Showing 69001 words to 72000 words out of 139785 words
Chapter 24 - Albi Book Complete document by Hajjace.txt
ɗin takeji yana jin yadda bayanta ke gogar b* ɗinsa. Cikin muryar rada yake faɗin. "Asuba ta gari Albi." Kusan minti goma ganin bai taɓa jikinta ba still yana rungume da ita yasa ta samu natsuwa, shi kuma abinda yasa ya ɗaga mata ƙafa yana son tasaba bacci ciki jikinsa, ta yadda baxata iya gujewa wannan sabon ba, haka baya son ta riqa yi masa kallo tamkar jikinta yake so, zai daure da duk yadda zaiji akanta, zai bata space na wata ɗaya yaga iya hankalinta da gudun ruwanta, duk da yasan zai wahala sosai. Ba'a daɗe ba taji saukan numfashinsa ta cikin wuyanta a hankali take kokarin sauke hannunsa dake zagaye da kugunta, kara riqeta sosai yayi, ɗan murmushi tayi itama bata daɗe ba ta samu bacci daman duka a gajiye suke. Sun kusa makara a sallar asuba, tare sukayi wanka ya jasu jam'i. Sai kusan 7 suka koma bacci, wannan karon da hijab ajikinta da riga marar nauyi ya haɗe rai yana kallonta yana girgiza kai yake faɗin. "Har kin manta rules ɗin kwanciyar mu?" Ta maqe kafaɗa da shagwaɓa take faɗin. "Yanzu rana yayi fa." Ya girgiza kai yana faɗin. "Koda tsakiyyar rana zamu kwanta, ko a parlor ko a ina cikin gidan nan bana son ki saka kaya ajikin ki Albi, bana son maimaitawa." Yana faɗin haka ya juya mata baya. Ta gane yayi fushi kenan, jiki a sanyayen ta sauke hijab ɗin jikinta ta cire doguwar rigar a hankali ta kwanta bayansa tana faɗa masa kalmar sorry, juyowa yayi ya sakata cikin jikinsa duka ya subbaci goshinta, da haka suka koma bacci wannan karon ta rigasa yin baccin, shima dama ya ɗauki hutun wata ɗaya, baida damuwa da zuwa clinic, ya turawa Maheera Matawalle test akan ta aiko driver da breakfast nan da zuwa 12. Kiranta ne ya shigo a wayarsa yana ɗauka ta gaishesa "Meya faru? Zaki tayar min da mata daga bacci." Ya faɗa yana shafa dogon gashin kan Rahama. "Yaya dama cewa zan yi na kawo maku nida driver?" Da sauri yace "Nooooo Mahee kiyi zaman ki, driver kawai ya kawo karki zo dan Allah." Ya faɗa yana sauke wayar ba tare da ya jira mai zata faɗa ba. Shima bai daɗe ba ya samu bacci ya kanainaye Rahama cikin faɗeɗen kirjinsa tamkar wanda za'a yiwa kwacenta, dukan su baccin gajiya su kayi, basu tashi ba sai kusan 1. Wanka sukayi a tare suka gabatar da sallar azahar suka haɗe cikin ƙananan kaya ita pencil jeans ne ajikinta da kuma top wacce ta sauka har kan gwiwarta. Shi kuma tree quarter ne ajikinsa da kuma shirt. Sauka sukayi ƙasa, tare sukayi breakfast tana zaune akan cinyoyinsa dan yace nan ne wajen cin abincinta koda ƴaƴan su sunzo bazai canja ba. Sai zuba masa shagwaɓa takeyi kala-kala shi kuma sai biye mata yake suna gamawa suka qara gyara gidan.
************
Ayinin ranar duk inda Rahama ta ɗora ƙafa anan Imran ke sauqe tashi, kwana biyu Imran yayi a gida ko kofar gate baya lekawa, abinci kuwa daman Maheera Matawalle ta daɗe da zama kukun su, idan ta gama driver zata saka ya kawo masu zuwa gidan su, kuma ta hakura da nacin da take yiwa Imran Matawalle zuwa gidansa, amman suna waya da Rahama sosai, Rahama tayi korafin rashin zuwan Maheera ɗin Maheera ta faɗa mata ba laifin ta bane laifin Yah Imran ne yaki bada damar zuwan nata, amman tayi mata alkawarin zata shigo. Kwanan su uku da tarewa a gidan su, su Mommy suka dawo, haka daddy ya faɗa xa'a daura aure, tarewar a bari sai next week idan kayan sun iso. Hakan yasa su Mommy suka cigaba da shirye-shiryen biki, daman babu Maheera cikin lamarin su, kuma hutunta ya kusa ƙarewa gara ta tattara tabar masu ƙasar duka. Misalin ƙarfe 9 na safe ta shiga parlorn mahaifinta cikin shigar blue shadda na doguwar riga wanda ya dace da kalar fatan jiki ta, ta gaisheda iyayen nata cike da fara'a mai girma Matawalle ya kalli ƴartasa da murmushi yana faɗin. "Mamana irin wannan farin ciki haka fa? ina xuwa kuma?" Ya jero mata tambayoyi yana kallonta ta kallesu duka tana faɗin. "Zanje gidan Yah Imran yinin wannan ranar duka na sane." Ta faɗa sounding so very happy cikin fuskarta. Mommy ta girgiza kai tana kallon Maheera cike da takaici, wani irin abu taji yana tsaya mata arai, "Mommy na tafi lokaci na tafiya." Ta faɗa tana yiwa iyayenta sallama, driver ya jata zuwa gidan Imran Matawalle.....
#Asmy b Aliyu
#Hajja ce
#Imran Matawalle
#Rahama Galadanci
#Humaida
#Maheera Matawalle
#Albi
Haske Writers Association
[11/24, 1:10 PM] Asmy B Aliyu😘: *ALBI...*
(my heart❤️)
*ASMY B ALIYU*
DA
*HAJJA CE*👈
PAID BOOK..#(500)
*Account Details*
0004157137
*Jaiz Bank*
*Asma'u Buhari Aliyu*
Shaidar biya ta
08086207764
*Katin waya MTN. Ta 07043079282 shaidar biya ta 07065283730 view WhatsApp*
31.....
Rahama na kitchen tana haɗawa bakuwarta abubuwan tarba, tana cikin yanka albasa sai ga Imran ya shigo kitchen ɗin, kallanta ya shiga yi, ganinta yake tamkar ƙara mata kyau akeyi kullum, tana sanye ne cikin wasu riga wacce ko cibiya bata rufe mata ba da wando wanda iyakarshi saman guiwarta, I Matawalle yaji zuciyarsa na shiga cikin wani irin farin ciki. Ta bayanta ya tsaya tare da kamo duka kugunta yana haɗe cikinsa a bayanta, kansa ya sakala a wuyanta tare da sumbatar kumatunta yana cewa. "Mahee tasa min ke tashi tsaye gashi nan na kasa yin baccin saboda bakya kusa dani." Rahama ta ɗan saki wani kayataccen murmushi tana faɗin. "Mahee ta cancanci lokaci na fiye da hakan, tana da kirki sosai ita kaɗai ke sona duk gidan ku." Imran ya saki wani tattausan smiling tare da riƙe hannunta da take chopping ɗin albasa. Door bell sukaji, cikin sauri Rahama ta fara shirin kwatar jikinta zata gudu ya riƙe sosai. A ruɗe take masa wani irin kallo idanunta ta fito dasu tana cewa."Kabarni naje na nemo kaya nasa kanajin dai Mahee a bakin kofa." Kin sakinta yai, yana riƙe da hannunta suka haye stairs. Rahama da sauri ta fizge hannunsa daga cikin nata, wardrobe ta buɗe da gaggawa ta zaro wasu riga da xani tasa, agaggauce tai hanyar fita zataje ta buɗewa Maheera ya riƙota cikin sauri, kallanta yake mai cike da tsantsar soyayyarta yake faɗin. "Wai duk saboda Mahee ake ta wannan rawar jikin?" Kafin tayi magana ya riga ta, "Kibi a hankali karki faɗi." Daga masa kai kawai tayi ta zare masa hannun ta fice. A hankali ta buɗe ƙofar, da wani irin farin ciki Rahama ta rungume Maheera tana janyota zuwa ciki, har kan 3seater ta kaita bakinta yaki rufewa dan daɗi har Maheera nacewa. "Aunty Rahama ke kaɗai ce a gidan ne naga kina ta murnar zuwa na?" Tayi magana cike da fara'a. Kafin ma Rahama ta bata amsa turaren jikinsa ya bayyana musu fitowarsa. Yana sakkowa daga stairs yake faɗin. "Mahee zuwanki ya hana min mata sukuni, komai da ance tayi zatace bari ta ƙarasa abun Maheera." Daɗi-dai lokacin da yake zama cikin soofa, ya ɗan kalli Rahama wace ke faman kallan Maheera tana dariya. Dukansu dariya sukayi kafin Rahama ta shiga kitchen dan kawowa Mahee abubuwan rabawa kafin ta gama girki. Cikin katon tray ta zubo su, Imran yace."Maimakon kice taje ta dauka shine zaki je kaɗai salon ki sha wahala?" Sai da ta ajiye akan center table sannan ta ɗago, hararasa tayi tana faɗin. "Meka maidani.?" Ta faɗa a shagwaɓe tana yakuna fuska, bece komai ba ta kama bakinsa da hannu alamar bazai koma cewa komai ba. Sai da suka ɗan taɓa hira shida Maheera kafin ya tashi, bedroom ya koma ita kuma Maheera ta koma kitchen wajan Rahama tana tayata aikin suna hira. Yana kwance a ɗaki yana aiki a system ɗinshi, jin shiru babu wani abu yasa shi miƙewa tsaye dan Rahama ko ɗan lekowa taganshi batayi ba. Wani kyakkyawan kit ya buɗe wanda cike suke da kwalayen sigarret, kwali ɗaya ya ciro ya maida sauran ma'ajiya. Wajan wardrobe yaje ya ɗakko lighter tare kunnawa ya koma gefe akan gado yana tada wani iri hayaƙi. Sai da suka kammala komai sannan suka jera kan dining table Rahama ta bar Maheera tana mopping ɗin kitchen ɗin ita kuma ta wuce dan gyara jikinta. Toilet ta shiga tayo wanka da alwala ta shirya jikinta cikin wasu riga da wando masu kyau. Gaban mirror ta ƙarasa tana gyara fuskar daga hoda sai lipstick da ta goga ta shafa turarukan dake kan mirror ɗin, tayi kyau ita kanta ta tasani. Parlorn ta dawo inda ta tarar Maheera tana kallo take ce mata. "Ya bakici abincin ba sis?" Maheera tayi dariya taba cewa. "Sai anjima Aunty Rahama yanzu kam cikina a cike yake." Zama Rahama tayi tana cewa, "Idan kinji yunwa dai ga abincin nan ki zuba kici." Toh kawai Maheera tace tare da faɗin. "Kinyi kyau Aunty Rahama Allah yasa dai Yaya na yagani?" Cike da jin kunya Rahama ta kawar dakai tana murmushi. "Aunty Rahama duk da cewa Aunty Humaidah kamar uwace a wajena wallahi bana san auran nan da za'a haɗa da Yaya Imran, ita kuma tun ba yanzu ba take mutuwar san shi, baya santa sam kowa ya sani bansan meyasa ita da Mommy suka dage ba. Ke kaɗai Yaya Imran yake so, duk wacce kikaga ta aure shi to zata sha muguwar wahala ne." Rahama dake sauraran Maheera zuciyarta kawai tafasa takeyi, duk lokacin da taji an ambaci sunan Humaidah sai taji kamar ranta zai fita, itafa ko Imran baya san Humaidah bata san ayi auran tafi son kowa ya kama gabansa. "Wane course kike yi ne Mahee?" Rahama ta canza topic ɗin nasu zuwa wani sashe dan ta tsani a kira sunan matar can a gabanta. Ganin haka yasa Maheera girgiza kai dan tasan za'a yi wani zama ne a gidan nan duk lokacin da aka kawo Aunty Humaidah. "Sechology." Cewar Maheera tana sake nazartar yanayin fuskar Rahama. "Wow masha Allah, Allah ya bada sa'a." Mahee tace amin. Hira sukaci gaba dayi har aka yi azahara suka gabatar da tasu sannan Rahama tace da Maheera taci abinci bari taje wajan Imran. Batayi knocking ba kawai ta murda handle, idanunta ne suka shiga karaɗe ɗakin ganin yadda ya cika da hayaƙi gashi warin siggaret, yana baje kan gado sai narkar baccinsa yakeyi hankali kwance. Jiki a sanyaye Rahama ta isa wajan shi ta zauna a gefenshi tana kare masa kallo. A hankali ta zura yatsunta cikin sumar kanshi tana hautsinata kafin ta shiga zubar da hawaye, bakinta takai saitin nashi ta sumbata tare da kwantar da kanta saman faffaɗan kirjinsa. Kamata yayi taji haushi ganin yasha mata sigari a cikin gidan auranta, sai dai tana haɗa ido da kyakkyawar face nashi taji ana ninka mata soyayyarsa cikin zuciya. Hannunta taji an riƙe ta miƙar da kanta suka hada ido dashi, ganin hawaye a fuskarta yasa shi saurin janyota ta faɗa jikinsa, kamar ya taɓo ta kawai yaji ta fashe da kuka. Ya shiga lallashinta yana tambayarta abinda akai mata, cikin kuka take faɗin. "Kafiso a dinga cewa mijin Rahama bashi da kamun kai ko?" Imran ya cije lips tare da jan numfashi yana sake mannata a kirjinsa. "Zan dena my Albi, kici gaba da addu'a wani lokacin ne ina jin kamar idan ban shaba zan haukace, idan har bansha ba ina jin zuciya ta da numfashi na suna kokawa but Insha Allahu zan dena kinji.?" Ya faɗa da wani irin slow voice. "Haka kake cewa kullum zaka dena amma ni bana ganin alama dan Allah ka dena kar kasa bakin cikin shan abubuwan su kashe ni." Da wani irin sauri ya ɗago mata da kai yana kallan beauty face nata yake cewa. "Kidena cewa haka, ke kadai gareni da keyi min addu'a, kidena maganar mutuwa na rokeki." Daga kai kawai tayi ta miƙe zata tashi ya wani fizgota ta koma kan kirjinsa, lips nashi ya turo yana lumshe ido murya ƙasa-ƙasa yake faɗin. "Kiss me Albi." Harararsa tayi cike da shagwaɓa take san kwacewa ya janyota sosai jikin tare da kai bakinsa tsakiyar kirjinta yana bata wasu kisses masu zafin tsiya. Wani irin numfashi Rahama ta sauke tana wani rintsa ido tare da hadiyar wani tsinkakken yawu data rasa daga ina ya fito bakinta ya wuce zuwa cikin cikinta. Tunawa tayi da Maheera a parlor da sauri ta shiga kokarin kwace jikinta tana gaya masa Maheera zatajita shiru, amma Imran yaki sakinta har sai da ta biye masa. Ganin yana shirin sanyata wanka dole yasa ta dinga yi masa magiya akan ya barta ta koma wajan Mahee sannan ya rabu da ita. Turo baki tayi tana yi masa wani kallo mai cike da tsantsar soyayyarsa tace dashi. "Kuma sai na gaya mata abinda kai min." Ta juya zuwa kofa yace. "Idan na fito zan gwada yi agabanta sai muga wazaiji kunya."
Ficewa tayi murmushi ɗauke a fuskarta, tana sauka suka haɗa ido da Maheera Rahama ta nufi wajan dining tana cewa. "Baccinsa yake sha bashi da wata matsala da kyar ma ya tashi." Dariya sosai Maheera keyi ganin yadda Rahama kesan kare kanta, abincin ta zubo takai gaban Maheera tana cewa. "Gashinan na zuba mana tunda naga ke bazaki zubo ba, faraci bari nazo." Ta sake komawa ɗakin still ta ganshi a kwance, wannan karan yayi ruf da ciki tabi cinyoyinsa masu cike da gashi da kallo, sannu a hankali ta ƙarasa wajan tasa hannunta tana sake kwantar dasu. Kamar tasan idanunsa biyu tace. "Ka tashi anyi azahar fa tun ɗazu." Yadda take shafar masa cinya ne yake neman tayar masa da hankali, jin hannunta a karshen cinyarsa yasa shi saurin riƙota, shanyayyun idanunsa ya zuba mata yana cewa. "Please Albi karki hargitsani bayan kuma rowa kike min." Turo lips tayi tana wani kifta idanuwa ya kawar da kai yana sakar mata hannunta. Shaye da toka ta miƙe tsaye zata bar masa ɗakin yai saurin fizgota yana mannata akan gadon, da wata irin murya yake cewa. "Mekuma nayi?" Ta harareshi tana faɗin. "Bakomai." Hannunta ya kamo ya ɗora a kirjinsa, yadda taji bugun zuciyarsa yana sauri ne yasa ta ware ido tana sake danna hannun a wajan take faɗin. "What is wrong with you ALBI.?" Yadda take furta kalmar Albi ɗin yasha banban da yadda ake faɗa, da wani irin salo tare da murya mai daɗi take furtawa, Imran ya zura idanunsa cikin nata yana sake mannata a jikinsa yake cewa. "Soyayyarki, ALBI kaunarki ce take neman fasamin zuciya, gashi kishi ya hanaki mallaka min gabaki ɗayanki, ko so kike wata ta fara karbe samartaka? Uhmm? Kinsan adadin matan dake buɗe legs suna so muyi dasu? Kinsan adadin matan dake amfani da desire pills suna bawa maza suna son dan mu kusance su?" Yai shiru yana sake matse shoulders nata, face nata dake gefe ya juyo da ita yaga tasha toka tana wani irin huci yace."I'm telling you the truth, please Albi ki kula dani karna faɗa halaka." Fizge jikinta tayi ta miƙe tsaye ba tare da ta kalleshi ba take faɗin. "Ka tashi kayi sallah kazo kaci abinci." Ta faɗa tare da ficewa daga ɗakin. Imran ya saki wani huci yana rintsa ido. Sakkowa yai ya faɗa toilet, shower ya sakarwa jikinsa a jikin jacuzzi, lumshe idanuwa yai yana hango Rahama a cikinsu, gaba ɗaya ya rasa yadda zai yi da rayuwarsa musamman yanzu da sukai aure duk tunaninsa Rahama ce, jin daɗin shi itace walwalarsa itace, farin cikinsa Rahama taya zai yi rejecting auran Humaidah dan ya samarwa da ALBI ɗinsa jin daɗi? Da kyar ya iya yin wankan tare da alwala ya fito daure da towel ya nufi bedroom ɗin da suke kwana. Jeans da t-shirt ya sanya wadanda sukayi dai-dai da fatar jikinsa sukai masa kyau, yabi sumar kanshi yasa handrayer ya busar da ita tare da hawa kan praymat ya gabatar da sallar azahar, yana idarwa ya miƙe, wajan mirror ya nufa ya gyara sumarsa tare da bin duka jikinsa da wasu turaruka masu matukar tsada da sanyaya zuciya. Wayarsa yaje ya ɗakko yasa sneekers wanda ya hau da kayan jikinsa sannan ya fito zuwa parlorn. Ƙamshin sa kawai zai tabbatar maka da zuwansa, duk da Rahama nasan ganinsa daurewa tayi taki juyawa, batasan wajan su ya nufo ba sai da taji ya sargafo hannayensa ya rungumeta tare da bata wani side kiss a gefen kuncinta, ta ware ido akan fuskar Mahee wacce gabaki ɗaya lamarin ya gama burgeta. "Wow Yaya gaskiya kana bawa soyayya hakkinta, kai min addu'a nima na samu mai min irin soyayyar da kake yiwa Aunty Rahama." Imran ya leka fuskar Rahama ganin tana ware idanu yasa shi miƙewa sosai ya janyota suka koma wajan dining yana faɗin. "Kina so mijinki ya mutu da wuri ne kawai Mahee." Maheera ta ware ido baki buɗe take faɗin. "Amma ai baka mutu ba kai." Imran na zaunar da Rahama saman kafafunsa yace. "Nima kiris ya rage ta kasheni, but Albi tana bani wahala right?" Ya ƙarasa maganar yana dagawa Rahama gira. "ALBI.. AL..BI..Yaya menene kuma ALBI?" Smiling ya saki yana sake rungume Rahama a kirjinsa yake faɗin. "Ohhh Mahee kin samana ido, kawai ki shirya muje nai drooping ɗinki a gida." Cike da sanji ta marairaice tana faɗin. "Pleaseeeee." Hannayensa ya ɗora saman kirjin Rahama yana matsasu idanun a lumshe yake faɗin. "ALBI yana nufin my Heart da Hausa kuma Zuciyata, Mahee bana san sa ido kinsani." Murmushi Maheera tayi tana toshe baki da hannunta batace komai ba. Maida hankalinsa yai wajan Rahama da haɗe fuska yana faɗin. "Albi Feed me." Rahama ta kawar da fuska ya sake kissing tsakiyar bayan wuyanta, tayi saurin rintsa ido jikinta na wani irin sanyi. "Please Albi." Tana shan toka ta wani ɗakko plate tana zuba abincin. Yana murmushi yake karɓa har sai da yaji ya koshi sannan ya miƙar dasu yana riƙe da hannunta suka ƙarasa wajan Maheera yana cewa. "Kuyi hira bari naje na dawo." Ya sumbaci hannunta sannan ya fice daga parlorn. Sosai suka sha hira suka sake yin girki wajan karfe biyar da rabi Imran yaje ya ɗaukesu suka maida Maheera gida su kuma ya wuce da Rahama Ado Bayero mall suka hau liloo aka ɗan caccafke kafin su koma gida.
*************
Tana kwance a cikin jikinsa