Showing 138001 words to 139785 words out of 139785 words
Chapter 47 - Albi Book Complete document by Hajjace.txt
zata nufi ƙofa taga Imran ya sakawa ƙofar key. Wani irin kallo take yi masa tana cewa. "Ka buɗe min zan fita malam." Ta faɗa cikin tsiwa, bai ko kalleta ba da zuciya ya nufi kan bed yayi kwanciyyarsa daman kuma already yaci kazarsa, ya rufe har fuskarsa ko wutar ɗakin kashewa yayi yabar masu dim light. Baki ta buɗe tana kallonsa a fusace. Jin little Aysha ta fara kuka yasa ta nufi kan soofa ta zauna har lokacin Ayshaa ihu take zubawa tun kafin ta fitar mata da nonon, a fusace Imran ɗin ya miqe zaune yana faɗin. "Kina jin yarinyata na kuka bazaki ji da ita ba? Zan iya ɗaukar komai a gidan nan amma banda kukanta." Ya faɗa da ɗan ɗaga murya. Hakan ba ƙaramin ɓatawa Rahama rai yayi ba, tana baiwa little Aysha Nono hawaye na zuba acikin fuskarta. Haka Imran ya riqa jin sheshekar kukanta, duk da yana taɓa masa zuciya amma yayi mata banza. Sai kusan 1:00 ya farka yana jin fitsari ya kunna fitilar ɗakin haske ya gauraye ko'ina, ya kalli Rahama dake bacci little Aysha na kan jikinta, a hankali ya ƙarasa ya zare little Aysha ya mayar da ita kan bed, hakama Rahamar ya ɗagata duka ya mayar kan bed. Bayan ya fito daga banɗakin rungumeta yayi cikin jikinsa yana jin yadda ƙamshi ke fita acikin jikinta. Dakyar ya rabata da kayan jikinta dan shi bazai iya kwana da ita da kaya ajikinta ba, yabarta daga pant sai bra, a haka ya koma bacci tana manne acikin jikinsa. Tsabar rashin baccin da bata samu da kuma gajiyar da tayi yasa bata san yana yi ba. Da Asuba da taji ta babu kaya a jikinta sannan kuma tana manne cikin jikin Imran ba ƙaramin fusata tayi ba, cikin fushi ta fizge masa hannu daga riƙon da yai mata ta fice daga kan bed ɗin. Sai da ya kammala wankansa yai sallah sannan ya buɗe ƙofar ta fice. Tun daga ranar bata ƙara yadda ta kwana a ɗakinsa ba, da tayi magrib take shigewa ɗakinta ta rufe bugun duniya Imran keyi bazata buɗe ƙofar ba. Hakan kuma ba ƙaramin fusatasa tayi ba, duk da yasan yayi mata laifi kuma ya bata hakuri shin ita bata yafiya ne? shima ɓacin rai yasa ya furta mata haka, furucin kuma yasa sai lokacin yasan da Rahamar jinin A Galadanci na yawo saman kanta. Babu abunda ba tayi a gidanta tamkar rayuwarsu ta baya, tun daga kan breakfast, lunch har dinner tanayi, sai dai yadda ta aje haka take dawowa ta kwashe kayan ta. Kusan sati ɗaya suna wannan wasan dashi ko little Aysha yabar ɗauka duk sabida ita.
************************
Yadda Rahman taga maheera Matawalle ta shigo cikin parlorn nasu yayi mugun ɗaga hankalinta, Maheera na ƙoƙarin saita numfashinta take faɗin. "Yaya Aunty Rahama!" Wannan lokacin Rahama ji tayi komai na jikinka ya tsaya cak! ta xaro duka idanunta gabanta na mugun bugawa sai gata gaban Maheera Matawalle tana faɗin. "Meyasa mesa?" Cikin tashin hankali Mahee tace. "Bashi da lafiya yana asibiti." Nan take hawaye suka fara rolling kan fuskarta da gudu ta nufi stairs tana haɗa hanya, hijab babba ta saka ta tarar da Maheera ta ɗauki little Aysha. Rahama ta karɓi car key ɗin motar Maheera suka fice. Itake driving Maheera ta kalleta tana faɗin. "Ki natsu dan Allah Aunty Rahama.." Wani irin tura ƙofar sukayi sai kuma Rahama ta juyo da mamaki tana kallon Maheera itama Maheera ido ta fiddo zatayi magana saqo ya shigo a wayata, buɗewa tayi da sauri Rahama, ta fisge wayar tana kallon sakon da Imran ɗin ya turo. "Meyasa zakije kiranta Mahee? are you stupid? an faɗa maki ta damu da rayuwarta ne? Toh na bar asibitin yadda bata buƙatar gani na nima haka." A Sanyaye Rahama ta miqawa Maheera wayar ta juya ta nufi ƙofa. Wannan karon Maheera ce ta karbi tukin suka nufi gidan Matawalle, Ita dai har lokacin Rahama bata magana tana rungume da Little Aysha a jikinta. Dama kuma Aunty na gidan, dan haka har part ɗin Imran sukaje baya ciki, jiki a sanyaye suka shiga part ɗin Mommy wanda ya zama na Aunty yanzu, itama tun bikin Imran bata koma Abuja ba. Maheera ta kalli Rahama da sauri tana faɗin. "Karki faɗawa Aunty komai muyi sallar magrib sai nasa driver ya kaiki gida Aunty Rahama, nasan lokacin yana gidan tunda yace min baya san kwanan hospital, and please Aunty Rahama ki kula dashi dan Allah." Sosai Aunty amarya tayi munar ganin Rahama, sai da akayi magrib Rahama tace zata koma Aunty tace ba tare da Imran ɗin zaku koma ba?" Rahama ta girgiza kai tana faɗin. "Yana clinic shima daga can gida zai wuce." Suka yi sallama Maheera ta saka driver ya kai Rahama gidanta. Ta daɗe tana bin motar Imran da kallo wacce ke ajiye a ƙofar gidan, da sauri ta nufi entrance ta shiga gidan, door dell ta shiga dannawa cikin minti biyu aka zo aka buɗe ƙofar, wayar hannunsa yasa yana haske fuskarta sabida babu haske a parlorn, ta rasa kuma dalilin da yasa babu hasken. Kallonsa kurum take yana sanye cikin kananun kayan da suka karɓesa sosai, hannu yasa ya karɓi little Aysha tabi bayansa tana neman ta inda zata hango rashin lafiyarsa.
Sama ya kai little Aysha ya sakata cikin kyakkyawan gadonta na yara ya kunna mata suratul baqara a wayarsa tare da ajiye mata kusa da kunnanta. Tun daga Saman yayi tsaye yana kallon yarda Rahama tayi tsaye a tsakiyyar parlorn nasu tana ganin yadda aka ƙawata parlorn da wasu irin flowers masu matuƙar kyaun gaske, ɗaga kai tayi tana kallonsa a hankali yake taka stairs ɗin tamkar mai tausayin ƙasa, da wata irin murya yake faɗin. "Happy bornday Albi, my Allah blees ur new age# Allah ya raya mana Aysha cikin aminci." Tsaye tayi tana kallonsa, shi kuma yana kallon reaction ɗinta, kamo hannunta yai har kan soofa ya kai ta ya zaunar da ita, hannu yasa ya sauke hijab ɗin jikinta yana bin dogon gashin kanta da kallo wanda yasha gyara. Wani ɗan ƙaramin kwali ya ɗakko yana buɗewa sai ga sarqar gold ta bayyana, da kansa ya saka mata sarqar a wuyanta wacce tayi mata wani irin kyau a jikin wuyanta. Bai bata damar faɗar komai ba ya nufi kitchen sai gashi ɗauke da cake da knife ɗin cutting ɗinsa, tare sukayi cutting cake ɗin da kansa ya saka mata a baki yana faɗin "Happy birthday one's again Albi......" Samun kanta tayi da gutsuro cake ɗin ta bashi ta haɗe rai tana turo baki. Murmushi yayi ya riqe hannun nata yana yi masa wani irin shan da takejinsa har cikin jikinta. Fisge hannunta tayi yana kallonta da idonsa dake cike da kaunarta, zatayi magana ya fisgota duka cikin jikinsa, zatayi magana yayi saurin haɗe bakinsa da nata. A wannan daren ya kara kafa wani tarihin da bazasu taɓa mancesa ba, Imran ya amayar mata da duk wasu sirrin dake cikin zuciyarsa ta yarda ta amince itace Albi ɗin Imran Matawalle. A wannan lokacin Rahama ta amince ta karbeshi a matsayin mijinta a karo na biyu.
5years leap.......
A hankali ya turo ƙofar room ɗin da take sukayi ido biyu, ya ware mata ido yana kallonta lokaci ɗaya ta fashe da kuka. Da sauri ya kalli kyawawan babys ɗin dake cikin gadon jarirrai waɗanda basufi a wanni shida da zuwansu a duniya ba. Imran ya jawota zuwa jikinsa yana wani irin smiling, ta shige cikin jikinsa tana masa kukan shagwaɓa take faɗin. "Anyi na farko anyi na karshe ba za'a ƙara maimaitawa ba wallahi." Ta faɗa sounding so very serious a muryarta. Ya kalli duka yaran da suke maza, kana kallon fuskarsu duka babu abunda suka baro na Imran ɗin, yace. "Haba my sweet Albi, anyi little Albi ɗina, yanzu kuma ga Abba da Daddy, please ki daure sauran Ummi da Hajja." Duka idanunta ta fitar tana muzurai ya fashe da dariyar farin ciki yana jawota duka cikin jikinsa yana sauke mata kananun kisses cikin wuyanta......
*Karshe......*
Alhamdulillahi anan mukazo ƙarshen book ɗin (Albi❤️) wanda tun daga farkon book ɗin nan har karshensa muna bawa duk wanda muka ɓatawa rai yayi hakuri dan Allah, komai na duniya baka rasa kuskure muma mun yafewa kowa. Wannan book ɗin it's not a free, dan Allah a kiyaye hakki, akwai ranar gobe kiyama.
*Sadaukarwa....*
Allah ya zama gatanku ya raya mana ku cikin amincinsa Ihsan, Areef, Jannat da Aydah. Allah's khair and blessings a duk inda zaku taka kafarku. We loves you....
*Tukuicin littafin Albi..*
Tukuici ne zuwa gareku. Ayusher Muh'd, Nana Diso da Billy s fari. Allah ya raya mana su Husnah dasu Muhammad cikin aminci,
Allah ya kawo mana little Albi cikin aminci@billy s fari muna miki babban fata, Alkhairin Allah ya kai maku a duk inda kuke. mun gode da kwarin gwiwa.......
*Godiya ta musamman*
Zuwaga groups ɗin Albi fan's da suka siya book ɗin mu na Albi, kuma saboda Allah basu fitar mana dashi ba. Mungode sosai muna alfahari da hakan Asmy with Hajja ce greeting u with respect.... Bye 👋
#Hajja ce 👈 Paid books...
#Zo GARENI #300
#Rayuwar Aurena #300
Free books
Musayar zuciya
Ɗa Nagari
Sawun giwa
Saɓanin so
Tattalin mace
Izgilanci
So.. So.. So on
#Asmy b Aliyu Paid books
#nida Raheema #300
#waminal Hoob #500
Free book
Dangin Juna
Abuuturub
Neesah Adeel
Wata Rana
Nida sakeena
Maheer
Tasneem
Laylah Khalifa
Hafsatul Ikraam
And the new one is👇
*Moohabatul Qalb*
Asmy b Aliyu
"Yaya Maina bazai taɓa sona ba Mama, shin wani irin wasa da rayuwa ne haka Abba ya ɗauke ni ya aura masa ita? kuma Addah Hafsat idan ta dawo fa? Kin san irin soyayyar da sukayiwa juna kuwa? Akwai dalilin da yasa Adda Hafsat tabarsa, amma meyasa bazamu jirata ba? The situation is getting worse.!" Ta faɗa cikin rawar murya still wiping off her tears. Ita dai Mama kallon ƴartata kurum take tana jin xuciyarta na matsewa wuri ɗaya da sabuwar qaddarar da zata hau kan yarinyyarta. Gara ta faɗa wuta ta fito da auren Maina saraki, ita kanta dauriya kurum take a gaban ƴartata..
(Zamfara Gusau)
#Falala hotel#
Tana shafa sumar kanta take faɗin. "Haba besty sabida nace karki auri Maina Saraki shine kika shiga wannan tashin hankali?'' Farida ta faɗa tana kallon Hafsat da duk bata cikin natsuwarta." Toh Besty ya kikeso na faɗawa iyayena? ya kikeso na faɗawa yaya Maina? nasan duka yanzu na karya masa zuciya bazai yafe min ba, ina sonsa tamkar yarda nake sonki besty, dukan ku kuna da muhimmanci a rayuwata." Shaye da toka Fareed a ke faɗin. "Ni dai bazan yarda ki aure sa ba, saboda zuciyata zata tarwatse ne kawai sabida kishi." Da haka ta fara wasa da kirjinta cikin wani irin salo, duk da ko kaɗan Hafsat saraki bata wani enjoying ɗin wasan, haka ta riqa beyewa bestyn ta suna faranta ran junansu.
The new year and new love and perfect romantic story.
*Moohabatul Qalbi*#🔥🔥🔥🔥
#moohabbatul qalb
#asmy b Aliyu
#maina saraki
#Hafsat Saraki
#Asmaa saraki