Header Ads
Showing 33001 words to 36000 words out of 163596 words

Chapter 12 - YANCNKI Book Complete by Aisha Bagudu.txt

Ads the beginning of article before Image

02 Jun 2024

1288

Ads at the middle of Article

abinda zai je yazo .
abinda malik bai sani ba gbdy mgnrsa acikin kunnesa yayita,wanda take ran fu'ad ya 'baci zuciyarsa tazo har wuya tana tafarfasa sai dai ya kudirici aniyar zai ganar daita kurenta ta hanyar tarkonsa data fad'a .


sai gurin tara na dare me'ad ta sake gwada kiransa da dayan layinta, bugu biyu ya d'auka cikin dakakkiyar muryarsa duk da bai san ko number waye ba, "hello..... ji tayi tamkar an mata bushara da gidan aljanna ne dan dadi, lokacin dataji sautin muryarsa ta ratsa cikin dodon kunneta, tayi sallama cikin sanyayyiyar muryarta amadadin "hello din daya ce mata, ," daga can bangarensa yayi shiru kawai yana sauraran yaji ko waye duk da zuciyarsa ta soma gano masa ko wace saboda sautin muryar mace dayaji, ita km hucin Numashinsa dake fita ta cikin wayar ne yayi nasarar kashe mata ilahirin jikinta har yasa ta kasa mgn, jin shirun yayi yawa ne yasa shi cewa "waye yake kok'arin shiga cikin lokacin hutuna?


murmushin fariciki tayi gefe daya kuma hawaye ya cika kwarnin idanunta sakamakon sake jin sautinsa a hassale , sai da ta sake kwantar da muryarta sosai sannan tace "me'ad ce.


"wace hk?


jin abinda yace ya sata mikewa zaune daga kwance datake "uhmm ammm dan Allah karka ce baka ganeni ba, gurin abokinka malik na amshi numberka ?


"kit taji ya katse kiran ta sake kiransa back bai d'auka ba daga karshe taji ya kashe wayar gbdy ranar dai kwanan zaune me'ad tayi ,duk inda ta juya fuskarsa take gani da komai nashi bata ta'ba tunanin zata fad'a tarkon d'a nmj irin hk ba. washegari bata tashi da wuri ba saboda rashin baccin dabata samu yi daren jiya ba. sai gurin 12 ta tashi tashiga wanka.
ta sake neman layinsa da wata number daban yana d'auka tace "barka dai me'ad ce take magana ...kit taji ya katse kiran wani irin sarere tayi agurin ahankali tayi kasa ta zauna akan gadonta sai ga hawaye yasoma ciccikowa a idanunta ta tsurawa wayar ido tana kallo gani take kmr shine acikin wayar.


wani tunani tayi ,zuciyarta ke umartata data kira number malik, take batayi sanya a gwiwa ba tashiga neman layinsa, bayan ya ta sake bashi hakuri akan abinda ya faru sannan ta d'aura da damuwarta "hakuri yabata Inshaallahu zan masa mgn. "ok nagode sosai sai kaji kirana ta katse kiran shi km ya sauke idanunsa akan fu'ad dake tsaye yana shirin zuwa gurin inna kakarsa "fu'ad yakira sunansa.. ya d'ago kansa tare sauke kyawawan idanunsa akansa batare da yace komai ba "dan Allah saurari yarinyar nan ,ka duba kaga yadda ta ajiye jin kanta, gadara takama da komai nata akanka ...


"an so what?


"na aiketa ko nasata?
"kai nifa banida lokacinta yakarasa shirinsa tare da barin d'akin ..misalin karfe 11 :00 na dare kiranta yashigo cikin wayar malik ya d'auka dan lokacin idonsa biyu yana kallon ball tare da su kabeer fu'ad ne dai ke kwance har yasoma bacci ,gaisawa sukayi sama sama "dan Allah malik ka had'ani da fu'ad "ok ya mike tsaye yayinda su kabeer suka bishi da wani irin kallo har yakarasa inda fu'ad ke kwance ya manna wayar a tsaitin kunnenshi ,sautin muryarta yasashi bude idanunsa ahankali yana duban malik dayayi saurin had'e hannuwansa guri daya yana rokonsa daya saurarera. lumshe ido kawai yayi batare da yace komai ba yaji ta sake mgn "fu'ad... dan Allah kayi hakuri da kiran danayi adaidai lokacin nan dole ce tasa hk gbdy na kasa runtsawa.. lip's dinsa ya ciza da k'arfi kmr zai huda, sannan ya kamkame jikinsa guri daya sakamakon jin muryarta, kai bazai iya cigaba da sauraronta ba, saboda zai iya shiga wani yanayi a dalilin jin muryarta da kuma ya birkita masa lisafi idanunsa ya rufe gam yana kawar da tunaninta tare da tunanin hanyar da zai bi ya musguna kmr yadda ta wulakanta malik..... "ina son mu had'u da kai gobe a coster coffee domin akwai bayanai masu matukar mahimmanci danake son mu tautauna da kai "gud dama tasamu ya furta acikin zuciyarsa, wanda a zahirance cewa yayi "okay.
"nagode sai mun hadu gobe karfe biyar na yamma ya katse kiran batare daya tanka ba.


bai je kmr yadda ta bukata sai dai shi yana tabbacin taje tagama tsamanin ganinsa ta wuce sai bayan kwana biyu malik ya matsa akan zance,sannan suka had'u a coster coffee dake awolowo waya gabadaya ta rame fuskarta tayi fayat kallo daya zaka mata kasan bata cikin natsuwarta da hankalinta tsawon minti talatin tana tsaye kmr ance ta juya taganshi sanye cikin riga green me adon pinky a gabanta, gashin kansa a gyare sai sheki yake" kallo kallo sukewa juna kafin daga bisani ya runtse idanunsa tare da zube hannuwansa duka cikin aljihun wandonsa muryata na rawa tace "ammmmm uhmmm sannu da zuwa gsky ka ..kayi kyau ..wannan ce maganarki mafi tsada ?ya fad'a tare da meida idanunsa ya runtse .


"eh but ta mika masa karamar flower ga wannan kai na kawowa ,dan girman allah ka amsa koda kuwa bazaka amshi tayin abinda nazo maka dashi ba.


a banzace ya kawar da flowers yasamu guri ya zauna yana juya mata baya zagayowa tayi ta zauna ta gabansa tana fuskantarsa "me zaka sha ice cream coffe ko shayi da madara?


"da kyar ya fizgo numfashi kmr zaiyi mgn sai kuma ya fasa .


Zuciyartace tayi tunanin watakilla zai bukaci coffee
Dan hk take tabawa masu kula da gurin umarnin akawo masa coffee ta meida idanunta a kanshi tana satar kallonsa juyar da kanshi gefe yayi kmr baisan me takeyi ba tare da datse lip's dinsa ....
Ganin ta kasa d'auke idanu akansa yasashi yi mata wani irin kallon wanda yasa kirjinta bugawa da karfi, sannan ya d'auke kansa dan shi duniya babu wanda yake jin yana matukar so kmr ita,amman ji da kanta gadara takama da kudin mahaifinta tare da wulakacin abinda tayi malik yasa yake jin kaunarta na neman riked'ewa ,a lokacin ji yake kmr ya tashi ya bar gurin sai dai kafin yayi hk sai ya wulakantata, sun jima tare da yin shiru kowanensu zuciyarsa na saka da warwara, fuad yaji shirun yayi yawa har sanda maikacin gurin ya ajiye tire me d'auke da cups guda biyu ya juya siririn tsaki yaja batare daya kalleta ba " yana da kyau kiyi abinda ya kawoki domin duk lokutana atsare suke babu wata dakika da take a wajena dazata zo face tana cikin tsari don haka kiyi gaggawa sannan ki takaita wajen maganarki dan banason mutun mai surutu ko dogon magana dan hk ina sauraranki .


Me'ad tayi mugun tsaresa da idanunta tare da gyara zamanta tana saukar da numfashi" hakika so wani shu'umin abu ne wanda yake sarrafa duk wanda ya shigesa ,fu'ad da fari dai sunana me'ad kmr yadda na sanar maka a ranar farko da muka had'u muna zaune agarin nan tare da mahaifana ,ba sai na tsaya gaya maka waye mahaifina ba, kana ganinmu kasan muna da milloyoyin Kudi da bazasu lisafu ba sannan...."dakata dan Allah malama kafin ki cigaba da wad'an banzayen kalaman naki "jikeke ke wata jaruma ce ko me dakike zubo dogon bayanai hakan kmr agidan radio ?


kanta ta girgiza tare da cewa "aa.


"ok Kamata yayi ki yi magana me ma'ana da takaitawa kmr yadda na fad'a miki tun farko,
"Ko kin d'auka da hkn da kika soma zaki birgeni ne ?
"dan kin wani zo kina zancen dukiya, kin d'auka soyayya ce a ganin farko bari kiji ba wata soyayya irin haka kin siyo furi kin kawowa saurayi abu ko tsari babu sannan saurayin dasani minti kwanaki kalilan kika yi masa, ki kashe kudinki a wasu abu na kirki wata killa zaki iya samun lada..


Me'ad batayi musu ba tabishi da shu'umin kallo wanda ke bugar masa da zuciya sannan tayi wani irin murmushi duk abinda take bukatar nmj dashi, fu'ad ya tattara, aji kyau kamewa tare da sanin Ciwon kai shima ya juya ya kalleta wani irin shaukin sonta na dibarsa.
" a zahirin gsky maganar dakayi tasa ilahirin jikina yayi sanyi ...


" go straight to your point dan Allah malam.. tsura masa ido tayi gbdy ya d'aureta duk ta inda tayi tunaninsa ya zarta hkn cikin sanyi murya tace ".tun ranar farko dana d'aura idanuna akanka naji kamin, na dad'e ina tunani kmr bamu dace ba amman zaune da nake agabanka na tabbatar da babu nmj daya dace dani kmrka ,ka cancanta kazamo uban ya'yana shiyasa zanyi kok'arin domin naga na fayyace maka na kamo da matsanancin sonka, duk da nasan kaima hk ne dan na cika budurwar da dole nmj ya kalleni ya soni ,ba dan komai kodan kyawuna kudina da kuma tarin ilimi na, da iya kalamai duk da nasan a yanzu hk ka gama amincewa, amman zanso ka furta kanasona kmr yadda na furta maka, sannan ga sakon zuciyata danazo maka dashi takarasa mgnr cikin murya me sanyi ta mika masa wata karamar akwati , amman sam yaki amsa illa idanunsa daya tsura mata"ka amsa dan Allah ni fa sonka nake tsakani da Allah kuma a shirye nake dana aureka.. zan iya sadaukar da komai nawa akanka ciki kuwa har da rayuwata.


Fu'ad yaji gbdy dry ta kufce
Masa yayita dry abinda bai taba yi ba kenan dryr data bayyana hakorarnsa "ni kike so...?
" yes ofcourse dole nasan zakayi mamakin kamata na furta ina sonka, amman kayi la'akari da so ba karya bane ,kuma kagaggen abu ne tunda kan Annabi adamu (a.s) kaga kuwa babu mamaki dan nace ina sonka.


"Tabbas kin burgeni dan naga ala'mun kema jaruma ce da har kika iya kallon wad'an idanuwana kikace wai kina sona duk da kinsa ko acikin mafarki baxakiyi tunanin ni fu'ad zan amince da uzirinki ba, yayi shiru tare mikewa a fusace yasoma kok'arin barin gurin batare da ya amshi abinda ta miko masa ba da sauri tabiyo bayansa tana share gumin daya jikata mata fuska "ka tsaya dan Allah ko coffee din fa baka sha ba , tafiya yake tana biye dashi tare da kokarin son magana " yayi saurin daga mata hannu "karki dameni da banzayen kalamanki, I thought tun farko nace banso mgn dayawa ko? "Ummmm amman Dan girman allah ka tsaya ka saurareni bakasan yadda nake jin zuciyata .
" yi min shiru tare da d'auketa da wasu maruka har guda uku ajere sannan yace "wawiya kawai kinyi zaton a banza zaki samu soyayyarta ko? Har da zuwa da shukun fure da akwatin zoben masoya, kina zaton zan amince da soyayarki ne saboda kina da kudi, iyayenki ma hk kisani wannan talakan daban yake da sauran talakoki koda nake talaka ina tabbar miki wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa dan kije ki samu daidai dake mai kudi da duk abinda kike takama dashi .


"fu'ad ka mareni a bayyanar jama'a dan nace ina sonka?


"yes na mareki ko zaki rama ne?


girgiza masa kai tayi kawsi ala'mun a'a, "ok na d'auka tak'amarki zai sai ki rama dakikiya kawai yana gama karasa wannan mgnr ya juya kai tsaye bakin titi yaje yana tsaida me adaidaita "kai zaka capitol road?


ta biyosa da sauri "kabari na rage maka hanya nima hanyar zanbi "kai me adaidai wuce abunka tare muke dashi batare da bata lokaci ba me adaidaita ya wuce ya sake saida wani nan ma ta hana tare da fito da id card din acp aliyu ta nuna masa kana kuskuren d'aukarsa sai dai ka iske kanka amagark'ama nan take ya wuce yana cewa "kan wani dalili aiko bazam jawowa kaina ba.
tafiya fu'ad yke tana binshi a baya tana rokonsa yazo ta rage masa hanya amman yaki saurarata har sukayi nisa da inda tayi parking din motarta


tsaida me okada yayi kawai kafin tasoma dogon bayaninta tuni me okada ya wuce hk jiki a sanyaye ta koma tashiga motarta cikin tsananin damuwa da bakin cikin abinda fuad yayi mata ta figa motar aguje ta nufi estate dinsu kai tsaye tana wani irin mahaukacin gudu Wanda zai kayi mamaki matuka in idan akace macece take tuka wannan motar ta miliyoyin kudi ,wani irin sautin kidan soyaya ne ke tashi acikin motar tamkar zai tarwatsa motar.


Yayinda samarin dake zaune a layi masu ji da kansu kuma yayan masu kudi irinta sai binta suke da wani irin kallo cikin bakinciki domin duk isarka duk iyawarka da iya wankanka baka isa tayi ma koda kallon arziki bane ballanatana kasanyawa ranka zata saurareka, hk ta ratsa har ta iso makeken gate din daya lullube ilahirin gidan hon daya ,tayi duka mutun ukun dake kula da get din suka taso suna kokarin bud'e mata get tare da jero mata sannu da zuwa amman babu wanda ya isheta kallo balle har ta amsa gabadaya idanunta a rufe suke .


bayan tayi parking a inda aka tanada domin ajiye motocin ta fito jikinta a sabule still zuciyarta na mamaki tareda alajabin abinda fu'ad yayi mata wanda ko a mafarki bata taba expecting wani bil adama zaiyi mata ba da wannan tunani ta taka zuwa parlour mahaifiyarta, inda ta cusa kai tare da yin sallama aciki .


Momy ta d'ago tana dubanta kallo daya tayi mata tasan tana cikin damuwa amman sai ta ajiye hkn akan aikin data fara ne, yasanya yanayinta ya sauya cikin sakin fuska momy tace " duk gajiyar hk?


Naunayen ajiyar zuciya ta sauke batare datace komai ba illa kwanciya datayi akan kujera tace ".ganin nan dai momy kwata kwata bansa abinda ke damuna ba "allah ya kyauta momy tace kawai tare yin shiru kana ta sauke ajiyar zuciya momy tayi "ni kuwa me'ad ina son nayi wata tambaya . " kai momy zaki fara ko, kwana biyu kin barni nayi kiba amman yanzu zaki soma yi min zance safwan abinda kika san banason jin a halin yanzu....


Momy ta maso kusa daita tare da dafata "haba me'ad yanzu arayuwa babu wanda baya son cigaba ,idan kika aure safwan zaki samu cigaba arayuwarki da wata daraja ta Musamman..


"Kai momy meyasa zaki dinga yin irin wanna bayanan , ada kinsa duk duniya babu mutumin Dana fi muradin kasance dashi kmr sa, amman yanzu an wayi gari bana bukatar hk, momy kudi fa da kike ganinsu a yanzu nasan basa siyan kima daraja mutunci kwarjini soyayya ,dan hk momy ki daina irin wanna tunanin kiyi fatan na auri wanda zai bani farinciki ina son fuad .....
Duk da nasan takala ne tulis......kuma zan auresa duk da talau...


Subuhallahi karki sake ki karasa wannan kalmar domin fiyayen halita ma yanemi tsari da ita dole ina son kiyi aure wanda duniya take damawa dashi wanda shi da mahaifinsa, suka maza masu abin hannunsu kuma bazan so ki auri Wanda bai kai ubanki kudi ba, sai wanda yafi shi dan haka a kullun adduar da nake miki kenan, ki janye batun yaron nan tun mahaifinki bai ji ba, idan dad dinki zai amince da aurenki dashi ni meye nawa aciki ?duk yadda nake son kiji dadi a gidan safwan hk zan hakura amman da zaki yarda ki amince kwarya tabi kwarya atsakaninku dana ji dadi sannan ki shiry tarban safwan yana kan hanyar dawowa .


Me'ad ta ta'be baki aranta tana jin zata iya yaki da kowa akan fu'ad , ahankali ta mike ta nufi bangarenta inda ta iske ummi tana faman goge goge tayis din dake barandar .


Ummi tana ganinta ta mike da sauri tana cewa "aunty sannu da zuwa, tsaki me'ad taja a maimakon ta amsa mata tayi shigewarta ummi tacigaba da abinda take yi aranta tana mamaki yanda me'ad ta d'auki duniya da zafi hk, duk da tun kafin tazo duniya anyi wad'an da suka fita wulakanta mutane amman babu wanda aka taba nunawa aka ce yayi nasara, balle itama tasanya ran wata rana zatayi nasara wannan girman kan nata ta sake ajiye numfashi tacigaba da aikinta.


mmn sudais ce
[11/3, 8:26 AM] El~hajj: 💗💗💗💗💗💗
'YAN CINKI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗


~NA~


*AYSHA A BAGUDO*


~DEDICATED TO~
MRS ADAM
( YAR MUTAN KAGARA)


Page 51 to 52


.......kwance take akan makeken gadonta kiran italy tana kallon saman d'akinta ,sosai tayi zurfi cikin tunanin lamarinta da fu'ad tare da neman mafutar yadda zatayi, ahankali ta mike zaune ta koma gefen gadonta ta zauna tare da lullu'be kanta da hannuwanta duka sakamakon bugawar da zuciyarta keyi akansa ,tamabayoyi tashiga jerewa kanta d'aya byn d'aya "me yasa fu'ad yaki amincewa da tarin soyayyata garesa?"me yasa ya mareni akan nace ina sonshi? "Kodai Malik ya gaya masa abinda ya faru ne da hkn yazamo silar d'aukar fansa gareni ta hanyar disgani cikin bayanar nasi..."ga shan mari har uku ga rashin amincewa da soyayyata da bai yi ba... "yanzu ya zanyi da rayuwata ? Ta sake jehowa kanta tmby.
" ina bukatar fu'ad arayuwata kuma zanyi komai akansa domin naga na mallakesa. wani abu ne data samu yazo wa zuciyata shine sake jin fu'ad datayi ajikinta yana yawo cikin jinin jikinta, tayi saurin goge hawayen da suka cicciko a kwarnin idanunta ya kawowa kuncinta ziyara, tasa hannunta ta dango d'igan hawayen tana kallo "yau itace ke kuka akan nmj?"nmj ma d'an talakawa wanda ba kowa bane...mikewa tayi ta isa gaban dress mirror dinta ta tsaya tana karewa kanta kallo daga samanta har k'asa "meye tarasa ajikinta kyau ne ko me da har fu'ad yake mata kallon ita bakowa bace?
Ahankali take karewa cikar halitar da Allah yayi mata, tayi imani ko ita ta isa tasa fu'ad ya fuskanci lamarinta yasota fiyye da yadda take masa, sai alokacin ta lura da irin yadda gashin kanta data d'aure duk ya wargaje a saman kafad'unta adalilin tunaninsa ,hannuta ta kai kan wayarta tasoma neman layinsa, Amman yaki d'auka, kasa hakuri tayi tacigaba da kiransa har sai data yi masa kira yafi sau goma bai d'auka ba sannan ta nemi layin malik kira

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads