Header Ads
Showing 117001 words to 120000 words out of 139785 words

Chapter 40 - Albi Book Complete document by Hajjace.txt

Ads the beginning of article before Image

11 Jun 2024

1015

Ads at the middle of Article

tunanin Imran Matawalle a ranta. Shirye-shiryen zuwa bikin Farooq Galadanci sukeyi, Hajja tace ta shirya su tafi tare Rahaman tace ita dai zata zauna gidan Hajiya Babba har suje su dawo. Ummi ta goyi bayan Rahama sosai tana da juna biyu tasan kuma gidan cike yake da ƴan uwan Mami kar a riqa watsa masu habaici. Ana gobe zasu tafi Ummi ta ɗauki Rahama a mota har gidan Hajiya Babba dake Hotoro. Sosai Hajiya Babba ta shiga hidima da ita, cikin kwana biyu da tayi a gidan Hajiya Babba amai da zazzabin dare ya dawo mata musamman idan ta shaki kamshin girkinsu ko kaɗan bata kaunar spaces ɗin da suke sakawa a abinci, kamshinsu yana matukar ɗaga mata hankali, dan haka kullum tana kwance a ɗakin Aunty Kausar bata yadda ta sauko ƙasa. Sannan Hajiya Babba ta hana ƴan aikinta saka spaces ako wane irin girki duk saboda Rahama bata so, gata bata iya cin abinci, sai kayan kwalam, tayi missing ɗin kokon da Hajja ke dama mata da hannunta har Aunty Kausar ta dama mata ta faɗa mata wannan bai kai na Hajja ba. Kwanan su Hajja huɗu a Abuja suka dawo Kano ranar da suka dawo Rahama ta koma.....


************
Kwanan Yusoof matawalle biyu a Kano ya koma daman saboda Ilham yazo wanda Imran yasha mamakin yadda Yoosuf ɗin yake wani rawar jiki da ita, ana gobe zai koma ya nemi Imran ɗin da ya rakashi gidan Aunty Azeezah Matawalle, Imran ya zille yana yi masa wani kallo yake faɗin. "Wai kai da gaske sonta kakeyi da aure?" Yusoof ya ɗage masa gira alamar tabbatarwa. "Ban baka shawara ba duka-duka shekarun Ilham nawa Yusoof? sa'ar su maheera ce fa? ai sai ta rainaka." Yusoof yayi rolling eye's ɗinsa yana faɗin. "Irin su sunfi ai. kai naga ai ƙatuwa ka kwaso." Lokaci ɗaya kuma Imran ya haɗe rai yana faɗin. "Ni dai bazanyi rakiyyar nan ba haka kurum yarinyya ta raina ni." Yadda yayi maganar ne yaba Yoosuf dariya sosai. Shima cikin sati biyu yagama shirin fita india, haka yasha faɗa sosai a wajen daddy na sakin Humaidah da ya yi, Mommy kan ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba. Amman taga ko ajikin Humaidah sai taga ma Humaidahn ta zamar mata wata sabuwar mutum duk wani rawar kai ta sauke shi. Yaje yayiwa Hajiya babba da Aunty Kausar sallama haka ya turawa Aunty kausar naira miliyan 3 a account nata akan Rahama tayi hidima dasu idan sun kare su kira shi. Wani iri suka rinqaji da zaya tafi musamman Hajiya Babba dan tasaba da Imran ɗin na kwana biyu, sallama da fatan alkhairi kawai sukayi masa. Aunty kausar ta kira Ummi ta faɗa mata yadda sukayi da Imran ɗin, itama Ummi sai taji babu daɗi ga Rahama kwance a gida babu lafiya yau gobe ciwo jibi lafiya haka aketa fama gashi sun koma school tayi wata irin rama ta ban mamaki wanda Ummi ta lura harda rashin Imran ɗin yana damunta. Haka Hajja tayi umurni akan Rahama ta riqa hawa motar da Matawalle ya kawo tana zuwa makaranta wacce sai da ta nunawa Abba ɓacin ranta sa'anann yabar Rahaman ta riqa jan motar zuwa school. Rahama tayi magana da Ihsaan akan sun rabu da Imran Matawalle Ihsaan ta jinjina al'amarin haka ta riqa bata shawara ta rage damuwa aranta ta riqa sallolin dare tana kaiwa Ubangiji kokenta idan Imran Matawalle alkhairi ne acikin rayuwarta zai dawo. Jin irin shawarwarin da Ihsaan ke bata taji wani irin kwarin gwiwa na shigar ta, sosai take ganin haske acikin lamurranta, yanzu kam burinta ɗaya a duniya ta kammala karatunta lafiya ta fito da kwali mai darajar da tasan Imran ɗin zaiyi alfahari da ita. Ko tana gida da wuya ta zauna a parlor, tafi zama a study room tasa littafai a gaba tana dubawa, sallar dare kuwa da karfe biyu tayi take miqewa tana kaiwa Allah kokenta haka tana yiwa Imran addu'a Allah ya tsareshi yabashi kariya a duk inda ya taka ƙafa. Tasan ko babu komai uba ne ga abinda yake cikinta


****************
6month leap......INDIA (Mumbai University) Ƙarfe huɗu na yammah agogon dake can ya buga, fitowarsa kenan daga lecture sanye yake cikin dogon wandon Armani baki da kuma farar rigar sanyi mai kauri taxi ta ɗaukeshi har cikin gidajen indian-villa, mai aikinsa mai suna urmi ƴar asalin ƙasar wacce bazata wuce shekaru ashirin ba a duniya ta karɓi jakar hannunsa tana yi masa sannu da zuwa cikin harshen turanci. Kai tsaye master bedroom ya nufa ya faɗa kan bed yana lumshe idonsa a hankali yana jin cikinsa na wani irin kukan yunwa, wayarsa ce ta fara ringing ba tare da ya duba mai kiran ba ya ɗaga, jin muryar Maheera Matawalle yayi a tsakiyyar kansa, yana sauke ajiyar zuciya "Maheera Matawalle..!" Ya faɗa can ƙasan makoshi. A shagwaɓe take faɗin. "Da gaske yaya bakazo graduation ɗina ba?" Tayi maganar cikin muryar kuka. Ya girgiza kai tamkar yana kallonta yake faɗin. "Daddy da Mommy zasu zo ai, kuma karatun mu ya ɗauki zafi am sorry Mahee." Ya faɗa cikin muryar rarrashi. "Toh kabar Bassam yazo dan Allah." Ya girgiza kai cike da gajiya yake faɗin. "U Are very stupid Maheera Matawalle suna exams ɗin ne zaizo? please kibarni yanxu na dawo school." Zatayi magana ya kashe wayar duka.


NIGERIA.
Akan hanyarta ta dawo daga School Ra'is ke jan motar tana zaune a front seat mai yalo ta gani gefen hanya ta yiwa Ra'is umurni akan su tsaya zata siya, lokaci ɗaya ya haɗe rai ya juya a fusace yake faɗin. "Wai ke dan Allah komai idan kika gani sai kin tsayar damu kan titi?." Wata irin harara take yi masa tana nuna masa yatsunta guda uku, ya qara haɗe rai sosai ya riga da yasan mai take nufi wato ta bashi shekara 3 da haihuwa. Afusace ya fito daga motar ya nufi inda mai yalon yake, Kwantar da kanta tayi jikin seat ɗin tana shafa cikinta ɗan watanni 8 da yayi wani irin girma tamkar lokacin haihuwarsa yayi. Ledar Ra'is ya jefa mata ajikinta sannan yayiwa motar key da wani irin speed suka bar wurin duk masifar da takeyiwa Ra'is ɗin akan ya rage gudu ƙin saurareta yayi. A fusace ta fito daga motar ta kwace car key din hannunsa tana faɗin. "daga yau na haramtawa kaina shiga motarka Ra'is." Da haka ta nufi ɓangaren su afusace tun a ƙofar shiga parlor take kwalawa Ummin su kira, ji tayi wani abu ya jata, runtse ido tayi tana kiran sunan Allah a ranta, jinta kawai tayi a hannun mutum, mutumin da bata taɓa tunanin ta gansa a wannan lokacin ba. Zuciyarta na wani irin bugawa take kallon fuskarsa da babu alamar fara'a acikinta. Rumana tana zaune cikin parlorn Ummi tana kallonsu ji tayi tamkar zata haɗe zuciyarta duka sabida kishi. Jin muryar Ummi akansu yasa yayi saurin sakinta a masifance take kallon Ummi tana faɗin. "Ra'is bazai kara kaini school ba Ummi kasheni ya soyi a hanya." Cikin daure fuska tace da ita "Meyasa bakya bin komai a hankali ne ke?" Ummi ta faɗa cikin ɓacin rai. "Da ƙin faɗin a wajen nan kika jima kanki ciwo da ɗan dake cikinki fa?" Wani irin harbawa kirjin Farooq Galadanci keyi da sabon kishin Rahama a cikinsa wanda yaji yana cika masa zuciya. Juyawa tayi tabar parlorn zuciyarta na mugun tafasa daman kuma Ummi tasan fushi tayi abu kaɗan za'ayi mata ta hasala koda kuwa bai taka kara ya karya ba. Kai tsaye ɓangaren Hajja ta nufa tana jin turaren Farooq Galadanci na manne a kayan jikinta. Ummi ta kalli Rumana da murmushi cikin fuskarta take faɗin. "Jeki yi serving mijinki daughter." Rumana ta ɗaga kai gamida bin umurnin Ummi. Ummin na wucewa Farooq zai riqo hannunta ta wani fisge a fusace ta nufi cikin dining area tamkar zata tashi sama, suma basu daɗe da shigowa Kano ba, yazo yin wani aiki ne har na tsayin sati biyu, shine Abba yace su sauka a gidansa. A ɓangaren Matawalle kuwa duk wasu kayan barka da na jariri ya gama ya gama tanadars, shima Imran ya aiko da kayan babys kusan trolley biyu, haka kuma ya turawa Maheera matawalle kuɗi akan ta duba wasu a ƙasar marocow dama Aunty Kausar ta tabbatarwa da Imran cewa anyi scanning har kusan 3 duka macce ake nuna masu zata haifa, duk garin Allah ya waye sai Imran ya rubuta kwanakkin da suka rage na little Albi wanda zata zo duniya a cikin diary ɗinsa. Haka babu ranar da zaya wayi gari baiyi tunanin Rahama aransa ba. A ɓangaren Daddy Matawalle kuwa shirye-shiryen kara aure yakeyi, sannan ya faɗawa Mommy kudurinsu, bazawara ce tana da ƴaƴa uku maza biyu suna da aure kuma sai macce ɗaya dake jami'a a garin Abuja, mahaifinsu yayi zaman aminci tare da daddy. Auren Matawalle yayi mugun ɗaga hankalin Mommy duk irin barazanar da ta riqa yi masa ko kulata bai yi ba, ɗaurin auren kuma sati biyu masu zuwa haka ya shirya masu tafiya ƙasar marocow graduation ɗin Maheera idan ya dawo kuma Mommy ta zabi ƙasar da takeso suje su haɗo kayan lefe ita da Amaryar. Da farko cewa tayi bazata ba har sai da Humaidah ta faɗa mata ta godewa Allah, Allah yana sonta da rahamarsa daddy ya buɗe baki ya faɗa mata bataji a wani wajen ba. Kawai ta tuba tabi Allah da Manzon sa ta nemi gafarar daddy da Imran a duka abubuwan data aikata masu a baya. Ranar da Humaidah ta faɗa mata haka kasa bacci tayi duk lokacin da taso ta tunkari Daddy da maganar akan ya yafe mata sai tsoro da fargaba su hanata yin hakan....




(Complete Decuments)
*WAMINAL HUB* #500
*ZO GARENI* #300
*NIDA RAHEEMA* #300
*RAYUWAR AURENA* #300


#Asmy b Aliyu
#Hajja ce
#Imran Matawalle
#Rahama Galadanci
#Farooq Galadanci
#Yusoof Matawalle
#Team Albi
#Haske Writers Association...
[12/14, 5:20 PM] Asmy B Aliyu😘: *ALBI...*
(my heart❤️)


*ASMY B ALIYU*
DA
*HAJJA CE*👈


PAID BOOK..#(500)


*Account Details*
0004157137
*Jaiz Bank*
*Asma'u Buhari Aliyu*
Shaidar biya ta
08086207764


*Katin waya ta MTN.ta 07043079282 shaidar biya ta 07065283730 view WhatsApp*


50....


Atsai tsaye take yin breakfast ɗin, kai daga ganin yadda takeyi kasan yunwa takeji kuma tana so tayi sauri dan ta kusa makara gashi practical suke yi lecturer ɗin bashi da mutunci indai ka ƙara ko one second ne bazai barka ka shiga ba. Ganin lokaci bazai barta ba yasa kawai ta ɗauki handbag ɗinta da car key na motarta, ko su Ummi bata shiga ta yiwa sallama ba ta nufi ƙofa. Farook Galadanci ne ya fito shima cikin shirinsa na fita, kallo ɗaya Rahama tayi masa tai saurin kawar da kai, tun kafin ta ƙarasa tayi unlock ɗin ƙofar motar tana zuwa kawai shiga tayi tare da gyara zamanta tana lumshe ido. Cikinta kawai take kallo wanda yai mata wani irin shirgege ya cika wajan sitiyarin ma kaɗan ya rage ya tabo tsinin cikin. Ra'ees bashi da kirki yana ganinta tana shiryawa koya ce zai kaita. Farooq Galadanci ne ya iso wajan ya riƙe murfin motar yana kallanta, cikin turo baki ta gaishe da shi ta fara kunna motar yace. "Muje na ajiyeki." Sosai take buƙatar taimako amma saboda faɗin rai sai tace. "Kabarshi kawai Yaya Farooq zan iya." Cike da rashin damuwa yai kamar zai juya wanda hakan ya faɗarwa da Rahama kirji har ta fara tunanin yadda zata tuka motar a cikin ƴan sakanni, sai kuma taji yace "Ki fito muje." Babu yadda zatai haka ta fito suka shiga motarsa, Rumana tana can daga window tana kallansu wani irin takaici yana damunta kamar zata fashe da kuka, gaba ɗaya taji Kano tayi mata zafi ji take tamkar zata kashe Rahama ganin yadda Farooq ɗinta yake ta wani lallaɓata. Akan idanunta suka bar gidan ta jiyo cikin ɗaki tana sakin tsaki a karo na babu adadi. Da yake safiya ce masu saye da sayarwa basu fara fitowa ba hakan yasa sukaje school ba tare da tace a siya mata komai ba. Yana direta yace idan ta kammala ta kirashi yazo ya maida ita gida, tayi masa godiya sannan ta wuce tana sauri hango lecturer ɗin ya nufi lab ɗin. Ba ƙaramin daɗi practical ɗin yai mata ba, bata kuma sha wata wahala ba sakamakon Ihsan taje mata da agwaluma da kantun gana. Suna fitowa kuwa ta kira wayar Yaya Farooq shima a lokacin ita yake jira ta kirashi saboda ya gama, babu ɓata lokaci ya ɗakkota suka dawo gida. Rumana dake zaune a parlorn Ummi tana danna waya taga shigowarsu, babu wanda taiwa sannu kawai ta tashi ta nufi masaukin su. Bayan Farooq ya tsaya sun gaisa da Ummi kai tsaye ya wuce masaukinsu, yana shiga ya tarar da Rumana ta cika tayi fam kamar zata fashe, ya kalleta yana ƙoƙarin riƙo hannunta ta wani koma gefe tana maida su baya. "Lafiya? Wani yai miki wani abun a gidan?" Ya faɗa sounding so cool, ta wani sha toka tare da kallansa tana cewa. "Da kasani baka taho dani ba, kawai ka ajiye ni a gefe kana soyayya da tarairayar tsohuwar budurwarka, duk abinda kuke yi ina kallanku ni bazan ɗauki cin fuska ba wallahi." Da wani mugun mamaki Farooq Galadanci ke kallan matar tashi, ya dinga murza lallausan gemunshi fuskarsa a tsuke yake faɗin. "Baki da hankali Rumana? Wace irin magana kike gaya min haka?" Cikin zafin rai tace, "Ai ba karya nayi ba Farooq, tunda muka zo kake wani lallaɓa Rahama. Haka fa da tazo faduwa ka wani tareta a jikinka bayan kuma kai ba muharraminta bane idan ba iskan....." Bata kai ga ƙarasawa ba ya ɗora hannunsa kan fuskarta ya bata wani kyakkyawan mari, take Rumana ta daura hannu a wajan tayi shiru tsabar hankalinta da ya gushe na wani lokaci. Muryar Farooq takeji cikin masifa da bala'i yake faɗin. "Bakida hankali ne Rumana? Ɗan iska kika maidani ko me? Kishi hauka ne da zaki dinga cewa ta faɗo jikina? Ko meyasa wani lokacin mata bakuda tunani? Bakiga Rahama ciki gareta ba na wani ba nawa ba amma ki dinga maidani wani ɗan iska, ya isheki Rumana bana san irin waɗannan abubuwan." Kuka ta sake fashewa dashi yana jinsa har cikin zuciyarsa sai dai bazai iya bata hakuri ba saboda yana so ta gane abinda tai masa baiji daɗi ba. Har ya kusan shigewa bedroom yaji tana faɗin. "Shikenan bazan faɗi gaskiya ba, ai Rahama yanzu bazawara ce na sani ko har yanzu kana tare da santa." Farooq ya saki wani murmushin takaici ya juyo yana kallanta cike da tausayi yace. "Ya rage naki ko da har yanzu ina san Rahama ke baki isa ki hanani ba, kuma ko nayi niyar auranta Rumana bazaki iya hanani ba foolish girl." Yana faɗa ya shige cikin ɗakin tare da rufe ƙofar, kai mata dai akwai takalo tashin hankali. Tana nan tana banzan kishinta bata san shi ganin cikin jikin Rahama wani irin bakin ciki yake ji ba. Wanka ya shiga wata irin yunwa yakeji amma da yake Rumana matar bahaushen zamani ce daga dawowarsa ta ɓata mishi rai har yaji baya jin yunwar. Ita kuwa zama tayi a parlorn tana ta tirƙar kukanta tsanar Rahama na yi mata yawo cikin lungu da sako na cikin jikinta. Gabaki ɗaya Mommy ta rasa nutsuwarta komai bayayi mata daɗi a cikin duniyar, wannan auran na Matawalle ba ƙaramin girgizata yai ba musamman da aka turo mata hotunan amaryar gani tayi tamkar budurwa bazaka taɓa zaton tayi aure bama bare ace ta haifi zabga-zabgan yara ba, irin matan nan ne da ake yiwa auran wuri kuma suka samu gidan hutu da tattali. Humaidah da Maheera ne ke sanyaya mata zuciya sai dai ganin Matawalle harkar bikinsa da siyasar kawai yasa a gaba yasa ta kasa sauraran su bare ta fahimci abinda suke nufi. Yauma zaune take a cikin bedroom ɗinta Matawalle ya kira wayarta, ganin sunanshi kaɗai sai da gabanta ya buga saboda tasan zancen bikin shi zai yi mata, daurewa tayi ta ɗauka batace komai ba taji yana faɗin. "Yau zasu zo jere a can sabon gidan dana gina a rellway, idan babu damuwa ina so nan ma da kike ciki a zuba miki komai sabo." Tamkar Mommy tace bata so, sai dai tayi shiru tana haɗiyar wani yawu mai bala'in ɗaci. Goshi ta dafe tana faɗin. "Yadda kace haka za'a yi." Matawalle da ya fara tsinkewa da lamarin Mommy yaja numfashi, gaba ɗaya ta sauya masa, tunda yai mata maganar aurensa shikenan duk abinda ya faɗa bata masa jayayya kamar a baya. Tun daga lokacin da Rumana suka samu saɓani da Farooq Galadanci shikenan ya tattare duk wata kulawa tashi ya ɗora su akan Rahama wanda yayi hakan ne dan ganin Rumana zata doke shi ko kuwa zata hanashi yiwa Rahama magana, abu ɗaya ne ta hanashi kanta wanda hakan be wani dameshi ba bare yaje ya lallaɓata, tayi kuka harta gaji gani take Farooq baya wani ƙaunarta. Da yamma har wani ɗaukar Rahama yake a mota su fita, tayi shiru ganin abin yana damunta yasa cikin dabara suna aiki a kitchen ita da Ummy take tambayarta ta hanyar cewa. "Oh Ummy yau kuma ko ina su Rahama suka lula? Sunyi dare sosai ƙarfe takwas fa yanzu." Ummy ta gama markada fura da nono tana zuba madara take faɗin. "Kin gani dai Ruma daga fita motsa jiki, koda yake jiya shopprite tace ya kaita sun zazzagaya da ƙafa yau kam su suka sani." Rumana ta cije lips maza basu da mutunci idan suka so, saboda ɓacin rai bata bari sun gama aikin ba ta koma ɗaki ta haɗa kayanta cikin trolley. Yana gama yin parking Rahama ta nufi sashen Hajja shi kuma ya nufi masaukin su nan ya tarar da Rumana ta gama haɗa kayanta, da mamaki yake kallonta yana faɗin. "Wannan kayan kuma fa?" Cikin ko'in kula tace. "Gida zan koma gobe bazan iya ci gaba da zama a nan ba." Farooq yasan duk saboda abinda yake yi ne yasa ta shirin komawa, xama yayi tare da riƙo mata hannuwa ya jata jikinsa yana faɗin. "Duk mai yai zafi madam? Kin min laifi kuma kina fushi dani sannan kina so ki sake aikata wani laifin." Hawaye ne suka ziraro mata, bata damu da sharewa ba tana

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads