Showing 72001 words to 75000 words out of 139785 words
Chapter 25 - Albi Book Complete document by Hajjace.txt
fatar bayanta na manne da ta cikinsa ya saƙalo hannunsa saman na shanunta, bacci yake yi sosai ita kuwa Rahama gaba ɗaya bataji idanunta a soye yake ta miƙa hannunta karshen gadon ta janyo wayarta, data ta kunna kai tsaye ta shiga WhatsApp. Abinda ya bata mamaki shine ganin sunan Deejah Galadanci ta turo mata sako, tunda Rahama taki auran Farooq Galadanci kowa na family ɗin Galadanci suka dena kulata, Deejah kuwa blocking ɗinta tayi amma gashi ta buɗe. Jiki a sanyaye Rahama ta shiga sai taga an turo hoto, buɗewa tayi yana gama viewing ta fara karantawa. Gabaki ɗaya bata gane kan iv ɗin sai da tazo dai dai sunayen taga _Imran Bashir Matawalle & Humaidah Khaleel Makarfi._, cike da tashin hankali ta fizge masa hannunsa dake jikinta wanda yasa Imran buɗe ido ba shiri, ganin zata sauka daga bed ɗin ya fizgota ta dawo, cikin masifa ta turesa tana furta. "Ka sakeni bana so." Tayi maganar tana fashewa da kuka, zuciyarta na zafi ranta kamar zai fita . "Meya faru?" Taji tambayar kamar ta rainin hankali dan haka cikin ɓacin rai ta sake tureshi yai saurin.......
#Asmy B Aliyu
#Hajja ce 👈
#Imran Matawalle
#Rahama Galadanci
#Maheera Matawalle
#Deejah Galadanci
#Haske writer's association
[11/25, 5:32 PM] Asmy B Aliyu😘: *ALBI...*
(my heart❤️)
*ASMY B ALIYU*
DA
*HAJJA CE*👈
PAID BOOK..#(500)
*Account Details*
0004157137
*Jaiz Bank*
*Asma'u Buhari Aliyu*
Shaidar biya ta
08086207764
*Katin waya MTN. Ta 07043079282 shaidar biya ta 07065283730 view WhatsApp*
32.....
Saurin riƙo mata fuska yayi yana son su haɗa ido taki bada hadin kai saboda ɓacin rai. "Idan kina cikin fushi ina tambayarki please ki gaya min, kina min irin wannan taya zansan abinda yake damunki haa?" Ya faɗa yana shan toka. Da wani irin fushi ta fisge jikinta tana miƙewa ta sauka daga bed ɗin, daga ita sai Pant red color ta buɗe wardrobe tana neman kayan da zata saka, still hawaye basu dena ambaliya a saman fuskarta. Sakkowa yai daga kan bed ɗin shima daga shi sai boxer ya wani fincikota tare da haɗe bayanta jikin murfin wardrobe ɗin yana sake ware eye's nashi cikin nata. Haɓarta ya ɗago da hannunsa idanunta a lumshe ya manna cikinsa a jikinta yana saka ɗaya hannun yana kwantar mata da lallausan gashin kanta, hosky voice nashi ya daki cikin kunnanta yana cewa. "Tell me waye yasaki kuka?" Da wani irin yanayi ta ware idanunta cikin nasa tana yi masa kallon kai kasani, murya na rawa take faɗin. "Auranka da Humaidah yana nan ko? Kai dole sai ka aureta?" Imran yaja wani irin numfashi tare da ɗora goshinsa a saman kanta, fashewa da kuka ta kuma yi tana faɗin. "Bazan zauna a gidan nan ba, kaje can ka cinye Humaidah itace matar so, Imran ka nuna min cewa banida hankali, amma meyasa baka ci gaba da nuna baka so na ba sai ana gobe daurin aurena ka furta min kalmar love?" Ta buɗe jajjayen idanunta tana kallan kwantaccen gashin dake kirjinsa sakamakon bazai ga face nata ba saboda ya ɗora habarsa saman goshinta. "I know dan kaga ina sanka ne ko? Kasan shine kawai abinda zaka gaya min naji na sake tsanar auran Farooq Galadanci ko? Ni bazan zauna ina kallo wata ta shigo cikin rayuwar mu ba, ina so na zauna da miji na saboda na shirya irin rayuwar da zanyi dashi, kaje ka auri farin cikin ka, am not your ALBI." Da sauri ya buɗe idon, kallanta ya shiga yi tana faman tureshi, kukan ta yana taɓashi dan haka ya daure duk da irin ɓacin ran da yake ji na cewa shi ba Albi ɗinta bane. Kan bed ya cilla ta yabi samanta ya kwanta tare da sanya hannu biyun saman na shanunta ya shiga yi musu wani irin murza, bakinsa saman cibinta yana goga harshensa. A hankali ya ɗan kalleta duk ta wani sandare masa jikinta sai faman rawa yake ya matseta yana faɗin. "Koki yadda ko ba haka ba na gaya miki bada san raina zan auri Humaidah ba, and na gaya miki ke din Albi na ce, shima koki yadda kobaki yadda ba na gaya miki dai." Ya fada yana kai bakinsa kasan mararta ya sakar mata wani mayataccen kiss kafin ya mike yabar wajan. Kuka ta fashe dashi ganin ya tada mata fitina ya kuma barta. Ta kuma sakin wani kukan, da wani irin ɓacin rai itama ta sakko tare da zura kayanta ta ɗauki mayafi. "Intafi in barmaka gidanka kacinye abinka, dama ai ni na kawo kaina wajanka yanzu kuma zan barshi kaje kaita auran Humaidan." Kamar yasan zata iya fitowa ta tafi yaje ya garkame entrance din duka. Tana sakkowa daga stairs taganshi tsaye ya haɗe hannu a kirjinsa yana kallanta. Harta gama sauka bata kalleshi ba tana murda handle din taji kofar a rufe, ranta yai mugun baci, kallansa tayi tana kuma shan toka tace. "Ka buɗe min zan fita." Imran Matawalle yai mata wani mugun kallo yana sake riƙe ƙarfen jikin stairs. Afusace take faɗin. "Ka buɗe min nace." Imran yai mata kallan mamaki ganin yanayin da take masa magana, da kyar ya hadiye ɓacin ransa tunda ita aka taɓo dole ne ya san yadda zai lallasheta. Sakin karfen yai ya ƙarasa inda take, dariya ma taso bashi amman ya daure dan kada ya sake ɓata mata zuciya. Kusa da ita yaje ganin yana shirin kamota yasa ta saurin jan baya, shaye da toka take faɗin. "Cewa nai kawai ka buɗe min na fita bana ra'ayin ka sake taɓani." Imran ya wani fizgota ya mata wani irin riƙo yasanya idanunsa cikin nata, kawar da nata tayi da sauri jin wani ɓangare na sashen jikinta da yake mugun son Imran ɗin yana neman sanyayar mata da jiki. Sosai ya rungumeta a cikin jikinsa, kansa ya sakalo ta wuyanta murya a sanyaye yake faɗin. "Banace miki kidena sanya Humaidah a cikin rayuwarki ba? Humaidah itace ta dage sai ta aureni, na gaya mata bana sonta ta dage har sai da mahaifina yasa min sharaɗi akan indai ina san zama dake dole sai na aureta. Albi please kidena damuwa da ita sam bata cikin tsarin rayuwata ki yadda dani." Yadda yake yi mata ne yasa wasu hawayen zubowa a idanunta, wata sabuwar kaunarsa ta kuma samun wajan zama a cikin zuciyarta, cikin ɓacin rai take faɗin. "Nidai kawai kaje kace bazaka aureta ba, idan ka auri Humaidah baz...." Da sauri ya juyo da ita tare da manna bakinsa cikin kunnanta yana masa wani irin abu mai wahalar fassarawa. Nan da nan jikin Rahama ya mutu ta sake shigewa jikinsa tana hawaye. "Zanje nasan yadda zanyi ganin auran nan beyiyuba saboda farin cikin ki." Da wani irin murna ta makaleshi hakan ya bashi damar sauke wata katuwar numfashi na jin daɗin nasarar kwantar mata da hankali. "Kiyi mana lunch bari naje gida muyi magana da Daddy." Kallansa tayi tare da ɗora hannunta saman kirjinsa tana wasa da lallausan gashin kirjinsa take faɗin. "Nifa karka dawo ba tare da kayi nasarar janye auran ba." Da murmushi a saman fuskarsa yake cewa. "Karki damu kedai ki kwantar min da hankalinki." Da haka ya samu ta sakko da ita daga cikin fushinta. Ɗaki suka koma tayi shirin shiga kitchen shi kuma ya shirya tsab ya nufi gidansu. Cikin sa'a yana gama parking ya hango Humaidah suna fitowa da wasu ƙawayenta, ya ɓalle murfin motar ya fito fuska shaye da toka yake cewa ta biyo shi. Cike da farin ciki ta kalli ƙawayenta tana cewa su jerata ango ya kirata. Apartment ɗinsa ya wuce, yana faman zagaye parlorn ta shigo cike da kwarkwasa idanunta sunsha eyelashes ga wasu pink ɗin farce da ta ƙara a yatsunta ta isa wajansa tana cewa. "Gani my." Imran ya watsa mata wani kallo tare da yin taku biyu ya iso gabanta yana huci yake faɗin. "Ina so ki gaya min duk wani abu da kike so wanda zan miki ki fasa aure na, Humaidah ina tausayinki idan kika bari aure ya shiga tsakaninmu saboda ina da wacce zuciyata ta nutsu akanta, ki gaya min ko menene zan miki shi indai befi karfi na ba." Da wani irin kallo take kallanshi kafin ta kawar da kai tana faɗin. "Babu wani abu da ya fiye min kai a duniyar nan Imran, babu wani abu dana rasa sai kai." Afusace yaje gaf da ita har suna bugun numfashin juna, ransa a mugun ɓace yake kallan cikin kwayar idanunta yake cewa. "I said banda ni ko bakiji ba? Ina so ne kibar cikin rayuwata Humaidah, daga 10 millions zuwa sama ki gaya min saboda ina so ki rabu dani." Yadda sukai kusancin nan kaɗai yasa ta kuma jin wata irin soyayyarsa, sake buɗe hanci tayi tana shakar numfashinsa, yaji tamkar ya kasheta dan haushi. "Komai zai biyo baya karkiga laifina Humaidah, ina da wacce nake so ke kuma kin dage ko? Ki gaya min abinda kike so nai miki ki barmu." Cikin kwantar da murya Humaidah tace. "Idan kana so Imran abun mai sauki ne, bana san dukiya ko kadara, ina so kawai ka kusance ni kai min ciki sai na koma gefe naci gaba da kulawa da babyn, nasan ko babu komai abinda zan haifa zai ringa tuna min kai." Imran yaja wani irin tsaki tare da hankaɗata gefe haushi kamar zai kasheshi yake faɗin. "Get out of here Humaidah, koke manyya ce kyabar namana saboda ɗacinsa. Tunda bakida tunanin muje zuwa stupid kawai." Ficewa tayi zuciyarta na zafi, hango ƙawayenta da tayi yasa ta kakalo murmushi dan karsu zaci wani abun, tana zuwa take ce dasu maganar bikin sukai daga nan ficewa sukai a ranta tana cewa. "Wallahi sai ka aureni indai akan shegiyar yarinyar nan ne kake kina mu zuba mugani." Shi kam fitowa yai ya shiga motarsa saboda Matawalle baya gidan, wajan su Al-Amin yaje duk dan ya huce ɓacin ran Humaidah amman bai ji sassauci ba. Ganin hakan ne yasa shi komawa gidan, fuskar Rahama kawai da ya kalla yasa shi jin wani irin nutsuwa, kallanta kawai yake yadda tayi masa wani irin kyau, sanye cikin wasu English wears skirt ɗin ko cinyoyinta bai rufe ba irin na jeans ɗin nan, sai wata half vest mai Kamar bra ta gyara gashinta ya zubo ta gaba tayi kyau so masha Allah. Hannunsa ya ware alamar tazo, da sauri Rahama ta shige cikin jikinsa ya maida hannuwan ya matse ta a jikinsa. "ALBI you're so cute." Murmushi tayi tana sake shigewa jikinsa. "I love you ALBI I mean it." Farin ciki ya cika zuciyarta tama manta da cewar ta turashi yin yakin janye auransa da Humaidah shi kuma sai yaji daɗi da bata tada zancen ba. Itace tayi feeding ɗinsa yai nata cike da soyayya.
*******
Da wani irin gudu take sakkowa daga stairs, saboda idanunta a rufe yake biyu-biyu ta dinga hadawa har ta sauka kasa. Shima Imran da gudu ya biyo ta daga shi sai boxer ya cafkota tare da dauko ta gabaki dayanta. Ciki ya koma da ita tana faman dukanshi ta ko'ina ajikinshi, cikin soofa ya zube still tana jikinsa tana kuka tare da dukanshi tana cizonsa amman yaki sakinta. Idanunsa alumshe yana jin kukanta har can cikin ransa, sabida kar yaji kukanta yasa tun jiya da aka daura auran yaki gaya mata, yau din ma ya sanar da ita ne dan Matawalle ya kirashi cewar za'a zo yin jeren kayan Humaidah dan karta gansu daga sama yasa shi gaya mata an daura. "Albi please ki bani aran hankalinki." Da wani irin fushi tana huci take fadin. "Bazan saurara ba Imran, mezaka gaya min? Yeah I know zakace Rahama baki da hankali ko? Kai kayiwa iyayenka biyayya ni kuma na kunyatasu a idanun mutane, na nuna cewa su basa da kima da mutumci a waje na, toh ni bazan zauna dakai ba, dole ka rabu dani kaje can kai da katuwar matarka." Ta karasa fada tana ture shi. "Kina hauka ne?" Cikin sauri tace, "Eh bani dashi tunda har na guji iyayena na biyoka gashi da abinda ka saka min." Ta kuma ture shi tana so tabar jikinsa amman ya hana. Cikin serious dinshi yake mata magana. "Kina zaton zan rabu dake ne? Kin dauka bani da hankali? Ina so kisa a ranki cewar aure na dake mutuwa kadai zata rabamu, kema kinsan idan har ina san abu to bana yi masa rikon wasa, duk wani abu dayazo hannuna bana barinshi sai in har ya mutu, ke kuwa ina ji a jikina tare zamu mutu dan haka ki shirya zama da Humaidah a cikin gidan nan." Yana kaiwa nan ya sassauta rikon da yai mata yana jira yaga ko zata sauka daga kan kafafunshi. Afusace yaga ta daga shi tana yi masa wani irin kallo mai cike da wani irin bakin ciki, tasha toka tana wani huci kamar wata zakanya take fadin. Sai dai ku mutu kaida ita, ni kam ko ka sakeni ko karka sakeni tunda nabar su Ummy kaima zan iya barinka kuma zaka gani." Tana kaiwa nan ta juya tare da hayewa stairs tana wani irin huci. Rintsa idanuwa yai yana cusa yan yatsunsa cikin lallausar sumarsa, gabaki daya Daddy ya jefashi cikin trouble, besan yanzu ya zai yi da rigimar Rahama ba, be kuma san abinda take kitsawa a zuciyarta ba, abu daya ya sani duk wuya duk rintsi ba zai taba rabuwa da ita ba, yanzu ne ma shi yaji wata fitinanniyar kaunarta,Wata zazzafar soyayyarta tana sake samun waje a zuciyarsa musamman da take cewa saboda shi ta watsawa iyayenta kasa. Kasa bin bayanta yai saboda yasan tana cikin jin haushinsa, shi kuma baya so yana ganin bacin ranta akanshi. Rahama kam kan bed ta fada sai kuka takeyi, bata da buri a yanzu irin ta ganta a cikin school, tana bukatar wani a kusa da ita wanda zai nuna mata kuskuran da takeyi, idan da halima tana bukatar mai yi mata dukan tsiya. Tana cikin kuka Aunty Kausar ta fado mata a rai, duk da tana tsoranta ta kuma san cewar idan har ta buga mata waya zata iya yi mata rashin mutunci ta zazzageta ma. Sai dai zuciyarta taji tana da bukatar irin Aunty Kausar din ko ta samu sassaucin zuciya. Hannunta har rawa yake ta nemo sunan Aunty Kausar din, bugu biyu taji ta dauka cike da fushi kamar tana gabanta take cewa. "Ashe a cikin wadanda kika raina hardani Rahama? Ke yanzu kina da idanun da zaki iya neman inda muke? Toh bari kiji na gaya miki, duk lokacin da kika sake kirana sai na ci miki mutunci wallahi, very stupid girl." Zata kashe taji Rahama cikin tashin hankali tana cewa. "Dan girman Allah Aunty kiyi hakuri ki saurareni dan manzan Allah." Jin yadda ta hadata da Allah ne yasa Aunty Kausar ta fasa katsewa tayi shiru tana sauraranta. Cikin kuka Rahama take mata magana. "Aunty dan Allah kuyi hakuri ina bukatarku a kusadani, Aunty Kausar munyi aure da Imran and videon da kuka gani anyi kawai na fasa auran Yaa Farooq ne, amma wallahi bamu taba aikata zina ba." Aunty Kausar tasha toka kamar suna ganin juna take cewa. "Ina da aiki ln yi fa Rahama, ki tafi kai tsaye ki gayan abinda kike san gaya min sauri nake." Hawaye suka shiga zirarowa Rahama take cewa. "Aunty ina san zuwa wajanki dan Allah karkice min a'a please." Da yanayin takaici take fadin. "Kizo kiyi min mene Rahama? mekike so nayi miki kuma? Ba kina tare da masoyinki ba me kuma zamuyi miki? Karkizo min dan idan na ganki babu abinda zai hanani cin ubanki wallahi." Tayi maganar so pissed up tana ƙoƙarin kashe wayarta, wani irin kuka ta fashe dashi tana faɗin. "Please karki katsemin wayar Aunty ina cikin damuwa, ina cikin tashin hankali, ina son naganki Aunty dan Allah ki bari nazo ko zan samu sauƙi cikin raina." Ta faɗa da kuka mai cin rai, lokaci ɗaya jikin kausar ɗin yayi sanyi tamkar tana ganinta ta wani haɗe rai tana faɗin. "Zuwa dare ki shigo, yanzu bana gida." Da haka ta katse kiran. Kifa kanta tayi acikin pillow ta cigaba da rera kukanta.....
(Complete document)
*WAMINAL HUB* #500
*ZO GARENI* #300
*NIDA RAHEEMA* #300
*RAYUWAR AURENAH* 300
#Asmy b Aliyu
#Hajja ce
#imran Matawalle
#Rahama Galadanci
#Humaida
#Haske Writers Association....
[11/25, 5:32 PM] Asmy B Aliyu😘: *ALBI...*
(my heart❤️)
*ASMY B ALIYU*
DA
*HAJJA CE*👈
PAID BOOK..#(500)
*Account Details*
0004157137
*Jaiz Bank*
*Asma'u Buhari Aliyu*
Shaidar biya ta
08086207764
*Katin waya ta MTN.ta 07043079282 shaidar biya ta 07065283730 view WhatsApp*
33.....
Ya tsayarda motar dai-dai ƙofar gate ɗin gidan Hajia babba dake unguwar Hotoro (NNPC). Har lokacin Rahama taki sakin fuskarta, sanye take cikin dogon hijab kalar blue black fuskarta ta kumbura sabida kukan data yini tanayi, ya kamo hannunta ta fisge da sauri tana mai dasu can baya, ya girgiza kai kawai ya kalli agogon rolex ɗin dake cikin damtsen hannunsa yana faɗin. "Minti nawa zaki yi aciki?" Wani irin kallo take yi masa ta haɗe rai tana kama handling ɗin motar, da wani irin yanayi take faɗin. "Ni na dawo nan dan na baka waje kaci amarcin ka kai da amarya Humaidah." Tayi maganar sounding so very jealous cikin muryarta. A haukace ya juyo yana kallonta, lokaci ɗaya ya dannawa duka ƙofofin motar lock. Ya haɗe rai yana faɗin "Kina so mu koma inda muka fito ko? karki fara trying ɗina a daren nan please Albi. kije bayan sallar isha'i zanxo mu koma gida, dan Allah idan nazo karki fito dan wallahi zan shigo har cikin gidan na fito dake sai naga mai tsayar dani." Ya faɗa a fusace lokaci ɗaya ta buɗe motar itama a fusace ta fice daga motar ta nufi gate ɗin gidan tamkar zata tashi sama sabida masifa. Imran ya kwantar da kansa jikin seat ɗin motar ya lumshe ido a hankali yana jin wani irin ciwon kai, yasan kuma duka sabida rigimar Rahama, yanzu ya zaiyi da wannan rigimar? Tunda yayi masifar yayi rarrashin duka a banza. Yayiwa motar key da wani irin speed yabar wurin, yana buqatar shan beer sai dai yasan bazai yuyuba sabida zai dawo ɗaukar Rahama. Har kusan minti biyu tana tsaye a bakin ƙofar parlorn tana danna door bell, Malika ce tazo ta buɗe ƙofar wato ƴar Hajiya Babba ta uku, wacce ta girmi Rahama.