Header Ads
Showing 108001 words to 111000 words out of 139785 words

Chapter 37 - Albi Book Complete document by Hajjace.txt

Ads the beginning of article before Image

11 Jun 2024

1008

Ads at the middle of Article

yana cije leɓe, sosai yake jin ɓacin rai amman ya daure. "Abubakar kayi hakuri ka yafewa Rahama girman laifin da tayi maka na barin rayuwarku, tabbas ta kunyata ku a idon duniya amma ka duba ka gani kawai zallar kurciya ce." A fusace Abba ya katseshi. "Daman shine ya kawo ka har cikin office ɗina? Okay fine dan Allah ka tashi ka tafi, kuma na yafewa ɗanka ita tun daɗewa." Cikin zafin rai Matawalle ke faɗin. "Kai baka yafiya ne a rayuwarka Abubakar Galadanci?" Abba ya dafe kansa zuciyarsa na mugun bugawa saboda tsananin ɓacin rai, ya ɗago idonsa da suka canja kala yana faɗin. "Zan yafewa Rahama amman da sharaɗin." Da sauri Matawalle yace, "Ina jinka insha Allahu Imran zaibi duk wani sharaɗinka da ka ɗora masa." Wani irin murmushin mugunta Abba yayi yana faɗin. "Ina so nan da sati biyu ka dawo kai da ɗanka da matar tashi cikin gidana sai na faɗa maka sharaɗin. "Daddy ya ɗaga kai alamar amincewa dan yasan saboda kawai ya wulakanta shi ne yayi masa haka. Amman babu komai zai yi masa hakan da yake so saboda farin cikin yaronsa. Sallama ya yiwa Abubakar Galadancin sannan ya fice daga office ɗin...........




(Complete Decuments)
*WAMINAL HUB*#500
*ZO GARENI*#300
*NIDA RAHEEMA* #300
*RAYUWAR AURENA*#300




#Asmy b Aliyu
#Hajja ce
#Imran Matawalle
#Rahama Galadanci
#Humaida Makarfi
#Team Albi
#Haske Writers Association.
[12/10, 7:08 PM] Asmy B Aliyu😘: *ALBI...*
(my heart❤️)


*ASMY B ALIYU*
DA
*HAJJA CE*👈


PAID BOOK..#(500)


*Account Details*
0004157137
*Jaiz Bank*
*Asma'u Buhari Aliyu*
Shaidar biya ta
08086207764


*Katin waya ta MTN.ta 07043079282 shaidar biya ta 07065283730 view WhatsApp*


46....


Yadda yaga Mami ta shigo cikin parlorn nasa ne yasa ya miƙe zaune, kallo ɗaya zakayi masa kasan baya cikin natsuwarsa da kuma walwalarsa, ba abinda yaja masa shiga cikin wannan halin sai sabida Rahama Galadanci, mace ɗaya tilo daya kasa cirewa acikin duniyarsa duk kuwa irin girman laifin da ta aikata masa a baya, still ya kasa cireta aransa. Mami ta girgiza kai a karo na babu adadi tana faɗin. "Wallahi kana bani mamaki, wai saboda wannan yarinyyar kake neman kashe kanka?wannan wane irin bala'i ne? an saka ranar aurenka amman kullum abinka cigaba yake ƙarayi. Tsorona Allah tsorona kar kaje ka kasa baiwa Rumana farin ciki Farook. (An saka auren Farook Galadanci da ƴar gidan abokin Abbie wanda shi Abbie ɗin ne yaje ya nemarwa Farook aurenta dan ya rage masa damuwar da ya tsinci kansa aciki.) Tun daga ranar da Rahama tabar cikin rayuwarsa ya rasa duk wani farin ciki da walwala, jin daɗi sukayi ban kwana cikin tashi rayuwar. "Gaskiyarki ne Mami tana can tana farin cikinta tana baiwa wani kato farin ciki da jin daɗi wanda ta mallaka masa jikinta tun a titi, ni kuma ina nan ina hasarar tunaninta." Ya kalli Mami da idonsa da suka gama canza kala yake faɗin. "Kiyi hakuri Mami." Haka kaɗai ya iya faɗawa Mami, Mami ta bishi da harara tana faɗin. "Yau da yamma ka tabbatar kaje ka samu Rumana kun kai karshen abubuwan da zaku tsara a bikin ku." Ɗagawa Mami kai kurum yayi. Bar masa parlorn tayi tana ta banbamin faɗa..
**********


Har Imran ya fara shirye-shiryen fitarsu waje sai Daddy ya dakatar da tafiyar ya faɗawa Imran ɗin cewar Abubakar Galadanci yana so zai yi zama dasu nan da sati biyu masu zuwa. Imran ɗin bai kawo komai aransa ba sai murna ma da ya hauyi saɓanin Rahama da maganar ta tsaya mata a rai sosai kullum da abin take kwana take tashi a ranta. Sun haɗu da Umminta a gidan Hajiya Babba take shaida mata yadda Matawalle yayi da Abba. Ummi itama tasha mamaki amman tayi murna ba kaɗan ba jin za'a sasanta Abba kuma zai yafewa ƴarta. Acikin sati ɗaya Rahama tayi wata irin rama wacce Imran ɗin ya rasa dalilinta, tun yana faɗa har ya dawo rarrashin cewar ta kwantar da hankalinta. Ita kuma babbar fargabarta a duniya shine ta rasa Imran Matawalle duka. Haka ta nemi dalilin dake cikin zuciyar Abbanta na cewa dole sai sunje gabaki ɗayansu ta rasa dalili har kirgen kwanaki takeyi. Ana cikin haka Imran ya dawo da Humaidah saboda matsawar da Matawalle yayi masa. Mommy tayi-tayi da Humaidah su koma wajen Malam mai tasiri dan a samu a juya hankalin Imran ɗin ya dawo kanta, amma Humaidah ta nuna sam bata yadda da asiri ko tsafi ba, saboda tana tsoron mutuwa idan kuma asirin ya karye ya dawo kanta kuma fa ya zatai? Tasan iya barikinta kawai da kissa zasu iya samar mata da soyayyar Imran Matawalle a zuciyarsa. Kallan Mommy tay take cewa. "Gaki dai kina yiwa Matawalle asiri dashi da ɗansa, amman ko kaɗan babu amfanin da asirin yake miki, tunda idan suka tashi yi miki rashin mutunci babu wanda ke tsaida su. kawai ki barni naje naji da gidana, tabbas kinyi min ƙoƙari acan baya Aunty nagode, amma ki barni zan ƙarasa sauran da kaina." A lokacin Mommy baki ta saki tana kallon Humaidah rakiyyar datafasa yi mata kenan na komawa gidanta sai dai Humaidah ɗin taja motarta da kanta ta koma gidan Imran Matawalle. A cikin sati biyu ɗin da sukayi na jiran ranar da Abba ya basu kullum Imran Matawalle yana manne da Rahama, Itama a haka take biye masa ko yana clinic da yaji yana buƙatarta zai dawo gida duk da itake tsokanoshi da dirty talks ɗinta, haka zata ta tura masa saƙo a waya wanda irin abubuwan da take tura masa tun acan zai fara jin yanayinsa ya canza, agigice yake dawowa gida sai idan yasan zasuyi theater ne zai kashe wayarsa duka dan kar a samu matsala. Yau ta kasance Ranar Lahadi kuma tayi dai-dai da ranar da zasuyi zaman da Abba ya buƙata wato Alhaji Abubakar Galadanci. Sai dai tun safe Rahama take ta fargaba da kuma faɗuwar gaba. Imran har fushi yayi kusan 12 ya kira daddy ya faɗa masa zasu iya zuwa yanzu? Daddy yace a'a sai bayan la'asar Yayan daddy na hanya wato Abbie. Yinin ranar kasa tabuka komai tayi, ko abinci sai da ya fita ya samo masu wannan karon da takeaway ɗin Humaidah yana aje mata ya fito daga cikin ɗakin itama kallo ɗaya tayi masa ta ɗauke kai tare da taɓe baki iya lokacin da ta ɗibar masa ya kusan cika, ƙiris ya rage Imran Matawalle ya zama nata ita ɗaya ta dalilin shi mommy ta daina ɗaga wayarta idan taje gidan bata wani sake mata fuska. Baki ya buɗe yana kallon yadda hawaye ke zubar mata ya tura abincin da sukeci zai fara masifa tayi saurin shigewa cikin jikinsa tana fashewa da kuka mai tsayawa arai, saboda karfin hali kawai takeyi a gabansa. Yadda take kukan yayi bala'in ɗaga hankalinsa, ɗagota yayi ajikinsa yana kallon cikin idanunta abunda ya gani acikin idanunta yasa yaji numfashin sa na barazanar ɗaukewa duka. Da sauri ya kamo dogayen yatsun hannunta yana binsu da kallo, wata irin runguma yayi mata yana sakin kabbara yana dariyar farin ciki. Haka ya ɗagota yana yi mata wani irin kallo tamkar zai canyeta gaba ɗayanta. Imran ya zamar mata tamkar wani mahaukaci, ya sake rungumeta cikin jikinsa, wani sabon sonta dake huda cikin zuciyarsa yaji yana bin jinin jikinsa, hawayen farin ciki ya rika sauke mata a saman ƙafadarta. A ruɗe Rahama take ta ɗauka yana jin yadda takeji ne, ta dauka yana jin tamkar za'a raba auren su ne. Ya ɗagota yana riqe da ita ajikinsa yake faɗin. "Daga yau daga yanzun nan karki ƙara ɗaukar wani abu mai nauyi, please komai kikeso ni zanyi maki shi. Yanzu muje kiyi wanka muje clinic na duba lafiyar babyna." Baki ta buɗe tana kallonsa da shock cikin fuskarta, shin da gaske ne tana ɗauke da cikin Imran acikin jikinta? Bata taɓa kawo haka acikin rayuwar aurensu nan kusaba na ɗaukar ciki . Ko a wajen wanka sai wani irin lallabata yake tamkar wata kwai. Yau duk wannan wasan da suke a toilet babu shi, duk yadda Rahama taso ya bari suyi sallah ƙin yadda yayi haka ya ɗauketa da ita da hangbag ɗinta ya nufi mota. Wani irin shegen kallo Humaidah ta rinƙa yi masu dan tana zaune a cikin dining area tana cin abinci suka fice daga parlorn akan idonta. Wani abu taji yana tsaya mata arai da wani irin kishin Imran ɗin. Da kansa ya ɗibi jininta haka yasa tayi fitsari lab ya wuce da sauri yana tsaye akayi komai yadda ake ganin rawar jikin Dr. Imran Matawalle yasa suka san koma na waye to yana da matukar muhimmanci a wajansa. Result ya fito har scanning yana zaune aka yi mata, nan suka tabbatar masa da cewa tana dauke da cikin sati biyu da kwana biyar. Juya takardar ya shiga yi a hannunsa, kasa daurewa yayi yana zaune cikin office ɗinsa, dukansu suna cikin soofa a kwance Rahama na cikin jikinsa tana bacci daman kuma fargaba ta hanata komawa tun asuba sai yanzu. Kiran maigirma Matawalle yayi bai tsaya ya gama amsa sallamarsa ba ya fara ihu ta cikin wayar, "Yessss... Yesss... Yessss! Daddy da gaske na kusa zama Paapa, ina farin ciki Daddy I'm so happy so..so..much." Ya faɗa sounding so very happy. Shima wani irin farin ciki Matawalle yakeji a wannan lokacin, wai Imran ne zai zama Daddy da gaske? "Alhamdulillahi ya rabbi!" Daddy ya faɗa yana jin kwallar farin ciki na cika masa idanunsa, cikin kulawa yake faɗin. "Ka kula da ita please Imran." Daddy ya faɗa da wani kalar farin ciki a muryarsa. Bayan sallar la'asar Daddy ya kira Imran yana faɗin ya har yanzu basu zoba gashi har kusan karfe huɗu da rabi. Imran ya kalli fuskar Rahama yana shafawa a hankali sai yanzu ya lura da mugun hasken da tayi, fuskarta har wani irin glowing takeyi, yaja numfashi yana faɗin. "Daddy tana bacci idan ta tashi zamuzo, kasan ba'a son ana tada mai juna biyu daga bacci." Murmushi Matawalle yayi kawai ya kashe wayar yana jinjina rashin kunyar Imran ɗin. Ita kuwa da yake ta samu baccin sai kusan biyar Rahama ta farka tayi miqa acikin jikinsa tana zubawa fuskarsa ido, da sauri kuma ta miƙe zaune tana kallon agogon dake maƙale acikin hannunta, ta wani zaro ido tana kallon Imran ɗin tamkar zatayi masa kuka take faɗin. "Karfe biyar meyasa baka tasheni ba Abba na can na jira kar yayi fushi ko yace mun saɓa umarninsa." Ya ware mata ido shima bece komai ba. Miƙewa tayi da sauri ta nufi toilet ɗin dake cikin office ɗin nasa, da gudu shima ya cimmata, tare suka ɗauro alwalar sukayi sallah, ta miƙe da sauri sai kawai taji tana jin wani jiri da sauri Imran ya dawo da ita jikinsa hankalinsa a tashe, cikin ɗaga murya yake faɗin. "Meyasa bakya bin komai a hankali ?." Ta turo baki tana ganin yadda yake yi mata masifa, zai rikota ta fisge idonta na cika da hawaye, ya girgiza kai kawai yana bata hakuri cikin rarrashi yake faɗin "Ya isa to please kinsan fa bake kaɗai bace please ki kula sosai." Haka ya ɗagata zuwa mota haka nurses ɗin wurin suka rinƙa binsa da kallo suna gulmarsa kasa-kasa daman yana iya taraiyar macce har haka? sosai kansu ya daure dan shi bama ya nuna musu cewa yana da mata. A hankali ya dinga jan motar har sukaje gida. Ya ɗauketa haka ya shiga da ita har cikin parlorn Matawalle, kallo ɗaya Daddy yayi masu ya ɗauke kai tare da girgixa kai. Da wata irin kunya Rahama ta sauka ƙasa tana gaisheshi da sauri Imran ɗin ya ɗagota ya zaunar daita cikin sofa. Shaye da toka yake faɗin. "Waya faɗa maki ana zama a ƙasa? Daddy ka ganta koh?" Imran ya faɗa yana ɓata rai. Girgiza kai kawai Matawalle yai yace su fito. Su ukun suka nufi gidan Abubakar Galadanci zuciyar kowa na bugawa da wani irin yanayi, maigadi yayi masu jagoranci har cikin parlorn Abba. Duk yadda Rahama taso Imran ya sakar mata hannu ƙin yadda yayi, amman suna haɗa ido da mutanen dake zaune cikin parlorn tai saurin fisge hannunta da sauri ta nufi Hajja lokaci ɗaya hawayen farin ciki na taruwa a idonta. Itama Hajja ba ƙaramin ƙewar jikartata tayi ba, sosai tayi bala'i tayi masifa tayi rarrashin duniya akan Abubakar ya dawo da Rahama cikin gidan nan ya yafe mata laifin da tayi musu amman yaki saukowa. Hajja ta ɗagota tana yi mata wata irin harara tana faɗin. "Kuka kuma? Toh kukan me zakiyi kina tare da abun sonki da kaunarki." Ta faɗa tana yiwa Imran ɗin wani ɗan iskan kallo mai cike da tsantsar jin haushinsa, dan saboda shi duk tarasa jikarta tsawon wata da watanni, sannan duk saboda shi ba'a ƙara zaman lafiya a cikin danginsu ba, saboda shi zumunci yake son watsewa. Gaisuwar da yake yiwa Hajjan ma bata karɓa ba sai ma ɗauke kai da tayi tana ƙara damƙe hannunta cikin na Rahama, wannan karon zata tsaya da kafafunta bazata ƙara barin Rahama tabarsu ba, duk da cewa sun samu labarin an ɗaura musu aure da Imran ɗin. Cikin mutunci da girmamawa Matawalle ya gaisawa da Abbie, shima Abbie ɗin da fara'a yake amsawa tamkar babu abunda ya faru. Saɓanin Alhaji Abubakar Galadanci da yayi mugun haɗe rai. Imran ya gaishe da Ummi ta amsa masa sai dai fuskarta babu wani walwala. Jikin Rahama yayi wani irin sanyi sai taji duk babu wani alkhairi acikin wannan zaman nasu. Abbie ya buɗe musu taro da addu'a sa'annan ya kalli Abubakar Galadanci yana faɗin. "Muna saurarenka Abubakar." Abba yayi gyaran murya ya kalli gefen inda Rahama take, kallon da taga Mahaifinta nayi mata a wannan lokacin yasa taji wani mugun fitsari ya bala'in cika mata mara. "Ina so ku zama shaida, yanzu zanyi zama na farko da karshe nida Rahama. Sannan zan yafe mata duk laifin da tayi min amman da sharaɗin." Da wani irin razana ta ɗaga ido tana kallon Abban nata. "Yanzu gata a cikin gidana, ta yadda da cewar ta dawo kenan haka bazata ƙara kula ɗan gidan Matawalle ba har abada.!" Dukan su babu wanda shock bai bayyana cikin fuskokirsu ba. Da rawar murya Rahama taja ɗuwawunta har gaban mahaifinta zuciyarta taji tana ƙara cika da wani irin sabon tashin hankali wanda bata san kalarsa ba. Abba ya maida kallonsa wajan Imran Matawalle da shima shock ke bayyane cikin fuskarsa, ya miƙa masa biro da takarda yana faɗin. "Ina so ka rubuta takardar sakin ƴata ka bata yanzun nan, ni kuma zan yafe mata laifin da tayi min gabaki ɗaya idan har ka yadda da cewar kai masoyinta ne." Imran ya kalli Rahama wacce kanta ke sauke a ƙasa ta kasa kallon Imran ɗin dan yana iya karyar mata zuciya. Ji tai kawai wannan karon ko mai zai faru sai dai ya faru zatayi biyayya akan duk abunda mahaifinta zaice zata bishi koda hakan zaizo ƙarshen numfashinta, bazata ƙara yin kuskuren da tayi a baya ba. Duk yadda Imran ɗin yaso ta kalleshi ƙin yadda tayi ta kalleshi, zuciyarsa na wani irin harbawa da sauri da sauri tamkar zata fito. Zai yi haka dan farin cikin Rahama wannan karon zaiyi ƙoƙarin ya danne duk wani abunda yakeji akanta, zai bar rayuwarta ya bata damar daidaita rayuwarta da iyayenta. Samun kansa yayi da ɗora hannu akan takardar ya shiga rubutu, cikin minti ɗaya ya gama ya dunkule takardar ya isa har gaban Rahama ya kamo hannunta ya saka mata a ciki hannayensu yana ta faman rawa. Da wata irin sassarfa yabar parlorn, Matawalle ya jinjina kai yana kallon Abubakar Galadanci da wani irin yanayi cikin fuskarsa yake faɗin. "Nagode da dukkan karammawarka Abubakar, duk ranar da Rahama ta haihu zamu zo mu karɓi yaron ko yarinyar da ta haifa." Haka ya fice daga parlorn jikin kowa yayi wani irin mugun sanyi, babu kalmar da tafi tsaya masu arai kamar ta _Idan Rahama ta haihu._ Da wani irin sauri Hajja ta dagota sosai ta kurawa kwayar idon Rahama ido, zuciyar Hajja na tsinkewa da wani sabon tashin hankali take faɗin. "Abubakar ciki gareta shine zaka raba auren dan zalunci?." Ya girgiza kai zuciyarsa na matsewa da wani kalar yanayi, batareda ya cewa Hajjan komai ba. Dakyar ta iya ɗaga ƙafarta Ummi na rike da ita suka bar parlorn. Duk dauriyarta kasawa tayi, fashewa tayi da wani irin kuka mai sosa zuciya, yanzu da gaske Imran ya rubuta mata takardar saki.? Addu'a kawai take Allah yasa mafarki ne bawai gaske ba. Hajja ta karɓi takardar ta kalli Ummi tana faɗin. "Karɓa ki duba saki nawa yayi mata? Allah yasa ba duka bane." Ummi ta karɓi takarda itama jikinta duk ya gama mutuwa, duk da tasan bata son auren Rahama da wannan yaron, amman mutuwar auren a yanzu kuma ya tsaya mata arai ga kuma rabo a tsakanin su. Cikin dauriya ta buɗe takardar zuciyarta na harbawa. _"Kina nan manne a cikin zuciyar Imran Matawalle a duk inda nake Albi, please ki kula da kanki da little Albi banda zama da yunwa"._ Ummi ta shiga girgiza kai tana jinjina rashin kunyar Imran ɗin. Ta kalli Hajja tana faɗin. "Saki ɗaya ne." Hajja ta girgiza kai tana faɗin. "Toh ai da sauki tunda ɗaya ne." Taja hannun Rahama zuwa ɓangarenta tana faɗin. Suje tayi mata tuwo taci yanzu ba ita ɗaya bace bazata barta da yunwa ba. Da haka suka nufi ɓangaren Hajja. Koda Matawalle ya koma gida bai samu motar Imran ɗin a harabar gidan ba, hankali tashe ya shiga neman layin sa sai dai a karo na babu adadi ake faɗin a kashe, gaba ɗaya zuciyar Matawalle wani iri ya rike jinta. Abbie ya kalli Abba yana girgiza kai yake faɗin. "Kana ganin wannan hukunci shine zai sanyaya zuciyarka? karka manta Hajja ta tabbatar akwai ciki a jikin Rahama." Abba ya girgiza kai cike da gajiya da zancen yake cewa. "Idan ta haihu sai akai masu tsiyarsu yaya ba shikenan ba dai? wannan karon ai na nuna masu nike da iko da ƴata wancen ma da Rahama tayi ƙoƙarin binjire min kyaleta kawai nayi, a wannan karon wallahi sai na tsine mata albarka tabi duniya, dan kyaleta zanyi taje duniya ta koya mata hankali." Abubakar Galadanci yayi maganar so pissed up...


(Complete Decuments)
*WAMINAL

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads