Showing 3001 words to 6000 words out of 139785 words
Chapter 2 - Albi Book Complete document by Hajjace.txt
kasa munyi latti ne? Kasa uniform kawai sai ka tsaya kana yiwa mutane nawa, dalla can ka fito ko sai Abba yazo ya, fara min faɗa yace nice babba?" Ra'is ya ƙarasa sanya rigarsa yana ɓalle botin yace. "Yaya Rahama wahala nasha a toilet, kinga yadda nai wani irin k..." Rahama ta juya tana cewa. "Banza ni basai ka gaya min kayan amai ba, kazo muyi breakfast kafin Abba ya sakko." Saida ya gama sanya safarsa da takalmi kafin ya sakko daga stairs ya biyota zuwa dining. Suna cikin yi Abba ya fito bayansa Ummi ce riƙe da jakarshi, tun kafin ya gama sakkowa yake faɗin. "Oya a tashi mu tafi."
Duk suka miƙe kowa ya ɗauki school bag nasa ya goya. "Allah ya bada sa'a." Ummi tai addu'a tana komawa ciki. Sai da Alhaji Abubakar ya fara zuwa wajan Hajja ya gaida ita sannan ya fito ya shiga mota. Ra'is ne a front seat Isa driver na wajan tuki, Rahama da Abba suna baya. Kokarin fita daga gate ɗin sukeyi, Farooq yai saurin zuwa gurin mota. "Abba bari na rakaku, idan naga school ɗin anjima sai naje na ɗakko su." Abubakar Galadanci yaji daɗi yake. "Thank you my beloved son, ɗakko motar sai ka biyomu." Juyawa Farooq yai, mota ya ɗauka Rahama zuciyarta tamkar konewa zatai, indai haka Yaya Farooq zai mata batajin zasu kai alaƙarsu tai musu nisa dan tun yanzu taji ba zata iya ba.
Abba na sauke su Rahma tai saurin shiga wa class ɗinsu cike da damuwa. Abba ya wuce wajan aiki, shi kuma Farooq ya koma gida suka sha hira shida Hajja. Ana tashin su break ya ƙarasa cikin makarantar, neman ta ya ware idanu yanayi, ganin ko mai kama da ita be gani ba yasa ya kuma kiran wayar ya tambayeshi, gaya masa ajin nasu yai hakan yasa Al-Amin ƙarasawa, ta window ya hangota zaune tayi shiru, yasa wata yarinya dake tsaye wajan door ta kirawota. Hango Al-Amin yasa Rahama tashi da sauri ta fito, bakinta yana rawa tace.
"Imran yana ina?" Wayar hannunsa ya miƙa mata dai dai lokacin Imran ya sake kira Rahama ta kalli wayar, my favorite friend tagani a rubuce, da sauri ta ɗaga hawaye na zirarowa daga idanunta tace. "Why Imran? Why?" Imran ya rintsa idonsa, kukanta da yakeji cikin kunnuwansa ya shiga sara masa kai yana faɗin.
"Sorry R Galadanci, kina zaton zanyi miki haka da gangan ne? Yanzu haka muna Russia, Daddy ya lura banayin abinda ya kawo mu ƙasar nan ya kwace passport ɗina da duk wani abu da yasan zan iya dawowa Nigeria, nasan randa kika koma gida Abba ko Ummi wani ya dokeki saboda kinzo gurina ba?" Hawaye basu dena zubowa a fuskar Rahama Abubakar Galadanci ba, jin muryarsa kaɗai yasa taji tana jin rigima tsantsa, duk kuwa da farin cikin da zuciyarta ke ciki, bayan hannu tasa tana gogewa murya so cool take faɗin. "Imran baka sona?" Tambayar ta zo mai a wani irin yanayi dan beyi expecting ɗinta ba a wannan lokacin, dan haka ya rasa abinda zai ce da ita. "I know kana ɗaukata like your blood sister, amma ni kuma..." Rahama Galadanci ta kasa ƙarasawa sai kuka da ya kwace mata. Cikin tashin hankali Imran Matawalle ya riƙe handle ɗin motar da yake tsaye ajikinta, ji yake tamkar ya fasa wayar ya ganshi a gaban Rahama. Besan mezai ce mata ba saboda shi kanshi har yanzu ya kasa tantance wane irin matsayi Rahama take dashi a ransa? Wace irin alaka yake jin zuciyarshi nayiwa yarinyar, kawai yasan dai tana da matuƙar muhimmanci a cikin rayuwarsa.
"Kaga Abba aure zai min da cousing brother ɗina." Cewar Rahma cikin wata irin murya, kirjinsa yaji ya wani irin harbawa cikin wani irin tsoro da fargaba ya dafe wajan da zuciyarsa take yadda yaji tana wani bugawa ba yadda ya dace ba. Muryarsa na rawa yace. "This can't be happen Rahama, wane mai ƙararren ƙwanan ne yake shirin kasancewa da abin hannuna? R baki sanar dashi cewa ke ɗin abin hannuna bace?" Imran Matawalle yai maganar tamkar zai fito ta cikin wayar saboda masifa. Da kakkausar murya yake faɗin. "Ki sanarwa da duk mai shirin yin wannan gangancin cewar ba'a taɓawa Imran Matawalle abinda ke hannunsa da abinda yake da muhimmanci acikin rayuwarsa. Imran Matawalle baya sharing abin hannunsa ga kowa." Farin ciki ya kama Rahama Galadanci, sai dai zuciyarta ta kasa nutsuwa tana san ta gano mai kalaman Imran Matawalle suke nufi na cewar ita ɗin abin hannunsa ce? Santa yake yi kokuma dai wani abu yake nufi? A ruɗe tace "Do you love me Imran?" Rahama ta kuma jefa masa tambayar, zuciyarta cike da tsoran abinda zataji daga bakinsa......
#Asmy B Aliyu
Da
#Hajja ce👈
[11/12, 9:31 AM] Asmy B Aliyu😘: *ALBI....*
(My Heart❤️)
NA
*ASMY B ALIYU*
DA
*HAJJA CE*
PAID BOOK..#(500)
*Account Details*
0004157137
*Jaiz Bank*
*Asma'u Buhari Aliyu*
Shaidar biya ta
08086207764
*Katin waya ta MTN.ta 07043079282 shaidar biya ta 07065283730 view WhatsApp*
*Free page 7*
Shiru yayi mata yana jin zuciyarsa na bugawa, baya son zuciyarta ta budee da soyayyah yanzu, ya fison tayi karatu mai zurfi dan yana son matar aurensa ta zama likita kamar shi, wannan alƙawari ne tun kafin ya mallaki hankalin kansa yake faɗin. 'Babu namijin da matarsa zata ware legs ya dubata idan tana da ciki ko wata larurar, shi xai duba kayansa da kanshi idan tana buƙatar ɗinki idan ta haihu shi zai ɗinke wurin da kanshi saboda yana da wani irin kishi wanda shi kansa bai san iyakar sa ba.
Hawaye taji suna zubo mata dan shirun Imran Matawalle ya tabbatar mata da cewa Imran Matawalle baya yi mata soyayyar aure tamkar yarda zuciyarta keyi mata khuduba a kullum. Imran yafi ɗaukar ta a matsayin blood sister ɗinsa. A hankali ta cire wayar daga kunnenta ta miƙawa Al-ameen dake faman kallonta. Juyawa tayi tabarsa tsaye a wurin ba tare da tace komai ba. Al-Ameen ya kara wayar a jikin kunnensa yana jin yarda Imran ke sauke wani irin numfashi. "Yaushe zaka dawo?" Imran Matawalle yace. "Zuwa jibi insha Allah." Da haka yayi masa sallama, Imran yana ji ajikinsa cewa fushi Rahama tayi, amma zai samu ya lallaɓata idan ya dawo. Shi karatu yake so tayi sosai, idan ya fara buɗe mata zuciya da soyayyarsa zaiyi wuya ya samu ta cika masa burinsa, dan ya fahimci Rahama da gaske take san auransa ko a yanzu, haka kurciya na dawainiyya da ita. Zai tsaya da kafafunsa, da jininsa da lafiyarsa wajan ganin Rahama tayi zurfi cikin neman iliminta, musamman karatu irin (medicine) da babu wani ɗaga ƙafa.
Har Rahama suka koma gida yinin ranar wani irin suku-suku take yinsa wanda Farook ya lura da haka, amman duk yarda yaso yaja Rahama a jikinsa tayi walwala taki basa haɗin kai ya kuma rasa meya canzata lokaci ɗaya. Haka duk yarda yaso yaji damuwarta nan ma ta faɗa masa babu komai har kusan sati ɗaya Rahama taƙi dawowa normal. Idan Farook yayi fushi sai ta dawo tana bashi hakuri kar yace ya fasa bazai saka baki wajan magana da Abba ba. Cikin wannan lokacin ne Farook ya koma Abuja sabida aikin sa. Amman yayi mata alkawarin zai riƙa kiranta waya a wayar Hajja.
Kafin ya tafi sai da yayi maganar karatunta da Abba wanda dakyar Abba ya amince dan sai da Farook ya haɗa da Hajja sannan Abba yace shikenan amma data fara jami'a koda aji biyu ne cireta zai yi yayi mata aure. Rahama taji daɗi a ranta dan tasan zuwa lokacin Imran Matawalle ya dawo cikin hankalinsa. A ranar da Farook ya tafi a ranar su Imran suka dawo har suka kwana biyu bai nemeta ba, itama batasan ya dawo ba, kasancewar sun fara jarabawar zango karatun ƙarshe shi yasa yanzu basa samun hutu, amman tunanin Imran na manne a ranta. Yau ta kasance ranar lahadi misalin ƙarfe goma sha ɗaya na safe ta fito daga ɗakinta sanye cikin Turkish abaya kalar maroon da mayafin kayan tayi rolling kanta dashi, sai ƴar ƙaramar handbag, ta nufi ɗakin Umminta ta sameta tana gyara kayan wadrobe ta xauna cikin soofa tana faɗin.
"Ummi na shirya" Ummi ta kalleta tana faɗin "Toh ga kuɗin kitson can a kan mirror idan kikaje kice ina gaisheta." Rahama ta ɗauki kuɗin kusan 3k harda na adaidaita. Ta ɗan marairaice fuska tana faɗin "Ummi ki ɗan saukeni mana, wallahi na tsani shiga adai-daita sahun nan Ummi," Ko dai na hakura da kitson yau sai zuwa jibi.?" Wani kallo Ummi tayi mata tana faɗin. "Yau zakije kitso babu ɗaga ƙafa Rahama, satin kanki nawa a tsife? kuma acikin adai-daita zaki tafi, idan na samu lokaci zanyi waya da Saratun idan angama miki zanzo na ɗaukeki, idan kuma ba'a gama ba ki ƙara shigo a dai-daita ki dawo gida." Cike da baƙin ciki Rahama ta nufi ƙofa tana turo baki, gashi Yaya Adamu sunje Katsina shida Abbanta. Ra'is ta gani a parking lot yana jefa ball ya rugo da gudu yazo gabanta yana haki yake faɗin. "Ina zakije Yah Rahama?" Tace "Kitso xanje rijiyar xaki." Ra'is yace. "Kenan adai-daita sahu zaki shiga.?" Wani kallo Rahama ta shiga yiwa Ra'is ta nufi gate a mugun fusace tamkar zata tashi sama.
Imran Matawalle dake fitowa daga cikin gate ɗin gidansu, yayi parking motarsa a ƙofar gidansu ya fito yana ya hangota tana fitowa rai a ɓace. Girgiza kansa yai yana jan numfashi, Rahama rigima ko'ina kuma zataje haka haka?Motarsa ya shige ya zauna sai da ta kusan barin layin nasu sannan ya tada motar yabi bayanta. Wani irin horn taji ana yi mata a bayanta ta ɗan turo baki ta cigaba da tafiyar ta. Haka kuma mai nacin bai daina bin ta ba. Afusace ta juyo zata yi bala'i, ware ido tayi tana kallon motar, lokaci ɗaya kuma idonta ya cicciko da kwallar shagwaɓa. Ta cikin motar yake hangota, yasan ta gane shine a motar, ya kuma san idan ba fitowa ya yi ba bazata je gurinsa ba. murmushi yayi ya fito daga motar, kananan kaya ne a jikinsa wanda suka yi mugun karɓarsa, Sai Rahama taga har ƙiba yayi da ɗan haske, kasancewar Imran ɗin black beauty chocolate ne, yana da manyyan ido masu matuƙar ɗaukar hankali, ga kuma tsawo masha Allah. Haka kuma kakkarfane kasantuwar yana yawon motsa jikinsa shi yasa jikin nasa kullum a murɗe yake, ya tara uban suma akansa wadda yake kashewa kuɗi sosai wajen gyaranta.
Baice da ita komai ba yaja hannunta har zuwa wajen motar, sai turo masa baki takeyi, haka kuma ta haɗe rai sosai. Da kansa ya buɗe mata front seat ya zaga ya shiga ya tada motar gamida harbata kan titi. Kuka kawai ta saka masa mai sauti wanda yasa shi saurin runtse ido dan sosai kukanta ke hurting ɗinsa. Da wata irin murya yake faɗin. "R Galadanci kin san yarda kukanki kesa na gigice kuwa? for God sake kiyi shiru Rahama, ko sokike na saki motar ta watsar damu kan titi.?" Bata kallesa ba ta saka fuskarta cikin tafukkan hannunta gamida kara volume ɗin kukanta, babu shiri Imran ya taka wani mugun burki ya tsayar da motar a gefen titi tare da ɗora kansa kan sitiyarin motar yana ƙoƙarin janyo numfashi, cikin wani irin yanayi yake kallon cikin idanunta yana faɗin. "Please faɗa min mekike so nayi miki Rahama? faɗa min what wrong with you?" Ya faɗa yana saukar da muryarsa akanta. Nan ma shiru tayi masa ya girgiza kai kawai yana mamakin rigima irinta ta, murya a sarke yace. "Kona ciro kaina na baki ne? Ya faɗa yana zura tattausan hannunsa ya riƙo nata guda ɗaya yana murzawa a hankali. Wani irin sanyi Rahama taji cikin hannunsa sai kawai ta turo baki ta kallesa hawaye a fuskarta take faɗin." Shine ka dawo amman baka neme ni ba ko? haka
ranar muna waya dakai kaƙi amsa min da nice da yanzu ka tsareni da masifa. Haka kuma ranar mun haɗu da Mommyn gidan ku take nunawa mutane wacce zaka aura." Ta ƙarasa maganar tana kuma fashe masa da wani sabon kuka. Sosai ransa ya ɓaci, kenan Mommy ta nunawa mutane Humaida? Ya sha toka yana faɗin. "Shine ke kuma sai kika yarda.?" Rahama ta fisge hannunta ta haɗe rai tana faɗin. "Nika buɗe min mota na fita kitso zanje." Da mamaki yake tambayarta "Driver fa?" Ta sake turo baki tana faɗa masa sun tafi Katsina tare da Abba. "Ummi fa?" Rahama ta yatsina fuska tace dashi "Tace naje cikin adai-daita sahu bata da lokacin kai ni." Imran ya haɗe rai sosai yana faɗin. "Amma mena faɗa maki akan shigarki adai-daita" Ta buɗe masa hannuwa tana faɗin. "Toh ya kake so nayi da Ummi?" Tada motar kawai yayi yana jin wani sabon ɓacin rai na sauka a cikin zuciyarsa. Har ya sauketa a rijiyar zaki yaƙi yai mata magana, ya kaita har ƙofar gidan mai kitson ya buɗe Walert ɗinsa ya ciro dubi biyar ya miƙa mata. Bata karɓa ba take faɗin." No need Imran akwai kuɗi a tare dani." Wani kallo da yayi mata ne yasa ta karɓi kuɗin tasa a jaka, yace da ita idan ta gama tayi masa text da wayar mai kitson, idan yazo zaiyi mata shima.
Sai da yaga shigarta cikin gidan kitson sannan ya tada motarsa yabar wurin da wani irin speed. Kusan 1pm ya shigo gidan ya baro daddy a office ya dawo gida. Yadda Mommy taga ya shigo cikin parlorn ko sallama bai yi ba ya taho tamkar wani arne, suna zaune tsakiyyar parlorn ita da ƙanwarta Humaida ƴar autar dakinsu wacce bazata wuce shekaru ashirin ba a duniya. Ganin yadda Imran ya shigo cikin parlorn yasa Humaida ta taso da murnata taje gabansa tana ƙoƙarin riƙo hannunsa ya wani jada baya yana zare mata manyyan idonsa masu gigita duk wani marar wargi yake faɗin. "What Humaida? Shin yaushe muka fara irin wannan wasan dake acikin gidan nan? sau nawa zan faɗa maki stay away from me? I don't want you in my life any more .!" Shaye da toka juya wurin Mommy yana yi mata wani irin kallo yake faɗin. "And you da kika buɗe baki kina faɗawa mutane cewa ita zan aura, yaushe nayi haka dake? kina tunanin zan iya auren ƙanwarki ragin bisa titi?" Cikin ɓacin rai da kalamansa Mommy tace "Ni kake yiwa rashin kunya Imran?" Tayi maganar da wani irin shock a muryarta, ganin tamkar ba dashi take ba yasa ta ɗaga hannu zata zabga masa mari ya riƙe hannun yana girgiza kansa cike da takaici, lokaci ɗaya kuma ya saki hannun ya watsar gameda ɓacewa daga cikin parlorn.
Dabas Mommy ta zauna cikin soofa ta kalli Humaida dake faman zubar da hawayen baƙin ciki tana cewa. "Wallahi idan ban auri Imran Matawalle ba mutuwa zanyi Aunty, dan Allah kiyi wani abu akan lamarin nan dan Allah. Na rantse Ina son Imran Matawalle, Ina sonsa da dukkan zuciyata Aunty, amman har yake kirana da sauran bisa titi." Mommy ta girgiza kai tana faɗin "Toh kuma meye na asarar hawaye Humaida? Wallahi kota tsiya kota bala'i sai ya aureki dan ko uban nasa bai isa ya hana wannan auren ba. Share hawayenki bana san ganinsu." Ta faɗa tana janyo Humaida zuwa ajikinta. Kwafa tayi zuciyarta na mugun tafasa, wai yau ita Imran ke ɗagawa murya? lallai tayi sake ɗan zaki ya girma, dole ta tashi tsaye akan lamarinsa. Sai kusan ƙarfe 3pm Ummi ta fita da mota dan ɗauko Rahama, wacce ita kuma a ɓangaren Rahama har ta ɗauki wayar Saratu ta yiwa Imran text cewar sun gama. Motar Imran na tsayawa sai ga motar gidan su Rahama, hango wadda ke ciki yasa yai saurin tada motarshi gamida barin ƙofar gidan. Ummi ta shiga da fara'a Saratu ta tarbeta gamida shimfiɗa mata tabarma a ɗan ƙaramin tsakar gidan su. Gaban Rahama ya shiga faɗuwa, addu'a kawai take Allah yasa Ummi bata samu Imran a ƙofar gidan ba. Cikin sauri ta shige ɗakin Saratu ta ɗauki wayarta sai taga text ɗinsa yana faɗa mata cewa ya wuce yaga Ummi nan tazo daukarta. Saurin goge sakon tayi ta saka Hijab dinta ta fito. Ummi ta faɗawa Saratu zasu koma, sukai sallama suka fito. Sun hau hanya Ummi ta kalli Rahama tana faɗin. "Hajja tace dake zata wuce Abuja idan kunyi hutu, dan haka sai ki fara shiri." Da wani irin hanzari Rahama ta juya zuciyarta na bugawa take faɗin. "Ummi nifa babu inda zanje." Wani banzan kallo Ummi ta ringa yi mata tana faɗin. "Dole kije ko dan wannan tsinannen yaron." Har suka isa gida ran Rahama a mugun ɓace yake, kuma zataje ta faɗawa Hajjan ita fa bazata bita Abuja ba. Bayan sallar magrib ta nufi part ɗin Hajja da basket na abincin daren ta, ko sallama ba tayi ba ta faɗo cikin parlorn. Baki wangale Hajja ta buɗe tana kallonta wacce ke zaune akan sallaya da alamar tunda tayi sallah bata ɗaga daga wurin ba. Can gefe Rahama ta kai basket ɗin abinci ta dire kan wani ƙaton carpet wanda nan ne wajen cin abinci Hajja, sannan ta dawo ta zauna akan ɗaya daga cikin kujerun dake kewaye da parlorn, sai wani harɗe hannuwa take akan kirji, ta sha toka sosai, ba tayi magana ba har Hajja ta idar da addu'arta ta gaisheta tamkar bata so, Hajja ta harareta tana faɗin. "Yau ni naga abunda ya isheni ni Hadiza, anya kanki ɗaya kuwa Rahama? kin shigo parlor babu ko sallama tamkar wacce bata sallah, yanzu kuma kin gaisheni kina wani bata rai tamkar wani shege ya aikeki yin gaisuwa. Ita dai Rahama dawowa tayi gaban Hajja ta ƙara haɗe fuska tana faɗin. "Ni Hajja yaushe nayi dake can biki Abuja? nifa babu inda zan biki, saboda kar karatun haddana ya tabarbare." Hajja ta girgiza kai cike da takaicinta take faɗin. "Oho nidai na gama magana tafiya dake kuma zan tafi babu fashi, kuma waya faɗa maki cewargidan Usman babu malamin dake koyawa ƴaƴansa karatun Alkur'ani?" Ganin dai da gaske Hajja take yasa Rahama ta miƙe tabar mata part ɗinta. Kallon gate ta shiga yi tamkar taje gidan su Imran, nan take kuma gargaɗin Abbanta ya dawo mata, juyawa tayi ta koma part ɗin Hajja tana faɗin bari