Header Ads
Showing 102001 words to 105000 words out of 139785 words

Chapter 35 - Albi Book Complete document by Hajjace.txt

Ads the beginning of article before Image

11 Jun 2024

1005

Ads at the middle of Article

ganga kiɗan yai mata daɗi har ta taka tawa ta hanyar siyar da duk wani mutunci nata. Haƙiƙa duk wanda Allah yaso shi da shiriya ya godiwa Allah, ba kowace rayuwa bace take zama wayewa. Duk wayewar da bata haneka aikata bayyana jikinta a fili ba ki gujeta, duk abubuwan zamanin da bazasu ɓoye kimarki ta ya mace musulba ba ki gujeta, mutuwa gaskiya ce hisabi gaskiya ne Allah bai ɗora kowane abu ba sai da ya faɗi makomarsa da hukuncinsa. Iyaye nagari rahama ne a garemu musamman uwa. Haka Humaidah taita bacci gefenta kwalbar wine ce riƙe gam a hannunta.
Imran ne ya fara tashi, a hankali ya buɗe idanunsa ya ɗorasu akan na Rahama yana jin yadda ta wani maƙaleshi a jikinta kamar zata koma jikinshi. Ɗan murmushi yai tare da shafar sumar kanta yana jin wani irin nishaɗi a zuciyarshi. Kallanta yake yana tuna yadda ta shigo rayuwarsa sannu a hankali, ɗan murmushi ya saki tuna wani lokaci can baya farkon ganinta dashi ya fito daga gida akan mashin ɗinshi zashi BUK ita kuma ta dawo daga makaranta ta tsaya a gabanshi wanda sauran kiris yai gaba da ita, ya juyo zai yi masifa kawai yaga ta riƙe kugunta tana ɗan girgiza jikinta tace masa. "Ina zakaje?" Wata uwar harara ya buga mata saboda yadda tai masa maganar tamkar wacce take da iko dashi, ya zare mata ido ya samu kanshi da cewa. "Indai kika aike ni." Hannu tasa tare da kaɗa masa yatsa tana wani yatsina fuska tace. "Ni ban aikeka ba sai ka koma gida." Ta ƙarasa maganar tana masa alamar ya koma ha hannunta. "Sannu Mamana." Ya faɗa a kufule yana sake murɗa kan mashin ɗin, tayi tsalle tare da kamo hannunsa tana faɗin. "Sunan Mamanku gareni?" Tana washe masa baki cike da fara'arta. "Stupid girl." Sakin masa hannun tayi tare da matsawa daga kusa dashi ta fashe da kuka ya murza mashin ɗin zai tafi yaji tace "The stillborn." Da sauri ya kalleta tai saurin tashi ta ruga da gudu tayi cikin gidansu. Yanzu kam dariya ya saki yana sake mannata a jikinsa tare da sumbatar saman idanunta da suke a lumshe. Zare jikinsa yayi, sauka yai daga kan bed ɗin jallabiya ya janyo yasaka ya fito, down stairs ya sakko har zai wuce ya fita sai kuma ya nufi ɗakin Humaidah da ya hango a buɗe, kwance ya hangota bata ma kwanta akan bed ɗin sosai ba, jiyai yana san shiga ciki sosai, gabansa ne ya buga ganin kwalbar beer a hannunta irin wacce ya taɓa gani a room ɗinsa, da sauri yaje ya fisge sai dai babu komai a ciki ta shanye tas! Ya kalleta da mugun mamaki dan a iya tunaninsa duk wani iskancin Humaidah bata shan sigari bare kuma wine. Wata muguwar tsawa ya daka mata, sai dai ko motsi batai ba, yai wurgi da bottle ɗin hannunsa ta tarwatse a cikin ɗakin. Wata irin masifa yake ji a zuciyarsa sai dai wacce zai yiwa bata cikin hankalinta, ya buɗe toilet ɗin cikin ɗakin cikin sa'a ya samu ruwa a cikin bucket ya ɗakkoshi, yana zuwa ya juyeshi jikin Humaidah yana daka mata uwar tsawa. Cikin maye take wani irin juyi, ruwan daya zuba mata a jiki ya manne mata kayan a fatarta, ƙoƙarin buɗe ido takeyi amma ta kasa, sai dai tana ɗan jin maganarsa sama-sama. "Ashe iskancin naki har giya kina sha? Kina sona amma kina bani gudun mawa wajan ganin kin bani abinda zai kawar da duk wani tunanina? Natsaneki Humaidah dama kuma can ba kaunarki nakeyi yi ba ." A fusace yabar ɗakin cike da bala'i akan face ɗinsa, Rahama da ta fito jin hayaniyarsa ta hangoshi ya fito daga ɗakin Humaidah cikin wani yanayi. Da sauri ta dinga sauka ta isa wajanshi da gudu tare da shigewa jikinsa, yadda taji zuciyarsa na wani harbawa da sauri ne yasa ta ɗago tana kallan kyakkyawar fuskarshi da ta koma tamkar ta basawa. Da yake tafi kowa sannin waye Imran da kuma wace irin zuciya gareshi sai ta fara shafa gefen quarter millions ɗinsa, da muryarta mai sanyi take faɗin. "Waye ya maidar min da kyakkyawar fuskarnan daga farin ciki zuwa akasin haka? Smile a little ko makiya suji haushi." Kallanta yai ya rintsa ido, janshi tayi zuwa kan kujera ta zauna tana shirin ɗora shi kan ƙafarta Imran yai saurin riƙo ta tare da yi mata hararar wasa. Zama yai ya ɗorata akan tashi ƙafar yana kwantar da ita saman kirjinsa yace. "Kina tunanin zaki iya ɗaukata ne?" Cike da tabbatarwa take faɗin. "Sosai ma." Ta ƙarasa da turo baki. Yasa yatsunsa biyu ya ɗan kamo lips ɗin tare da matsawa, ƴar ƙara ta saki tana sake shigewa cikin jikinsa, tuni da kawar masa da kaso cassa'in da tara na ɓacin ran da yake ciki. "Dole ne na rabu da Humaidah tun kafin tasa min ciwon zuciya." Rahama ta ɗago da mugun sauri ta kalli Imran Matawalle tana girgiza kai. "Albi please kaga zaka iya batawa Daddy rai yace ka saɓa umarninsa." Ya ɗan numfasa tare da cije lips "Dole ne Humaidah ta barni koda kuwa ace nine mahaɗin da yake sanya numfashinta yin aiki dole ta barni dan bazan iya zama da macen da take san ganina kullum a cikin maye ba. Ni ɗan maye itama haka mekike tunanin zai faru Albi?" Rahama tayi shiru, abin ya matuƙar bata mamaki wai Humaidah ke shan beer kamar wata arniya kuma a gidan auranta. "Muje ɗaki muyi wanka ina san leƙawa clinic akwai wata mai diabetes za'ai mata aiki Ina san na kasance a wajan, but sai 2:30pm za'ai aikin. Wuyansa ta riƙo cike da murna take faɗin."Tare zamuje ko? Nidai bazaka barni a gida ba zan bika." Haɗe rai yai hakan yasa Rahama gane cewa bazai tafi da ita ba, tayi ƙasa da, kai bata ce komai ba. Suna wanka tana janshi da wasa wannan ya nuna masa cewa ta fara sakin jiki sosai dashi, amma ya gane so take ya saki fuskarsa hakan yasa ya biye mata suka dinga ɓata lokaci a banɗakin. Ita ta shafeshi da tsadaddun mayukansa ta gyara masa sumar kanshi tace haka take son style ɗin, daya kalli kan nashi sai ya saki dariya, suka nufi cloth set koya ya ciro wanda zai saka. Suit yaso sakawa amma gyaran gashin yasa dole ya ɗakko shadda ya sanya tare da hula ya ɗora. "Wai kai gurin daurin aure zakaje ne?" Tayi maganar tana juya bayanta dan ya zuge mata zip. "No asibiti nace miki." Sake kallansa tayi tun daga sama har ƙasa ta wani shagwaɓe fuska, "Gaskiya ni a'a." Imran ya ɗauki turare sai fesa ta karbe ta mayar kan mirror, wajan kayan ta koma da kanta ta ciro masa wasu riga da wanda hakan nan ya hakura ya cire wanda yasa ya karɓi wanda ta bashi ya sanya. Gani tayi ya kuma yi mata kyau, ta shiga rintsa ido tana zaune a gefen gado ya matso inda take tare da ɗagota yace. "Sa hijab mu tafi." Tsalle tayi ta rungume shi tana faɗin. "Thank you Albi, thank you so much dama wallahi ina ta jin tsoran kar ka tafi wata ta kalle min kai." Ya shafi gefen kuncinta yana murmushi. "Ni naki ne, only you Albi." Da sauri ta ɗakko ɗankwalin ta daura da hijab wanda ya dace da takalmin da ta ɗakko. Turaruka suka sanya ya rike hannunta suka fice a gidan.




(Complete Decuments)
*WAMINAL HUB* #500
*ZO GARENI* #300
*NIDA RAHEEMA* #300
*RAYUWAR AURENA* #300




#Asmy b Aliyu
#Hajja ce
#Imran Matawalle
#Rahama Galadanci
#Humaida Makarfi
#Team Albi
#Haske Writers Association....
[12/10, 7:08 PM] Asmy B Aliyu😘: *ALBI...*
(my heart❤️)


*ASMY B ALIYU*
DA
*HAJJA CE*👈


PAID BOOK..#(500)


*Account Details*
0004157137
*Jaiz Bank*
*Asma'u Buhari Aliyu*
Shaidar biya ta
08086207764


*Katin waya ta MTN.ta 07043079282 shaidar biya ta 07065283730 view WhatsApp*


44....


Da wani irin sauri ta miƙe tsaye tana kallan jikinta kafin ta karewa ɗakin kallo idanunta suka sauka akan bottle ɗin beer, dafe goshi tayi tana furzar da numfashi. Gadonta ta gani ajiƙe sannan ƙasan tiles inda babu rug duk ruwa ne, waye yai mata wannan aikin? Ko ita tai bayan tayi mankas da ita? Babu amsa ta girgiza kai kawai tare da cire kayan ta faɗa toilet a lokacin karfe 6:40pm babu azahar, la'asar da magrib ga isha'i na gabatowa. Cikin takaici tuna abinda Mommy tace mata yasa ta dinga ƙaro karfin shower ruwa yana zuba a jikinta. Indai itace ta haifu jinin Maƙarfi sai ta nunawa Imran Matawalle cewa ita ƴar titi ce, wannan lokacin ba HIV aids ba komai Imran yake ɗauke dashi a jikinsa sai ta mallakeshi ta tabbatar da mafarkinta ya zama gaskiya. Fitowa tai ta shirya cikin wasu fitinannun riga da wando na bacci white color tabi jikinta da wata cholectur mai shegen ƙamshi da khumra mai bala'in ƙamshi taja stole ta zauna tana tsara makeup a face ɗinta. Tayi kyau ba karya ta ɗakko iPad ɗinta da iPhone tayo parlor, kan kujera ta ajiye sannan ta shiga kitchen tana neman abinda zataci, dole ta samo mai mata aiki dan bazata iya wahala ba dan ko a gida ba wani abun takeyi ba. Cornflakes ta hado ta dawo parlorn tana sha tana danna waya kunnuwanta na jiran jin motsin su Imran daga upstairs, ganin har an idar da isha'i bataji wani a cikinsu ya sakko ba yasa ta fita compound anan taga babu motar Imran taja tsaki ashe ita suka barwa gadin gidan, da tasan basa nan da tun ɗazu ta fita itama. Komawa tai ta zauna cike da takaici tana sake jin wani tsanar Rahama a ranta. Su kam tun wajan karfe huɗu suka baro clinic, kai tsaye Imran ya wuce da su wajan da zai fara koya mata mota, farin ciki a wajan Rahama ba'a magana cike da confidence take kallan yadda yake murza kan motar, parking yai ya ɗan kalleta, murmushi ta sakar masa yai saurin rintsa ido yana ɗan matsawa ya nuna mata gabanshi yana faɗin. "Dawo nan kigani yadda ake yi dan nasan bakya gane inda nake saka ƙafata." Rahama ta kalleshi da mugun sauri take faɗin. "Kana so ƴan sanda su kwamashe mu koh? Ƙatuwa dani shine zan wani zauna a gabanka? Ni dai ba ruwa na da ƴan sanda." Juyawa yai yana kallan glass, maido da fuskarsa yai yana sake kallanta yace. "Ki dawo nace." Ganin yai maganar cikin umarni yasa ta buɗe ta fito, side ɗin nashi ya buɗe mata tare da janyota ta faɗa jikinsa, zaunar da ita yai sosai sannan ya rufe murfin ya ɗora hannunta kan sitari, ƙafafunta kuma ya ɗorasu akan nashi ya ɗaura musu seatbelt, murmushi yai yana rungumeta yace. "I love you Albi koda mun mutu kisani ba wata a zuciyata sai ke." Gabaki ɗaya Rahama ta gama tsurewa, lamarin Imran ya tayar mata da hankali, jira kawai take ya fara tafiya, yana murza giya ta fara kalmatusshahada. Dariya ya saki yana riƙo ƙugunta yasa fuskarsa a bayanta yana dariya sosai wacce Rahama bata taɓa jin yayi ba, da alama ta mugunta ce, ta turo baki ya shige cikin jikinta yana cewa. "Albi tsoran mutuwa?" Rahama tayi shiru ya leko fuskarta suka haɗa ido kafin ya juyo da fuskarta yana faɗin. "Kinajin tsoro ne?" Rahama ta ɗaga masa kai da sauri dan har ga Allah idan tace bata tsorata da cewa a haka zasu yi tukin ba tayi karya, yace. "Okay bari na sauka sai ki ja mugani in zaki iya." Ya zareta daga jikinsa ya fito ya koma front seat ya zauna, kallanta yai yaga taki bari su haɗa ido. "Look at me Albi." Dariya ce ta kwace mata dan haka ta saki abarta ya tsaya kawai yana kallanta cike da so, ta wani haɗe rai kamar ba ita ke dariyar ba tana faɗin. "Kawai kasa na tsure." Murmushi yai tare da kwantar da bayansa jikin seat ɗin. Key ta yiwa motar ya ɗan ɗago ya nuna mata yadda zata fara sannan ya maida bayansa yana cewa. "Duk da yin farko ne ni bazan ji tsoro ba, nasan zaki kula dani." Ya lumshe ido kamar mai bacci. Rahama ta girgixa kai tana jinjina irin girman son da yake yi mata da har ya bata duka rayuwarsa tayi yadda taga dama. Sosai yai mamakin yadda lokaci ɗaya ta iya, ya dinga yaba mata tace sai ya siya mata sabuwa yace tashi ta ishe su, zai kaita duk inda take so amman bazai mallaka mata mota ba dan baya so idanunta su buɗe sosai. Sai da suka hau babban titi ya karɓa ya kaisu wani restaurant sukai takeaway sannan suka koma gida. Imran Matawalle ne ya fara ɗora idanunsa kan cinyoyin Humaidah da suke a buɗe, Rahama dake bayan Imran tai saurin dirowa zuciyarta na wani irin bugawa, lallai Humaidah ta cika ƴar bariki, wato duk irin waɗannan abubuwan da Aunty Kausar tace ta dinga yi bata faraba ashe Humaidah ta iya su? Kayan jikin Humaidah ta sake kalla wanda gaba ɗaya babu abinda ya rufe a jikinta, ta rintsa ido zuciyarta na wani irin tururi kamar zata ƙone. Upstairs ta nufa da gudu tana dafe kirki, shi kuma Imran ya riƙe ledojin hannunsa da karfi saboda wata irin zuciya da yaji tana taso masa. Dai-dai kanta yaje yana buga mata ƙafarsa da takalmi, da yanayin magagi Humaidah tai wani juyi wanda ya ɗage rigar jikinta nashanunta suka bayyana waɗanda babu bra a jikinsu. Idanuwa ta watsawa Imran tare da tashi da sauri tana wani irin layi, jikinsa ta faɗa ta rungume shi tsam tana sumbatar gefen wuyansa. Tureta yai yana watsa mata shanyayyun idanunsa da suka fara canzawa zuwa zallar masifa yana cewa. "Naga iskancin naki kullum daɗa karuwa yake yi Humaidah, kinsani sarai bani dake kaɗai ne a cikin gidan nan ba, toh ina so kisan wani abu guda ɗaya Humaidah, koda tsirara zaki dinga zama a cikin gidan nan ba burgeni zaki yi ba bare har nai sha'awarki, kuma bari kiji na kara tsanarki dan bakya kaunar ganin na zauna lafiya bare na kasance cikin rahamar ubangiji, beer ɗin da kika bani nasha Allah ya isa, na kuma sakeki kije ki auri wanda zakici gaba da bawa beer." Ya wuce zai bar parlorn Humaidah ta sha gabansa tana zare ido, cike da tashin hankali take kallansa tana faɗin. "Kasakeni Imran? Kasakeni fa kace?!" Ya tako gabanta tamkar zai rungumeta dan numfashinsu sai bugun na juna yake yana cewa. "Haka nace na sakeki saki ɗaya saboda bazan iya zama da mai ci gaba da ɗorani a shan giya ba, wacce nake shama zuciyata ba so takeyi ba, ina ji ne tamkar ana tunzurani akan dole sai nasha." Ya wuce upstairs da sauri yana wani cije lips. Ihu Humaidah ta saki tare da rugawa ta ɗauki wayarta, cike da tashin hankali ta nemo lambar Mommy. Tana dagawa ko gaisawa basu yi ba take faɗin."Nashiga uku Aunty Imran yasakeni wayyo Allah na..!" Kashe wayar kawai tayi ta nufi upstairs da wani irin gudu. Imran na shiga ɗaki be kalli inda Rahama take ba dan yasan koyai mata magana tana cikin fushi shi kuma bazai yadda babu abinda yai mata ba yaje ya dinga wani lallabata ba, yafi san ko lallashinta zai yi ya kasance shine yai mata laifi ba a irin wannan abubuwan ba. Rahama tana cire kaya ganin be kulata ba yasa ranta ya ɓaci ta shige toilet ta barshi nan yana cire kaya. Bugun da Humaidah ta dinga yi ne yasa shi yin wurgi da rigar daya gama tuɓewa, yaje ya buɗe ƙofar cikin ɓacin rai ya shaƙo mata wuya jikinsa har wani rawa yake saboda ɓacin rai ya haɗata da ƙarfen stairs kamar zai hantsilata ƙasan yake faɗin. "Idan baki fita daga rayuwata ba Humaidah zan zama ajalinki, wallahi zan iya kasheki a yadda na tsaneki Humaidah. Oya get out of my way...!" Da gudu ta juya tabar wajan tana kuka mai tada hankali. Ɗaya ɗakin ya shiga kai tsaye bathroom ya wuce ya shige cikin ruwan da ya gani a bathtub wanda karara yake amman dake yana cikin zafin zuciya bemaji sanyin ruwan ba. Yana fitowa ya tsane jikinsa da small towel, babu abinda ya shafa boxer kawai yasa tare da ɗakko kwalin sigari da lighter ya zauna cikin sofa tare da kunna kara biyu a lokaci ɗaya ya zura su cikin yatsunsa ya fara tada hayaƙi. Rahama kam har ta gama wanka tana mamakin abinda ya hanashi shigowa, tana shafa mayuka tana tunanin ko itama haushinta yake jine? Toh ina ya tafi haka? Hawaye ya ziraro saman kyakkyawar fuskarta, shikenan ya tafi mashaya tasan kodai ya kwana acan ko kuma Al-Amin ya shigo mata dashi a buge. Zama tayi a bakin gado tasa fuskarta cikin kafafuwanta tare da fashewa da wani irin kuka, sun dawo cike da farin ciki wata banza ta hargitsa musu komai. Warin da ta fara jiyowa ne yasa ta saurin ɗago kanta, cikin sanyin jiki ta miƙe tana gyara towel ɗin dake ɗauka a jikinta, inda warin yake fitowa sosai nan ta dinga bi har ta buɗe labulen ɗakin. Kwance ta hangoshi cikin sofa kansa a sama yana ta hura hayaƙi daga bakinsa cike da kwarewa. Da sauri ta share hawayen tana tunanin komawa sai kuma ta daure kamar babu abinda yake damunta ta isa wajanshi, ya ɗan kalleta kaɗan ya kauda fuska kamar baya san ganinta. Saman kafafuwansa ta zauna yasa hannu ta zare sigarin, ƙoƙarin kaiwa bakinta take ya cafko hannun yana wurga mata wata shegiyar harara. "Are you out of your sense?" Wani irin kallo Rahama keyi masa wanda yasa Imran riƙo fuskarta, janyota yai gaba ɗaya ta faɗa cikin jikinsa ya kamo bakinta da nashi ya shiga yi mata wani irin kiss mai tayar da hankali, zare towel ɗin yai tare da wulla shi gefe ya tattarota gaba ɗaya ya ɗora akan cinyarsa bombom ɗinta na gogarsa ya kalleta da idanunsa da suka ƙanƙance yana faɗin. "Ko a mafarki ban yadda ki gwada shan waɗannan abubuwan ba, don't try to do this dirty behavior. Bakisan suna da illah ba?" Hawaye ya ziraro mata ta dago ido ta kalleshi tana cewa. "Kasani amma kakeyi? Kabarni nima ina so naji abinda

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads