Showing 135001 words to 138000 words out of 139785 words
Chapter 46 - Albi Book Complete document by Hajjace.txt
Hawaye ne suka zubo mata ta fice daga gidan tana jin kamar zuciyarta zata fito. Ta window yake hangenta har ta fita ta shiga mota, ɗan murmushi ya saki ashe dai har yanzu akwai soyayyarsa a zuciyarta, kawai tana so ne da karfi da yaji sai ta guje masa saboda Abbanta. Tana komawa gida Abba yace ta bashi lambar Imran, hankalinta ya tashi dan tasan haɗuwar su babu wani alkairi a cikinta. "Abba ban sani ba ko ya canza wani layin." Ta faɗa dan ta sake tabbatarwa da Abban nata cewa tana yi masa biyayya. "Bani wacce kike da ita." Nan da nan ta karanta masa ya fito daga sashen Hajja yana kiran lambar. Sai da yai kira kusan biyar ana shida yaji anyi picking, kai tsaye yace. "Abubakar Galadanci ne ina fatan da Imran Matawalle nake magana?" Imran da zaman shi kenan cikin office mamaki ya kamashi yace. "Eh ni ne." "Ina san ganinka da daddare." Cewar Abubakar Galadanci, Imran ya cije lips tare da cewa. "Okay." Rahama kuwa waya sukayi da Ihsan Galadima take tabbatar mata da zuwanta gidan su, hakan yasa ta murna da kuma kawar da haushin Imran na waya da Humaidah.
******
Aiki suka dinga yi ita da Ummy da kuma mai aikinsu, tunda suka fara take tambayar Ummy suwaye ake yiwa wannan shirin amman sai kawai tace mata baƙi za'a yi. Komai a sitting room suka jera saman table, ana idar da sallar isha'i suka shigo gidan. Matawalle da Imran ne Abba da kanshi yai musu iso cike da sakin fuska ya nuna musu wajan zama. "Abubakar Galadanci sai kawai naji kiran gaggawa, kasan US naso tafiya yau ka kirani kace akwai magana tsakanin yaran nan shi yasa kawai na hakura nace bari na jira Allah yasa wannan karan alkairi ne ya tara mu?" Abba ya saki dariya yana faɗin. "Aikuwa dai dan ko kana sama sai ka dawo anyi maganar nan." Suka kwashe da dariya Matawalle ke cewa. "Aikuwa gashi na dakata, amma idan zan tafi dole ka rakani." Suka sake yin dariya, sai abin ya zamewa Imran wani iri ganin maƙiya juna yanzu suna ta ɓaɓɓaka dariya. Juice Abba ya zuba musu cikin cups guda uku ya ɗauki cup ɗaya ya kai bakinsa yana cewa. "Dan ku tabbatar babu guba a ciki." Matawalle ya ɗauka yana cewa. "Ko akwai ma ai bazamu mutu ba tunda Aysha ta shiga tayi kane-kane a tsakiyar mu." Suka sake yin dariya, shi kam Imran besha ba saboda shi yafi san na shago sunfi masa daɗi. "Muna jinka Alhaji Abubakar meke faruwa?" Gyara murya yayi yana cewa. "Da farko dai so nake komai ya wuce, abubuwan da duk suka faru dan Allah ya wuce a yafewa juna. Kuma kamar yadda abubuwa suka faru yaran nan sunje an ɗaura musu aure bada yaddar mu ba, sannan bada amincewar mu ba gashi har saki ya shiga tsakani, shine na yanke shawarar tunda dai suna san juna dama mune bama so me zai hana a sake yin taro dan kowa ya tabbatar da auran nasu? Na yadda cewa yaran nan Allah ne ya haɗa su, uwa uba gashi ta sanadinsu gabar dake tsakanin mu ta kare daga yau babu ita." Wani irin farin ciki ne ya mamaye cikin ran Imran, betaba zatan wannan ranar zata zo ba sai gashi tazo a lokacin da bai taɓa tsammani ba. "Alhamdulillahi wannan abu yayi daɗi, Allah yasa ayi a sa'a Alhaji gwara da ka sakko wallahi da na kwace maka yarinyar nan mai kama da kai, amma yanzu na bar maka dama kaine mata ɗaya kaga sai ka ƙara da ita." Suka yi dariya dukkan su, Imran kuwa ya rasa inda zai saka ranshi. Nan aka sanya sati biyu biki, wannan albishir ɗin ne yasa Imran cin abubuwan da aka tanadar musu. Sun jima a sitting room ɗin kafin suyi sallama kowa ya nufi muhallinsa........
(Complete Decuments)
*WAMINAL HUB* #500
*ZO GARENI* #300
*NIDA RAHEEMA* #300
*RAYUWAR AURENA* #300
#Asmy b Aliyu
#Hajja ce
#Imran Matawalle
#Rahama Galadanci
#Team Albi
#Haske Writers Association....
[12/20, 7:30 PM] Asmy B Aliyu😘: *ALBI...*
(my heart❤️)
*ASMY B ALIYU*
DA
*HAJJA CE*👈
PAID BOOK..#(500)
*Account Details*
0004157137
*Jaiz Bank*
*Asma'u Buhari Aliyu*
Shaidar biya ta
08086207764
*Katin waya ta MTN.ta 07043079282 shaidar biya ta 07065283730 view WhatsApp*
57.......
Da wani irin shock a fuskarta take kallon Ummi tana girgiza kai hawaye na taruwa a cikin idonta lokaci ɗaya, bakinta yana wani irin rawa take cewa. "Ummi da gaske Abba ya yarda da aurena nida Imran?" Ta ƙarasa faɗa cikin rawar murya. Ɗaga kai kawai Ummi tayi da wani irin murmushi cikin fuskarta. Hawaye na zubar mata tana tare su ta shiga girgiza kai zuciyarta na suya tace. "Ni bana son auren nan Ummi." Ta faɗa sounding so very serious cikin muryarta. Sakin baki Ummi tayi tana kallonta lokaci ɗaya kuma ta haɗe rai tana faɗin. "Ban da yau kar na kara jin haka daga bakinki, mu daman saboda mahaifinki ne kike zaune a gidan nan right? Toh yanzu komai ya wuce daga yau za'a fara shirye-shiryen bikin ku." Cikin murya kuka tana tare hawayen idanunta take faɗin. "Idan kuma muka cigaba da zama yayi tayi min gori fa? Ni wallaji yanzu bana son auren Imran Matawalle." Ummi tayi murmushi tana girgiza kai tana kallon Rahama da ta haɗe kai da pillow tana rera kuka da alamar gorin da Imran Matawallen yayi mata ya taɓata sosai. Ummi batayi wani mamakin ganin reaction ɗin Rahama ba, daman so take ta dawo cikin hankalinta kuma ta dawo ɗin tunda gashi yanzu tana jin ciwo aranta har tana faɗin bata son auren su da abinda tafi kauna a duniya. Ummi bata qarabi ta kanta ba suka cigaba da shirye-shiryen bikin wanda har mai gyaran jiki Ummi ta ɗauko. Kallonsu kurum Rahama takeyi a yadda taga suna rawar jiki da auren musamman ma mahaifinta wanda ba ƙaramin shan mamaki tayi ba, ya zage yana mata komai irin wanda uba keyiwa ƴarsa. A cikin satin bazata iya kirga kiran da Imran Matawalle yayi mata a waya ba, text ɗin ban hakuri babu kalar wanda baiyi mata ba amma ko kallon wayar batayi, da ya dameta ma duka ta kashe wayar ta kai cikin kayanta ta ɓoye. Wannan karon zata nunawa Imran Matawalle cewa itama macce ce mai daraja da mutunci tamkar sauran mata masu tarbiya da kamun kai. Duk da tasan da gaskiyyarsa a maganar da ya kwaɓa mata, dan da bata kai masa kanta gareshi ba da bazai taɓa yi mata gori ba, Allah ne ya saka mata soyayyarsa acikin zuciyarta tun kafin ta san kanta. Haka da tana iyawa da ta dawo da duka abubuwan da suka faru a baya ta gyara kuskurenta, sai dai kash...! Bakin alƙalamin ya riga ya bushe, haka bazai taɓa dawowa ba har abada ya riga da ya faru tamkar yadda mutuwa ke zuwa ta ɗauka babu dawowa da wannan ran. Amman tayi alkawarin sai ta koya masa mugun hankali, sai ya gane cewa a bayan ma da ta biye masa shine yaja. Sai da Ummi ta nuna mata ɓacin ranta sosai sa'annan ta saki jiki aka cigaba tsare-tsaren abubuwa tare da ita, idan kuma ta tuna duk saboda Imran ne ake mata wannan gyaran sai taji ranta yayi mugu ɓaci. Haka zata faki idon Ummi ko Hajja taje ta zubar duka rabin abubuwan da take sha acikin toilet tayi flushing ɗin su. Lefe na gani na faɗa Matawalle ya saka aka haɗawa Rahama wanda ya girgiza shi kansa Imran ɗin ba kaɗan ba. Ya rasa da me zai sakawa mahaifinsa kaunar da yake nuna masa akan duk wani abu da yake so. Ranar da aka kai lefen gidan su Rahama, Abubakar Galadanci ya kira Matawalle a waya ya riqa faɗa sosai saboda sunyi yawa kamar za'a siyar da ita. Shi dai Matawalle bai ce komai ba ya jinginar da kansa cikin soofa yana sakin wani irin murmushin da Abubakar Galadanci yana jin sautinsa ta cikin wayar. Ƴata nayiwa Abubakar ba wani ba, so wannan ba wani abun damuwa bane ba." Sosai Abba yaji daɗi yayi ta godiya a wayar. Ana sauran kwana biyu ɗaurin aure duk yadda Imran Matawalle ke ɗokin ganin Rahamar ta rufe ko wace hanya sai dai yazo parlorn Hajja ya zauna rungume da ƴarsa, idan ya ƙare zaman sa yayi tafiyar sa, har tambayar kansa yake wai shin me ya yiwa Rahama zata kaurace masa haka? Ko yanzu bata son auren nasa ne? kullum da wannan tambayar yake kwana da ita kuma yake tashi a ransa. Lokaci ɗaya duk ya rame ba wanda zai gane yana cikin damuwa kowa harkar gaban sa yake yi, wacce ma zata fahimci yana cikin damuwar bata da lokacin sa yanzu. Ana gobe ɗaurin auren Humaidah ce zaune a ɗakin Mommy da ta samu ta zuba tagumi, Humaidah ta girgiza kai tana janye hannun daga haɓar, hakan yasa Mommyn ta ɗago da wani yanayi cikin fuskarta take faɗin. "Aunty ki daina damun kanki haka dan Allah, haba sai wani ciwo ya kamaki babu gairi babu dalili? na faɗa maki kiyi amfani da shawarata ki samu Daddy yanzu yana cikin farin ciki ki nemi gafarsa daga shi har Imran ɗin nasan zasu yafe maki bazamu iya canja kaddarar mu ba haka Allah ya tsara." Cikin sanyin murya Mommyn ta girgiza kai muryarta na rawa take faɗin. "Fargabata ɗaya Humaidah shine idan na gayawa Matawalle ya datse igiyoyin auren mu, shine babban abunda zuciyata bazata iya ɗauka ba, saboda zan iya mutuwa. Idan har Matawalle ya rabani da aurensa
Ina zani Humee? idan ya sakeni me zan kama?" Mommy ta faɗa hawaye na taruwa a idanunta. "Amma zanyi ƙoƙari da daddare muyi maganar." Ta faɗawa Humaidah haka tana miqewa tsaye ta nufi toilet. Ita dai Humaidah bin Auntyn nata kurum take da ido tana jin tsananin tausayinta na cika mata zuciya.
*DARE*
kallonta kurum maigirma Matawalle yake shida Imran wanda ya buɗe baki yana kallonta da wani irin yanayi cikin fuskarsa, hawayen idon Maheera matawalle har lokacin sun kasa tsayawa ta ɗago tana sakin wani wide smile cikin fuskarta wanda kowa yayi mamakin hakan, ta buɗe ido tamkar wata zararra tana kallon mahaifiyarta tana faɗin. "Ke uwa ce a garemu, kowane ɗa ko ƴa zai so ya samu nagartacciyar uwa wacce da anga ɗanta aka ce nata ne jama'a zasuyi rububin mu'amala dashi, but amma mu kam kin cucemu Mommy, wannan wace irin rayuwa ce? kina da labarin nan da ake cewa kaikayi ne ya juye ya koma kan masheqiya? Ashe saboda kene Bassam yake shaye-shaye? saboda ke Bassam yake aikata zina da yaran mutane? duka-duka shekarun Bassam nawa a duniya Mommy? he's just 20 year's fa. Me muka maki a duniya Mommy da zaki zame mana irin wannan uwar? Me yasa kika yi mana wannan muguwar sakayyar?!" Ta faɗa tana fashewa da mugun kukan dake fitowa tun daga karkashin zuciyarya, babu wanda bai shiga tashin hankali ba a lokacin jin cewar wai Bassam na shaye-shaye har yana neman matan banza. A hankali Imran ya kwantar da kansa cikin soofa yana lumshe idonsa sannu a hankali, addu'a kurum yake kar zuciyarsa ta buga a lokacin, saboda sosai maganganun Maheera Matawalle yaji suna birkitasa. "Dukanku kuna mamaki ko?" Ta girgiza kai tana share hawaye idonta. Ta kalli mahaifinta zuciyarta na karyewa da wani yanayi acikinta take faɗin. "Daddy kayi hakuri kayi hakuri dan Allah, nima abunda yasa na sani na taɓa kai masa ziyara a ƙasar da yake karatu 1 year back, ban faɗa masa zanzo ba. Abunda na tarar acikin gidansa ya kaɗani sosai Daddy, saboda ko ranar ban kwana gidan Bassam ba, hotel naje na kama." Ta faɗa tana fashewa da wani irin kuka. Mommy zata riqo Maheera cikin tashin hankali ta miqe tsaye tana jada baya tamkar taga mugun abu tana rufe duka fuskarta hawaye na zubar mata take faɗin. "Karki taɓani." Da gudu tabar parlorn, Imran zai bita Matawalle yayi saurin dakatar dashi. "Kabar Maheera tayi kuka my Son daga nan har zuwa gobe." Sannan Matawalle ya kalli Mommy da hawayenta suka kasa tsayawa yake faɗin. "Me nayi maki da zaki cuceni Hajiya?" Daddy yayi maganar sounding so very harsh cikin muryarsa. Mommy babu magana sai hawaye taji yace. "Nagode da irin halin bala'in da kika jefa mu nida zuriya ta, kije bazan iya zama dake ba Hajiya na sakeki." Daga haka Daddy ya nufi sama dafe da kirjinsa. Wani mugun kallo Imran Matawalle ya shiga yi mata yana faɗin. "Wallahi idan kika kashemin uba na yau! Ina mai tabbatar miki da cewar sai na kasheki da wannan hannun nawa." Ya faɗa yana nuna mata damtsen hannunsa yana sake zaro mata duka manyyan idanunsa. Daga haka kuma ya nufi Daddy hankalinsa a tashe. A cikin master bedroom ɗinsa ya ganshi, wanda har numfashinsa ya fara yin ƙasa.. Cikin wani irin tashin hankali Imran ya taro mahaifinsa ya kwantar dashi, wajan magungunansa yaje ya ɗakko masa wadanda ya kamata yasha sannan ya zaro ɗaya daga cikin aluran da ake yi masa yai masa, kafin wani lokacin ya samu bacci. A ranar Mommy da Humaidah basu kwana a gidan ba, ɗaya daga cikin gidajen da Matawalle ya mallaka mata suka nufa.
**************
Aunty Amarya ta kalli daddy da take bawa tea cikin mug kusan karfe goma sha ɗaya na safe itama bata daɗe da isowa ba ta jirgi tazo ita da autarta mai suna Amaani wacce zasu zo sa'a ɗaya da Maheera Matawalle kasancewar yau za'a daura zure idan an taso daga masallacin jummu'a. Auntyn tana kallon Matawalle tana faɗin. "Anya ba za'a ɗaga ɗaurin auren nan ba Daddyn Imran? Ni naga duk jikinka yayi weak sosai wallahi, ko Dr mai ka gani kai?" Ta faɗa tana kallon Imran Matawalle dake tsaye bakin ƙofa harɗe da hannu a kirji yana kallonsu. Shi dai Imran baice komai ba murmushi kurum yayi yana shafa kansa ya bar cikin room ɗin duka. Aunty Amarya ta kalli Amaani dake danna waya tana haɗe rai sosai take faɗin. "Ya aka yi baki gaishe da yayanki ba?" Amaani ta haɗe rai sosai ta turo baki tana faɗin. "Baki ganin yadda yake amsawa ne Mum? ko kallon mutane fa bayayi dan wulakanci, ni bazan ƙara gaishesa ba yana yiwa mutane yanga dan yaga yana da kyau." Ta faɗa so pissed up tabar ɗakin. Aunty ta bita da ido baki buɗe, banda murmushi babu abunda Daddy keyi. Aunty amarya ce ta taimaka masa yayi wanka anan kuma suka ƙara tattauna matsalar Mommy da Matawalle, Auntyn tace idan ya sauko sai ya maida ita ɗakinta saboda ƴaƴan su. Wani irin kallo Matawalle ya riqa yi mata yana faɗin. "ƴaƴana biyu ta halaka fa, gaskiya bazan yafe mata ba wallahi." Ya faɗa yana barin ɗakin. A can gidan su Rahama shagali kawai ake yi Abbie da iyalansa tun jiya suka iso harda matar Farooq Galadanci wacce ke ɗauke da yaron ciki. Ana sakkowa daga masallaci ɗaruruwan mutane suka shaida daurin auren Imran Matawalle da Rahama Abubakar Galadanci akan sadaki Naira dubu ɗari biyu. Waleema ta maza Abubakar Galadanci ya sa aka haɗa musu, bayan sallar magrib duka suna zaune cikin parlorn Abubakar Galadanci, Imran, Rahama da kuma Matawalle da yayansa Ali Matawalle, sai Abiee da kuma Hajja, nasiha suke masu mai ratsa zuciya inda Abbie ya kalli Imran yana faɗin. "My son ka ɗauki matarka da ƴarka ku tafi Allah ya sakawa auren nan naku albarka." Aliyu matawalle yana riqe da hannun Rahama har zuwa gaban wata arniyyar jeep da sai sheki takeyi, ya buɗe back seat Rahama ta shiga fuskarta lullube cikin wata black lifaya mai ratsin gold ajikinta ta kasa tantance farin ciki take ko akasin haka. Da murmushi cikin fuskar Maheera Matawalle ta miqawa Imran Matawalle little Aysha dai-dai kunnensa take faɗin. "Yaya gobe karfe 7:00am zanzo ganin little Albi ban gaji da ganinta ba." Da sauri ya riqe mata hannu. Yana riqe da little Aysha a ɗayan hannunsa yake faɗin. "Mahee karki zo wallahi karki zo, na gaya miki banda gobe a zuwa gidan mu." Ya faɗa sounding so very serious cikin muryarsa. Dariya Maheera tayi gamida ware masa ido tana faɗin. "Nifa ba wurin ka zanzo ba Yaya." Amaani dake kallonsu ta taɓe baki gamida ɗauke kai, gaba ɗaya ita bata san meke damunta ba akan Imran. Haka Imran yaja motar yabar cikin gate ɗin gidan Abubakar Galadanci, little Aysha na cikin jikinsa haka yake driving ɗin. Tsayawa yayi a hanya ya siya masu gasassun kaji da fresh milk. Har suka isa gidansu babu mai magana, horn yayi da sauri maigadi ya buɗe masu gate ɗin, Imran yayi parking kamar ya san Rahama fita zatayi yayi saurin danna lock a duka kofofin baya sannan ya fito daga motar ya rufe ya nufi entrance ɗin shiga gidan da Little Aysha a ƙafadarsa. Wani irin ɓacin rai ya ziyarci zuciyar Rahama ta dinga zabgawa hanyar harara. Ko minti biyar bai yi ba ya dawo ya nufi side ɗinta ya buɗe mata ƙofar. A fusace ta fito har tana neman faɗuwa ƙasa, da sauri yayi saurin tarota zuwa cikin ajikinsa. Ɗagata yayi gabaki ɗaya ya nufi ciki da ita tun a falo ta buɗe fuskarta da tagama kumbura sabida kuka. Ganin yanayinta kawai da yayi ne yasa ya saukar da ita. Wani irin kallo ta riqa yi masa cikin sakan biyu ta nufi stairs tamkar zata tashi sama saboda fushi, ko kallon kofar room dinsa batayi ba ta shige nata ɗakin. Anan jikin ƙofar ta zube tana sakin kuka mai fitowa tun daga cikin zuciyarta, haka ta riqa bin room ɗin da kallo ganin irin dukiyar da mahaifinta ya zuba mata. Shima bai kulata ba ya nufi nasa ɗakin ya sakarwa kansa shower. Sai kusan 11:00pm ya fito da boxer ajikinsa ya nufi ɗakinta nata, knocking yayi a bakin ƙofar ɗakin, jin shiru yasa ya tura ƙofar. Hangota yayi cikin soofa tana danna waya. "Kizo ki bata nono tashi tayi bacci." Jin little Aysha ta tashi yasa ta miqe tsaye ta saka silifas a kafarta ta nufi ƙofa dan zuwa ɗakko ƴarta. Shidai Imran kallon reaction ɗinta kurum yake, ko ɗakin Imran ɗin an zuba sababbin kaya acikin sa sai wani kamshi ke tashi a cikinsa. Tasa hannu ta ɗauki little Aysha dake kallonta ta juya