Header Ads
Showing 120001 words to 123000 words out of 139785 words

Chapter 41 - Albi Book Complete document by Hajjace.txt

Ads the beginning of article before Image

11 Jun 2024

990

Ads at the middle of Article

lafe a jikinsa take faɗin. "Kai bakaga abinda kake min ba ko?" Ɗagota yai yana kallan fuskarta yasa hannu ya share mata hawayen tare da faɗin. "Kece kika ɓata min rai, taya zaki dinga kallan mu nida Rahama tamkar wasu ƴan iska? Tazo zata faɗi Allah yasa ina tsaye taya bazan taimaka mata ba koda bamu da alaƙa Ruma? Bare kuma Rahama a wannan lokacin tana buƙatar kulawa ta musamman, ki duba ki gani ga ciki gashi ƙiri-ƙiri aka rabata da mijinta idan da kice a matsayinta zaki so ki ga ana wulakanta ki?" Rumana ta girgiza kai tana goge sauran kukan da ya fito. "Ki kwantar da hankalinki ki dena saka damuwarki akan duk abinda zakiga na yiwa Rahama, abinda ba zama muka zo yi ba gidan." Wani sanyin daɗi ne ya dinga shiga zuciyarta nan da nan ta yafe masa duk wani haushinsa da takeji. Hannunsa taji a saman kirjinta yana yi musu wani irin matsa, bakinsa a saitin kunnanta yake faɗin. "Kwana biyu ba'a bani hakkina saboda kishi, tsaya muga menene a cikin rigar." Ya faɗa yana zuge mata zip ɗin rigarta, sarai ta san wayo zai yi mata bata hanashi ba kodan kar ma yaje ya dinga kallan Rahama yana jin wani abun. Daga nan kiɗa ya canza suka shiga farantawa juna cike da kulawa. Da yake abin na manya ne, komai a Abuja akai, babu yadda Matawalle beyi ba akan Mommy tazo duka event ɗin amman tace bata san zuwa Abuja, su Maheera su Bassam tamkar ba uwarsu ake yiwa kishiya ba haka suka zage suna taya mahaifinsu murna. Sati ɗaya aka kwashe ana shagali daga nan ƴan uwa da abokan arziki suka kama gabansu. A can gidanshi na Abuja suka fara tarewa shida amarya dan samun damar cin amarci. Imran da baya ƙasar yaiwa Matawalle Allah yasanya alkairi dan koda Daddyn yace ya dawo bai samu damar hakan ba saboda sun kusa fara exams.


******
Rahama ce gabaki ɗaya tayi wani irin wujiga-wujiga, banda kuka babu abinda takeyi hannunta riƙe gam a cikin na Ummi gani take tamkar tana tafiya zata rasa rayuwarta. Hajja ta shigo ɗakin riƙe da wani katon mug da koko mai zafin gaske ta zauna a gefen Rahama tana faɗin. "Daure ki kafa kai ki shanye shi tas zaki samu saukin haihuwar Insha Allahu." Rahama taiwa Hajja wani kallo tana cije lips sai juya kai take side by side tana faɗin. "Hajja ki kyaleni da wannan kokon, wayyo Allah Ummy mutuwa zanyi bazan iya haihuwar nan ba." Cike da ƙarfafa guiwa Ummy take faɗin. "Insha Allahu zaki iya Rahama duk wanda kika ganshi da ɗa shi kaɗai yasan irin kwakwar da yaci. Kicigaba da addu'a zaki haihu da ikon Allah." Wani irin murmushi Rahama tayi tasan ba zata taɓa yin rai ba dan abinda takeji yayi daidai da alamun mutuwa, duk da ranta ya ɓaci akan rashin ɓullowar Imran tun lokacin da ta, dawo gida bezo ya ga halin da take ciki ba, hakan be hanata jin ina ma ace yana wajan nan ba. Wani irin uban nishi tayi tana ririƙe Ummi da Hajja kamar zata haihun sai dai ina abu ya cutura, gashi bata da wani sauran karfi saboda jikinta duk ya saki Hajja tace. "Toh ance kisha kokon nan kinki da kinsha da tuni ya ɗan taimaka miki kinji kwari yadda zaki iya." Da wata irin murya Rahama ke cewa. "Hajja kin dameni da kokon nan, nasan mutuwa zanyi Ummy na shiga uku." Ganin yadda duk hankalinta yake a tashe ne yasa Ummy fitowa ta samu Abba dake tsaye a parlor, yana ganinta yace. "Ta haihu?" Ummy ta juyar da kai tana cewa. "Ina tunanin sai munje asibiti dole sai anyi scanning mungani, wannan doguwar naƙudar tayi yawa abu tun jiya har yanzu? Wallahi duk ta galabaice idan muka zauna a gida komai zai iya faruwa da ita har da babyn ma." Abba ya jinjina kai yana cewa. "Toh azo aje mana me aka tsaya yi?" Juyawa Ummy tayi ɗaki ta wuce ta ɗakko trolley wacce already an kammala haɗa komai na haihuwa, ta kira Aunty Kausar ta sanar da ita cewa ta bisu hospital ɗin. Suna gama wayar ta kira Imran wayar bata shiga. Kai tsaye aka tafi asibitin da Ummy ke aiki suka wuce labor room. Traying numbers ɗinshi ta shiga yi, cikin ikon Allah ta samu guda ɗaya ta shiga. Da girma da mutunci ya shiga gaishe da ita, Aunty Kausar tace. "Kaci gaba da addu'a Imran Rahama na asibiti zata haihu." A lokacin Imran na sakkowa daga stairs ɗin jirgi, wani irin shock yaji zuciyarshi ta wani tsinke yace. "A wane hospital Aunty?" Gaya mishi tayi yasha toka tamkar yana gabanta yake cewa. "Waye yace a kai min mata hospital? Meyasa ba'a gaya min ba tuntuni? Aunty kice kar shegen da ya leƙa min mata da sunan karɓar haihuwa gani nan zuwa." Yana kaiwa nan ya katse, da sauri ya ƙarasa reception yana gama komai ya nufi inda motocin da suka zo ɗaukarshi suke. Yana zuwa yace su bashi key ɗaya babu musu suka bashi ya shiga motar da wani irin speed ya bar airport ɗin. Aunty Kausar na zuwa ta sanarwa da Ummy cewa Imran yana hanya sai dai bata sani ba ko daga can Indian yake ko kuma yazo Nigeria ita dai kawai yace ace kar shegen da ya taɓa masa mata. Abba dake gefe yaja wani irin tsaki ransa a mugun ɓace yake cewa. "A gidan ubanshi ta zama matarshi, yaron nan bashi da kunya wallahi." Ummy ta sanyaya murya tana faɗin. "Ka kwantar da hankalinka Abban Ra'ees, ta iya yiwuwa ya faɗi hakan ne cikin rudewa tunda ance masa haihuwa ce." Abubakar Galadanci ya ɗaga kai yana hura hanci yake faɗin. "Kika bibiya ma a buge yake yaje yasha kayan mayenshi suna gaya masa karya da gaskiya, banda hauka taya kana ƙasar waje ka wani ce kar a taɓa yarinyar dake ƙoƙarin haihuwa a yanzun nan." Ummy da Aunty Kausar basu ce komai ba sai ma komawa cikin ɗakin da Rahama take da Ummy tayi. Cike da tashin hankali ya shigo reception ɗin yana duban inda zai hango fuskar da ya sani, Aunty Kausar ya fara gani da sauri ya isa inda take, jikinsa na rawa yake tambayarta ina Rahama, idanunsa sun rufe ko Abba bai gani ba a tsaye. Zai shiga ɗakin kawai yaji an riƙoshi ta baya, yana dagowa suka yi ido huɗu da Abubakar Galadanci, cikin hade yake kallanshi yana cewa. "Ina zakaje?" Imran yaji tambayar kamar ta yara, ya kalli Abba yana faɗin. "I'm a Doctor and cikin nawa ne ina so naga babyn tazo lafiya that's all." Ya faɗa tare da zarewa Abba hanunu daga shoulder ɗin sa ya shige room ɗin......


(Complete Decuments)
*WAMINAL HUB* #500
*ZO GARENI* #300
*NIDA RAHEEMA* #300
*RAYUWAR AURENA* #300


#Asmy b Aliyu
#Hajja ce
#Imran Matawalle
#Rahama Galadanci
#Farooq Galadanci
#Rumana
#Team Albi
#Haske Writers Association...






[12/15, 9:02 AM] Asmy B Aliyu😘: *ALBI...*
(my heart❤️)


*ASMY B ALIYU*
DA
*HAJJA CE*👈


PAID BOOK..#(500)


*Account Details*
0004157137
*Jaiz Bank*
*Asma'u Buhari Aliyu*
Shaidar biya ta
08086207764


*Katin waya ta MTN.ta 07043079282 shaidar biya ta 07065283730 view WhatsApp*


51....


Da sauri Abba yake kallan Aunty Kausar cikin tsananin masifa wacce tasa jijiyoyin goshinsa bayyana yana faɗin. "Kingani ko Kausar? Na gaya muku yaran nan bashi da tarbiya kun kasa ganewa, ni yake kalla yana cewa wai cikin nashi ne saboda rashin mutunci, yana ganin yarinyata a cikin hatsari amma shi ta cikin jikinta ma yake." Kallan Abba kawai Kausar ta tsaya yi tana so tace masa Abba kai ka fara kulashi da ka kyaleshi ya gama abinda zai yi ya bar wajan haka duk baza su faru ba. Amman dan kar ya dawo kanta sai taja baki tayi shiru. Imran kuwa a haukace ya faɗa ɗakin, hango yanayin Rahama da yai ya ɗaga masa hankali. Gaba ɗayanta ya tattaro zuwa jikinsa yana wani shafar gashin kanta a haukace, girgiza kai kawai yake yana kallan yadda take kuka tana rirriƙe mutane. Ƙamshin jikinsa ne ya tabbatar mata da cewa shine duk kuwa da tana cikin wani hali. Ta sake fashewa da kuka tare da buɗe ido da kyar tana kallanshi. "Sai randa zan mutu kazo? Sai da nace maka bana san haihuwa shine...." Yai saurin kamo face ɗinta yana girgiza kai. "Karki ce haka just kiyi addu'a zaki haihu kinji?" Ya faɗa mata cike da hope. Hana kowa taɓata yai kuma be ma san Ummy na tare dasu ba, ganin yadda yake ta wani lallaɓa Rahama ne yasa ta fice kar Imran yayi abinda yafi karfin kallonta. Shi yama manta cewa yanzu ba matarshi ba dan taga yadda bawa Rahaman wani irin caring. "Please ku bamu guri." Wata nurse ta wani kalleshi tana faɗin. "Taya zamu fita bayan muna kan aikin mu?" Imran ya watsa mata birkitattun idanunsa itama ta dake taki jin tsoransa. Tashi yai ya ɗauki Rahama tana sakin ihu ya nufi hanyar fita, a gigice nurse ɗin take masa magana. "Meye haka dan Allah? Ina zaka kaita kuma." Ci kanki Imran bece mata ba ya buɗe ƙofar da ƙafarsa, su Abba dasu Ummy duk sukayo kanshi suna faɗin. "Lafiya?" Yana sauri yake faɗin. "Bana san ta haihu a hospital ɗin, clinic ɗina zamuje." Abba zai yi masifa Ummy ta riƙoshi tana girgiza masa kai. Back seat ya kwantar da ita ya kira Aunty Kausar ta riƙeta, da wani irin gudu yaja motar cikin kankanin lokaci suka isa clinic ɗin, yana ɗakkota faya ta fashe, be damu da yadda jikinshi ya ɓaci ba suka nufi labor room yace kar wanda ya biyoshi yasa key ya rufe. (Asmy da Hajjace suma basu samu damar shiga ba)🤣 Motar su Ummy tun kafin su gama parking sai kukan jaririya sukaji, farin ciki a wajan Aunty Kausar sai da tayi ƴar kwalla, taje da gudu ta rungume Ummi dake janyo trolley tana faɗin. "Rahama ta sauka." Wani farin ciki ya cika zuciyar Ummy sai dai bata nuna ba a fuskarta saboda Abba wanda ya zo ne dan ana cewa ta haihu ya ɗauke yarsa su bar clinic ɗin. "Toh ai ga kayan Kausar sai a shiga dasu a shirya su." Aunty Kausar ta kalli ƙofar, mayar da idanunta tayi kan Ummy tana faɗin. "Ummy Imran shida Rahama ne kawai a cikin room ɗin sai dai kuma mu jira fitowarsa." Abba wani irin bakin ciki ya kamashi, yaro ƙarami sai gara kansu yake yi, amma rahama ce taja musu dan da bata biyewa Imran ɗin ba da hakan bata faru ba. Mota ya koma ya zauna sai huci yakeyi kamar wanda yaci uban gudu. Shi kuwa Imran da suka shiga room ɗin kwantar da Rahama yayi da rawar jiki ya kama hannunta ya daure tana kuka ya koma ya durƙusa, cikin yan sakanni ya cire mata babyn dan ganin hakan ne kawai mafita saboda ta gama galabaicewa. Yana yanke cibin ya rungume babyn yana jin tamkar ya saki kuka, da sauri ya kwance hannayen Rahama wacce tuni ta sume saboda tashin hankali. Bedsheet ɗin dake ninke akan side table ya janyo tare da naɗe babyn a ciki ya kwantar da ita, cike da tashin hankali ya koma wajan Rahama yana jijigawa, ganin bata dawo hayyacinta ba yasa shi sanya bakinsa cikin nata ya shiga hutawa, ta saki wata ajiyar zuciya yaje ya ɗakko allura yai mata yasa zare zai yi mata ɗinki ta fashe da kuka tana matse ƙafafuwanta ya kalleta da sauri cikin serious yake faɗin. "Ki bari nayi miki shine kawai samun lafiyarki, idan kika ki yadda nan gaba zaki zama abar kyama wajan mutane dan wari zaki dinga yi." Ta kuma sakin kuka wanda Imran kejinsa har cikin ransa, ya ware legs ɗin ya ɗinketa tsab, babynsa ya ɗauka yai mata khuduba yana lura da Rahama da ko kallansa bata son yi, sannan yaje ya kwantar da babyn yaje buɗe ƙofar ba tare da ya kalli kowa ba ya wuce office ɗinsa yana mai ciro wayarsa ya danna tare da karawa a jikin kunnansa yace da Musbahu a kawo masa kayan sawa clinic ɗin shi. Su Ummy kuwa ganin ya fice yasa su kuma suka shiga room ɗin, kwance suka tarar da ita tana ta uban kuka. Ummy ta ɗauki babyn mai kama da A Galadanci sai dai hasken Rahama ta ɗakko jawur da ita. Shi kansa Abba da ya shigo ya kalli ƴar sai da zuciyarsa ta kusa bugawa a lokaci ɗaya. "Ga sabuwar amarya Abban Ra'ees." Abubakar Galadanci ya hadiye wani kakkauran yawu yana sake kurawa babyn ido. "Da kai take kama fa." Ummy ta sake faɗa tana buɗe face ɗin jaririyar. "Ya kamata ku ɗakko Rahama mu koma gida tunda duk lafiya lau suke." Ya faɗa yana ƙarasawa wajan Rahama wacce taki buɗe ido ta kalle su. "Sannu Rahama bari su gama gyaraki sai mu koma gida." Aunty Kausar ce tai mata komai tayi tsab da ita tamkar ba itace aka kawo shame-shame ba. Suna fitowa Aunty Kausar da A Galadanci riƙe da ita, Ummy kuma rungume da baby sai wasu ma'aikata biyu da suka ɗakko ragowar kayansu suna bin su dashi. Da mugun mamaki Imran yake kallansu cikin shirinsa na shadda dark blue tana ta kyalli, ɗinkin ba ƙaramin kyau yai masa ba. Ganin sun ɗakkota yasa shi saurin ƙarasawa yana musu kallo mai cike da san jin ƙarin bayani. "Zamu koma gida ne Imran Abba baya san zaman hospital." Cewar Aunty Kausar dan kar a samu matsala, sai dai duk da haka ba'a tsira ba sai da Abba yace. "Gida zan tafi da yata bana san wata magana Imran." Cike da ɓacin rai yake kallan ƙasa yau dai shima zai nunawa A Galadanci karfin iko, ya gaji da wannan abin da yake masa. Smile ya saki tare da ƙarasawa wajan Ummy ya karɓi babyn ta bashi ba tare da sun kawo komai ba a ransu. Kallon Ummy yai da yanayi na rashin damuwa a face nashi yake faɗin. "Am a great Doctor kuma zan iya kulawa da baby na da ikon Allah." Yana kaiwa nan ya nufi mota already masu kula dashi wadanda sukaje airport ɗakko shi suna wajan, back seat ya zauna shida babyn ya rungume yace da driver yaja su tafi. Wani irin kallo Rahama take bin motar dashi zuciyarta na wani irin bugawa, yayin da A Galadanci ya shiga zaro ido domin duk wani abu da yake ganin Imran yayi yau ya matukar bashi mamaki. "Ina jin yaran nan zuwa yai yayi shaye-sayen shi shine yazo yake yi min hauka anan." Wannan karan Ummy takai matuƙa wajan ɓacin rai, cikin wani yanayi take cewa Abba. "Kayi nasara wajan kwace ƴarka Alhaji, sai dai karka manta shima Imran iko ya nuna maka akan tashi ƴar, ya nuna maka cewa ƴa batafi ƴa ba, wannan wane irin abin takaici ne kakeyi?" Kafin ya bata amsa tuni Rahama ta sulale cikin Aunty Kausar, suka maida hankali kanta kafin azo a ɗauketa ayi emagency da ita. Jininta ne yai mugun hawa wanda ya tashi hankalin likitocin dake asibitin, gashi duk sun shaida matar oga ce. Yana zaune a cikin motar gaba ɗaya duniya tayi masa zafi komai baya jin daɗinsa, ya rasa mahaifiyarsa wacce zata zama mai share masa hawaye, cikin ikon Allah Rahama ta shigo rayuwarsa gashi itama an rabashi da ita. Kallan babyn yai cike da tausayi tasha kayan sanyi sai bacci takeyi, a hankali yace. "Mamanki zata zo gareki am very sure." Jin wayarsa na ringing yasa shi ɗauka ganin Dr Fawwaz yasa shi peeking, cike da respect yake sanar dashi condition ɗin da Rahama take ciki. Kamar yace driver ya koma sai kuma ya dake yace da Fawwaz. "Kuyi mata abinda ya dace I entrust her to you Doctor, koda parents ɗinta zasu ce a nemo ni kuce nace am very busy. But Fawwaz ka kular min da matata." Katsewa sukai Imran ya jingina bayansa jikin kujera yana faman rintsa ido ga kanshi da yake barazanar faɗowa ƙasa. A hankali ya furta. "My poor Albi, am so sorry but wannan itace hanyar da zata sa mahaifinki ya dawo min da ke da amimcewarsa." Sai da ya tsaya a wani store ya siya Nan da sauran abubuwan da baby zata buƙata sannan ya ce su kaishi gidansa, tun kafin ya ƙarasa ya kira Maheera a waya yace ta same shi a gida. Zagaye ya shiga yi ransa a ɓace, yadda suke shiga da fita daga cikin room ɗin da Rahama take ne yasa shi zaro waya ya kalli Ummy yana faɗin. "Bani lambar yaran can yazo yaga halin da ya jefa min yarinya, idan zai yi iskancinshi bana so yana yi akan gudan jini na." Ummy da ta gama zuwa wuya tai masa banza tamkar bataji abinda yake cewa ba, ya daka mata tsawa cike da bala'i yake faɗin. "Bakyaji ina miki magana ne?" Ta kalleshi da wata irin angry face tana cewa. "Banda ita Alhaji ai baka bani damar da zan iya ajiye lambar wayar surukin naka ba." Da bala'i yake cewa. "Karki sake haɗani da sakaran yaron nan marar mutunci." Ummy ta gyara murya tace. "Allah ya kyauta." Karshe dai sai da Dr Fawwaz yace subar Rahama a asibitin saboda tana cikin mawuyacin hali, sosai jininta yai mugun hawa. Babu yadda Abba ya iya dole ya baro asibitin aka bar Ummy da Aunty Kausar. Imran na zaune yana karewa babyn kallo yajiyo knocking ya sakko tare da buɗewa, Maheera ce ya bata hanya ta wuce sannan ya maida ƙofar ya rufe. Ko magana beyi mata ba ya nufi upstairs tabishi tana mamakin yadda ya sauya ya zama mai haɗe rai duk ta tsorata tayi zaton ko wani abun tayi masa. Bude duka idanunta tayi ganin baby a cikin towel, gabanta ya bada wani irin ras. "Mahee ina so ki zauna a gidan nan zanje na yiwa Mommy magana dan ta sani hope ba matsala?" Bakinta yana rawa take cewa. "Yaya wannan babyn fa tawaye?" Saboda babu wanda ya sanarwa a nashi family ɗin. Ƙarasawa yai wajan yana sauke numfashi yace. "Rahama ce ta haihu ɗazu." Maheera naji ta wani ruga zuwa wajan babyn cike da wani irin farin ciki a fuskarta. "Yaya shine baka faɗa mana ba?" Ta faɗa

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads