Header Ads
Showing 132001 words to 135000 words out of 139785 words

Chapter 45 - Albi Book Complete document by Hajjace.txt

Ads the beginning of article before Image

11 Jun 2024

1008

Ads at the middle of Article

kuma ki buɗe wayarki ki turo min new number ɗinki umarni na baki." Da wani irin gudu ta fice tana sake fashewa da kuka jikinta na yi mata rawa. Cikin sofa ya faɗa tare da lumshe idanunsa yana jin gaba ɗaya ransa babu daɗi, gaba ɗaya Abubakar Galadanci ya sauya masa Rahama, ya cusa mata ƙinsa ya rasa dalili kuma. A yadda yake jin soyayyar Rahama baya jin zai iya kyaleta duk abinda za'a yi masa, ya ɗauki alƙawarin mallaƙeta koda kuwa mahaifinta baya so, ya riga ya saba da ita. Rahama ta zame masa jini a cikin hantarsa, zai bata ɗan lokaci ƙanƙani yaga idan zata dawo gareshi, in har taki kuma to zai nuna karfin iko da kuma dukiya tare da ƙarfin mulkin mahaifinsa ya ɗauketa kacokam. Da sauri ya tashi ya nufi upstairs ya faɗa toilet yana so yasan me take nufi da ya raba Ummy da Abban su dan sam be fahimci abinda take nufi ba. Rahama na shiga gida ta shiga ɗaki ta kulle, Imran ya gama raina mata hankali. Girgiza kai kawai take tana so taji ta tsaneshi cikin ranta amma ta kasa, a fili ta furta. "I hate you... I really hate you Imran." Knocking taji ta miƙe tana share hawaye. Hajja ta gani rungume da little Aysha, miƙa mata ita tayi tana tabe baki tare da faɗin. "Gulmammiya kyaji da guntun iyayinki, kuma Allah yasa Imran ya sake yin wani auran matar ta sace zuciyarsa kinga sai yaji daɗin mantaki, keda ba goal ba kuma ba mace ta karshe a duniyar nan ba." Ta juya ta barta a gurin. Gefen bed ta zauna tana kallan little Aysha hawayenta yana sauka a jikinta, dole ta shirya taje gidan Hajiya Babba gurin Ummy ta lallasheta su dawo. Ta kwantar da Aysha ta shiga shiryawa cikin wata doguwar rigar atamfa orange da ratsin black na zanan stars a jiki. Mayafinta black tayi amfani dashi sannan ta zura little Aysha a cikin babybag tare da kwantar da kanta a saman kirjinta. Ko Hajja bata yiwa sallama ba ta ɗauki car key ɗinta suka fito, kwantar da little tayi a seat ta maƙala mata belt sannan ta tashi motar. Imran na fitowa da hancin motarsa itama Rahama na danno tata, ɗauke kai tayi kamar bata ganshi ba. Shi kuwa mamaki yake ina zataje? Yana ganinta taja motarta yabi bayanta a ɓoye. Gidan Hajiya Babba ta nufa dan haka tana gama yin parking shima ya dire tashi, haushi ya kamata cikin sauri ta ciro little suka nufi ciki. Yana bayanta tamkar tare suke, shi suka yiwa sannu da zuwa ma ba ita ba, ta sake jin wani haushin. "Imran tare kuke ashe?" Cewar Ummy tana gyara zamanta kanta a ƙasa saboda kunyarsa takeji yanzu. Shi kuwa ganin Ummy yasa ya fara gane abinda Rahama take nufi, kenan saboda auransu suka samu matsala da Abba? Meke damun Abubakar Galadanci ne? Cike da respect yake cewa. "Ta sameni ne akan cewa sai na rabu da ita tana cewa na shiga tsakanin iyayenta. Ummy indai akan Rahama dani ne hakan ya kasance banji daɗi ba. Wannan karan da gaske zan rabu da ita saboda zaman lafiyarku, zan hakura gabaki ɗaya da ita." Cikin kuka Rahama ke cewa. "Yafi ai nima ka barni na yiwa mahaifina biyayya kamar yadda kake yiwa naka, kaje can kaji da matarka." Zuciyarsa na suya yace. "Shikenan zanyi yadda kike so dama biyu ne ya rage." Da wani irin fushi tace. "Katse su duka kaga sai ka dena ganin iskanci na." Da sauri Ummy ta daka mata tsawa, da kuka Rahama tace. "Ummy cewa fa yai yasan dole na kai kaina gurinsa, meya maidani?" Da fuskar fushi Ummy tace. "Tashi ki shiga wajan Kausar." Rahama ta ruga da gudu tana kuka. "Ummy dan Allah kiyi hakuri bana tare da Rahama dan na ruguza ahalinta idan har nayi hakan tabbas ban kyauta ba." Ummy tayi murmushi kawai tana faɗin. "Indai kana san Rahama Imran na amince maka, abinda nake so da kai kawai shine kajira lokacin da Abbanta zai sakko daga zafin zuciyarsa. Dawowata gidan nan kuma babu wanda yasan dalili ina fatan ka fahimceni?" Da wani irin kwarin guiwa yake amsawa Ummy wannan ya bashi damar sake nunawa Rahama cewa shine mijin kuma mai cikakken iko akanta. Sallama yai musu ya tafi cike da kwarin gwiwa. Tashi Ummy tayi ta shiga ɗakin da suke, zama tayi gefen bed tana kallan ƴartata dake wani irin kuka. "Meya faru Rahama?" Cikin sheshekar kuka take cewa. "Ummy Imran kallan ƴar iska fa yake min, kuma wallahi Ummy ban yi iskanci ba na rantse da Allah." Ummy taja numfashi tana girgixa kai take faɗin. "Toh ai ba karya yayi miki ba Rahama." Saurin kallan Ummyn tayi da tsananin mamaki, cikin takaici taci gaba da cewa. "Zuwa wajanshi da kika dingayi ba tare da aure ba me sunanki a wajansa Rahama? Jikinki da kika buɗe masa ya gani ya taɓaki yadda yake so meye matsayinki a gurinshi? Kin ɗauka dole sai ya kusanceki sannan ya zama iskanci? Capital NO..! Ai kinyi babban kuskure Rahama na biyewa zuciyarki akan soyayya. Duk soyayyar da ƴa mace zatayi karta kuskura ta bari namiji ya riƙe koda mayafinta bare ya kai ga hannunta, tokefa ana gobe auranki da ɗan uwanki kikaje kika buɗe masa komai naki Rahama ya taɓa, ki gaya min wane mutunci ko kima zakiyi a wajansa? Rahama koda shi zaki aura indai ba'a daura muku aure ba ai be dace ki bashi jikinki ba. Ke badan Imran ɗin ma yana sanki wallahi da kinsha wulakanci da cin mutunci a wajansa. Ku yaran nan kun ɗauka cewa da muke ku tsare kanku ku kare martabarku a tunaninku mu kuke yiwa? Ki godewa Allah da har yanzu Imran ɗin yana sanki kuma ya maidake ɗakin ki. Ki yadda ki koma Rahama dan yanzu idan kin fito ba wani daraja zakiyi ba saboda mutane da yawa sunji labarin ku duk da cewar ba'a turawa kowa videon ba, wannan dalilin yasa nake so ki koma gidan Imran Matawalle." Rahama tayi shiru zuciyarta na wani irin suya, gaba ɗaya wani irin haushinsa takeji tunda ya gasa mata wannan maganar, hawaye ke rolling kan kyakkyawar face nata ji take tamkar ta rataye kanta saboda baƙin ciki. "Rahama ki lallaɓa mahaifinki ya barki ki koma gidan Imran tunda ko kin zauna dai ba auranki zai yi ba. Sannan ga yarinyar nan Allah ya baku wayasan nawa zaku haifa tare? Nidai na baki shawara a matsayina na mahaifiyarki, kije kiyi shawara." Ummy na kaiwa nan tabar ɗakin, hakan yasa Rahama faɗawa kan bed tare da sakin wani sabon kukan. Tsab ta gama haɗa jakar kayanta tana zaune a parlor tana tagumi, ta nemi Rahama ta rasa ta fita compound ɓata ga motarta ba shine ta tambayi mai gadi ya tabbatar mata da ficewar Rahamar. Abba ya shigo part ɗin cikin shirinsa na fita, ganinsa yasa Hajja miƙewa tana gyara mayafi yace. "Hajja ina zakije haka?" Ta wani haɗe rai. "Bance maka Abuja zan koma ba? Yau a gidan ɗan uwanka zan kwana na gaji da duka halayen nan naku." Hankalin Abubakar Galadanci yai mugun tashi...


(Complete Decuments)
*WAMINAL HUB* #500
*ZO GARENI* #300
*NIDA RAHEEMA* #300
*RAYUWAR AURENA* #300


#Asmy b Aliyu
#Hajja ce
#Imran Matawalle
#Rahama Galadanci
#Team Albi
#Haske Writers Association....
[12/20, 7:30 PM] Asmy B Aliyu😘: *ALBI...*
(my heart❤️)


*ASMY B ALIYU*
DA
*HAJJA CE*👈


PAID BOOK..#(500)


*Account Details*
0004157137
*Jaiz Bank*
*Asma'u Buhari Aliyu*
Shaidar biya ta
08086207764


*Katin waya ta MTN.ta 07043079282 shaidar biya ta 07065283730 view WhatsApp*




56.....


Jakar kayanta ta kuma janyowa tana faɗin. "Idan kai bazaka kaini ba ina da wanda zai kaini babu ɓata lokaci." A Galadanci yai saurin karɓar jakar yana riƙo hannunta, kan sofa ya zaunar da ita yana faɗin. "Kiyi hakuri Hajja komai ya kusa wucewa, yau zanje na dawo da Ummy Rahama kuma zanyi magana da ita akan shi Imran ɗin, amma dan Allah kiyi zamanki anan wallahi hankalina yafi kwanciya idan ina shigowa gidan nan idanuna suna kallanki." Hajja ta taɓe baki tare da kawar da kai tana cewa."Naji ina nan ina jiran ka dawo da matar gidan nan kafin ka tafi wajan aikin ka." Cike da ladabi Abubakar Galadanci yake faɗin. "Yanzu kuwa Hajja, ina Rahama ne banga motarta ba.?" Yatsina fuska Hajja tayi tana cewa. "Ita ta sani, ka bibiya tabi mijinta tunda dai tana san kayanta." Gaban Abba, ya wani buga ransa yai mugun ɓaci, bece komai ba saboda kar Hajja ta sake fusata, yai mata sallama ya fice daga gidan. Sai da ya zauna a mota sannan ya kira wayarta, tana kwance sai uban kuka takeyi taji kira tana dubawa taga Abbanta ne. Picking tayi tana share hawayen taji yana cewa. "Kina ina?" Rahama ta dafe kirji jin yanayin yadda yake mata magana da fushi. "Abba ina gidan Hajiya Babba." Wata irin nutsuwa ce ta saukar masa kafin ya kashe yaja motar, kai tsaye gidan ya nufa aka yi masa iso kansa a ƙasa suka gaisa da Alhaji Lamiɗo dake zaune cikin sitting room ɗinsa. "Alhaji ya akai waɗannan abubuwan suke ta faruwa ne? Haba Alhaji Abubakar kana Babba mai hankali da nutsuwa amma ka biyewa yara kuketa wannan shirmen? Tun farkon rigimar nan naso yin magana sai dai nayi shiru dan kar na baka shawara bakai amfani da ita ba raina ya ɓaci shi yasa nayi shiru. Sai dai wannan karan dawowar matarka gidan nan yasa nace duk randa kazo zamuyi magana." Abubakar Galadanci yai shiru yana sauraranshi. "A yadda matarka tai mana bayani babu wata hujja ƙwaƙƙwara da zata sanyaka hana auran Rahama da Imran, duk wannan kiyayyar da kake yiwa auran su kana yi ne sanadin wacce kake yiwa maƙocinka wato Matawalle. Yanzu dan Allah Abubakar aibatawar da kake yiwa surukinka dame ta amfaneka? Gashi nan dai harda jika tsakaninku idan yarinyar taji yadda kake aibata mata uba mekake tsammani?" Abubakar Galadanci ya shafa goshi jin wani gumi yana tsatuwa da wajan. "Insha Allahu komai ya wuce." Abba ya faɗa da respect dan ba ƙaramin ganin girman Alhaji Lamiɗo yake ba. Da sassanyar murya yake cewa. "Alhaji dan Allah ace su shirya mu koma gida, Hajja tace idan bamu koma tare ba karna koma gidan." Miƙewa yayi yana cewa. "Yanzu kuwa zasu fito me suke yi a gidan." Ciki ya shiga ya samu Ummy ya dinga lallashinta, ya kuma tabbatar mata da cewar matsalar Rahama tazo karshe Abubakar Galadanci zai kawo karshen rikicin. Babu yadda ta iya haka ta shirya su Aunty Kausar suka kai mata kayan booth. Koda ta fito bata bari sun haɗa ido da Abban ba kawai ta shiga front seat ta zauna, Rahama kuma ta shiga motarta suka bar unguwar Hotoro. Hannunsa yasa ya kamo nata yana ɗan matsawa a hankali, kallanta yai yaga kanta na kallan glass, murya a sanyaye yake faɗin. "Kiyi hakuri madam ." Juyowa tayi ta kalleshi tana murmushi hakan ya sake kwantarwa da Abubakar Galadanci hankali. Suna gama yin parking sashen Hajja suka nufa, da ladabi Ummy ta gaisheta sannan Hajja ta kalli Abubakar Galadanci ranta a haɗe take cewa. "Toh gashi ka dawo da mai ɗakinka saura muji meka yanke akan ƴarka?" Abba yaja numfashi tare da faɗin. "Na amince Hajja Rahama ta auri Imran, sai dai bazan bashi ita ba har sai anbi hanyar da ake bi wajan yin auren, ina so muyi zama dasu can ɓangaren dan muji ta bakin su idan zasu amince." Kallan juna Ummy da Hajja suka yi tare da sakin murmushin jin daɗi. "Muma daman abinda muka shirya kenan, mukace koda Rahama zata koma gidan Imran sai anyi sabon daurin aure yadda hankalin mu zai fi kwanciya." Tashi sukai dukansu suka nufi sashen su, ganin Rahama bata shigo ba har lokacin yasa Abban kiranta nan take gaya masa cewa faci tayi shine take neman inda za'a gyara mata tayar. Yana zaune a office ɗin clinic ɗinshi aka kira wayarsa, ganin sunan dake kai yasa shi ɗagawa da sauri, cike da girmamawa yace dashi. "Yallaɓai madam tana tsakkiyar titi motarta tayi faci." Da wani irin sauri ya miƙe tsaye yana tambayar. "A wajan ina ne?" Yaran nashi da Imran yasa ya dinga kula da duk wani motsin Rahama ya gaya masa wajan, ajiye biron hannunsa yai kan disk ya ɗauki wayarsa yana cewa. "Please kaje kasan yadda akai motar ta bar tsakiyar titi gani nan zuwa." Cikin ƙaramin lokaci Imran ya bayyana a wajan, Rahama tasha mamakin ganinsa ta wani haɗe rai tana sake manna little jikin kirjinta. Sanye take da riga da skirt na green ɗin lace da ratsin golding a jiki ta yafa mayafi gashi ta sako little cikin jakar yara da ake ratayawa, kallo ɗaya zakai mata ka kasa tantance matar aure ce ko budurwa saboda tsabar yarinta gashi wajan duk maza ne, sassanya ƙamshin jikinta kaɗai abin tsayawa a shaƙa ne bare kuma ita kanta. Cike da kishi ya ƙarasa wajanta jama'ar gurin suka zuba ido ganin mezai faru. Wajan kunnanta yaje murya ƙasa-ƙasa yake faɗin. "Ki wuce mota na ko kuma yanzu na ɗagaki gaba ɗaya dake da babyn." Rahama ta ɗan ja baya tana masa wani kallo, sanye yake cikin wani tsadaddan yadi da yai matuƙar karɓarsa, ta kawar da kai gefe tana hura hanci. Ganin yana gyara hannun riga yasa ta turo baki tana faɗin. "Ni bana san wannan abin, ina ruwanka dani? Dan Allah Imran ka tafi ka barni." Wani irin haɗe rai yayi yana sake matsawa dap da ita, hannunsa yasa yana shafar kan little yake cewa. "Idan na ɗaukeki nakai mota nayi miki mugun mutunci, wallahi kinji na rantse miki da Allah ko? Yanzu zansa a ɗaukeki a samin ke a ciki, ba human rights ba ko duka duniya zasu taru akai na indai ƙattannan sun kai min ke cikin mota naci riba." Rahama taji kamar ta rufeshi da duka, cike da fushi taje ta buɗe back seat ta zauna tana wani matse hannunwa irin na masu ji da masifar nan. Ko a jikinsa shi dai tunda ta shiga ba damuwarsa bace idan ma a saman motar ta zauna, abu ɗaya ya sani shi ya ɗakkota ragowar fushi da ɓacin rai ya rage nata. Key ya yiwa motar suka bar wajan, hanyar guest house ɗinshi taga ya yi tayi saurin cewa. "Ina kuma zaka kaini?" Yai mata banza, cike da masifa take cewa. "Abba yana gida yana jirana please ka juya motar nan." Ci kanki Imran bece mata ba har suka isa guest house ɗin, mai gadi ya buɗe ya shigar da motar. Yana gama yin parking ya ɓalle murfin ɓangarensa ya fito ya buɗe mata tayi masa banza. Little ya fara ƙoƙarin kwacewa amma ta hana shi dan haka ya fara ƙoƙarin janyota duka, ganin zata faɗi yasa ta sakin ihu tana cewa. "Ni ka kyaleni na fito da kafata." Saketa yai ta fito ya fizgota leftside ɗinshi suka nufi entrance na gidan. Shar parlorn kai kace akwai masu rayuwa a cikinsa, ta tsaya a bakin ƙofar tana wani tsole fuska take faɗin. "Ban san me yasa baka san ganin ina yiwa iyayena biyayya ba, na gaya maka Abba na gida yana jirana shine zaka taho dani nan? Kana nufin yin wani abu dani ne ko me kake nufi Imran?" A hankali ya juyo yana shafar quarter millions ɗin face nashi tare da cusa yatsunsa cikin sumar kanshi yana faɗin. "What ever you think shi nake nufi." Yaja numfashi tare da riƙo hannunta yaja ta da karfi suka nufi upstairs, suna shiga ta fizge hannunta tana faɗin. "Sai ka bari sai na kawo kaina wajanka kayi abinda zakayi, amma yanzu ina so ka maidani gida gaban iyayena." Hannunta ya riƙo ya lanƙwasa shi, zafi da azaba yasa Rahama sakin ihu hawaye suka fara taruwa a idanunta, ɓalle jakar goyan little yai wacce dama itace keyi masa shamaki da nunawa Rahama da wanda take magana. Da sauri ta riƙe jakar jin zata faɗo tana wani buɗe masa ido. Kwace little ɗin yayi ya kwantar da ita kan bed tare da fizgo Rahama duka jikinsa yana zare ɗankwalin kanta yai cilli dashi. Wasu irin yara-yaran kitso ne da tsagar su ma sai kayi dagaske zaga gane cewa anyi su, ya sake matseta cikin jikinsa tare da riƙo ƙugunta yana wurga mata wani irin kallo da idanunsa da suke mugun karya duk wani girman kai nata. "Kina tunanin jikinki ne yake ruɗata? Kidawo cikin hankalinki Albi, me yasa sai da lokacin yin rayuwa mai cike da daɗi tazo mana ke kuma zaki juya bayanki uhmm? Kinsan irin wahalar da kike bani? Yanzu bakya sona ko?" Rahama tayi shiru yadda taji numfashinsu yana sauyawa dana juna, ƙafafunta suka fara sanyi tana jin kamar ba zasu iya ɗaukarta ba. "Ina sanki Albi bazan gaji da gaya miki ba. Sannan ban kawo ki nan dan nayi wani abu ba dake ba. Bazan iya barinki cikin mazan nan ba shi yasa na taho dake nan. Nasa a canza miki taya idan an gama za'a kawo miki motarki nan sai ki tafi gida hope hankalinki zai kwanta yanzu?" Ya faɗa yana sakar mata jikinta. Lumshe ido tayi tana maida numfashi, wajan little Aysha ya nufa tare da cirota daga jakar yana mannata cikin kirjinsa. Har yaushe ne zasu dawo jikinsa suci gaba da rayuwarsu? Juyi ya shiga yi da ita tana ta dariya, Rahama wani juyawa tayi tare da ficewa daga cikin ɗakin, parlorn ƙasa ta zauna tare da zaro wayarta tana dannawa. Sai da ta ɗauki kusan rabin awa tana jiran ya fito yace mata an gama amma be fito ba, horn da taji ne yasa tai saurin miƙewa ta nufi upstairs ɗin, cak ta tsaya daga bakin ƙofa jin yana waya. "Humee ki gayawa Daddy kawai I know zai yi." Gabanta ne ya wani buga nan da nan wani irin kishi ya rufeta kawai ta shiga cikin ɗakin, ganinsa rungume da Aysha yasa taje zata karbeta. "Naji an kawo motar sai ka barmu mu tafi ko ka samu damar yin magana da matarka." Katsewa yai yana miƙa mata babyn, cike da rashin damuwa da yanayinta yake cewa. "A gaida gida." Ta waigo taga ya sake gyara kwanciyarsa yana kuma manna wayarsa cikin kunnenshi.

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads