Header Ads
Showing 129001 words to 132000 words out of 139785 words

Chapter 44 - Albi Book Complete document by Hajjace.txt

Ads the beginning of article before Image

11 Jun 2024

1004

Ads at the middle of Article

aikin banza aikin wofi." Ya faɗa yana gyara jallabiyar jikinsa yasa room silifas ɗinsa ya fito. Ummy da tunda ya fara surfa bala'i ta rintsa ido tana jin wani irin baƙin ciki a ranta, ganin ya fice yasa ta tashi da sauri taje gabansa ta tare ƙofar, Abba yana mugun haɗe rai yake kallanta yana cewa. "Ke kuma menene hakan? Matsa min daga hanya na wuce." Ummy ta sake tare hanyar idanunta suka cika da ruwan kuka, muryarta na rawa take faɗin. "Alhaji na kasa gane inda zuciyarka take akan lamarin Rahama da Imran, yaran nan aure yaje aka daura musu, kasa ya saketa bada niyarsa ba, ya fita kuma ya maida matarsa ko duk da haka bazaka bashi ita ba? Zaka ɗaura mata aure ne da wani? Dan Allah ka kori duk wani shaiɗanin da yake san hanaka ganin gaske kabar yaran nan suci gaba da rayuwarsu." Kallan da taga yana yi mata shine ya tabbatar mata da cewa baya gane zancenta. Yasa hannu zai tureta tai saurin riƙe handle ɗin tana faɗin. "Idan har kai nasarar fasawa Rahama zuciyarta, ko kuma kaki gane manufata akan ƴata ina mai tabbatar maka da cewa zan tafi in kyaleka tunda bani da wani ƙima da zan bayyana maka rufin asirin zuriyar mu." Abubakar Galadanci ya wani kalleta a ƙanƙance yake faɗin. "Hajiya! Kina maganar zaki barni? Saboda ina nemawa ƴata mutunci da darajarta? Zaki banni fa kika ce?" Ya wani kalleta kafin yaci gaba "Kin daɗe baki barni ba, indai akan Rahama sai ta koma gidan wancan yaron ne kike cewa zaki barni, kin daɗe baki tafi ba, bani hanya na wuce ko yanzun nan ranki ya ɓaci." Tureta yai ya fice daga cikin parlorn, kai tsaye part ɗin Hajja ya nufa yana wani huci kamar tsohon kumurci ya shiga kiran Rahama kamar zai yaga baki. Tana zaune gefen bed tana haɗa tea zata sha taji muryar Abban ta, da sauri ta ajiye ta fito tare da buɗe ƙofar tana kallansa. "Idan kikai min karya sai na kakkaryaki a gurin nan. Kece kikai magana da Imran akan cewar ya maida auran ku?" Hankali a tashe Rahama take kallan Abbanta tana girgiza masa kai, ya daka mata wata uwar tsawa, "Ki buɗe baki ki gaya min tun kafin ranki ya ɓaci." Da tashin hankali take faɗin. "Abba wallahi tun da ya bani takardar nan bamu sake magana dashi ba, wallahi Abba ban karya dokarka ba." Hajja ta fito wacce har ta fara bacci hayaniyarsu ta farkar da ita. "Lafiya?" Ta tambaya tana kamo hannun Rahama dake hawaye. "Ashe yaron can zuwa yai ya raina muku hankali Hajja? Taya za'ai ace wai har yanzu da auransa akan Rahama? Dan uban shi da mun aurawa wani ita fa me yake nufi? Wato ni ban isa nasashi yayi abu ba ko? A hakan kuma yake so na bashi ƴata ta zama matarsa?!" Hajja ta kare masa kallo tana kallan Ummy dake can wajan ƙofar kanta a ƙasa. "Wai Abubakar meke damunka ne? Wai kai baka yadda da ƙaddara bane ko kuwa baka da lafiya?" Zuciyarsa na zafi yake cewa. "Hajja bana san yaron can, kwata-kwata bana san ya rabi jinina me yasa kuka kasa fahimta ta?" Hannu Hajja ta watsa masa irin kai tafi can ɗin nan tana faɗin. "Jini wanne kuma Abubakar? Wane jini ne Imrana be shiga ba a jikinka? Ya auri Rahama ya kwanta gado ɗaya da ita ya haɗa jikinsa da nata, karshe sai da Imrana yasa gudan jininsa a jikin Rahama kuma ta haifo shi duniya, gata can indo kwance a cikin gidanka, dan ka tabbatar da cewar jininka ce sai Allah yasa kukayi matuƙar kama yadda kasan kaine kayi kaki ka tufar. Gasu nan daga Rahama har Ra'ees babu wanda ka haifa yayi kama da kai sai Indo Aisha jika a gareka, ka gaya min menene yai saura?" Kamar Hajja na soya masa zuciya haka yakeji, yace. "Gobe-goben nan za'a kai musu jininsu nima zan riƙe tawa, amma kam har yanzu banji ina ƙaunar yaron can ba wallahi." Yana kaiwa nan yabar parlorn, ta gefen Ummy ya wuce bebi ta kanta bama bare ya gane irin kukan da takeyi. Rahama ta durƙushe a wajan ta saki wani irin kuka hakan yasa Ummy kasa shiga ciki kawai ta juya ta shiga part ɗinta, kai tsaye ɗakinta ta koma toilet ta shiga tayo alwala tazo ta shimfiɗa sallaya, sallah take hawaye basu dena zuba daga idanunta ba, tsawon shekaru suna tare da Abba be taɓa yi mata wannan disgin ba sai yanzu, ta riga tasan kaddara ce ta haɗa Rahama da Imran amma me yasa Abba ya kasa fahimta? Meyasa baya ganin laifin Rahama sai na Imran kaɗai? Meyasa ya kasa fahimtar Imran ya rufawa Rahama asiri da be gama watsar da ita a titi ba kuma yaki auranta? Tabbas dole ta bawa Abubakar Galadanci waje dan yayi nazari da kuma tunani. Addu'a tayi sosai kafin ta miƙe ta fara haɗa kayanta cikin trolley zuciyarta cike da yiwa ƴarta ta addu'ar fatan alkairi. Ran Hajja yai mugun ɓaci ta kalli Rahama dake wani irin kuka mai cike da tashin hankali tace mata. "Ki rufe min baki ni dan ubanki ai hardake ake haduwa a ruguza komai, yanzu ki gaya min har yanzu kina san mijinki ko naje na bashi hakuri Allah ya bashi wacce tafiki?" Kamar kunnata Hajja tayi haka Rahama ta sake fashewa da kuka, ta daka mata tsawa cike da bala'i take faɗin. "Wallahi zan lakaɗa miki na jaki a parlorn, zaki gaya min ko sai na fita daga sabgarki? Sai na tattara kayana na koma Abuja Farooq yai ta lallaɓani." Jin abinda tace ne yasa Rahama rage sautin kukanta. "Gaya min kina san komawa gidan mijinki?" Girgiza kai Rahama tayi bakinta yana sarƙewa take faɗin. "Hajja me yasa zan koma bayan Abba baya so? Ki barni nayi masa biyayya shi Imran ɗin ai yana da wata matar, rainin hankali ne kawai zai wani ce ya maida auran mu." Wani kallo Hajja ta bita dashi tare da juyawa ta nufi bedroom ɗinta tana cewa. "Kya karaci munafuncinki, ina lura da duk wani motsinki, kina sonshi kina biyewa babanki sai kuje kuyi tayi." Ta shige tana turo ƙofa. Kukan little Aysha yasa Rahama miƙewa ta ruga ɗakin tana hawaye. Ranar dai kaf gidan Alhaji Abubakar Galadanci babu wanda yai bacci mai daɗi. Tunda ta idar da sallah ta sake haɗa kayanta, kitchen ta shiga tun kafin mai aikinsu tazo ta haɗawa Hajja da Abba breakfast. Tana gamawa ta shiga toilet tayi wanka tsab tai shirin tafiya asibiti. Trolley ɗin ta kai mota da sauran abinda tasan muhimmaine, sannan ta fito taje suka gaisa da Hajja tashiga ɗakin da Rahama take tana kwance little Aysha na shan nono, gaisawa sukayi ta ɗauki Aysha tana kallanta take yiwa Rahama magana. "Ki kula da ita sosai kinji ko?" Rahama ta ɗaga kai jikinta duk ba kwari. Tashi Ummy tayi Rahama tayi mata a dawo lafiya.


Koda Abba ya dawo da daddare beyi zaton Ummy bata gidan ba sai da ya shiga bedroom ya gama komai yaji shiru batazo ta bashi abinci da magani ba, ya fito daga cikin ɗakin yana kwala mata kira amma shiru, kuma da ya dawo yaje side ɗin Hajja beganta a can ba. Ɗakinsa ya koma ya ɗauki wayarsa ya jirata amman bata shiga, ransa ya ɓaci ya kira wani abokin aikinta inda ya tabbatar masa da cewa yau bata shiga asibitin ba ma. Sashen Hajja ya nufa ya tarar da ita rungume da Aysha ya fara rarraba idanuwa yana cewa. "Hajja ko kunyi waya da maman su Rahama ?" Cike da damuwa tace. "Wallahi muma tun ɗazu muke kiranta amma bata shiga ko aikin ne yau har dare? Na zata na safe gareta ganin ta fita da sassafe." A sanyaye Abba ya juya yabar sashen hajja, sai da ya fito compound din gida ya tabbatar da babu motar Ummin,a parking lot Wanda bai lura da hakan tun farko ba .babu tantama Ummy gidan Hajiya Babba ta wuce. Gaba ɗaya sai ya rasa ame zai sanya wannan abin na Ummy, yaji tayi kome? Ɗaki ya shiga gaba ɗaya sai yaji duniyar tayi masa girma, gidan yaji tamkar wani kango, besan lokacin da ya shiga maida kayansa ba, ya ɗakko car key ɗinsa yana faman baza babbar riga. Kai tsaye parking lot ya nufa, da wani irin speed ya bar layin. Yana zuwa yasa mai gadi ya buɗe masa, be kira Ummy ba sai ya kira Aunty Kausar yace mata gashi a compound ya kashe wayar. Zaro ido tayi tana kallan Ummy dake danna laptop tana cewa. "Abba ne yana cikin gidan nan." Ummy tayi murmushi kawai batace komai ba. Tashi Aunty Kausar tayi taje wajan Abban suka gaisa yayi shiru can kuma yace. Ya tambayi kausar ummi ?" Tace masa "Tana ciki amma tunda tazo babu wanda tayiwa magana." Cire hula yayi ya sake maida ita kansa yace. "Kice mata nazo." Aunty Kausar tace. "Wallahi Abbansu Rahma,na gaya mata sai dai bata kalleni bama taci gaba da aikinta." Da sauri ya fito kai tsaye ya nufi cikin gidan bakinsa ɗauke da sallama. Hajiya Babba na zaune a parlor tana jan carbi. Gaisawa sukayi a sake yace. "Hajiya ayi hakuri dan Allah." Da mamaki tace. "Meya faru Alhaji?" Abubakar Galadanci yai shiru kafin yace. "Ummy tana gidan nan na kirata kuma wayarta duk bata shiga, dan Allah Hajiya ki bata hakuri kice ta fito mu tafi, yanzu munfi karfin wannan abubuwan." Hajiya Babba ta kalli upstairs kafin ta kalli Abba tace. "Badai yau ba, yau ni kaina duk tambayar da nai mata cewa take babu komai amma bazata koma gidanka ba." Da wani irin tashin hankali Abba ya kalli Hajiya Babba. "Dan Allah Hajiya." Ya sake faɗa yana jin kamar ya hau saman yaje suyi magana da Ummyn. Kiri-kiri Hajiya Babba ta bashi hakuri akan ya bari zuwa wani lokacin. Babu yadda ya iya dole ya koma gida zuciyarsa na yi masa zafi.......


(Complete Decuments)
*WAMINAL HUB* #500
*ZO GARENI* #300
*NIDA RAHEEMA* #300
*RAYUWAR AURENA* #300


#Asmy b Aliyu
#Hajja ce
#Rahama Galadanci
#Ummy
#A Galadanci
#Team Albi
#Haske Writers Association....
[12/20, 7:30 PM] Asmy B Aliyu😘: *ALBI...*
(my heart❤️)


*ASMY B ALIYU*
DA
*HAJJA CE*👈


PAID BOOK..#(500)


*Account Details*
0004157137
*Jaiz Bank*
*Asma'u Buhari Aliyu*
Shaidar biya ta
08086207764


*Katin waya ta MTN.ta 07043079282 shaidar biya ta 07065283730 view WhatsApp*




55.....


Washe gari haka Abba ya dinga abubuwa duk babu daɗi cikin zuciyarsa, hakika mace rahamace a wajan namiji, be taɓa zaton zai iya shiga irin wannan damuwar ba. Ko aikin kwanata Ummy keyi suna waya kuma da gari ya waye take dawowa gidan saboda ta bashi kulawar da yake buƙata, haka ya fito down stairs yana kallan hanyar kitchen tamkar zai ga fitowarta. Sashen Hajja yaje suka gaisa ta sake tambayarsa ko ya samu Ummy a waya? Abba ya sauke numfashi yace. "Hajja jiya fa Ummy gidan Hajiya Babba ta tafi." Da sauri Hajja ke faɗin. "Ince dai lafiya ko?" Abba ya shiga shafa fuska tare da cewa. "Tun abinda ya faru shekaran jiya akan maganar Imran shine ta tafi, naje gidan kuma bata fito ba da alama bazata dawo gidan nan ba saboda nace yata ba zata koma gidan wancen yaron ba." Hajja ta shiga jero salati tana tafa hannuwa tana cewa. "Shikenan Abubakar ka tarwatsa gidanka da hannunka, wannan wace irin musiba ce kake ɗorawa kanka iye? Nace me yake damunka Abubakar? Tsawon shekaru ashirin da uku kana tare da baiwar Allahn nan da daɗi babu daɗi tana tare da kai yau gashi nan saboda bakar zuciya da ka aro ka yafawa kanka matarka ta tafi ta barka. Ka bani mamaki Abubakar bansan haka kake ba sai kwanan. Ai shikenan sai kayi ta zama ga Rahama nan ka kwaɗanta ka cinye abarka, nima yau ba sai gobe ba kasa a maidani can Abuja inda zan samu nutsuwa gidan nan duk ya gundireni." Ta faɗa tana haɗe rai. "Kiyi hakuri Hajja komai zai daidaita." Afusace tace. "Karma yayi ina ruwana." Ganin ta ɗauki zafi yasa shi ficewa bayan ya karbi little Aysha. Rahama da taji cewar Ummy ta tafi gida zuciyarta tayi matuƙar girgiza, jikinta ya hau rawa ta koma gefen bed ta zauna tana wani girgiza kai. "No... This can't be. Ummy na? Ummy na ce ta fita daga gidan mu saboda matsalata?" Ta fashe da kuka tana riƙe kirjinta da takejin kamar zai faɗo yabar kirjinta. Hijab ɗinta ta janyo tasa tare da fitowa, ganin Hajja a parlorn yasa ta ƙarasa wajanta tana gaisheta sannan ta miƙe tana cewa."Bari naje mu gaisa da Abba." Ko takanta Hajja batabi ba ta fice. Sashen su ta kallah ganin babu kowa yasa tayi hanyar gate kamar zata faɗi dan sauri. Mai gadi be hanata ba saboda ya dauka ma school zata ba da mota ba. Kai tsaye ta nufi gidan Matawalle duk da bata da tabbacin Imran yana ciki, tasan yana gidan shi tare da matarsa Humaidah. Knocking tayi a karamar ƙofar, mai gadi ya leƙo ganinta yasa shi buɗe mata ta shiga tana kallon, zata yi magana yace. "Yana nan a ɓangarenshi." Rahama ta cije lips ta nufi apartment ɗin cike da tsantsar masifa. Yadda ake dannu masa knocking ne yasa ransa mugun ɓaci, ya diro daga kan bed tare da niyar yana zuwa ko waye sai yasha mari. Da wani ɓacin rai ya buɗe ƙofar, sai dai wacce ya gani tsaye a wajan ce yasa shi jin zuciyarsa na yin sanyi. Komawa yai zai haye sama ta daka masa tsawa. "Ina so nasan me kake nufi dani Imran?" Yadda ta kirashi da Imran ya ɓata masa rai, tsayawa yayi tare da juyowa yana yi mata wani in kallo. "Me yasa baka san ganin Abba na ya zauna lafiya ne Imran? Kai kana yiwa iyayenka biyayya ni meyasa ba zaka barni nayiwa nawa iyayen ba Imran? A yau sanin da nai maka bai min wani amfani ba, ka sani cikin tsananin tashin hankali Imran, ka sanya family ɗina cikin kunci, nayi nadamar soyayya da kai..." Cike da tashin hankali yake kallanta, duka kalamanta babu wanda bai taɓa mishi zuciya ba. Dawowa yai gabanta ganin yadda take wani irin kuka mai cike da tashin hankali. Fizgo hannunta yai ya riƙe da karfi tare da janyota cikin jikinsa, kwacewa ta shiga yi tana kuka mai sosa zuciya. Gaba ɗaya ya ɗauketa ya nufi upstairs da ita tana ta tureshi ga wani uban duka da take kai masa har a fuskarsa amma yaki sauketa har ya shiga master bedroom. Wani irin ƙamshi ne ke tashi daga cikin room ɗin da ya haɗe da sanyin ac ya bada wani irin ni'imataccen daɗi. Kan bed ya wullata tayi saurin tashi zaune zata sauka ya ɗora mata duka nauyinsa a jikinta. Cike da masifa take masa tureshi tana faɗin. "Bana san haka Imran ba shi ya kawo ni ba." Ɗagowa yai ya kalleta da idanunsa wanda lokaci ɗaya suka canzawa zuwa na ƙaunarta. "Daman nasan zaki kawo kanki duk inda nake." Da ɓacin rai take faɗin. "Meka maidani?" Ƙoƙari yai ya riƙo hannunta da kyar yai musu riƙon ƙarfi. Lips ɗinta da tun da ya haɗa ido dashi yake matuƙar san ɗanɗanawa yaiwa wani irin cafka. Rahama ta fashe da kuka zuciyarta na mata wani irin zafi. Sai da ya tsotse shi ya ɗago ya ƙoƙarin zare hijab ɗin jikinta. "Imran bana so karka taɓani." Cak ya tsaya yana mata wani kallo yace. "Da kika bani jikinki a arha ma bare yanzu da kike a matsayin my wife? Yanzu ma ai bani na nemeki ba, kece kika kawo min kanki har cikin ɗakina, so let me.." Cak zuciyar Rahama ta tsaya dan jin kalaman Imran Matawalle, ji yai ta sakar masa jikinta gaba ɗaya. Hijab ɗin ya zare mata duka, sanye take cikin wando da riga cotton na bacci kalar pink da white babu ko bra a jikinta. Ita kam Rahama shock ɗin kalaman Imran ne yasa gaba ɗaya wani kalar tashin hankali ya ziyarce ta. Kallonsa kawai takeyi ganin yadda yake kallon kirjinta, zuciya ta ɗebeta tasa ta wani tureshi tana faɗin. "Ni zaka yiwa gori Imran? Ashe kallan ƴar iska kake yi min?" Tafaɗa tana wani zaro ido tare da ƙoƙarin sauka daga kan gadon. "Tabbas abinda ka faɗa ba karya kayi ba, dama ansha gaya min cewa wannan ranar zata zo koda ina cikin gidanka. Na buɗe jikina ka gani tun a titi, hakika ban taɓa yin nadamar saninka ba sai yau a wannan lokacin." Kuka ya sake ƙwace mata, tasa hannu zata fizge hijab ɗinta yai saurin janyota ta shiga yi masa masifa da bala'i. "Kadena taɓani nace, idan ka sake taɓa jikina zakasha mamaki na. Saboda kai Ummy ta bar Abba na, saboda kai na zubar da duk wani mutunci nawa, gashi yau ka tabbatar min da kallon da kake min, indai nice na barka har abada Imran koda kuwa soyayyarka zata kashe ne." Gaba ɗaya yaki bata damar kwace hijab ɗin bare ta kwace jikinta. Ya tashi tsaye yana riƙe da ita cikin wani yanayi yake faɗin. "Kece kika fara shigowa cikin rayuwata tun bana kulaki har sai da kika janyo zuciyata ta amince miki. Na baki dama da yawa na barinki cikin rayuwata amman baki barni ba har sai da kika zamar min *ALBI* (Zuciya ta) kika hanani kallon kowace mace idan bake ba, shine kike tunanin zan iya rabuwa dake? Koda na faɗa miki wannan maganar sai ki rama kice ai nine ɗan iskan that's all. But kisa a ranki ba zan taɓa rabuwa dake ba kome za'a yi." Ya ƙarasa faɗa yana fizgota yai mata wata kyakkyawar runguma, kaunarta na daɗa dabaibayeshi. Zareta yayi daga jikinsa yadda take kukan nan yana matuƙar hurting zuciyarsa. Hijab ɗin yasa mata tare da ɗakko turaruka ya fesa mata, hannunta yaja suka sakko down stairs ya buɗe mata ƙofar yana nuna mata hanya da hannunsa yana cewa. "Komai zakiyi ki sani cewa ina sanki, if I stay with you! if I'm choosing wrong I don't care all! If am loosing know but am wining let that's all I won't, so I don't care at all! I'm not..! Da duk wani wulakanci da zaki min *ALBI*. And

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads