Showing 39001 words to 42000 words out of 139785 words
Chapter 14 - Albi Book Complete document by Hajjace.txt
da Allah ya bani. Shi yasa nace ya bani duk wani abu da yasan na mallaka masa, yaje Abubakar Galadanci ya bashi koda wanda bekai jin daɗin da na bashi ba." Mommy ta dafe kirji tare da rarraba idanuwa tana. "Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun yanzu ya zanyi da Humaidah? Alhaji kasan irin masifaffan son da Humaidah ke yiwa Imran? Wallahi Humaidah zata iya shiga cikin wani halin idan har ta rasa Imran." Wani huci senator Matawalle ya saki tare da ɗaukar phone nasa ya shiga daddanawa, cikin ƴan sakanni aka ɗaga yace. "Ina so ka baza mutanan ku su binciko min ɗa na Imran, nasan yana cikin Kano, zan turo maka da hotunansa, please kawo min shi kawai zakuyi banda duka ko ɓacin rai." Yana gama magana ya shiga Gallery, hotunan Imran ya tura kusan kala goma sannan ya ajiye wayar a saman center table, Mommy da ranta duk yake a jagule ta miƙa masa cup ɗin ƴa karɓa tace. "Tabbas ya kamata a nemo Imran, ina kyautata zaton akwai abinda zuri'ar Abubakar Galadanci suka yi masa, duk yadda za'a yi ka dawo da Imran gidan nan Abubakar Galadanci yasan cewar ba'a faɗa da gwamnati duk karfin kuɗin mutum." Wani kwarin guiwa yake ji dan haka ya sake sawa ransa dawo da Imran cikin jikinsa.
*********
A wahalarce ta farka saboda har lokacin ba wai baccin ya isheta bane, kawai tana so ta yi karatun text ɗin da zasu yi. Mamaki ne ya kamata ganin lokaci yaja sosai dan har anyi la'asar. Toilet ta shiga tayo alwala, sallah tayi sannan ta sakko down stairs tana nemanshi, ganin alamar baya cikin gidan yasa ta shiga kitchen, takeaway ɗin da suka taho dashi a yawon da sukai ta ɗakko ta koma parlorn ƙasa tanaci. Tana gamawa ta ɗauki wayarta, Ihsan ta kira suka yi magana tace da ita gobe da sassafe zata dawo. Google ta shiga tana ɗan bincika course ɗin da zata halarci text ɗin shi gobe, sai dai gabaki ɗaya ta kasa fahimtar komai saboda tunaninta duk yana kan Imran, ina ya tafi ? Fitowa tai daga browser ɗin ta fara ƙoƙarin kiran wayarsa, bugu biyu kuwa ya ɗaga, kamar yana a gabanta ta shiga turo baki tana faɗin. "Kana ina?" Murmushi yai tare da cewa. "Saloon naje." Yatsina fuska tayi tana cewa. "An gama ko an kusa?" Imran ya lumshe ido, maganar ta kaɗai jefashi take cikin wani yanayi, shi yasa yake san suyi aure idan ba haka ba tabbas shaiɗan yana gab da yi masa kiɗa akan buƙatuwa da ita. "An kusa madam." Kwantar da kanta tayi sosai cikin soofa sannanta tace dashi. " come back soon please." Imran kamar ya shigo cikin wayar ya ganta, yasan tana cikin kewa ya barta ita ɗaya a gida . Sauke wayar tayi daga jikin kunnan tana sanci gaba da duba abinda zata karanta amman duk ta kasa, tunanin iyayenta ya cika mata zuciya, tabbas tasan tayi wauta, amman ba zata iya zama a gida ta auri wani ba zaɓin zuciyarta ba. Bata san tayi auran da zai zamar mata tashin hankali daga farkonsa har karshen sa, tasan idan har ta auri Farooq Galadanci ba zata taɓa yi masa biyayya ba, hasalima tana jin zata iya ɗauke rayuwarsa dan kawai ta fito ta auri Imran Matawalle wanda ya zame mata( ALBI) Idanuwa ta ɗaga sama tare da faɗin. "Allah ka cika mana burin mu, Allah ka tabbatar dani matsayin mata ga Imran Matawalle, ka bamu farin ciki a cikin auran da zamu yi." Wasu hawaye taji sun ziraro mata, bata san dalilin zuwansu ba, sai dai tana jin wani irin raɗaɗin rashin Ummy da Abbanta. Ra'ees ne ya faɗo cikin ranta, da sauri ta lalibo lambarsa ta kirashi, sai da ta kusa yankewa sannan taji ya ɗaga, murya babu daɗi taji yana cewa. "Ya akai?" Mamaki ya kamata jin a yadda ya yi maganar, tace. "Ra'ees baka gane ni bane naji ka amsa a wani iri?" Ga mamakin Rahama sai taji yana cewa. "Na ganeki mana, ba Rahama bace wacce ta gudu daga wajan iyayenta ba? Koba ita bace wacce ta zaɓi saurayi fiye da mutanen da suka kawota a dunia saboda rashin tunani har kikai ga mallaka masa gangar ji...." Cikin tsawa yaji ta katse shi, cike da bala'i ta fara yi masa magana. "Ni sa'arka ce Ra'ees? Wato ka shiga cikin turawa kanka ya fara hayaƙi shine zaka kirani da Rahama gatsal ko? Dan ka samu na kiraka shine zaka tsaya yi min rashin kunya Ra'ees?" Cike da rashin ganin girmanta yace. "Meye abin rashin kunya a cikin abinda na faɗa? Karya nayi? Wallahi kin bani kunya, ace wai kin zaɓi Imran Matawalle akan ɗan uwanki na jini Ya Farooq Galadanci, kin watsawa iyayen mu ƙasa a ido saboda farin cikin ki shine kike so wani yai miki biyayya, to ai ko haihuwa kikayi banajin ƴaƴanki zasu yi m...." Da sauri ta katse jin yadda Ra'ees yake gasa mata magana tamkar ba kaninta ba. Kuka ta fashe da shi tana jujjuya kai a cikin soofa. Tabbas tajawa kanta bakin jini a wajan danginta, gashi ƙaninta, wanda take matukar so ya juya mata baya shima, wai meyasa suka kasa gane manufar zuciyarta? Me yasa idanunsu ya rufe suke shirin hanata samun nutsuwar zuciya? Wani irin kuka ya kwace mata ta shiga rerawa a hankali.
Tun daga entrance ɗin parlorn yake jin sautin kukanta, zuciyarsa ce tai wani irin tsinkewa saboda a duniya babu abinda ya tsana irin yaji kukan Rahama, ya ƙarasa wajan da take taji an dafo ta daga baya, ƙin ɗagowa tayi saboda ta riga tagane ko waye ta hanyar shaƙar daddaɗan ƙamshin turaren jikinsa. Gabaki ɗaya ya ɗagota ya ɗorata saman ƙafafunsa, idanunta a lumshe hawaye naci gaba da zirarowa, juyo da ita yai tare da kwantar da kanta saman ƙirjinsa yana jin yadda take shassheƙa, murya so cool yace. "What happened to you.?" Batace komai ba sai sake shigewa da tayi cikin jikinsa tana kuma fashewa da wani kukan, hannu yasa ya janyo wayarta, wajan call ya shiga ya duba last da tayi waya, sunan Ra'ees ya gani, kuma itace ta kira. "Me ya faru da Ra'ees my R?" Cikin kuka take faɗin. "Gida zan koma Imran." Tayi maganar tana sake fashewa da wani kukan. Cikin gigicewa ya ɗagota yana mata wani irin kallo yace. "Why?" Kallansa tayi da idanunta da suka rine da kalar kuka tana cewa. "Kowa ya tsaneni Imran, family na suna yi min kallan ƴar iska kowa baya sona yanzu." Ta ƙarasa maganar tana kuma sakin kuka. Sosai ya riƙe ta a jikinsa, cewar zata koma gida kuwa ba ƙaramin tayar masa da hankali yai ba, amma kuma yana san farin cikinta dan haka yace da ita. "Idan kika koma gida hankalinki zai kwanta?" Girgiza masa kai tayi tana faɗin. "Bazan samu nutsuwa ba Imran, kasancewa tare da kai shike ke sani farin ciki da jin daɗi. Gida da nake san komawa zan koma ne kawai dan su dena yi min wannan kallan." Jinjina kai yai tare da cewa. "Shirya na kai ki gidan, indai hakan shine zai sa kidena zubar min da hawayenki." Rahama ta sauka daga jikinsa ya rinƙa kallanta, juyawa tayi ta hau stairs ba jimawa sai gata ta dawo sanye cikin hijab, yanzu kam mamaki abin yake bashi, da gaske tafiya zatayi ta barshi? Kodai ta dena sanshi ne? Yayi saurin kaɗa kai tare da miƙewa ya ɗauki car key ɗinsa. "Muje ko?" Ya faɗa yana yin gaba. A baya ta bishi tana kallansa, sosai taga gyaran kan yayi masa kyau, inda zata zauna yaje ya buɗe mata kofar, Rahama ta tafi a hankali tana kallansa, gabaki ɗaya fuskarshi babu wani walwala, har zata shiga sai taji sam bazata iya ba kawai ta faɗa cikin jikinsa tana sake fashewa da kuka. "I can't leave without you Imran, I can't..." Ta maimaita cikin zubar hawaye. Wata irin ajiyar zuciya ya sauke tare da yi mata wata irin runguma wacce take tabbatar da cewa nutsuwa zuciyarsa ke samu. Da sauri ya ɗauketa suka koma ciki yana sake matse ta cikin jikinsa.
Cikin soofa ya zaunar dasu tare da rikota yana sauke numfashi yace. "Kin ɗaga min hankali R, kiris ya rage zuciyata ta buga." Zare jikinta ta shiga yi tare da zama agefensa tana turo baki tace. "Ina sanka Imran, sannan ina so na kasance tare da iyayena, sai dai hakan ya gagara, iyayen mu sunki bamu damar yin aure cikin kwanciyar hankali saboda gabar da sukeyi, meye tunaninka Imran?" Kwantar da jikinsa yayi sosai cikin soofa ɗin tare da janyo ta yana faɗin. "Zamu yi aure su Daddy suna so ko basa so zamu auri juna, ina so gobe idan na saukeki a school zan biya ta gidan uncle ɗina nayi masa bayani, idan shima yaki kawai solution ɗaya ne muje wajan wani Imam ɗin ya daura mana aure ko kuma muje court ayi mana acan, bazan iya jure ganin mu tare guri ɗaya babu aure ba, ina san ki zama halal ɗina koda wani abu zai shiga tsakanin mu, yanzu dai ki kwantar da hankalinki, karki kuma kiran wanda kika san zai ɓata miki rai kinji ko?" Rahama ta ɗaga kai sannan tace. "Ina da text gobe kuma na kasa yin karatun, gashi komai na baroshi a school." Kallanta yai yana cije lips yace. "Tashi muje kiga wani abu." Ta tashi still yana riƙe da hannunta suka nufi upstairs, wani door ya buɗe suka shiga, light ya kunna haske ya bayyana, Rahama ta shiga ware ido tana "Wowwww." Ɗan ƙaramin lab ne da ya kunshi abubuwa da yawa a cikinsa, seat ya nuna mata ta zauna ya tambayeta akan wane course zata yi text ɗin? Gaya masa tayi nan ya ɗakko joter da biro ya shiga tsarge mata course ɗin gaba ɗaya. Sosai ya shiga yi mata bayani, Rahama tana kwashewa cikin brain nata, ba ƙaramin fahimta tayi ba saboda yi mata yake tamkar a cikin class tare da student. Shima tayi masifar burgeshi ta yadda take bashi amsa, sai dai baya appreciating duk amsar da ta bashi sai yayi challenge ya kuma buɗe mata yadda abun yake. Sai da aka kira magrib sannan ya kalleta yana dafe goshi yace. "Am tired my R." Rahama cikin turo baki tace. "Nima haka fa." Ware ido yai yana faɗin, "Massage nake so." Ta ɗauke kai tare da cewa. "Gashi kuma kai gauro ne babu meyi maka." Wajanta ya isa tare da riko mata hannu yace. "Nan da kwanaki biyar na zama mijinki Ki shirya yadda zaki tarbeni dan ni ɗin nan fa da kike gani kallonsa takeyi da dukkan idanunta sai ya kasa karasawa juya ido tayi ya dauke kansa da sauri. Hannunta ya riqe suka koma master bedroom ta shiga bathroom tayo alwala shima yayi sukai jam'i, suna idarwa yace da ita zaije ya dawo wajan Al-Amin zaije. Suka fito tare ta zauna a parlor ya kunna laptop ɗin sa ya bar mata da yake solar ce a gidan ko'ina akwai haske basu da matsalar nepa. Fita yai ya barta, mota ya shiga ya nufi gidan small Aunty ɗinsa wace ƙanwace a wajan Senator Matawalle. Aunty Aziza na ganin Imran ta faɗaɗa murmushinta tana nuna masa wajan zama. Yarinyarta ta kwalawa kira mai suna Ilham , sanye da riga da wando jeans ta fito sam bataga Imran ba saboda wayar da take dannawa. "Kije ki hadowa yayanki kayan motsa baki." Jin ance Yayanta yasa ta saurin kallan parlon, ganin Imran yasa ta buga tsale tare da rugawa ta rungumeshi. Ɗan janyeta yai daga jikinsa ta shiga cewa. "Kai Yaya Imran idon ka kenan? Yaushe rabon da naganka? Ko zuwa mukai gidan Daddy Matawalle bama ganinka." Ya tsine fuska yai yana faɗin. " bana zama ne shiyasa bakya ganina." Zata koma yin magana Aunty Aziza tace. "Zaki tashi ki ɗakko masa ko sai kin gama cika shi da magana." Ilham ta miƙe da sauri, yau Yaya Imran ne a gidan su? Guy ɗin da Mamah take san ta aura mata. Shi kam Imran kallan Aunty Aziza yai yace. "Aunty aure zanyi." Gabanta taji yai wani mugun bugawa, tayi saurin kallansa tare da cewa. "Aure Imran? Ka samu wace zaka aure ne ko kuwa?" Imran ya shafa kwantaccen gashin haɓarsa tare da sunkuyar da kai yace. "Ina da wacce nake so Aunty, she is my life, my world, my happiness. Aunty Rahama is my everything I mean everything." Gani yai ta canza fuska dai-dai lokacin kuma ilham ta kawo masa juice da snacks ta ajiye akan sidetable, zata zauna Aunty Aziza tace ta basu waje. Cikin wani yanayi tace dashi. "Wacece wannan mai sa'ar Imran? A ina take?" Babu wani fargaba yace. "Rahama Abubakar Galadanci." Da wani irin shock Aunty Aziza tace. "Abubakar Galadanci wanne? Kar dai kace min wanda na sani?" Imran ya ɗan kalleta kaɗan ya maida kansa gefe yana faɗin. "Shine Aunty and na sanarwa Daddy sai dai ya nuna ɓacin ransa, ita ma kuma iyayenta sunki yadda yanzu haka tana waje na, ya karbe duk wani abu da yasan ya bani yace shi ba mahaifina bane indai na auri ƴar gidan makiyinsa. Aunty aure na da Rahama ba haramun bane, dan haka zan auri rahama." Tasha toka tare da girgiza kai tana cewa. "Ina nan ina ta mafarki ina ta jan daɗi zan baka auran ilham , haba Imran ya zaka bamu kunya? Me zakai da jinin Galadanci? Kuma har Matawalle ya nuna maka baya ra'ayin yarinyar amman ka dage cewar kai dole sai ita? Me yasa ba zaka duba a cikin family ka zabi wata ba? Bari kaji in gaya maka, ko ka auri Rahama take kowa, auranku ba zai yi albarka ba tunda iyayenku basu buƙata. Banda ma iskanci yarinyar da ta baro gaban iyayenta ita kake burin ka aura? Toh bari kaji na gaya maka, ko nan gaba sai ta zama ƴar iska tunda dama ballagaza ce... " Wata razananniyar tsawa Imran ya sake wa Aunty Aziza, cikin fushi da ɓacin rai ya miƙe tsaye yana cewa. "Banzo na gaya miki dan ki ciwa matata mutunci ba, idan kema bazaki sa albarka ba kiyi shiru Aunty ." Yana gama magana ya bar mata gidan zuciyarsa na zafi. Wai me yasa aka kasa gane muradin zuciyarsu? Me yasa saboda wata banzar gaba ake son haramta masa Rahama? Motarsa yaja ya wuce guest house ya ɗakko wasu bottles na beer yasa a mota. Kai tsaye gidan da ya ajiye Rahama ya nufa, maigadi ya buɗe ya shiga. Ya daɗe zaune a cikin mota zuciyarsa na raɗaɗi, baya san yasha beer ɗin saboda Rahama ɓata so, sai dai babu yadda zai yi, idan besha ba ji zai yi tamkar ya mutu. Sai da ya shanye su tas sannan ya buɗe ya fito yana layi. Rahama kuwa tana kitchen ta kunna electric cooker ta ɗora kettle tana dafa black tea ta ƙone a hannu, cikin jin zafi ta fito daga kitchen ɗin. Ruɗanin da take ciki ne yasa ta kasa fahimtar cewar baya cikin hayyacinsa gabaki ɗaya, da gudu ta nufi inda yake tana jin zuciyarta kamar zata faɗo tasan akan alaƙarsu ne aka ɓato masa rai shi kuma yasha giya. Girgiza shi kawai takeyi tana hawaye bakinta sai rawa yake tana cewa. "Kadawo cikin hayyacinka Imran, ka tashi muje inda zamu samarwa kanmu farin ciki da jin daɗi. Please Imran ka tashi kafin suzo su cimmana su hana mu jin daɗi saboda wata manufa tasu ta daban." Hannusa ya miƙa tare da janyo wuyan rigarta, hakan yasa nonowanta suka bayyana, yai saurin kallan inda suke yana kokarin kai bakinsa gurin tai saurin turashi. A haukace ta shiga jan ƙafarsa tana girgiza kai tace. "Allah ya tsinewa giya! koda yake dama can tsinanniya ce." Ta ƙarasa tana zubar da hawaye. "Kidena min kuka bana jin daɗin duniyar nan Habibty..." Yai maganar yana kokarin kamota tai saurin faɗawa jikinsa tana kuka mai taɓa zuciya........
*LITTATTAFIN Albi NA KUƊI NE, KIBIYA 500 KI KARANTA ABINKI CIKIN KWANCIYAR HANKALI. DAN ALLAH KUYI MANA ADALCI KARKUCI AMANAR KASUWANCI MU.*
#Asmy b Aliyu
#Hajja ce
#Imran matawalle
#Rahama Galadanci
#Team Albi
#Haske Writer's Association..
[11/12, 9:34 AM] Asmy B Aliyu😘: *ALBI....*
(My Heart❤️)
NA
*ASMY B ALIYU*
DA
*HAJJA CE*
PAID BOOK..#(500)
*Account Details*
0004157137
*Jaiz Bank*
*Asma'u Buhari Aliyu*
Shaidar biya ta
08086207764
*Katin waya na MTN.ta 07043079282 shaidar biya ta 07065283730 view WhatsApp*
20....
Wani irin amai yake yi a gurin, gaba ɗaya Rahama ta gigice duka ya ɓata matakayan jikinta. Da kanta ta riqa goge mai aman har ta gama da jikinsa tareda cire masa rigar jikinsa duka, dogon wandonsa ta riqaja har zuwa ƙasa. Sai da ta tabbatar ta cire kayan jikinsa ta goge wurin tas sannan wani irin wahalallen barci ya ɗaukesa anan akan rug. Wanka ta sake yi falo ta koma ta kurawa waje ɗaya ido, gaba ɗaya ji tayi duniyar na juya mata dama ta riga da tayi sallar isha'i, duk wata yunwar da takeji yanzu ji tayi ta fita dan ko ruwan zafin da ta ɗora masu tasan yanzu ya daɗe da yin sanyi. Cikin doguwar soofa tayi kwanciyarta gamida haɗe jikinta wuri ɗaya tana jin hawaye na cika mata idonta lokaci ɗaya. Tuno kwana biyu kawai da tayi da Imran acikin gidan nan yadda yake shigowa a buge yana mugun ɗaga hankalinta, idan sunyi aurema haka zai riqayi? ta tabbatar shan giya a jinin Imran Matawalle yake zai yi wuya ya daina lokaci ɗaya, a da yana shakkar ta gansa a buge yanxu babu wannan shakkar. Karfe huɗu na asuba ya farka jin kansa yai ya yi masa wani irin mugun nauyi yasa ya dafe kan, bin parlorn yayi da kallo haka yaga babu kaya a jikinsa, hannu yasa cikin sumar kansa gamida runtse ido yana jin xuciyarsa na wani irin harbawa. Kallon rug ɗin yayi yaga wayam, gabansa ya shiga faduwa ina Rahama take?"yayi maganar can kasan makoshi, daƙyar ya miqe tsaye dafe da kansa wanda yake jin tamkar ba nasa ba, yana dafa bango zai hau stairs, hangota yayi cikin soofa ta dunkule waje