Header Ads
Showing 9001 words to 12000 words out of 139785 words

Chapter 4 - Albi Book Complete document by Hajjace.txt

Ads the beginning of article before Image

11 Jun 2024

983

Ads at the middle of Article

zai haye stairs kawai yaji ta rungumeshi, kafin kace me zuciyarsa ta fara zafi, cikin shasaheƙar kuka yaji tana magana. "Dan Allah Imran karka hukunta zuciyata akan abinda ba ita ta ɗorawa kanta ba, bansan me yasa baka san ko kallona ba Imran. Daddy da Aunty suna son ganin wannan abin namu ya ƙullu amma kai ko a jikinka why.?" Hannu yasa ya fizgota daga bayanshi tare da hankaɗata gefe yana huci, nuna ta yai da yatsa yana cewa. "Allah ya tsinewa soyayyar da kike yi min Humaidah, to hell with banzar soyayyarki, mteww! kinga nayi miki kala da ƴan bariki? Barikiji na gaya miki duk iskancin mace tayi ta gama bana ra'ayinku, nuna min breast ko wasu boost bazai sa naji sha'awarki ba, idan da ina san mata da yanzu kinga suna biyoni cikin gidan nan. Humaida ki kama kanki kafin na nuna miki kalar nawa rashin mutuncin, oya get out of here right now..." Yaja mugun tsaki yabar mata parlorn ta hanyar hayewa stairs, yana shiga bedroom ya rufe yana jan tsaki a karo na ba adadi. Ya rasa me yasa mata basu da aji a wannan zamanin, kowacce sai tayi shigar banza tazo masa kamar sun ɗauka shi ɗin wawa ne akan su. Shi kam har yanzu beji yana ra'ayin wata ɗiya mace ba face Rahama, itace kawai ko kallanta yafiyayi sai yaji wani irin yanayi a tare dashi, idan kuwa ta riƙeshi ko tai hugging ɗinsa wani lokacin sai ya yi wankan tsarki, kuma be taɓa jin yana sha'awarta da zina ba, sha'awarta da soyayyarta a cikin jininsa suke baya tunanin akwai abinda zai ruguza musu wannan tafiyar. Buga kafafuwa Humaidah tayi ta juya tana zumɓurar baki, dama ta corridor ta biyo hakan yasa ruwa be taɓa ta ba da zata shigo, yanzu kam da yake ranta a ɓace yake ta cikin ruwan saman tabi, tana zuwa ta fashe da kuka Mommy ta shiga tambayarta.
"Ya akai kuma.?"
"Wallahi Aunty Imran zuciyarsa kamar ta kafiran farko haka take, sam yaki ya bani muhimmanci kullum cikin kyara da rashin mutunci haka yake yi min." Mommy shaye da toka ta riko Humaidah tana jijjigata tace.
"Ki rabu dashi nace miki, indai Imran Matawalle ne Humaidah ya kusa zama naki sai yadda kikai dashi, a tafin hannuna fa suke daga shi har Matawallen. Kedai abinda nake so dake kici gaba da kasancewa aduk inda idanunsa suke kafin na gama shirya miki komai." Cike da farin ciki Humaidah ta rungume yayarta tana yi mata godiya dan wani mugun so Humaidan keyiwa Imran.
Wata ƴar ƙaramar trolley bag Imran ya janyo ya buɗe, kwalaɓen beer ne a cikinsu a jere, ya zaro kwalba guda ɗaya ya rufe sauran ya mayar ya ɓoye, jikinsa har tsuma yake saboda ƙaguwa da yai yaji ruwan barasar cikin bakinsa, ya buɗe kenan zai fara sha yaji wayarsa tana ringing kuma ringing ɗin special ne yasawa Rahama shi. Dafe goshi yai yana jin kansa yana sarawa, yaje ya ɗauki wayar ba tare da yace komai ba.
"Jikina ya bani cewa kana cikin bad mood, tell me Imran meke damunka?" Imran ya rintsa ido yana girgiza kai, mezai gaya mata a wannan yanayin nashi? Kwalbar beer ɗin ya dire a saman mirror, gado ya hau tare da janyo pillows ya rungume yana jin wani zafi yana taso masa duk kuwa da sanyin da akeyi sakamakon ruwan sama. Saman kansa yai da kasa ɓoye mata cewa yana cikin damuwa, murya a sanyaye yace.
"Waccen matar ce take neman haukatani." Rahama kamar tana gabanshi ta marairaice fuska tana faɗin.
"Mommy ce right?" Imran Matawalle ya gyaɗa kai ba tare da yace komai ba.
"Shine ka damu?"
"Kinsan me sukai min ne? Idan kika san me sukai min sai kin fini shiga damuwa, but komai ya wuce karkisa cikin ranki yai affecting karatunki." Cikin serious Rahama take faɗin.
"Naji to amman karka sha beer Imran, ruwan sama akeyi a irin haka ana son bawa ya tashi ya roki lillahi duk abinda yake so. Don't be sad Imran."
Rintsa idanuwa yai yana jin ina ma a fili take yi masa managa, ya sake jan pillows ɗin yana rungumewa, Rahama daban take a cikin mata, tun bata kai haka ba tana da baiwa da fikirar yi masa magana. Sosai yake jin shakkar yarinyar dan ko Matawalle bayajin shakka kamar yadda yakejin ta Rahama Abubakar Galadanci. Sai dai ji yai bazai iya hakura da ƙin shan barasar ba, zuciyarsa tana sake kwaɗaita masa daɗinta da kuma yadda idan yasha zata kawar masa da, duk wata damuwa da yake ciki yanzu.
"Alright R Galadanci zan kiyaye." Tunda taji yace zai kiyaye baice mata bazai sha ba tasan sai ya sha, rintsa ido tai tana cewa.
"Allah ka nuna min randa Imran Matawalle zai dena shan beer." Yana jinta ya saki ajiyar zuciya tare da faɗin.
"Amin." Hawayen da suka zubu mata saman kyakkyawar face nata ta shiga gogewa, har cikin ranta take jin zafin shan barasar nan ta Imran, sai dai babu yadda zatayi dan a hakan take jin tsakanin kaunarsa a zuciyarta.
"Kayi alwala kai shafa'i ka roƙi Allah ya yaye maka matsalarka. Cikin dare idan ka farka sai kai wutir." Murmushi yai yana faɗin.
"As you wish R Galadanci."
Itama murmushin tai a duniya tana so taji ya kirata da wannan sunan, shi kaɗai ne ke kiranta da haka, dan ko a school A Galadanci suke kiranta. Sallama tai masa suka ajiye wayar, Imran ya tashi da saur, wajan beer ɗinsa ya nufa ya buɗe tare da janyo glass cup ya zuba yana sha, cikin rintsa ido dan beso yaki bin shawarar Rahama ba, kawai babu yadda zai yi ne dole sai yasha sannan zai dawo cikin hankalinsa.


*******
Washegari a azahar a garin Abuja tayiwa Alhaji Abubakar Galadanci, sashen Hajja ya sauka anan aka shirya masa abinci na ci dana sha, bayan sunyi sallah shida ɗan uwansa Alhaji Uthman suka zauna a wajan Hajja sukaci abincin tare cikin tsantsar zumunci da san juna. Hajja ce tayi magana daka ganta kasan cewa tana cikin farin ciki da ganin yanayinsu a haka. "Dole na sake miƙa godiya ta wajan Allah subahanahu wata'ala daya haɗe min kawunanku yasa muku ƙaunar junanku gashi har zaku sake kulla zumunci ta hanyar haɗa zuriyarku yin aure. Kai Alhamdulillahi, ina fatan wannan haɗin ya zama silar kullewar aminci da jin daɗin mu baki ɗaya." Duk suka haɗa baki wajan cewa, "Amin Hajja." Tayi murmushi tana faɗin "Yanzu gashi kun haɗu anan wane lokaci kuke ganin ya dace ayi bikin jikokin nawa?" Abubakar ne ya fara magana ta hanyar cewa. "Ni ko yanzu a ɗaura auran Rahama Hajja, bani da wani buri irin wannan lokacin, alfarma ɗaya zan rokar mata wajan Farooq ya barta taci gaba da karatu, nasan burin Rahama kenan tayi karatu mai zurfi." Hajja tace. "Shima yace bazai hanata karatu ba musamman da yanzu ta fara jin daɗin karatun, jiya ya gama faɗa anan inda kake zaune yace zai barta." Abubakar yai murmushi daɗi ya cika ransa, yasan idan Rahama tai aure dole jinin Matawalle yabar liƙe musu.
"Ina ganin me zai hana asaka wata biyu ko uku tunda an kammala masa gininsa, abinda ya rage kaɗan ne sai kuma haɗa kayan lefe da siyan kayan da za'a zuba cikin gidan." Cewar Uthman Galadanci idanunsa akan ɗan uwansa. Abubakar yaja numfashi cike da ƙasawa yake faɗin." Dan Allah a barshi one month komai da komai ba sai an sake jan auran nan ba tunda komai na gida ne. Ni yanzu ina komawa zan sanar da mahaifiyar Rahama dan ta fara shiri. Itama Rahamar zanje na sanar da ita dan ta sani." Hajja ta girgiza kai tare da cewa, "Mu barshi wata uku sannan anyi komai cikin nutsuwa." Gabaki ɗaya suka amince suka fara tattauna yadda abubuwan zasu kasance. Farooq ne ya shigo parlorn ya gaishe da Abubakar Galadanci wanda zai zame masa suruki nan gaba kaɗan. Amsawa yai cikin jin daɗi saboda yanzu wata irin soyayya Alhaji Abubakar Galadanci yake yiwa Farooq ganin zai raba yarsa da mashayin giya kuma ɗan gidan makiyinsa.
"Sai a fara shiri Farooq biki nan da wata uku." A gigice Farooq yake kallon Hajja bakinsa ya kasa rufewa yace. "Dagaske Hajja?" Tana zabga masa harara tace. "Kasan na saba yi maka karya ɗan rainin wayo." Dariya Farooq yai yana shafa ƙasan gemunsa yana faɗin. "Wannan albishir da kika bani my Hajja dole nai miki ankon biki idan an fitar."
Carbin hannunta ta jefeshi dashi su Alhaji Abubakar natai musu dariya. Sai da aka shirya duk yadda abubuwan zasu kasance musamman da komai yazo gida ɗaya sannan suka tashi, da yamma Alhaji Abubakar ya koma garin Kano cike da farin ciki. Ummy ya sanarwa da duk abubuwan da suka tsara tayi murna sosai dama bata da burin irin ganin takai Rahama ɗakin mijinta, dan tana shakkar halin Imran Matawalle karya ɓata mata rayuwar yarinya ta hanyar shaye-shaye ko ya kwace mata ƴan matanci basu sani ba.


*******
Zaune yake cikin katafaran sitting room ɗin mahaifinsa ya ɗora ƙafa ɗaya akan ɗaya yana faman girgizasu, tunda yaga Mommy zaune a gurin yasan akwai problem ya kuma shirya mishi kona menene dan ba zai sake bari a ringa raina masa hankali ba. Kamar ance ya ɗaga kai suka haɗa ido da ita tana wani irin murmushi wanda kana gani kasan na tsantsar mugunta ne, Imran ya ɗauke kai yana lasar kyakkyawan lips nashi mai matuƙar laushi sai kyalli yake yi. Fitowar Matawalle zuwa parlorn ne yasa Imran sake marairaice fuska, cike da kulawa yaji mahaifin nashi na cewa. "Morning yarona." Imran ya ɗan yatsina fuska cike da shagwaɓa yake faɗin. "Dad kasa na makara zuwa wajan aiki, nurses na can na jira na." Matawalle ya ƙarasa wajan da yake, hannu yasa a cikin sumar Imran yana cewa. "Ayya my son tun jiya da na dawo daga Abuja nake san ganinka, shi yasa tun asuba nace kafin ka fita kazo ina san ganinj, kayi breakfast ko?" Kallan Mommy Imran yai wacce ta zaro ido tana jiran taji amsar da zai bayar taji yana faɗin. "Daddy tun lokacin dana rasa wacce ta kawoni duniyar nan na fara kame-kamen abinci, you know Dad akwai abubuwan da banso amman gidan nan shi suka yi I don't know ko dan karnaci ne." Mamaki ya kusa kashe mommy ba buɗe take kallonsa, tana shirin yin masifa sai kuma ta tuna buƙatarta a wajanshi, ta karya murya cike da kulawa take faɗin. "Haba Imran, kaida zanta fama akan kazo ka faɗi abinda kakeso kullum sai dai kace aƙoshe kake? Ai shikenan korafi ya kusa karewa tunda aure zakayi kaga matarka komai kake so zatai maka." Matawalle ya saki murmushi yana riko hannun Imran "Soon Hajiya dan bani da buri irin ganin yarona yayi aure, kaga kaida Humaida kunyi matuƙar dacewa da juna, haka kuma zamuyi farin ciki idan....." Enough is enough Daddy, Humaidah kuma? Ni nace ina san wata Humaidah? Daddy bana santa wallahi, idan na tashi yin aure zan sanar daku bawai aje a nemo min matar da zan aura ba kamar wani gara. Mommy nasan duk shirin kune, to ki gayawa Humaida wallahi bazan aureta, idan ma zata je ta samu choice ɗinta taje ta samo amman ba dai ni Imran ba." Matawalle ya kalli Mommy ganin tayi kicin-kicin yasa hankalinsa ya kuma tashi yace. "Meye laifin Humaidah my son?" Shaye da toka Imran yace. "I don't like her that's all Dad." Ya juya yace da Mommy, "Kinji abinda yace." Shaye da toka ranta kamar zai fito tace. "Naji tunda Imran ɗan mai da mai ne shi yasa bazaka nuna muhimmancin wannan auran ba, Humaidah ina yi mata maganar ta amince me yasa shi bazaka tursasashi ba? Ni dama can Imran ya raina ni bare nasa shi yin abu, ya nuna min cewa na uwarsa bace." Tana direwa shima ya miƙe yana zura hannuwa cikin aljihu ya kalleta yana faɗin. "Dama da uwata ce bazata min tilas ba, duk wata uwa ta gari tana san farin cikin ɗanta. Maganar aure kuma bazan auri Humaidah ba koda zan mutu banyi aure ba." Yana kaiwa nan ya bar sitting room ɗin. Mota ya shiga mai gadi cikin sauri ya tashi ya buɗe masa, a fusace ya figi motar ya bar gidan zuciyarsa na zafi.


Bayero University Kano.....


Tunda ya parker motarsa ɗaliban dage wajan dama waɗanda suke wucewa suka zuba ido suna jiran ganin wanda zai fito daga ciki, shi kuwa gabaki ɗaya ji yake tamkar zai rabe gida biyu saboda tsabar zafin da yakeji a zuciyarsa. Wayarsa ya janyo ya shiga kiranta, bugu ɗaya Rahama ta ɗauka lokacin ta fito daga hostel zata tafi department ɗinsu. Ganin kiran Imran yasa ta dagawa cike da farin ciki dan batayi tsammani ba, tasan a wannan lokacin zai iya kasancewa yana kan gado yana shaƙar bacci. Tana karawa jikin kunnanta taji yanayin muryarsa gabanta ya faɗi.
"What happened to you Imran?" Yayi shiru ya kasa cewa komai, hankalinta ya sake tashi tace.
"Please say something kar kasa na shiga cikin tashin hankali." Muryarsa a can ciki taji yace
"Where are you now?" Rahama taja wani numfashi tace.
"Nafito daga hostel yanzu."
"Okay ki jirani gani nan." Cikin sauri tace.
"No ka sanar dani kai kana ina sai na ƙaraso, please karkai tuƙi naji muryarka ba kwanciyar hankali." Numfashi yaja yana ɗora goshisa kan sitari yace.
"Opposite department ɗinku." Bata kuma jin abinda zai faɗa ba ta sauke wayar, tafiya kawai take zuciyarta na sake-sake abinda ya ɓatawa Imran rai. Duk wanda ya ganta yasan idanunta a rufe suke saboda yadda take sauri, sanye take cikin Dubai Abaya red color tasa wani ɗan ƙaramin hijabi fari, shigar tayi mata matukar kyau, handbag ɗin dake hannunta white da flat shoe shima white in color, tana zuwa area ɗin ta hango motarsa kai tsaye ta nufi wajan, muryar Suraaj ce ta katse mata hanzari ta juyo shaye da toka tana kallansa. Imran kuwa kamar ance ya dago, idanunsa suka sauka akan Rahama tsaye da Suraaj, ransa ya kuma ɓaci besan lokacin da ya murɗa handle ɗin motar ya fito ba. Sanye yake cikin farin wando da red ɗin t-shirt, kafarsa sanye cikin sneaker red in color ya ƙarasa inda suke, kallansa kawai mata da mazan gurin suke suna mamakin waye shi? Ina zashi? Yana zuwa ya fizgo hannun Rahama dake yiwa Suraaj masifa yajata tare da jefata cikin motar ya rufe. Wajan Suraaj ya koma tare da riƙo masa wuyan riga yana faɗin.
"Last warning da zaka sake yi mata magana koda ta gaisuwa ce, idan ba haka ba zaka ƙarasa school ɗin nan cikin nadama." Yana kai nan ya hankaɗashi ya koma mota yana harararsa.
"How dare you zaki dinga kula maza irin waɗannan? Oh! dama ba karatun kika zo yi bako? Allah ya tona miki asiri da ido na ba wai labari aka bani ba. Da haka kike san ki faranta min? You say zaki cika min buri na kiyi karatu mai zurfi har ki zama Dr like me, shine kinzo kina biyewa samarin school Rahama." Yadda yake masifa ne kamar zai rufeta da duka yasa Rahama fashewa da kuka, nan da nan Imran ya shiga cikin hankalinsa, ya rufe idanuwa yana dafe kai yadda yaji kukan nata yana dukan duk wani jini dake bin jikinsa. Imran Matawalle ya riƙo forehead nata wanda hakan ya sake sanyawa Rahama ta sake fashewa da kuka tana kokarin fisgewa. Ganin haka yasa shi fizgota gabaki ɗaya ta dawo jikinsa already glasses ɗin motar tinted ne. "Shiiii so sorry R Galadanci I don't mean to hurt you, rai na ne a ɓace, kuma nazo naga kuna neman ƙara min wani ɓacin ran." Rahama ta fara magana cike da shagwaɓa wacce Imran ɗin ne kawai zai iya taking nata tace. "Shine kawai zaka fara min faɗa? Kai baka jira kaji me nake ce masa bane? Kana tunanin bana jin maganarka ko?" Banyanta ya shiga bubbugawa cikin lallashi yana faɗin "
sorry please." Jin tana san tashi daga jikinsa ne yasa haka kurum yaji baya san tabar chest nashi, yasa hannu ya kuma rungumeta, Rahama najin yadda zuciyarsa ke wani irin bugu tace. "Toh ka barni na zauna please." Imran Matawalle ya rintsa ido, taya zai gaya mata yana jin nutsuwa a yadda suke yanzu? Ji yake tamkar tana dagashi zai rabe biyu saboda yadda wani mugun feeling nata ke ratsa magudanar jininsa. "Wait a little while R Galadanci, stay like that ina wani ɗan research ne." Rahama tai luf har tana sake kwantar da kai ta yadda zai yi research ɗin da kyau. Gaba ɗaya suka shiga cikin wani yanayi ga ƙamshin turarukan su da ya hadu ya bata wani irin ƙamshi mai daɗaɗa zuciya yasa sun kuma fadawa cikin yanayin. "Ya Imran." Rahama ta faɗa a hankali, da sauri Imran ya ɗagota ta kalleshi taga idanunsa sun sauya, gyara zama tayi kan seat tana gyara rigarta tace. "Waye ya ɓata ma rai?" Imran ya kasa magana har lokacin be gama controlling nutsuwarsa ba.
Ganin ta zuba masa ido ne yasa shi yin wani ƙaramin murmushi yana faɗin. "Komai ya wuce, ya karatun?" Turo baki tayi tana faɗin. "Ni dai ka gaya min." Imran yai dariya har white teeth nashi suka fito yace "R Galadanci, you ko?" Kafaɗa ta maƙale tace. "Karkai min wayo kawai ka gaya min." yace "Mommy ce." Gaban Rahama ya buga, ta zaro ido tana faɗin "Humaidah again?" Ya ɗaga mata kai alamar eh tare da zuba mata manyan idanunsa. Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun yanzu idan aka aura masa Humaidah ya zata yi ita? Ina zata kai tarin kaunar da takeyiwa Imran Matawalle? Gashi tana jin wani mugun kishinsa, wanda bazai bari ta iya zama da kishiya ba, so take ta kasance ita kaɗai a gidansa dama zuciyarsa baki ɗaya. Wayarta sukaji tana ringing sai da Imran ya bata damar ɗakkowa sannan ta zaro wayar a, handbag, sunan Ummy ta gani kallon Imran ɗin tai tace. "Ummy ce." daukar wayar tayi tareda yin sallama tana faɗin. "Ummy Good morning."
Cikin farin ciki Ummy ke cewa, "Morning Rahama muna school ɗinku kina ina?" Gabanta ya faɗi ta kalli Imran Matawalle da ya kafeta da sexy eyes nashi. "Ummy lafiya dai ko?" Murmushi tai "Lafiya

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads