Header Ads
Showing 6001 words to 9000 words out of 139785 words

Chapter 3 - Albi Book Complete document by Hajjace.txt

Ads the beginning of article before Image

11 Jun 2024

982

Ads at the middle of Article

ta dauki wayarta ta shige dakinta ta kira Imran. Tana kiransa kuwa ya katse ya kirata sabida yasan itace lambar Hajja saboda tana kansa, kukan shagwaɓa ta sakar masa ya lumshe idonsa. Rahama bazata barsa ya huta ba, duka yau rigimarta da ya karba ta saukar masa da wani irin ciwon kai.
Yana kwance akan gadon Al'ameen daman yaga kiranta, murya a raunane yaji tana cewa "Ka faɗa min ya zanyi Hajja zata tafi dani can Abuja wai nayi hutu." Imran yasa hannunsa cikin sumar kansa yana hargitsata yake faɗin "Toh meye laifin Hajja? Ke kenan kullum kina cikin gida bakya son zuwa ko'ina?" Tajuya ido gamida turo baki tana faɗin "Hakama zakace kenan? baka ma damu ba dama nice na damu da kai, nasani zanbi Hajja na barka ka zauna da matar da Mommy zata aura maka kwanan nan." Ta ƙarasa maganar cike da kishi a muryarta. Murmushi Imran yayi wanda tana jin sautin murmushin nasa ta cikin wayar. "Haba Rahama mai kuma ya kawo wannan maganar? Ni na faɗa maki Ina sonta ne? Bari kiji na gaya miki, ni matar da zan aura, ina son tayi karatu sosai, sai ta zama likita ta mallaki hankalin kanta sai muyi aure. Kinga kuwa nida aure ba dai yanzu ba." Hawaye ne lokaci ɗaya suka cika idonta tana faɗin. "Dama kanada matar da zaka aura ban sani ba? Kuma ma wacce kake da burin ta zama likita shine baka taɓa faɗa min ba.?" Tayi maganar muryarta na rawa. A hankali Imran ya lumshe yana jin dole nema ya tsayar da tunanin Rahama a yau ko zai samu ta mayar da hankalinta wajan karatunta, yau dai zai danne duk wani abunda yakeji akanta dan ganin ya saita mata tunaninta. Cikin kawar da kai yace. "Yes of course, Ina fatan ma ku haɗu da ita wata rana, dan duk sanda mukayi waya sai tace tana gaisheki dan tana da kirki sosai, haka kuma tana karatu sosai, kema ina son ki dage da neman ilimi Rahama ko dan mijinki yayi alfahari da iliminki wata rana." Hawaye kawai ke zuba a fuskarta yana ji ajikinsa kuka takeyi yace. "Kema ina da burin kiyi karatu Rahama, haka bazan baki damar kula samari a yanzu ba ko bayan shigar ki jami'a. Ki saka karatu aranki Rahama har ya zamar miki is a (Albi..) ɗinki, nasan wata rana zanyi alfahari da karatunki. Mijin aurenki kuma yana nan tafe Rahama Abubakar Galadanci, ina ji a jikina cewa mijinki babban goro ne wanda babu kamarsa, zai tsaya maki acikin rayuwarki har ƙarshen numfashinsa. Rahama duk wanda ya nufeki da soyayya karya yake yi maki, kuma yaudarar kansa yakeyi, dan ko mahaifinki bai isa ya baki miji ba. Ni zan samo maki mahaɗin rayuwarki wanda nake fatan ya zama (Albi ) ɗinki. Ina sonki Rahama Abubakar Galadanci, ina jinki tamkar ciki ɗaya muka fito dake. So daga yanzu ki fara shirin bin Hajja Abuja da kun samu hutu, zamu riƙa waya dake a wayar Hajjan, idanma na samu lokaci zan kawo maki ziyara mu zagaye garin Abuja muna yawo haka yayi maki?" Ta share hawayen idonta tana jin wani irin soyayyar san zama likita yana shigarta lokaci ɗaya, haka kuma ya tuna mata da cewa itama fa macece tamkar sauran mata, bai kamata ta zauna tana zubar da ajinta akan soyayyar Imran Matawalle ba, wanda bai ma san tanayi ba.
Zata cika masa burinsa na zama babbar likita, haka kuma bata fitar da ran zata samu soyayyar Imran Matawalle ba watan wata rana. Daga yau, daga yanzun nan bazata ƙara roƙon soyayyar Imran Matawalle ba, zata soshi kawai da dukkan zuciyarta bazata ƙara furtawa ba.......
















#Asmy B Aliyu
Da
#Hajja ce 👈
[11/12, 9:32 AM] Asmy B Aliyu😘: *ALBI....*
(My Heart❤️)


NA
*ASMY B ALIYU*
DA
*HAJJA CE*👈


PAID BOOK..#(500)


*Account Details*
0004157137
*Jaiz Bank*
*Asma'u Buhari Aliyu*
Shaidar biya ta
08086207764


*Katin waya ta MTN.ta 07043079282 shaidar biya ta 07065283730 view WhatsApp*




*Free page 8*




Imran Matawalle jin Rahama tayi shiru batace masa komai ba yasa shi wani irin juyi akan gadon yana jin alamar yayi nasara, ya tabbatar kalamansa sunyi tasiri cikin ran mutuniyar tashi. Ya riga da ya gama tabbatarwa da zuciyarsa babu wanda zai rabashi da Rahama Abubakar Galadanci duk wuya duk rintsi. Maganar Humaida Kuwa ko ajikinsa, babu mai yi masa auran dole tunda dai shi ba yaro bane, ba kuma mace bane shi. Rahama itama dai taji bata fargabar Humaida, taji zuciyarta ta ƙeƙeshe da rashin tsoran duk wacce Imran zai aura, zata iya karawa da koma wacece tayi gigin shiga tsakanita da Imran Matawalle, karatu kuma tasa a ranta daga nan har birnin sin zataje tayi shi dan kawai tacika burin Imran. Sosai ta maida hankali wajen zana jarabawarta, takan daure wajan ganin ta hakura da ganin Imran Matawalle a tsawon rana, dan tayi alƙawarin cika masa burinsa. Ummy da Hajja sunga canji sosai a cikin rayuwar Rahama, har idan Farooq ya kira Hajja yace ta haɗasu suna ganin tana hira dashi cikin walwala da nishaɗi. Sai hakan yasa Farooq Galadanci ya ɗauka cewa Rahama ta fara kulasa , yadda Rahama ta dinga nuna masa cewa tana so tazo Abuja za kuma ta biyo Hajja, Farooq ya sake tabbatarwa da zuciyarshi Rahama tazo hannunsa ba tare da yasha wahalar da yake zato ba. Kwanansu biyu da kammala jarabawa Hajja ta shirya musu tafiya Abuja a washegari. Ummy ta shiryawa Rahama kayanta tsab, ita kuma tana can part ɗin Hajja, waya suke da Imran tana so suyi sallama dashi face to face, yace mata besan yadda za'a yi su haɗu ba dan shi ɓangarensa bashi da matsala ko yanzu zai iya fitowa itace su Ummy ba zasu bari tazo inda yake ba.
Rahama ta tashi daga kan gadon Hajja bayan ta ajiye wayar, ta nufi part ɗin Ummy. Ummy na ganin Rahama ta faɗaɗa murmushinta "Rahama gashi nan duk na haɗa miki abinda zaki buƙata." Cikin murna Rahama tace. "Nagode Ummy na, Ummy zanje gidan su Maryam muyi sallama." Ummy bata kawo komai cikin zuciyarta ba saboda tasan Maryam ƙawar Rahama ce kuma basu da nisa gidan su yana ƙarshen layin. "Kice ina gaida Ummanta, kar kuma ki daɗe Rahama bana san kiyi dare a can." Cike da murna ta ruga ta haye stairs, hijab ta ɗakko ta fito tana cewa Ummy. "Sai na dawo." Ummy tace. "Ayi tafiya a nutsu Rahama banda shirme akan hanya." Bata ce komai ba ta fice daga part ɗin, sashen Hajja ta nufa ta ɗauke wayarta tana shirin barin gate ɗin gidan ta kira Imran. "Kazo gidan su Maryam Sardauna gashi nan zan tafi can nima." Imran Matawalle yaja dogon hancinsa tare da lasar tattausan lips nashi yana faɗin. "Okay ganinan zuwa." Tana shiga ta gaishe da Umman su Maryam ɗin tana cewa. "Umma ina Maryam ɗin take?" Umma tace. "Aikuwa Maryam sunje suna gidan matar kawunsu." Rahma ta miƙe dama ta shigo ne dan kar a tambaya Umma tace bataje ba. Ƙofar gidan ta zauna tana jiran zuwan Imran.
A motar Al-Amin yazo Rahama ta isa wajanshi ta buɗe front seat, sai da ta zauna sannan ta juya tana kallansa. Riga da wando ne na shadda blue black ya saka hula wacce ta dace da kayan jikinsa, haka kuma ta fito da yalwatacciyar sumar kanshi ta gefe da gefen hular, yayi matuƙar kyau daga ganinsa kasan guy ɗin abin kallo ne. Ga wani sassanya ƙamshi yana tashi, wanda ya zamana turaran jikinsa ne da kuma na motar suka haɗu suka bada wani kalar daɗi. Rahama ta kawar da kai jin wani masifaffan son shi yana ƙaruwa, kishi ya mamaye zuciyarta tana jin kamar ta fasa tafiya tace dashi. "Ina zakaje idan mun rabu yanzu?" Imran Matawalle ya shafi gashin daya zagaye masa baki. "Babu inda zani by now, but nan da ƙarfe takwas na dare zamuje wata dinner ni da Al-Amin." Rahama tai saurin kallansa suka haɗa ido Imran ya ɗauke kai dan yaga zallar fitina a cikin idanunta, yanzu sai tace karyaje tana gudun ƴan mata suce suna sonsa dama kuma sun saba . Ai kuwa yaji tace. "A'a karkaje kawai kai musu addu'a." Murmushi yai yace mata, "Toh." Tace "Gobe zamu tafi." Imran ya juya yana karemata kallo yace. "Allah ya dawo min dake lafiya R Galadanci." Rahama ta juya idanuwa wanda ya zame mata jiki tace. "Amin bari na tafi kar Ummy tace na daɗe kasan har yanzu basu dena dukana ba." Ta ƙarasa maganar cikin turo baki. Imran ya zura hannunsa cikin aljihu ya ciro wani ɗan ƙaramin zobe, hannunta ya kamo yasa mata jikin ƙaramin yatsanta, farin ciki yasa Rahama rungume shi, Imran ya rintse ido sakamakon wani shock da yaji a jikinsa. Duk lokacin da suka haɗa jiki da ita sai ya tsinci kansa cikin wani yanayi wanda ya lura ko zai rungumi matan duniya ba zaiji abinda yake ji akan yarinyar nan ba. "Thank you, sai mun dawo." Ta faɗa tana buɗe murfin motar, cikin sauri Imran ya riƙo mata hannu, juyowa tai suka haɗa ido, ganin yanayin idanunsa ya canza yasa Rahma cewa.
"Menene ya sameka?" Sakar mata hannun yai yana girgiza kai ta fita da sauri saboda kar Ummy tai mata faɗa. Yabita da kallo har sai da ya dena ganinta sannan yaja numfashi da kyar yaja motar yabar unguwar. Da farin ciki ta shiga gidan, a ranar Rahama tayi bacci mai daɗi ganin zoben hannunta kaɗai yana sa taji tamkar Imran ɗin ne tare da ita. Washegari kuwa suka ɗauki hanyar Abuja babban birnin Najeriya.


3 year's left.....


Ado Bayero University Kano.


Yanayin yadda take tafiya kaɗai zai tabbatar maka da cewa agajiye take, tafiya kawai take tana yatsina fuska, Jefi-jefi takan kalli sararin samaniya daya fara haɗewa da wani irin bakin hadari mai haɗe da iska a cikinsa. Fara ce sol ƴar siririya doguwa wacce tsayin yai mata kyau domin bai yi yawa ba, sanye take cikin riga da skirt na lace baki da aka yiwa ado da yellow ɗin zare, tayi kyau sosai tana tafiya cike da nutsuwa. So take kawai ta ƙarasa hostel ta samu ko ruwa ne ta watsa a jikinta saboda hadarin yasa garin yayi zafi sosai. Daga bayanta taji muryarsa yana kiranta, tai masa banza ga zuciyarta dake mata wani irin suya, ta tsani koda jin muryarsa ne bare taganshi a cikin idanunta. Suraaj kenan ɗan ajinsu da yake ƙoƙarin shiga cikin rayuwarta da nufin soyayya. Jin ya sake kiranta yasa ta juya rai a mugun ɓace, kallan juna suka shiga yi ya miƙa mata ledar hannunsa mai ɗauke da juice da snacks yace.
"Naga baki tsaya kin sai wani abu, shine na siyo miki." Rahama tabi ledar da harara kafin ta kallesa tana cewa. "Thank you Suraaj amman a ƙoshe nake." Juyawa tai zataci gaba da tafiya, Suraaj ya duba ko akwai masu kallansu zata disga shi, yai saurin cewa. "Dan Allah Rahama ki karɓa koba dan ni ba please." Jin ya haɗata da Allah ne yasa ta daure tasa hannu ta karɓa, juyawa tai ba tare da tayi masa godiya ba, a cewar ta ai ba ita tasa shi ba kawai ganin damarsa ne. Tun a lokacin da taga yana yi mata wasu abubuwan kamar na love ta fara janye jiki daga gareshi, ada tana yawan manne masa saboda mugun ƙoƙarin da yake dashi, idan sun gama ɗaukar lecture tana binsa ya ƙara mata haske har ta sake fahimtar darasin sosai. Ranar da ya gaya mata yana sonta ji tayi babu wanda ta tsana a duniya sama dashi, gaba ɗaya batasan koya ya tunkareta da maganar soyayya, bata da buri irin ta zama babbar likita dan Imran Matawalle yai alfahari da ita.
Tana shiga hostel tun kafin ta cire mayafin jikinta ta miƙawa partner ɗinta ledar da Suraaj ya bata. "Na meye Rahama?" Cewar Mecy Abraham wacce ta kasance Cristian. "Kici na baki." Rahama ta bata amsa tana cuge ɗanƙwalin kanta da zafi ya isheta. Flask ɗin ruwan zafinta ta ɗauka ta zuba a bokita, wanka ta shiga babu jimawa ta fito. Kaya ta janyo marasa nauyi zata saka taji hadarin nan ya fara saukar da iska, garin ya fara daɗi tai sauri tasa kayan ta haye gado tare da janyo wayarta. Miss calls ɗin Ummy da na Yaya Farooq ta gani, da sauri ta rintsa ido ganin babu na Imran. Ummy ta fara kira suka gaisa ta tambayeta karatu Rahama tace alhamdulillahi sunayi sannan taja mata kunne akan kula da mutunci Rahama ta tabbatar mata da cewa tanayi sannan suka katse, kin ƙiran Farooq tai dan ba buƙatarsa takeyi ba. Tana tunanin kiran Imran sai gashi ya kirata, nan da nan zuciyarta ta fita daga kuncin da ta shiga, ta kara jikin kunnanta.
"Kina mene yanzu?" Imran ya tambayeta cikin hosky voice nashi. Shauƙinsa yasa Rahama yin juyi akan gadonta itama tayi ƙasa da murya. "Ina hostel." lips ɗinsa ya ciza na sama yana faɗin. "Ina cikin school ɗinku yanzu haka." Da sauri ta miƙe tana ware ido tace. "Really Imran? Me kazo yi?" Kamar yana kallanta ya lumshe ido tare da faɗin. "Wani supervision nazo, gashi anata iska dana tsaya mun gaisa." Rahama tasha toka tana turo baki tace. "Oh bazaka tsaya ba kenan?" Imran ya kwantar da kai jikin kujerar motarsa, duk wani furucinta yana jinsa a magudanar jininsa dan har baya san yaji tayi shiru batai magana ba, hosky voice ɗinsa ta kuma dukan kunanta yana faɗin. "Ana jirana a hospital, rashin zuwana da wuri kuma zai sa a fara gulmar hospital ɗina, bana san disappointing my patients. Zan sa rana nazo just for you, naga kina maida hankali wajan karatu ko kuwa." Ta sake turo baki,
"Nidai ka barni nazo mu gaisa kawai." Imran ya kalli yadda iskar ke tsakanin kaɗawa, students dake waje sai gudu suke kowa na neman wajan fakewa dan iskar zata iya ɗauke komai dake waje, taya zai iya barin ta fito? Yasha toka cikin buɗe murya yace mata, "Do as I said R Galadanci, iskar nan zata iya affecting eye's naki. Indai ni ne I promise you zan dawo." Babu yadda zatayi musamman da taji yayi magana da wani irin voice tace. "Shikenan sai kazo."
Murmushi yai da yaga ta haƙura, batasan ya fita san ya ganta ba, yana daurewa ne kawai dan karta sawa ranta cewa yana yi mata irin soyayyar da take mai. Sallama yai mata yana tabbatar mata da dawowarsa, yaja motar yabar cikin school ɗin cike da haushin rashin ganinta da beyi ba.


*****
Cikin sauri ya fito daga sashensa ya nufi na Hajja sai faman huci yakeyi, zaune ya sameta ita da Alhaji Uthman Galadanci, Farooq ya isa ciki shaye da toka ya samu kujera ya zauna, Hajja tace. "Kai kuma fa kamar wani yaro?" Farooq yaja numfashi yana ƙanƙance idanuwa yake faɗin "Hajja wai me ake jira ne da maganar auren mu? Yanzu sai na jira Rahama ta kammala jami'a sannan zanyi aure?" Kallansa ya mayar kan mahaifinsa wato Alhaji Uthman Galadanci yana cewa. "Abbie kuyi wani abu akai dan Allah, ni bazan iya kara good 1 years banyi aure ba. Rahama ƙara wayewa takeyi, tun kafin tazo tafi ƙarfinku gwara ayi a wuce wajan, tana gidana ma zata iya ci gaba da karatunta ba hanawa zanyi ba." Yayi shiru yana sauke numfashi. Uthman Galadanci ya kalli ɗan nasa yana murmushi yace. "Rashin hakuri ko Farooq? Yanzu zaman nan da kaga munyi da Hajja maganar mukeyi, kuma za'a tsaida rana da lokaci muna jiran Abubakar yazo gobe zamu yanke komai, kaci gaba da shiri kawai." Wani farin ciki ya mamaye Farooq Galadanci, tsorata ya farayi da lamarin Rahama dan yanzu kusan sati kenan bata ɗaga kiransa, yayi mata sms no reply shi yasa yake ganin kamar ta fara canza ra'ayi, tana neman ta ruguza alƙawarin da suka yiwa juna." Matsoracin ango kawai, anya ba Rahama ce zata juya gidan naka ba? Duk ka wani ruɗe saboda karta ce ta fasa auran?" Farooq dariya yai kawai, Hajja bazata gane abinda yake gudu ba, shi ya riga yasan idan be yi saurin ɗauke Rahama Galadanci ba, wani zai iya zuwa yaja ra'ayinta, musamman da yanzu komai na halittarta ya sake fitowa. "Karkasa damuwa Farooq kaida Rahama duk namu ne, abu guda ɗaya ne munsan babu wanda zai bamu matsala a cikin ku." Abbie ya faɗa cike da nuna kwarin guiwa, yayin da Hajja ta shiga jan numfashi dan har yanzu tasan da cewar Rahama babu kowa a ranta face shegen yaron nan ɗan gidan Matawalle, shi yasa itama take son ayi auran da Farooq ko banza ta cito jikarta daga faɗawa sharin mashayin giya, kuma ɗan gidan maƙiyin ɗanta na farko kaf duniya....














#Asmy B Aliyu
Da
#Hajja ce 👈
[11/12, 9:32 AM] Asmy B Aliyu😘: *ALBI....*
(My Heart❤️)


NA
*ASMY B ALIYU*
DA
*HAJJA CE*👈


PAID BOOK..#(500)


*Account Details*
0004157137
*Jaiz Bank*
*Asma'u Buhari Aliyu*
Shaidar biya ta
08086207764


*Katin waya ta MTN.ta 07043079282 shaidar biya ta 07065283730 view WhatsApp*




*Free page 9*




Ƙarfe tara da kwata ya iso gida mai gadi ya buɗe masa gate ɗin. Ruwa ake yi sosai tamkar da bakin ƙwarya dan ko da yaje asibiti yaga ana iskar nan be daɗe a ciki ba ya yi abin da zai yi ya taho gidan. Kasa zuwa inda yake parking yai, kawai ya nufi motar saitin part ɗinsa nan ya ajiyeta ya shige ciki, amman duk da haka sai da ruwa ya taɓa shi. Imran Matawalle yana shiga parlor ya shiga cire kayan jikinsa tun daga down stairs ya zama daga shi sai boxer da vest, ƙoƙarin hawa sama yake kawai yaji muryar mace a bayansa, ya waigo da sauri, Humaida ce sanye cikin kayan bacci shara-shara dasu tana wani yauƙi tace. "Mommy ke kiranka." Shaye da toka Imran ke kallonta yana faɗin. "Sai kuma an turoki sannan za'a sanar dani? Batada phone number ɗina?" Humaida ta matso gab dashi, yai saurin matsawa yana jan tsaki yace. "Fice ki bani waje, a cikin uban ruwan nan bazan iya fitowa ba ta jira ya ɗauke." Narke masa idanuwa tai tana sake matsawa gurinsa "Imran meye laifi na da bana cikin zuciyarka? Kasan yadda kake ruguza min zuciya? Please Imran love me as I..." Ya daka mata wata azababbiyar tsawa, idanunsa suka fara canza launi yace. "Humaidah leave me alone please karki ɓata min rai cikin daren nan." Yana faɗa ya juya

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads