwa shan beer duk da cewa ana tilastawa zuciyarshi buƙatar shanta. Sai kusan 11:30pm ya dawo gida, yasha mamaki da ya tarar da Humaidah kwance cikin sofa tana chatting, jikinta wata rigace wacce bata ɓoye komai na jikinta ba, yana kallanta ya ɗauke kai yai hanyar upstairs yaji tana masa magana. "Dan Allah ka tsaya ko mu ɗan yi hira ko ta ƴan mintuna ne, dan Allah dan Annabi." Afusace ya juyo ya watsa mata wani kallo a saman fuskarta, ganin yadda ta wani marairaice gashi ta haɗashi da Allah da annabi, ya daure fuska yana cewa. "Ina da aiki ke kuma kin tsaidani da haɗani da, Allah." Cike da haushi ya koma ya zauna cikin soofa fuskarshi babu wani walwala. Rintsa ido kawai yakeyi dan gaba ɗaya bayajin wani sukuni, turaran jikin Humaidah ya uzzara masa banda cije lips babu abinda yake yi, ganin yana nema kasa controlling kanshi yasa shi saurin miƙewa ya nufi sama da gudu. Da ido Humaidah ta bishi itama ta shiga ɗakinta, wasu turarukan ta kuma fesawa ta fito cike da kuduri a zuciyarta. A hankali ta murda ƙofar tana ware idanun ta ina zata ganshi, karar ruwa a toilet yasa ta gane yana ciki, labulen window ta buɗe ta shiga tana jiran fitowarsa. Yana fitowa yaji ƙamshin da farkon shigowarsa beji ba sai na Rahama dashi, yanzu kam ƙamshin irin wanda yaji a parlor ne ya fara waige-waigen ta inda zai ga Humaidah ko yaga abinda ta shigo dashi bai samu ba, gefen bed ya zauna daure kugunsa yake da towel ya zaro wayarsa yana dailing numbern Rahama, sai dai akashe take ya rintsa ido yana jin mugun haushin Abbanta. Kwanciya ya yi yana kallan pop yadda fanka take kaɗawa kawai ya kurawa ido zuciyarshi cike da tunanin Rahama da babyn dake cikinta, kamar ance ya buɗe ido kawai yaga Humaidah tsaye a gabansa da wasu tsinanannun kayan bacci a jikinta, sai yaga fuskarta ta juye masa ta koma ta Rahama sak.! Tana yi masa murmushi. Samun kansa yayi da miqa mata hannunsa alamar tazo, da sauri Humaidah ta miqa masa hannu ya wani fisgota ya mannata acikin jikinsa. Wata irin ajiyar zuciya Humaidah ta shiga saukewa tana ƙara shigewa cikin jikinsa, a hankalin yake shafa fatar bayanta yana shinshinar cikin wuyan ta yana manna mata wasu zafafan kisses. Humaidah kuwa wani irin shafa fuskarsa ta shigayi da sauri da sauri, a hankali Imran ya manne bakinsa da nata ya shiga yi mata wani irin hot kisses. Agigice Humaidah ta kai hannu ƙasansa ta shiga murza ƙasansa dake cikin boxer, sunfi karfin minti goma a haka gaba ɗaya Humaidah ta gama shiga cikin wani kalar yanayi so kawai take Imran Matawalle ya kasance tare da ita, tsayawa yayi cak! yana kallon cikin fuskarta tamkar wanda ake baiwa tsoro yayi saurin dirowa daga kan bed gabansa na mugun faɗuwa jikinsa na wani irin rawa yana nunata da yatsa, sai dai saboda shock ya kasa yin magana. "Ya..ya akayi tazo nan?" Zuciyarsa ke tambayarsa hakan. Agigice Humaidah ta miƙe itama ta shige jikinsa tana kwantar da kanta cikin jikinsa cike da wata irin kissa. fisgota yayi ya nufi ƙofa da ita, cike da wani irin tashin hankali ta shiga roƙonsa ya turata waje gamida riƙe ƙofar yana binta da kallon tsana yake faɗin. "Kwantawa gado ɗaya dake a matsayin matar aure na Humaidah shine mafi munin abu da zan aikata acikin rayuwata, inada kishi, inada kishin da duk ranar da na kwanta gado ɗaya dake na tuna kin gama watsa jikinki kan mazan titi zan iya kasheki idan na dawo hankalina, wallahi Humaida shine kawai yasa bazan iya kusantarki ba, inada kishi zabi ya rage naki da kibar rayuwata ko ki zauna ki cigaba da jiran tsammani.." Ya faɗa yana buga ƙofar cikin fuskarta. A hankali ta sulale ƙasan wajan tana jin hawaye na rolling akan fuskarta, tabbas idan tace maganganun Imran Matawalle basu taɓata ba tayi karya. Meye amfanin bariki? bariki bai yi mata rana ba tunda a yau tayi da nasanin harkar bariki, tayi dana sanin bin mazan titi, gaskiyar Imran ne bata cancanci zama cikin rayuwarsa ba. Ji tayi ta tsani komai da kowa a cikin duniyar nan, musamman ma Mommy wacce a hannunta ta taso, duk ita ta lalata mata rayuwa, amma ga ƴarta nan da ta haifa a cikinta meyasa bata sakata ta shiga harkar bariki ba sai ita? Wata irin tsanar Mommy taji ta lullubeta, yanzu kam tasan babu namiji mai mutunci da zai iya aurenta a haka, Imran shaye-shaye kawai yakeyi, kuma ko hakan ma asiri ne da sam bazai fara sha ba. Baya neman mata sam. Amma kuma Itafa? ga shaye-shayen ga kuma aikata zina. Da gudu ta riƙa sauka a stairs ɗin tana jin maganganun Imran Matawalle na cika mata kunnuwa......
(Complete Decuments)
*WAMINAL HUB*#500
*ZO GARENI*#300
*NIDA RAHEEMA*#300
*RAYUWAR AURENA*#300
#Asmy b Aliyu
#Hajja ce
#Imran Matawalle
#Rahama Galadanci
#Humaida Makarfi
#Team Albi
#Haske Writers Association.....
[12/13, 10:17 AM] Asmy B Aliyu😘: *ALBI...*
(my heart❤️)
*ASMY B ALIYU*
DA
*HAJJA CE*👈
PAID BOOK..#(500)
*Account Details*
0004157137
*Jaiz Bank*
*Asma'u Buhari Aliyu*
Shaidar biya ta
08086207764
*Katin waya ta MTN.ta 07043079282 shaidar biya ta 07065283730 view WhatsApp*
48.....
Washe gari ranar Lahadi Matawalle ya aikawa da Rahama motar hawa da kuɗin zuba mai naira dubu ɗari biyar sai kuma naira miliyan ɗaya na zuwa asibiti dan duba lafiyarta da na abinda ke cikinta. Wani kallo Abba ya rinqa bin ɗan aikin Matawalle dashi. Abban yana huci yake faɗin. "Saboda ni bani da arzikin siyawa ƴata mota, ko dan bani da arzikin kula da lafiyarta shine zai aiko min da kuɗi? Toh ka koma ka faɗa masa bama buƙatar komai daga garesu." Abba yayi maganar sounding so very harsh a cikin muryarsa, dai-dai nan Hajja ta ƙaraso tareda Usman Galadanci da alamar daga part ɗin Hajjan yake shima, sannan yayi shirin komawa Abuja. Da sauri Usman Galadanci ya tari numfashin Abba yana faɗin. "Me kuma ya faru?" Cike da takaici Abba yake nuna masu motar da Matawallen ya aikowa da Rahama da kuma kuɗin na kula da lafiyarta. Baki wangale Hajja ta buɗe tana kallon Abubakar ɗin, ta ƙarasa wajen ɗan aiken ta karbi key ɗin hannunsa da bag ɗin hannunsa wanda kuɗaɗen ne a ciki. Abba ya buɗe baki zaiyi magana Hajja tayi masa wani irin kallo tana faɗin. "Idan kayi magana zakaga fushina Abubakar tunda kai zuciyarka yanzu babu Allah a cikinta sai zalunci da bakin ciki. Kayi nasarar raba auren Rahama yanzu kuma sauran ranta zaka rabata dashi dan tun jiya babu komai acikin yarinyyar nan, banda kuka babu abunda takeyi, da yake itama yarinyyar bakin gadon kafiya tayi yanzu idan na nuna mata motar watakila na samu taci abincin." Hajja ta faɗa afusace ta juya zuwa ɓangarenta riƙe da jakar da kuma car key ɗin. Shima Abbie sallama ya yiwa Abba cike da takaicin abubuwan da ɗan uwan nasa yakeyi, ya kira drivernsa yaja mota suka tafi. Da wani irin yanayi Abba ya juya zuwa entrance ɗin shiga gidan, meyasa Hajja da yayansa suka canja masa lokaci ɗaya kuma duka akan makiyinsa? Aikuwa komai zai faru Rahama ta gama auren Imran Matawalle har abada. Fitowarta kenan daga wanka Hajja ta turo ƙofar ɗakin da take ciki. Hajja ta washe baki tana kallonta tana faɗin. "Ki shirya kizo muje kiga