Showing 45001 words to 48000 words out of 139785 words
Chapter 16 - Albi Book Complete document by Hajjace.txt
taji sunan sai da kirjinta ya buga, tayi zaton ko maganar mutuwar Rahama ya kawo mata, amman da ta tuna saboda shi Rahama ta barsu, sai tasha toka tare da cewa. "Sai aka yi me?" wani tashin hankali yake ji acikin zuciyarsa kardai Rahama bata gidan nan? Sai ya waske yace. "Ummy dan Allah ku yafe mata, ku barmu muyi aure tunda Allah be hanamu auri juna ba. Kullum kuka take tana Ummy ta tsine mata, Abba baya santa, tana tunanin fushinku zai sa ta faɗa halin da kuke tunanin tana aikatawa. Dan Allah Ummy ki yafe mana kisa mana albarka a cikin rayuwar mu." Imran ya ƙarasa maganar yana yana kallon ummi da wani yanayi acikin fuskarsa, ji yai kamar yazo gaban Mah, ji yake tamkar ita yake yiwa magana. Cike da ɓacin rai take kallansa tana cewa. "Yanzu ina ita Rahama take?" Kafin ya nemo abin cewa sukaji horn, maigadi da sauri ya nufi get yana riƙe da wuya ya buɗe, Abubakar Galadanci ne ya dawo, yana shiga Adamu driver yai parking ya fito, ganin Imran a cikin gidansa yasa ransa yai mugun ɓaci, cike da ɓacin rai yake faɗin. "Uban me kazo yi min a cikin gida? Wato abin naka ya shahara bayan ka hure mata kunne ta gudu wajanka shine yanzu ka shigo min gida? Ko kayanta kazo ɗiba tunda dama ba duka ta ɗauka ba?" Ya sake matsawa kusa da Imran ɗin, "Wanda ta ɗiba sune rabonta dama ni na siya mata ba wani ɗan iska ba, dan haka, kafin rai na ya gama ɓaci zoka bar min gidana stupid boy." Wani irin ƙululun bakin ciki ne ya rufe Imran, idanunsa a rintse yana jin tamkar kansa zai faɗo kasa dirar sojoji sukaji acikin gidan, Imran suka yiwa umarni akan ya fito daga gidan, motar aka gani a waje hakan yasa aka gayawa Matawalle yace a shiga kila yarinyar Imran ya shiga nema. "Idan na sake ganin ƙafar ka a cikin gidana wallahi sai na lahira yafika jin daɗi." Kansa kamar zai faɗi haka yabar gidan, Hajja kuwa ta kasa magana saboda ganin tsaurin ido irin na Imran Matawalle.
"Kuga yaro a haka kamar mutumin kirki wallahi." Cewar Hajja tana riƙe da haɓa, "Ɗan iska ne Hajja, yaron da yake shan giya, abokansa duk ƴan daba ne shege tsinanne, wallahi daga shi har uban nasa ba zasu taɓa ganin dai dai a cikin rayuwarsu ba." Yana kaiwa nan ya wuce ciki kamar zai tashi sama. Suna shiga ya kalli Ummy, "Me ya shigo yake gaya maku?" Ummy cikin raunin zuciya ta sanar da shi yaja tsaki tare da hayewa upstairs yana jan tsaki a karo na ba adadi.
*********
Apartment ɗinsa yaje zai shiga securities ɗin suka hanashi ɗaya daga cikin su ne yace yaje Matawalle nasan ganinsa. Cike da tashin hankali Imran ya shiga, a parlor ya tarar da Matawalle zaune yana shan fruit hankalinsa kwance. Imran na hangoshi ya ƙarasa wajansa, kansa ya ɗora akan ƙafafuwan mahaifinsa yana sauqe wani irin numfashi wanda yasa senator Matawalle rintsa idanu sakamakon har cikin magudanar jininsa yake jin bacin ran imran din. "Daddy na kusa haukacewa , tabbas Daddy kana gaf da rasani, I can't take it anymore, Wallahi Daddy I love her, I really love her. Daddy banganta ba, banga farin ciki na ba Daddy baxan iya rayuwa babu Rahama ba." Ya fada yana wani dafe kansa dq hannayensa duka biyu. abunda ya koma tayar da hankalin Matawalle kenan. "Ya isa haka my son, wannan daga hankalin da kake yana hurting zuciyata, tashi ka zauna sai ka gaya min damuwarka." Imran ya kasa koda kwakkwaran motsi bare ya iya zama inda mahaifinsa ke nuna masa ya zauna. "Taso ka zauna mana." Matawalle ya faɗa yana ɗago masa da kansa. Dakyar ya tashi ya zauna gefensa, sumar kansa Matawalle ya shiga shafawa kafin yace. "Oya tell me what is going on naga duk kabi ka tashi hankalinka har ana sanar min cewar kaje gidan Abubakar Galadanci why my son." A haukace ya ɗago ya zubawa Matawalle jajayen idanunsa yana cewa. "Banga Rahama ba Daddy, ban san Inda ta shiga ba, naje gidan su bata nan, Na rabata da iyayenta, ƴan uwanta da duk family nata taya zan iya rayuwa babu Rahama Daddy?" Haushi da tausayin Imran suka karyawa xuciya . Matawalle cikin zuciyarsa yana sake jin tsanar Rahama, yayi imani ɗansa yafi san Rahama akanshi, me ya kamata yayi akan yarinyar nan? Imran ganin Daddyn bazai ce komai ba yasa shi miƙewa zai tashi, da sauri ya riko shi, a hargitse Imran ke faɗin. "Daddy bazan iya zama a gidan nan ba banje na nemo ta ba." Matawalle ya haɗe rai, "Kanada hankali kuwa Imran?" Cikin fita hayyaci Imran yace. "Yanzu kam bani dashi Daddy, hankalina zai dawo jikina ne kawai idan nasa Rahama a cikin idona." Girgiza Imran Matawalle ya shiga yi yana faɗin. "Meye a wajan Rahama da har ka samu kanka cikin san fita daga hankalin ka? Menene aibun Humaidah Imran? Ga kuma yarinyar wajen azezah itama ƴar uwarka ce, haba Imran ga ƴaƴan ministoci kazo muje ka duba ka tsaya wajan ƴar ƙaramar yarinya sai juya ka takeyi? Koda yake bayin kanka bane ba, bita da kulli aka biyoka dashi har baka ganin kowacce mace a matsayin mace sai ita, amma zanyi maganin abun." Jin abun da Daddy yace ne yasa Imran saurin komawa cikin jikinsa ya rike hannun Matawalle yana da wani sabon tashin hankali yake fadin "Daddy kana da karfi da ikon da zaka iya sawa a nemo min ita, please Daddy dan Allah kanemo min Rahama." Lallashinsa ya shiga yi yana shafa masa kai. "Don't worry my son, yanzu dai ina so ka kwantar da hankalinka, yanzu zansa a shiga nemanta duk inda take sai na dawo maka da ita, but first ka fara kwantar da hankali kaji ko?" Kamar ƙaramin yaro ya ɗaga kai sannan Matawalle yace ya shiga bathroom yai alwala yazo suje suyi magrib. Jiki babu kwari Imran ya tashi ya shiga, tare suka wuce masjid dake cikin gidan Matawalle suka gabatar da sallah. Imran ya daɗe yana addu'a abinda yai matuƙar bawa mahaifinsa mamaki kenan dan yasan tun da Imran ana idar da sallah yake tashi ya tafi. Sitting room Matawalle ya nufa inda zai yi meeting da wata qungiya, Imran kuma yana fitowa yaje yana tambayar car key a wajan securities suka hanashi saboda umarnin da Matawalle ya basu cewar karsu sake subarshi ya fita daga gidan. Apartment ɗinsa ya nufa cikin kunar zuciya, kai tsaye upstairs ya nufa a haukace ya dinga birkita master bedroom ɗin yana neman beer, wani irin ƙara ya saki gamida dafe kansa, ji yake kamar zai yi hauka. Komai nashi ya kwashe ya bawa Al-Amin ajiya, extra phones nashi duk ya kwashe su ya bada ajiya a tunaninsa ba zai sake dawowa cikin gidan ba. Haka ya zauna yana zubar da hawaye zuciyarsa kamar zata ƙone saboda bakin ciki da damuwa...
*****
A hankali ta shiga buɗe idanunta da sukai mata mugun nauyi, numfashi taja tare da bin kowane sashe dake cikin ɗakin da kallo, bata gane ko'ina bane ta sakko daga kan bed ƙofar da ta gani tana facing nata ta nufa, a hankali ta buɗe. Tsaye tayi a upstairs tana kallan tanƙama-tanƙaman hotunan Matawalle, ita kam tunda take ma bata taɓa shiga tsararren gidan da ya kai wannan ba. Sakkowa ta farayi a hankali tana ware ido ta inda zata hango Imran dan tasan tunda taga frame ɗin Matawalle kuma a motar Imran aka ɗakkota. Wata dattijuwar matace ta fito daga kitchen hannunta ɗauke da warmers, mamaki ya kama Rahama, ta ƙarasa ta karɓi ɗaya tana faɗin. "Ina Imran ɗin?" Mama Rabi tace, "Imran yana Kano." Da sauri Rahama ta kalli Mama Rabi bakinta yana rawa tace. "Kano kuma? Nan kuma ina nake?" Mamah Rabi na ajiye warmer din hannunta tana faɗin "Kina garin Abuja Rahama." Cikin zaro ido Rahama take kallan Mama Rabi, hankali a mugun tashe take faɗin. "Meyasa nazo nan, me yasa Imran zai taho dani Abuja bayan yasan ina kan yin tests?" Mama Rabi ta juyo tana kallan Rahama take faɗin. "Imran besan kina nan ba, Matawalle ya bada umarnin a kawoki nan." Hankalin Rahama yai mugun tashi, agogo ta kalla dake jikin bangon falon, karfe 7:45am kenan tun jiya aka taho da ita nan babu sallar magrib da isha ga kuma ta safiyar yau. Fashewa tayi da kuka tare da komawa upstairs, ɗakin da ta fito nan ta koma ta faɗa ƙan makeken bed. Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun wace irin masifa ce wannan? Ya za'a rabata da komai a rayuwa saboda kawai Allah ya jarrabeta da soyayyar Imran? Yanzu wane hali Imran yake ciki? Tabbas tasan yau shan beer sai abinda hali yai dan tasan tabbas besan mahaifinsa yasa a kawota nan ba. Wayar landline ɗin da ta hango tayi saurin zuwa ta ɗauka, lambar gidansu tasa sai dai taki yi, ta kira ta Imran itama taki yi da alama an katse duk wata hanya da zata ba damar kiran wani. Tashi tayi tana kuka ta shiga toilet, alwala tayo tazo tayi sallolin da ake bin ta, tana idarwa ta fito daga ɗakin kai tsaye ta nufi hanyar fita, Mama Rabi na ganinta amma bata ce mata komai ba. Rahama ta buɗe ƙofar tana hawaye yau ba zata sake kwana a garin Abuja ba, duk yadda zatai sai ta koma Kano. Sojojin dake barbaje a gidan sune suka tayar mata da hankali, ta daure ta fara tafiya tana zatan ba zasu kulata ba, tsabar girma da gidan ke da shi gashi kuma yasha shuke-shuke da suka ƙawata gidan hakan yasa Rahma bata san inda gate ɗin gidan yake ba. "Madam ki koma ciki." Cewar wani ƙatan soja da harshen nasara yana yi mata wani kallo. Jikin Rahama ya fara rawa bakinta yana mugun kadawa tace. "Ina san phone zan kira Imran please." Shaye da toka yai taku biyu zuwa gabanta yana ɗora mata bakin bindiga a kanta, zuciyarta tai wani irin bugu ta juya ta koma tana fashewa da kuka. "Me yasa yanzu iyaye suke takurawa ƴaƴansu wajan neman miji ko mata? Me yasa idan akwai mutunci tsakanin iyaye suke rawar jiki wajan bawa ƴaƴansu aure koda kuwa su yaran basu so? Me yasa idan kuma basa mutunci duk irin soyayyar da ƴaƴansu ke yiwa juna basa sporting nasu? Yanzu me nayi dana cancanci haka? Na hakura da iyayena saboda soyayyar da nake yiwa Imran Matawalle, me yasa yanzu za'a baro ni daga mahaifata, a kuma yanke min jin daɗin karatun da nake ji dashi cikin rayuwata? Why? Why Matawalle zai yi min haka?" Tayi maganar tana sakin wani sabon kukan......
*LITTATTAFIN Albi NA KUƊI NE, KIBIYA 500 KI KARANTA ABINKI CIKIN KWANCIYAR HANKALI. DAN ALLAH KUYI MANA ADALCI KARKUCI AMANAR KASUWANCI MU.*
#Asmy b Aliyu
#Hajja ce
#Imran matawalle
#Rahama Galadanci
#Team Albi
#Haske Writer's Association..
[11/12, 9:35 AM] Asmy B Aliyu😘: *ALBI....*
(My Heart❤️)
NA
*ASMY B ALIYU*
DA
*HAJJA CE*
PAID BOOK..#(500)
*Account Details*
0004157137
*Jaiz Bank*
*Asma'u Buhari Aliyu*
Shaidar biya ta
08086207764
*Katin waya ta MTN.ta 07043079282 shaidar biya ta 07065283730 view WhatsApp*
*Areewabook*
https://arewabooks.com/chapter?id=6362e614d52c9563f327d94f
22.....
Bin farin hankacif ɗin kurum yake da ido, tunani kawai yake yana san tuno wanda ya taɓa gani dashi a hannunsa yanzu kuma ya ganshi acikin motarsa. Runtse idanuwa yayi da sauri ya buɗe idon saboda tunawa da yai, tabbas Misbahu ne, ya faɗi sunan da murya marar amo. Yasan duka cikin yaransa babu mai hawar masa mota, ya aka yi hankee ɗin Misbahu yazo cikin nan? Ya kalli ɗayan ya'n kunnen Rahama, yana zaune cikin parlorn yayi crossing legs ɗinsa yayi mugun haɗe rai gamida karkadasu. A hankali Misbahu ya shigo parlorn, ayadda Imran Matawalle keyi masa wani irin kallo yasa ya gigice ya fita hankalinsa wani irin fitsari yaji yana cika mararsa jin yake tamkar ya koma. "Waya baka izinin ɗaukar min mota na?" Imran yai magana cikin serious ɗinsa." Misbahu ya zaro ido yana dafe kirji yace. "Ayaushe kuma hakan ya faru?" Imran ya tambaya da kakkausar murya yana yi masa wani irin kallo, "Magana ta karshe idan kayi min qarya zanyi bala'in baka mamaki, haka kuma zaka rasa aikin ka duka." Babu abunda Misbahu ke haɗawa banda gumi dan yana matuƙar kaunar aikin nan da yake a ƙarƙashin Imran Matawalle. Duk da Matawalle na biyan su albashi mai tsoka haka yana samun alkhairi a wajan Imran, dan haka zai fidda kayan sakawarsa ya baiwa Misbahu su, sosai kuma yake yi masa alkhairi sabida mutum ne mai alkahirin gaske. Zube gwiwowinsa yayi dan da yarasa aikin sa kara ya faɗi gaskiyya yasan idan ya faɗi gaskiyya Imran bazai bari Matawalle ya koresa ba. "Nayi alkawari zan faɗa maka komai da komai, amman wallahi ba laifina bane nima umurnin maigirma Matawalle nabi na aikata hakan." Da mamaki Imran ya kallesa gamida girgiza kai jin ya faɗi sunan mahaifinsa. A nan Misbahu ya warware masa yadda Matawalle ya bashi umurnin yaje ya ɗakko masa Rahama ya tabbatar masa da cewa yanxu haka tana garin Abuja. Ya ƙarasa maganar yana kallon Imran wanda ya shiga shock da tashin hankali ya hanasa magana, "Jeka." Ya faɗa yana daka masa tsawa da sauri Misbahu ya miqe tsaye ya nufi ƙofa addu'a kawai yake Allah yasa ba ƙarshen samun sane yazo ba. Imran Matawalle kuwa, kwantar da kansa yayi cikin soofa yana sauke wani irin numfashi, tun a daren ranar yayi booking ɗin flight da zaije Abuja ɗan bazai iya tuki a mota ba, da kyar ya samu jirgin 12 na rana, gaba ɗaya tsawonsa yayi masa yawa, tun a daren ya karbi wayar Misbahu ya kira Al'ameen yazo ya kawo masa wayoyinsa duka. Washe gari karfe tara na safe ya nufi part ɗin Matawalle baya parlornsa sai Mommy ya samu a parlorn tamkar baya so ya gaisheta ya faɗa mata gobe Maheera zata dawo zata biyo jirgin karfe 8 na dare. Wani kallo Mommy ta riqa yi masa tamkar yana magana da dutse haka tayi masa banza. Matawalle ne ya fito cikin shirin fita cikin bakaken Italyn suit, Imran ya karaso gabansa ya basa side hug yana faɗin "Good morning daddy." "Good morning 2 Imran Matawalle." Imran ya shafa kansa yana faɗin "Ya karfin jikin." "Na samu sauqi sosai." Tare suka isa dinning area Mommy na gama serving ɗin Matawalle tabar parlorn dan idan ta cigaba da kallon Imran a wajen zata iya mutuwa. Yanzu sabida Imran Matawalle ya soke tafiyar da ta shirya yi da daddy, wannan tafiyar Mommy taso suyi ta da Matawalle kwana biyu babu kasar da suka leqa, Imran ya toshe duk wata kofar da xata shakata acikin rayuwar aurenta, yanzu kam lokaci yayi da zata cirewa mai girma Matawalle wannan soyayyar da yake yiwa Imran shekara ashirin kenan da aurensu Matawalle yana raba soyayyarta da Imran, soyayyar ma da yake yiwa Imran ɗin tafi ta ta yawa da ita da ƴaƴanta. Lokaci yayi da xata tsinka wannan soyayyar ta dawo da ita kan ƴaƴanta. Shiru Imran ɗin yayi sai juya spoon ɗin hannunsa yake yi, Matawalle ya kallesa da fuskar damuwa yake faɗin. "Me kuma ya faru?" Imran ya kwantar da kansa jikin kujera, baya son Matawalle ya fahimci yasan inda Rahama take, murmushi ya kirkiro yana faɗin. "Kawai kaina na ciwo daddy." "Harda wannan damuwar da kasa aranka ba dole kanka yayi ciwo ba, ka kwantar da hankalinka zan sa a nemo maka yarinyyar nan a duk inda take." A hankali Imran ya shafa sumar kansa yana faɗin "Nagode Daddy." Har wajen mota ya raka Daddyn nasa haka yayiwa security umurni akan subar Imran ɗin ya fita tunda yasan duk iya nemansa ba zai san inda Rahama take ba, shi kuma dama Imran abunda yakeso kenan. Kai tsaye wajen Al'ameen ya wuce suna zaune acikin parlorn sa yana zuqa sigari a hankali yana lumshe ido xuciyarsa na wani irin raɗaɗi yasan a duk inda take bata cikin kwanciyar hankali, meyasa Daddy zai yi masa haka? ya faɗa zuciyarsa na tafasa haka jijiyoyin kansa suka fito sarari ya ɗauki alwashin bazai dawo da Rahama Galadanci cikin garin Kano ba sai da igiyar auren sa akanta, zai kawo karshen wannan rigimar dake tsakanin Matawalle da Galadanci. Al'ameen ya girgiza kai yana faɗin "Look my Friend wannan fa ba shine solution ba, wallahi Imran kar kayi abunda zai tarwatsa rayuwarku duka daga kai har yarinyyar nan, musamman ma ita da take mace, rashin albarka acikin aure yana iya ja....." Cikin tsawa ya katse Al'ameen yana yi masa wani irin kallo. "Idan bazaka faɗi alkahiri ba malam kayi shiru dan Allah, kuma aurena da Rahama babu inda ya zama haramun albarka kuwa kar Allah yasa su saka albarkar suga idan zamu lalace, alhamdulillahi inada kuɗin da xan iya kula da Rahama da ƴaƴan da zamu samu, zan bata duka wani farin cikin da take nema ka faɗa min sai kuma me xata nema? Batana dani ba? mune da narasa, Insha Allahu nasara na nan tare damu a duk inda zamu taka ƙafar mu.." Kallonsa Al'ameen keyi yana girgixa kai yake faɗin. "Bazaka iya bawa Rahama farin ciki ba Imran sam bazaka iya ba, Iyayenta sune farin cikinta koda tana tare da kai zuciyarta da duka farin cikinta yana wurin iyayenta dan tana son iyayenta yadda take sonka, sannan duk bazata iya rabuwa daku ba, ta samu wani bangare na ta rasa wani haka kake tunanin zata samu farin ciki?" Al'ameen ya girgiza kai yana faɗin. "Dukan ku bazaku yi farin ciki acikin rayuwar auren ku ba." Miqewa Imran yayi afusace ya nufi ƙofa yana jin maganganun Al'ameen ɗin suna tabasa, "Auh bazaka tsaya na saukeka a airport ɗin ba." Yana jin Al'ameen ɗin amma yayi masa banza.
***********
A hankali Mama Rabi ta turo ƙofar room ɗin da take, hannunta ɗauke da ɗan madaidaicin tray ta ɗorasa akan center table dake tsakiyyar parlorn ta kalli Rahama wacce ta dunkule kanta cikin duvert sai rawar sanyi take tayi, kuka kuwa har taji babu daɗi, ga wani irin ciwo da kanta keyi, Mamah Rabi ta zauna a gefen bed ta kira sunanta a hankali, banza tayi mata, a hankali ta janye duvert