Header Ads
Showing 48001 words to 51000 words out of 139785 words

Chapter 17 - Albi Book Complete document by Hajjace.txt

Ads the beginning of article before Image

11 Jun 2024

998

Ads at the middle of Article

ɗin jikinta Rahaman ta taɓa jikinta taji wani irin mugun zafi, da sauri ta ɗauke hannunta tana salati tana faɗin. "Kashe kanki zakiyi ne ƴar nan? bari na kira maigida." Da sauri ta lalubi ƴar ƙaramar wayarta dake cikin zaninta, lokacin Matawalle yana cikin meeting yaga kiran Mamah Rabi ganin kiran nata yasan babu lafiya, nan take aka kira P.A ɗinsa ya karbi wayar Ya faɗa masa yarinyyar da take kula da ita ce babu lafiya, nan take p.a ɗin yayi magana da family doctor ɗin su dake kula da iyalan Matawalle idan suna a Abuja akan yaje gida ya duba marar lafiya suna da emagency. Cikin awa ɗaya doctor Khalifa Turaki ya bayyana place ɗin mai girma Matawalle, Da kyar da ban baki Rahama ta watsa ruwa Mamah Rabi ta bata ɗaya daga cikin suturar Maheera Matawalle wanda bata taɓa sakawa ba. Karɓa tayi ta saka, kayan sun zauna ajikinta sosai. Doguwar rigar atamfa ce super wax kalar brown da purple ajikinta anyi mata ɗinki A shape, sosai rigar ta zauna ajikinta tamkar dan ita aka ɗinka kayan, kasancewar Maheera Matawalle tana matuqar son traditional kaya a rayuwarta, sam bata fiye saka kayan bature ajikinta ba, ko acan ƙasar idan zata shiga school ta fiye saka traditional kaya fiye da kananun kaya, idan kaga Maheera Matawalle da kananun kaya to acikin gida take ko can jefi-jefi a takaice dai tafi ra'ayin traditonal kaya fiye da na bature. Tun daga kan stairs Khalifa Turaki ya qurawa kyakkyawar fuskarta ido duk takun da ƙafar Rahama zatayi yana jin bugun hakan har acikin zuciyarsa, abinda bai taɓayi ba a cikin gaba ɗayan rayuwarsa wato kallon mace fiye da sau ɗaya, haka kuma ya kasa ɗauke idonsa akanta, saboda wani irin abu yake ji na yawo tun daga cikin zuciyarsa har cikin tafin ƙafarsa, abinda yake ji akan wannan innocent soul ɗin dake agabansa bai taɓa jinsa ba akan ko wace ɗiya mace ba. Nan take wata zuciyar ta faɗa masa wannan shine love at first sight. Ta zauna kujera ta nesa da shi duk wannan kallon da Dr. Khalifa Turaki keyi mata cikin ƴan sakanni yayi mata shi. Mamah Rabi tayi masa sannu da zuwa ta kalli Rahama tana faɗin, "Ki faɗa masa meke damunki, kaganta nan tun ruwan shayin dake cikin cikinta babu komai acikin sa." Ya kalli gefen da Rahama Galadanci ke zaune da wata irin azababbiyar soyayyarta wadda bai taba jin haka ba a gabaki ɗaya cikin rayuwarsa. "Madam ki ɗan taɓa wani abu kafin na dubaki na baki magani." Mamah Rabi ta nufi Kitchen da sassarfa dan haɗo mata wani abu mai ruwa wanda zata iya sha. Da idonta da suka gama kumbura sabida kuka ta ɗago tana yiwa Dr. Khalifa Turaki wani irin kallo, ya riqa binta dashi kukanta na taɓa xuciyarsa haka kuma yana mamakin kukan me takeyi ko duk tsananin ciwo ne? Sai ga Khalifa Turaki durkushe agaban Rahama Galadanci abinda bai tabayi ba akan ko wace macce. Ya girgiza kai yana faɗin, "Karki karawa kanki ciwo, kiyi hakuri dan Allah." Shi kansa a rikice yake bai san da kalmar da xai rarrasheta ba. Lokaci ɗaya ya kai hannunsa saman goshinta wani irin shock yaji da sauri ya janye hannunsa zuciyarsa na wani irin bugawa. Wani irin unxpressable feeling da yakeji akan yarinyyar da yake durkushe a gabanta cikin minti ɗaya ya tashi daga gaban Rahama ya koma kujera ya zauna. Juya kai ta shigayi tana jin kamshin turarensa na cika mata hanci, dai-dai lokacin Mamah Rabi ta dawo ɗauke da mug a hannunta tare da damammen custard wanda yaji madara sosai a cikinsa, ta miqawa Rahama tana faɗin "Yi maza ki shanye kin barsa yana ta jira." Amsar mug ɗin tayi tacigaba da juya custard din kasancewar bata son abu mai zafi. Kallon nacin da Khalifa Turaki keyi mata ne yasa ta kafa kai, sai da taji babu komai ta aje ta haɗa da ruwa. Allah-Allah take ya dubata ya ɓace daga cikin parlorn, haka kurum haduwar su da Dr. Khalifa Turaki taji sam babu wani alkahiri acikin ta. Tambayoyi yake yi mata tana bashi amsa, ya dauko brifecases ɗinsa ya fiddo da magani ya bata yayi mata bayanin yarda xata sha kowane, karshe ya haɗata da Allah da Manzon sa akan ta rage wannan damuwar da takeyi kar yaja mata hawan jini. Sannan yayi min alkawarin gobe xai dawo ya sake dubani. Ni dai shiru nayi masa tamkar yana magana da dutse haka na zamar masa kurma bayan ya fita. Dakyar na sha maganin na kwanta ina jin bacci sai dai tunanin Imran ya hana, tunani take ta hanyar da Mamah Rabi xata aje wayarta ta ɗauka ta kira Imran. Har aka kira sallar isha'i bata samu damar hakan ba, sai dai ta samu zazzabin ya sauka. Mamah Rabi tayi waya da mai girma Matawalle cewar Rahama ta samu lafiya.
Ko yanzu ma tunanin Imran ya hanata sakat bata san wane irin hali yake ciki ba yanzu, tunda tayi sallar isha'i take kwance akan sallaya tana faman sharar hawaye tana ambaton Allah a ranta. Kusan karfe 9 ya shigo layin nesa da gidansu yayi parking motar ya fiddo da wayarsa ya kira Buzu maigadi cikin ransa yana addu'a Allah yasa aikin da ya basa yayi da kyau. Ganin kiran mai gida Imran yasa Buzu ya ɗaga da sauri ya gaishesa da wani irin respect wanda a haife Imran ɗin zaizo a yaronsa na uku da haifa. Imran ya karba yana shafa sumar kansa yake faɗin "Baba ya aiki? Ina fatan komai ya kammala ko? Buzu yace. "Komai yayi dai-dai yanzu hakan su duka sun samu bacci ka karaso kawai." Wani irin sly smile Imran ɗin ya saki yana kashe wayar. Daman tun da ya shigo garin Abuja sai da ya sauka gidan wani friend ɗinsa babansa minister kuɗi ne a yanzu ya dauko motarsa sa'annan ya kira Buxu maigadi akan ya tabbatar yau ya haɗawa duka security dake zagaye da gidan Matawalle shayin da xai sakar masu bacci. Idan yayi masa wannan alfarmar zai yi masa alkhairi mai yawan gaske. Buzu bai wani sha wahala ba sabida ya saba haɗa masu shayi wannan karon sai ya zuba ganyen dake saukar da kasala da kuma saka bacci. Da sauri Imran ya fito daga motar ya nufi ƙaramar ƙofa yayi knocking Buzu ya ƙaraso yana tambayar waye? Imran ya amsa yana faɗin nine baba da sauri buxu ya buɗe masa bai tsaya ba kai tsaye entrance ɗin shiga gidan ya nufa da sassarfa, daman kuma yasan Mama Rabi da wuri take kwanciyya barci da angama sallar isha'i. Kai tsaye stairs ya nufa ɗakunan ya shiga buɗewa a hankali yana saka hasken fitilar wayarsa acikin dakuna. hangota yayi akan rug ta dunkule waje ɗaya da sauri ta miqe tsaye tana rarraba ido tayi ido biyu dashi ta kara ware idonta dan tabbatarwa da sauri ta miqe tsaye da gudu ta nufesa ta wani faɗa jikinsa, sosai ta fashe da kuka, rungumeta yayi sosai yana sauqe wata irin ajiyar zuciya da sauri yaja hannunta suka sauka akan stairs cikin mintunan da basu wuce biyar ba suka bar gidan duka. Dukansu shiru suka zauna a motar ta kwantar da kanta akan kafadarsa tana sauke wata irin ajiyar zuciya hawaye na zubar mata. Daman yayi masu booking hotel kai tsaye can ya nufa da ita dan ya kudiri aniyar zuwa Kaduna gobe Insha Allahu can ya nufa zai tsaya a daura auren sa da Rahama ko a ina ne kafin su koma Kano.......








#Asmy b Aliyu
#Hajja ce
#imran Matawalle
#Rahama Galadanci
#Khalifa Turaki
Haske Writer's Association#
[11/12, 9:35 AM] Asmy B Aliyu😘: *ALBI....*
(My Heart❤️)


NA
*ASMY B ALIYU*
DA
*HAJJA CE*


PAID BOOK..#(500)


*Account Details*
0004157137
*Jaiz Bank*
*Asma'u Buhari Aliyu*
Shaidar biya ta
08086207764


*Katin waya ta MTN.ta 07043079282 shaidar biya ta 07065283730 view WhatsApp*


*Areewabook*
https://arewabooks.com/chapter?id=6362e614d52c9563f327d94f


23.......


Hannunta yana riƙe cikin nasa har suka hau upstairs, room 013 suka tsaya ya zaro key ɗin ya buɗe suka shiga ciki. Tsayawa yai a gabanta yana wani irin kallanta, dubawa yake ko akwai inda akaji mata ciwo, tana ta kallansa itama kafin ta turo baki ya langaɓe kai. Hannunta ya sake ja suka isa bakin bed ya zaunar da ita, cike da kulawa yake faɗin, "Mekike son kici? Nasan kina jin yunwa." Rahama ta kawar da kai tana sake haɗe fuska, ganin haka yasa shi juyawa yabar room ɗin ba tare da ya kuma yi mata magana ba. Cikin ƴan minutes ya dawo hannunsa riƙe da takeaway, tana nan a inda ya barta. Ciro abubuwan ciki yai tare da ajiyewa
gefenta still babu wanda yai magana a cikinsu.A spoon ya ɗebo tare da kaiwa bakinta tayi saurin kawar da kai, matsawa yai sosai kusa da jikinta waist ɗinsu yana gogar na juna yace. "Ki ajiye min wannan rigimar taki dan Allah, idan kikaci kika ƙoshi sai ki min duk kalar rigimar da kike so, oya yanzu karɓi kici." Ya sake kai abincin da ya ɗibo a spoon ta sake ɗauke kai. Ajiyewa yayi cike da jarumta ya ɗauketa dukanta ya ɗora saman cinyarsa, Rahama ta kuma kawar da kai tana sake tsuke fuska. "Okay gaya min laifi na tun kafin zuciyata ta buga." Ganin yadda jikinsa yai sanyi ne yasa ta kuma turo baki tana faɗin. "Kawai dan ina sanka shine Daddy Matawalle zai sa a sace ni? Ka gaya min Imran na cancanci haka?" Ta ƙarasa maganar tana jin hawaye nasan ziraro mata. Janyota Imran yai gaba ɗaya ta kwanta a jikinsa, wani irin riƙo yai mata wanda yasa Rahama fashewa da wani irin kuka, hakiƙa ta sani shima yana bala'in san ta, soyayyar da yake yi mata gabaki ɗaya tabi cikin hantarsa ta ratsa duk jinin jikinsa, babu abinda ruhi da gangar jikinsa ke muradi irin yaga ta zama mallakinsa, amma sai shamaki ake sanya musu. Cikin raunanniyar murya take magana, "Nayi kokarin ganin na cireka a raina ta yadda zan barka ko Matawalle zaiji daɗin rayuwarsa amman na kasa Imran, kullum soyayyarka sake ninkuwa take a cikin zuciyata, please Imran ka gaya min me zanyi ka tsane ni? Tell me Imran Ina ji kamar zuciyata zata fashe saboda kaunarka." Ta ƙarasa tana kuma fashewa da kuka, ta gaji da wannan abubuwan da ake yi musu, ta gaji da halin iyayen su, yanzu kam kota halin ƙaƙane tana son taga ta zama mallakin Imran Matawalle. Ɗagota yayi daga jikinsa tare da ɗago face ɗinta sukai 4 eye's da juna, yadda yaga hawaye na gudu akan kyakkyawar face nata shine yasa zuciyarsa kusan tsinkowa daga ma'ajiyarta, kuma janyota yai ta faɗa cikin jikinsa ya kuma yi mata wani irin runguma yana manne kanta a saitin heart nashi yana cewa. "Stop crying my dear R, stop please idan ba so kikeyi zuciyata ta fito waje ba." Ya faɗa cike da rigima . Jin tana sauke numfashi ne yasashi shafar face ɗinta yana cewa. "Wannan tunanin naki shine zai tarwatsa duk wani happiness nawa, do you think zan iya rayuwa babu ke ne? Insha Allahu gobe kamar yanzu kina a matsayin matata Ra..ha..ma." Ya ƙarasa faɗa yana rarraba sunan sounds so hope. "Waye zai mana auren Imran?" Ɗago da kanta yai ya zuba mata sexy eye's nashi, da sauri ta janye nata saboda yadda taji wani shu'umin abu yana fizgarta. "Kedai Allah ya kaimu goben lafiya, yanzu dai ki daure kici abinci then kiyi bacci ki huta." Rahama ta ɗauki spoon ta ɗibo abincin takai bakinsa, buɗewa yai babu musu ya faraci sannan itama taci da haka har suka cinye ɗaya ya kunna musu game ledo sunayi a cikin wayarsa, sai cinyeta yakeyi ta turo baki. "Nidai wayo kawai kake min banayi." Dariya yai tare da cewa. "Kin iya fa, zoki gani." Yasa hannu zai kamota tai saurin guduwa ta faɗa kan gado. Wayarsa ce tai ringing yana dubawa yaga Daddyn sa ne, rintsa idanuwa yai dan ya tabbatar tambayarsa zai yi yana ina? Shi kuma baya so asan a inda yake yanzu. Ganin wayar bata daina ringing ba yasa shi ɗauka yana cije lips. "Where are you son?" Imran ya kalli inda Rahama ke kwance, hannunsa ya saka cikin sumarsa tare da faɗin. "Daddy ina wajan Al-Amin." Matawalle ya sauke wani dogon numfashi "Ya akai baka dawo gida ba? Ko bakasan dare yayi ba sosai?" Imran ya miƙe tsaye yana cewa. "Nagani Daddy, kawai bazan iya kwana a ɗakina ba that's why zan kwana wajan Al-Amin." Matawalle yace. "Shikenan badai wani problem ko?" Murmushi Imran yai tare da cewa. "Yeah Daddy babu komai." "Okay bye and sweet dreams my boy." "Insha Allahu Daddy love you." Ba tare da ya jira amsa ba kawai ya katse. Sunan Rahama ya kira yaji tsit, tashi yai ya nufi wajanta, gani yayi har tayi bacci hakan yasa ya gyara mata kwanciyar shi kuma ya koma ya kwanta cikin soofa.


*******
Washe gari tunda ta farka daga bacci ta miƙe ta hau upstairs dan tashin Rahama tayi sallah, knocking Mama Rabi tayi taji shiru hakan yasa ta buɗe ƙofar ta shiga cikin room ɗin bakinta ɗauke da sallama, kiran sunan Rahama ta dinga yi amman shiru, wajan toilet taje ta sake kiranta bata amsa ba, Mama Rabi ta murɗa ta shiga babu Rahama a ciki. Nan da nan hankalinta yai mugun tashi ta dinga duba duk inda tasan mutum zai iya shiga bata samu Rahama a ciki ba. Compound tayo tana tambayar securities ɗin dake gidan cewar ko sunga Rahama? Duk sukace a'a. Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun shine kawai abinda suke cewa lokacin da suka gama tabbatar da cewa bata cikin gidan. Wajan Buzu mai gadi suka nufa, tarar dashi sukai yana ta haɗa kayan shayi a cikin kettle ɗinsa, ɗaya daga cikin sojojin ne yake tambayarsa. "Ina Rahama?" Cikin sauri Buzu ya kallesu, ganin sun tsare shi da bindigogi yasa shi jin tsoro, sai dai yana tuna cewa Imran ne yasa shi koma menene yasan Imran ba zai bari ayi masa hukunci mai tsauri ba, cikin sunkuyar da kai yace. "Gaskiya Imran ne yazo gidan nan, sai dai banga lokacin da suka fita da Rahama ba, Ya nuna min kawai wasu takardu yazo ɗauka a gidan." Wani irin naushi ɗaya daga cikin sojojin ya kaiwa Buzu yana furta "Are you mad?" Buzu ya shiga girgiza kai yana jin wani mugun tashin hankali. PA ɗin Matawalle suka kira nan da nan suka shaida masa abinda yake faruwa, a lokacin Matawalle yana sitting room suna waya da senate president hakan yasa ba'a sanar dashi ba. PA ɗin Matawalle ya basu umarnin cewa ayi maza-maza aje a nemo su yace "Nasan ba zasu wuce hotels ɗin garin Abuja ba aje a duba kowane dake cikin garin." Yaci gaba da jiran Matawallen ya gama wayar dan ya sanar dashi halin da ake ciki.
*********


Imran kuwa kamar yasan dole za'a bazama nemansa indai aka tabbatar da cewa Rahama bata cikin gidan Matawalle. Dan haka ana kiran sallar farko ya tashi Rahama sukai sallar nafila sannan suka fito daga hotel ɗin, ya tada motar Abokinsa dake hannun sa suka dauki hanyar Kaduna. Ahanya aka kira asuba suka yi parking suka gabatar da ita sannan sukaci gaba da tafia. A wani katafaran gida Imran Matawalle ya fara danna horn baa dauki lokaci ba maigadi ya leko ta karamar kofa yana karewa motar kallo Imran ya sauke glass sukayi ido biyu da Imran matawalle da sauri maigadi ya koma ya buɗe get.ya kalli Rahama dake binsa da kallo ya ɗaga mata gira yana faɗin. "Kina jin yunwa my R, mu shiga ciki kisa mu wani abin kici." Da sauri ta kalleshi cikin fuskar san karin bayani tace. "Ina ne nan Imran?" Hannunta ya kamo cikin nasa yana matsa ƴan yatsunta yace. "Gidan Yayan Daddy ne ba kuma shi da matsala daga shi har matarsa, yanzu dai muje naga kin fara cin abinci sai hankali na ya kwanta." Babu musu tabishi suka shiga cikin gidan. Da murna da farin ciki suka tare su kamar sun san da zuwan nasu, sunyi sa'a kuma Alhaji Aliyu Matawalle yana gidan, tare aka zuba masa abinci da Imran sukaci, suna gamawa cike da damuwa Imran ya kalleshi cikin fuskar tausayi ya sanar dashi duk halin da yake ciki shida Rahama, ya kalli Alhaji Aliyu yana faɗin. "Uncle idan ban auri Rahama ba komai zai iya faruwa tsakanin mu da ita, shi yasa na zabawa kaina solution na zuwa wajanka ka daura mana aure muje muyi rayuwa mai daɗi." Cikin tashin hankali Ali Matawalle yake faɗin. "Ya akai kukai wannan gangancin Imran? Meyasa ba zaku hakura da juna ba tunda iyayenku basu so? Hakika naji haushin hakan, banso zaku yi irin wannan auran ba." Cikin zafin rai Imran yake cewa. "Babu kyau ne uncle? Shin addini ya hanamu yin irin wannan auran?" Aliyu Matawalle yaja numfashi "Addini bai haramta muku ba, sai dai addini yana so a gina auran abisa albarkar iyaye, ku kuma gashi zaku yi duka iyayenku basu kaunar ku kasance tare da juna, baku san albarkar su ne Imran?" Cikin rashin damuwa Imran yake faɗin. "Uncle kasa mana albarka kawai zata bimu Insha Allahu, saboda Uncle idan har baka amince da auran nan ba zamu iya yin wata irin rayuwa ne nida Rahama, saboda we love each other more than you know, please Uncle ka tabbatar da auran mu ko zuciyoyin mu zasu samu nutsuwa." Ganin yadda Imran ya dage ne ya tabbatarwa da Aliyu Matawalle cewa yana san yarinyar da gaske, dan haka cikin amincewa yace. "Shikenan zan sanar da Imam sai a daura gobe." Da sauri Imran ya matsa kusa da Uncle ɗin nasa ya rungume shi yana godiya. Tashi yai ya nufi parlor inda su mum bilki suke zaune, idanunsa kyar akan fuskar Rahama wacce tunda ya fito suke kallan juna, tunda ta ganshi yana fara'a tasan Uncle ɗin ya karɓi buƙatarsu. "Mum gobe za'a daura mana aure kisa mana albarka." Da mamaki tace. "Auran wasa kona gaske Imran?" Yatsina fuska yai yana kallanta yake faɗin. "Haba mum ni na girmi playing Allah, am telling you aure Uncle zai daura mana nida Rahama." Cikin shock tace. "Wane irin aure ne wannan zaku yi Imran? Ina

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads