Showing 21001 words to 24000 words out of 163596 words
Chapter 8 - YANCNKI Book Complete by Aisha Bagudu.txt
gaba saboda ami.. ...
"dakata dakata malam, wani irin baki ne haka kake min ?
tambayarka kawai fa nayi ba dogon sharhi na nema daga gareka ba, da kake kokarin yi min mugun alkaba'i, idan budurwa kayi ko neman mata ka fad'a ,ai sai kasanar wa mutane bawai kasoma wa mutun mugun baki ba, duk ma abinda zaka yi kaje kayi yayi wannan matsalarka ce ba tawa ba, ni dai yadda gobe zata kasance nafi bukata son sani ba wani surutunka ba.
"who is going stay at home with our daughter tomorrow simple as that?
"i don't know, and if you dare ask me this stupid question again i will deal with you right now, "shasha kawai kina nan kina haukan banza ana miki zagon kasa a kan wannan banza aikin naki wanda nan gaba zai jawo miki nadama mara amfani ,amman muje zuwa ya 'karasa maganr yana maida idanunsa kan tv..
zabura tayi ta mi'ke a fusace" kaine zaka yi nadama domin kuwa ga tarin nadama nan a 'kwayar idanunka ina hangowa.
"nadamar aurenki ba ya juyo a matu'kar harzu'ke yana dubanta "nadamar aurenki kawai ke cikin 'kwayar idanuna da zuciyata ,wallahi mead i regret married you in my life ,a yanxu na tsani kaina da na zabe ki a matsayin abokiyar rayuwata .
" na d'auka aurenki farin ciki ne gareni ashe tarin damuwa da bakin cinki ne, wallahi ban san yadda zaki kasance min kenan ba da ban amincewa aurenki ba, nayi da nasani yafi sau ba adadi a kan aurenki da nayi ya 'karasa maganar yana me
jan dogon tsaki da zance zuci
" ban san me ya shiga cikin tunaninna ba a kanta?
ban san abinda ya kai ni amincewa zucuyarta a kanta ba?
"a da can baya da mahaifinta ya'ki yarda da aurensu , ya ha'kura da ita amman daga baya ta sake dawo cikin rayuwarsa wanda silar haka komai ya faru da shi ya furzar da iska me dumi ta bakinsa .
ficewa tayi daga cikin d'akin zuwa nata d'akinta, a hankali ta shiga zagaye d'akin hanunwanta sar'kafe cikin juna gaba daya ta kasa tsaye ta kasa zaune, sai zarya take tana yamutsa gashin kanta tare da ri'ke kungunta tunanin abubuwan da suka faru a baya kafin aurensu take"anya kuwa tayi masa adalci da hallaci a rayuwa.....?
"kasa sukuni tayi har zuwa sanda aka kira sallahr isha'i, gabadaya abubuwa ne suka shiga dawo mata, tun daga kan haduwar da fu'ad har zuwa rayuwar aurensu da rashin lafiyar NASREEN kawowa wannan matsalar dake faruwa dasu. tana kiyo sanda fu'ad ya fita tasan masallaci yaje dan haka jikinta a mace ta fito tashiga d'akin NASREEN taba abinci da magani sannan ta dawo daita parlour'n ta kwantar daita tare da yi mata makarin da pillow ,zata juyo kenan NASREEN ta riko hannunta "momy..
"yes dear kina son wani abu ne?
yarinyar ta girgiza kai tana dubanta sannan tace" momy meyasa bazaki zauna agida ki kula dani ba kmr yadda doctor yace?
"nafi son ki zauna atare dani..... ..
shiru tayi ta tsura mata ido kawai tana kallonta ,NASREEN ba dai fitar da zance ba, idan tayi mgn xaka d'auka shekarunta ya wuce yadda take.
"karki damu baby your dady will be with you zama agida akwai matsala, kinga babu wanda zai taimaka mana, ki duba nawa nake biya school fees dinki da sauran abubuwa idan nace zan ajiye aiki komai zai iya faruwa,kiyi hakuri dad dinki zai kula dake fiye dani kinji an...
k'arar bude kofar ta jiyo ne ya katseta ,dan tasan kowaye, yana gama sanyo kai taga malik abokinsa yashigo, mikewa tayi tana gaidashi cike da farincikinta ,shima ya amsa yana tambayarta me jiki "jiki da sauki gata nan sai rigima.
yayi murmushi yana zama kusa da NASREEN shima fu'ad guri yasa ya zauna yana shafa kanta,ita kuma me'ad tashege kitchen cikin kankani lokaci ta shake musu Center table da abun motsa baki dan tasan sai tara yake cin abinci, sannan ta nufi d'akinta gabatar da sallah ..
hira suke atsakaninsu wanda duk akan rashin lfyr NASREEN ne, sukaji sautin muryarta "dady momy said you are going to stay at home with me?
ya juyo ahankali yana duban fuskar kyakkwar diyarsa batare da yace mata komai ba, gbdy yarasa me ma zai ce wa yarinyarsa ,domin yasan idan yace mata bashi zai zauna tare daita ba , zata ji babu dad'i shi kuma bayason damuwarta, dan haka ya tsinci kanshi da ce mata "yes I m going to stay with you my baby.. fara'ar dayaga ta bayyana a saman kyakyawar fusakarta yayi matukar bashi mamaki .."thank you my dad that's why i love you more..
"i love you dady..... "i love more baby ya fad'a tare da shafa kanta .
malik yace " ni fa baki sona ko babanki kawai kike so?
tayi murmushi wanda ke fidda kamaninta da mahaifinta sannan tace "ina sonka amman sai kabani labaru mamana da babana ....ya kwashe da dry "kaji yarinya da wayo suna zaune me'ad ta sake dawo "honey dining ya kammala "okay kawai yace mata ataikace saboda bayason jan magana " uncle malik kana nan sauraren shirme NASREEN ko?
yayi murmushi "babu wani shirmen datake, hirarku muke daita, kuje kuci aninci larku biye mata dan ita taci .
kukan shagwaba NASREEN ta saki "dady kana jin momy ko?
"karki damu daita itace ke shirme bake ba.. me'ad ta juya ta sake komawa d'aki ,fu'ad ya mike shima "kaje kaci abinci malik. kai fa ?
"bana jin yunwa koma ina banji zan iya sakawa cikin komai.."dan Allah fu'ad ka cire damuwar nan hk..
"bazan iya ba, duk randa kaga na cire damuwar nan na rabu da me'ad ne yakarasa mgnr yana barin gurin jikin malik yayi sanyi sosai kmr zai zubar da hawaye haka ma NASREEN "uncle malik meyasa dady'na zai rabu da momy?
"basuna son junansu sukayi aure ba?
"dan Allah uncle malik kabani labarin.. ina son jin labarin iyayena... ..
runtse idanunsa yayi sosai ya kasa cewa komai kafin daga baya yasoma magana ahankali
mmn sudais ce
[11/3, 8:25 AM] El~hajj: 💗💗💗💗💗💗
'YAN CINKI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~NA~
*AYSHA A BAGUDO*
~DEDICATED TO~
MRS ADAM
( YAR MUTAN KAGARA)
page 36 to 40
ASALIN MAHAIFINKI
fu'ad Muhammed argungu d'an asalin karamar hukumar argungu ne dake jahar kebbi, cirani ne yashigo da kakaninsa garin lagos , wato malam musa da mai d'akinsa halima da yaronsu muhammed , inda sukayi masauki a unguwar g'begulori dake karamar hukumar agege, fu'ad bakabe ne daya fito daga cikin kabawan asalin jahar kebbi ,yayinda danginsa gbdy suka kasance talakawa ne tulis .
tunda malam musa ya dira a garin lagos bai ta'ba zama daidai da rana daya da sunan hutu ba, kullun yana fita neman abinda zai ci da iyalisa ,ba wata sana'a malam musa yake ba illa aikin dako cikin kasuwar matuwaf zuwa ketu ,Allah yasanyawa aikin dakonsa albarka domin basu ta'ba neman abinda zasu ci sun rasa ba ,kuma tun daga kan muhammed Allah bai sake basu haihuwa ba ,dan haka suka d'auki soyayyar duniya suka d'aura akan tilon d'ansu da Allah ya basu ,duk da kasancewarsu talakawa amman hkn bai sa sunyi sakaci da tarbiyar yaronsu ba ,suna iyakacin bakin kok'arinsu akan ganin sun inganta rayuwarsu data d'ansu ,domin sunyi kok'arin sanyashi makaranta gwanati dan samun cigaban rayuwarsa .
"haka rayuwarsu tacigaba cikin talauci da babu har yasamu ya kammala secondary school dinsa a ikeja high school daga nan bai cigaba da karatu ba , sai dai ya Kan fita buga bugarsa duk inda yaga aikin karfi zaiyi fassakare ne wanki da guga zaiyi . Muhammed ya taso tare da mahaifansa har zuwa girmansa , kafin Allah ya had'ashi da ramlat, wace suka kasance diyar makotasu ce ,sukayi aurensu bisa amana da soyaya.
fu'ad shi kad'ai iyayensa suka samu ya tsaya a duniya ,dan haihuwarsu biyar yaran suna mutuwa akansa suka samu ya tsaya wanda sanadiyyar haihuwarsa, mahaifiyarsa
ta rasu ,a cewar mutane bama tasan abinda ta haifa ba ta cika, sai rikonsa ya dawo gurin kakaninsa, lokacin daya kai shekara bakwai mahaifinsa ya rasu sakamakon ciwon hawan jinin daya kamu dashi a tun mutuwar matarsa ramlat, ba a d'auki wani lokaci me tsawo ba malam musa shima yace ga garinku. gidan ya saura daga halima sai fu'ad.
fu'ad yayi karatunsa na primary har zuwa jami'a ahmadu bello, bisa tallafi na gwanati da taimakon Allah dana kakarsa inda ya karanci business administration.
,fu'ad ya sha matukar wahala gurin karatunsa saboda rayuwar babu da suke ciki ,da taimakon scholarship dana abokai da tsohuwar kakarsa halimatu yasamu ya kammala karatunsa da kyar ,bayan kamala karatunsa da bautar kasa yashiga wahalar rayuwa sakamakon rashin samun aiki , kafin had'uwar sa da mom dinki ya kwashe shekaru sama da shida yana zaman banza batare da yasamu aiki ba duk da kyawun da takardunsa sukayi.
" sun had'u da me'ad ne
A wata safiyar litinin .
labari ya karad'e koina akan zance batakashin da'akayi a garin lagos duk gidan tv da radio daka kuna a lokacin fuskar ACP Aliyu rano ake nunawa da tawagarsa rike da bindigunsu suna harbi .
ni da fu'ad ne muka shiga cikin wani d'an madaidacin shago inda muka saba yada zango ,muna shiga na ja na tsaya ina murmushin jin dadi,yayinda fu'ad dake tsaye a bayana yasa hannusa ya buge min keya "banza kawai munafukin Allah ,gulma nacinka ko?
bud'ar bakina sai cewa nayi "abokaina yau fa fu'ad yayi kasuwa da ala'mun shima yau ya fad'a tarko kauna nakarasa mgnr ina kwashewa da dry har da tafa hannu.
"kajika da wani zance iska inji cewar sauran abankanmu, sudais, Abdul da kabeer .
kabeer yacigaba da magana idanunsa na kan kallon tv "yayi kasuwa fa kace kmr wani kayan marmari.
"allah kuwa yau naga qunjinsa domin ya had'u da yarinyar da bazai iya hakura daita ba.
" dan Allah malam karka damemu zauna ka kalli abinda duniya take ciki.. zaro ido nayi sa sauri lokacin da idanununa ya sauka akan TV "kai kai ai naga wannan mutumi da'ake nuno yanzu , wannan batakashin da kuke kallo agabana fa akayisa ,shi dai fu'ad bai ce komai ba yakarasa kan doguwar kujera ya zauna yana duban abinda ake nunowa a TV wanda agabansu komai ya faru.
"kana nufin ka ganshi inji cewar kabeer?
"Kwarai da gaske na ganshi da idanuna, "kai dai wallahi babban makaryaci ne ,yau kuma da karyar daka zo mana kenan?inji cewar abdul ..
"Na girgiza kai tare da kallon fu'ad ,"fu'ad dan girman allah kayi magana zasu fi yarda da maganarka saboda muna tare da kai lokacin da abu ya faru .
fu'ad na jinsa ya sake mikewa akan doguwar kujera yayi kwanciyarsa tare da lumshe idanunsa duka , ya d'aura hannunsa ya dafe goshinsa dayan hannunsa na saman ruwan cikinsa, kasancewarsa marason hayaniyya.
duk surutun danakeyi banza sukayi dani suka cigaba da sauraron labarin da'ake watsowa suna kur'ba ruwan Lietop.
" kunga wallahi da gaske nake kai dai fu'ad wallahi banza ne ,kana ji ana kokarin meidani makaryacin karfi dayaji amman kayi shiru.
"me ka keson nace fu'ad ya fadi hkn atakaice batare daya bud'e idanunsa ba.
"ka gani ba dan Allah kayiwa mutane shiru, shi kansa fu'ad din bashi da tabbas da zance dake fitowa daga cikin bakinka duba da yanayin da yayi magana to yaya kake son mu dake zaune agida mu yarda bayan karyar abincin ruhinka ne daka kashigo fa zance yarinya kake yi ,cikin minti biyu kacal kasanyo wani zance daban .
"eh naji karya abincin ruhina ne, amman wallahi wannan zance ba karya bane ,koda nasaba yi muku karya ,ku matso kuji yadda abun yakasance nakarasa maganar ina me zagayo na zauna akan table ,gabayansu suka zagayeni " muna jin ka fad'i kuma wallahi kana somawa da karya zan gane ka kuma san karshen abun..inji cewar kabeer.
"ina zaune wancan dan iskan yace na rakashi inji din ciro kudi ,muna isa aka fara ruwan sama tare da walkiyya.. nakarasa mgnr ina zabgawa kabeer duka ajikinsa "kai dan Allah malam da baki ake bada labari ba da hannu ba "yi hakuri abokina abinda idanuna suke hangomin ne abun birgewa ,tsawon lokaci muna tsaye har ruwan yasoma tsagaitawa mukayi tunanin mu fita saboda hango inuwar mutun tsaye"bude kofarmu ke da wuya sai naga wata kyakkwar yarinya kirar Japanese tsaye cikin doguwar rigar har kasa hannunta rike da lema ,kyakkwa ce yarinyar sosai ,ku tamabayi fu'ad dan lokacin na lura har yafini gigicewa akanta, amman sai naga ya waske ita kuma yarinyar idanunta na kansa ta tsura masa ido tana kallonsa, bud'e bakin yarinya keda wuya tace "sannu amman gsky kunjima da yawa sai wani zarar kudi kuke kmr wad'an da zaku cire kudin bank din duka.
nayi saurin cewa "dan Allah kiyi hakuri ai tuni muka cira , tsayawa mukayi domin fakewa ruwa ,amman bamu aron lemarki sai mun d'an tsaya daga waje ke km sai shigo idan kin cira sai mu dawo mu tsaya ana .
"a tunanina ni zatabawa lemar tunda ni nayi mata magana ta fahimta , amman sai naga ta mik'awa wancan dan isakan lema, ya nuna inda fu'ad ke kwance ,in dai takaice muku ko damuwa da kulawar data nuna masa bai yi ba ,sai ma zagayeta da yayi ya wuce yayi gaba ya tsaya tare da tura hannunwasa duka cikin aljihun wandonsa , ina lura da yadda yanayin yarinyar ya sauya, ba dan taso ba ta miko min lemar wanda kad'an yarage hannunmu bai had'e da juna ba, na matsa mata tashiga, ni kuma na fito na tsaya ina karewa halitar jikinta kallon , ina gaya muku kywaun yarinyar ya had'u sosai.cikin mintunan da basu wuce goma ba ta fito idanunta akan fu'ad ,sosai fa kura masa ido tana takowa zuwa inda yake tsaye.
cikin hk ruwan saman ya tsaya cak sai kuma harbi takoina a harabar gurin, harbi fa sosai ban san yadda akayi ba sai dai ganin nayi fu'ad ya kamo hannuta sai ga yarinyar manne da kirjinsa nan take suka tsurawa junansu ido suna kallon junansu, wanin harbin yasa tayi saurin shigewa jikinsa gabadaya domin neman mafaka.
cikin minti biyu kacal duk ilahirin gurin ya har gitse, jamar dake wucewa a gurin bubu wanda ya damu da halin da kowa yake ciki, kowa gudun ceton ransa kawai yake saboda gabadaya gurin ya hargitse da k'arar harbi, police na harbi ,y'anta'ada na meida musu .
"ai in gaya muku na rud'e tare da gigicewa amman fu'ad da yarinyar nan ko ajikinsu kallon junansu suke karasowa garesu nayi ina girgiza fu'ad domin shi nake da yancin tabawa, nayi sa'ar ya dawo cikin haiyacinsa amman ita yarinyar ruhinta yayi nisa akansa ,girgizata fu'ad yasoma yi amman ina bata ma san yanayi ba, cikin rud'u ya rike hannunta ya kwasa aguje yasoma gudu daita, ganin harbin na sake yawa, sannan yana kiran sunana ,ni kuwa daman tuni na boye bayan inji din cire kudi ina kirma..
"kusan awa daya ana batakashin tsakanin 'yanata'ada da police har zuwa sanda acp aliyu rano yayi nasarar harbe wannan mutumin a kirji sannan komai ya lafa gurin gbdy ya turnuke da hayaki daya bayan daya mutane suka soma bayyana fuskarsu cike da matsanancin firgici daga mubuyarsu, ni kuwa sai ware ido nake naga ta inda fu'ad zasu fito, ahankali sai ga fu'ad da yarinyar nan makale da juna sun fito daga mabuyarsu aiko gama bayanarsu ke da wuya sai agaban acp wanda naji yace"a'a me'ad me km kike yi anan ?
hankalinta kwance tace "uncle nazo cire kudi ne ina fatan babu abinda yasameka? ta fadi hkn ne saboda ganinsa rike da hannunsa ga jini na tsiyaya alamun an harbeshi .
" ina jin dai lafiya kalau nike me'ad, waye wannan da kuke tare dashi ?
da sauri ta juyo gefenta fu'ad tagani tsaye agefenta hannunwansu malake cikin juna ,jin Abind acp yace yasa fu'ad yin sauri zare hannunsa cikin nata yana shafa sumar kanshi .
d'an runtse idanunta tayi kana tace "amm bansashi ba ucnle ,yanzu muka had'u dashi ta juya tana kallon fu'ad kmr zata cinyeshi muryata a sanyaye "tace sunana me'ad nagode da taimakona dakayi.
"muryarsa a dake yace ni kuma fu'ad karki damu ya juya ,naga yasoma waige waige ala'mun yana nemana, ita kuma tabishi da kallo yayinda acp aliyu yakira daya daga cikin yaransa "md .
"na'am yallabai .
" taimaka ka'ajiye min wannan yar tawa a gida.
"ok yallabai kasa daga kafafunta tayi agurin, tacigaba da kallon bayan fu'ad .
ina kallonta, jiki a sanyaye tashiga bayan wata hadadiyar mota kiran toyata camry .
Ina kawowa karshen labarin nace ni dai dan Allah ku gaya masa idan bai sonta ni dai ta min, ina sonta kuma aurenta zanyi, aikuwa suka ce me zasuyi ba dariya.... "kai wallahi bazan ne a gbdy labarinka fu'ad take so bakai ba ,koda yace baya sonta kana tunanin zata soka ne?
take na marairaice murya da fuska "ni dai ku taimaka ku tambayar min shi idan bai sonta ya tsaya min na aureta, wallahi dagani yar babban gida ce kunga motar da za'a kaita gida dashi kuwa , kuma dagani akwai halaka me karfi atsakaninta da acp Aliyu rano..
"kai dan Allah malam rabudamu da wannan shirmen banza suka soma kokarin watsewa su barni ,nayi saurin kamo hannun sudais, kai ma tafiya zakayi kabarni?
"Kai rabu dani, idan kana son yarinyar da gaske kawai ka nemi gidansu Dan gsky