Header Ads
Showing 3001 words to 6000 words out of 163596 words

Chapter 2 - YANCNKI Book Complete by Aisha Bagudu.txt

Ads the beginning of article before Image

02 Jun 2024

1279

Ads at the middle of Article

kiran ya tsinke , ganin datayi har lokacin Number na tafiya yasa ta sake meida wayar kunnenta biyu biyu ta dinga taka matattakalar benen "wayyo Allah, Allah kasa ta d'auki wayar har ta karasa sauka akan step din kokarin neman layin mahaifiyar NASREEN take ...


bangaren me'ad kuwa tana nan tsaye tana cigaba da dogon bayaninta akan yadda take son company's dinsu zai samu cigaba takowani bangare "dan haka we need to........ karar sautin waya ne ya sake katseta ,kame ta kyam atsaye tana me runtse idanunta a matukar fusace tace "wayar wani tacencen d'an iskan ne ki ring kuma?
"waye wannan tantiri idiot din?
"waye wannan dolon daya bari wayarsa tayi ringing alhalin nace ko vibrating bana bukatar ji, take gabadayansu suka shiga duduba wayoyinsu, yayinda still wayar ke sake kara .
mr tahir wanda tun soma maganarta ya tsura mata idanunsa kawai yana kallon tare da cizan lip's dinsa yana ji aranshi dakace yana da iko da tuni ya tashi ya yaryarfa mata maruka tsabar haushinta dayake ji,a duniya babu macen dayake jin ya tsana kamarta ..


"wani jakin mara jin magana da disobey ne yabari tsinanniyar culcuting dinsa ke damun kwalkwaluwar mutane..takarasa mgnr a fusace ?


daya daga cikinsu ne yace "madam ,ai wayarki ce ke kara.


gabanta yabada wani irin rassssssss tayi tsurutsuru da kyakkyawan idanunta tana kallonsu daya bayan daya ,zuciyarta na wani irin hamaukacin beting , yayinda har lokacin idanun tahir ke kanta yana kallonta yana ta'be baki ,wani irin abu taji tun daga tsakiyar kanta yana yawo daita har zuwa sansar jikinta tamkar an mata wanka da ruwan sanyi, kunya ce ko kuma nadama ce ta rufeta alokaci daya ita dai batasani ba cike da matsanancin mamaki ta tsurawa mutumin dayace wayarta ke ringa idanunta d'auke da karin bayani "yes it ur phone ma tahir ya sake maimaita mata ,ta juya bayanta ahankali inda ta'ajiye wayar tana duban screen din wayar jikinta na rawa rawa ,tabbas wayar ce ke cigaba da kara "kina iya d'auka madam watakilla kiran gaugauwa ne inji cewar mataimakinta...


tsawon minti goma tana duban screen din wayar batare da tayi kokarin d'auka ba , ta juyo jikinta a sanyaye tana fuskantarsu gabanta na cigaba da bugawa, tacigaba da mgn"muna magana ne akan fluoride da mentho sai kuma abu na gaba , yadda zamu shigar dasu kasuwa da wasu bangarori acikin kasashen duniya ...
takasa cigaba da mgn"am..uhm ..am da kuma wanda daman a kasuwa ta kasa karasa maganar saboda yadda jikinta da bakinta ke rawa ...


yayinda teacher chioma tacigaba da kiran wayarta babu kaukautawa har takaroso harabar hospital din tashiga zariya " wayyo ni kam nashiga ukuna ta cire wayar a kunneta tana sake dealing "ina wannan matar ta ajiye wayar danaketa kira bata d'auka ba?
ta sake cire wayar a kunneta tana dubawa "ki d'auki wayar nan dan Allah ,still wayar ring take amman saboda tsautsauran ra!ayi irin na me'ad taki d'aukar wayar sai ma neman izini datayi agurinsu "one minti .. ta juyo inda wayar take still dai chioma ce take kiranta acikin zuciyarta take adduar Allah yasa wannan kiran ya zama kiran lfy, dan bata ta'ba kiranta irin haka ba .


tahir ne ya gyara zamansa tare shafa kasunbarsa yana kwa'be baki da fuskarsa yace "ranki ya dade ki d'auka mana killa zai zama kiran ne me mahimmanci.. tayi masa banza sai dai gabadaya ilahirin jikinta ya sake d'aukar rawa, ta d'auki wayar tana dubawa sannan ta mikawa daya daga cikinsu "can you take it to my office and just put it there for me? "idan kuma kagama karka dawo akan lokaci har mugaba gabatar da meeting kafin ka dawo, ya karbi wayar ya nufi hanyar fita ita kuma tacigaba da magana har yanzu dai muna magana ne akan flavor.. da kuma am uhmm wasu daga cikin flavor Wanda zamuyi amfani dashi acikin product ..


chioma takalli gabas da yamma tana kuka tare da girgiza kai"bata d'auka ba shikenan tawa tasameni ina cikin tashin hankali ta kwasa da gudu zata sake komawa cikin reception, direban da tun fitowar yake watsa mata harara cike da da jin haushin 'bata masa lokaci datayi ya biyo bayanta da sauri yana kiranta "ke ke ina kuma zaki?
" dawo nan ina kudina dakike kokarin wucewa?


"ga wawa kinsamu ko, sai wani zariya kike awa jigida "kaga kayi hakuri mlm yarinyar da muka kawo har yanzu batasamu lafiya ba tukun mahaifiyarta naketa kira wayarta tayi ring ring amman bata d'auka ba dan Allah ka kwantar da hankalinka kaji zan baka kudinka.


"oho sai yanxu na fuskance inda kika dosa saboda ni wawa ne , nacigaba da tsayuwa agurin nan akan matsalarki har sanda wannan yarinyar me kama da macijiya zata warke kafin na tafi gidana ko"dan Allah malama ni bani kudina na kama gabana"kasan abinda zai faru yanxu ?
" dan Allah kabari naje nasamu doctor nagaya masa zai biyaka kudinka .


ta juya zata wuce yasa hannuwansa duka ya janyota "na fahimta .."na fahimce maganarki amman miko wayarki nan "ka kwantar da hankalinka zan sa abiyaka kudinka.


direba yace "ina wallahi bazan yarda ba ni dai miko min wayarki kawai najita a hanuna idan kin koma gurin doctor idan yabaki kudin alabashi sai ki dawo ki karbi wayarki. ya kwace wayar ya koma jikin motar ya jingina jikinsa zaman jira , ita kuma ta juya da sauri tana magana "shikenan naji ai ba laifinka bane kwata kwata baka da laifi ,laifin wancan shashar uwar tatace dataki daukar wayar ..


shi kuwa direba yacigaba da tsayuwa agurin har ya daina hangota yana cike da mamaki "a'a wasu irin mugayen mutane ne wad'an nan mutane da suka haifi yarinyar kamar macijiya "ita kuma wannan stupid din tsamaninta nayita tsayuwa ne akan macijiyar nan har sai tasamu lafiya ko me ? yayiwa kansa tmbyr yana kwa'be baki.


a daidai corido chioma suka had'u da doctor wanda kad'an yarage bataci karo da dashi ba tayi saurin ja da baya tana kuka tace "doctor.


doctor yace "am ya'akayi ne yana duba agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa "kinsamu mahaifiyarta a waya kuwa?


"uhmmmmm ita naje kira a kasa amman wayarta tayi ring sau ba adadi bata d'auka ba .


"ok dad dinta fa? inj cewar likita.


"mom dinta muke da kusanci banida number dad dinta.


"okay I will call thorough to her father duk abinda ake ciki i will let you know.


"nagode doctor.


ya wuce ita kuma takarasa zuwa d'akin da'aka kwantar da NASREEN .


********


mahaifin NASREEN zaune a makeken office din me gidansa suna tautaunawa akan lamaran daya shafi yau da kullun akan aikinsu. me gidansa sir malik yace "wad'an abubuwan suna da matukar mahimaci amman abinda nake son kamin shine ka meida hankalinka sosai akan lamarin aikinka sannan ka sake meida himma ta haka ne zaka samu cigaban dakake bukata arayuwa.


"nagode sosai sir duk abinda ka fad'a na fahimata ,zanyi kamar yadda kace zan meida hankalina kuma Inshaallahu zaka sameni kamar yadda kake so ,ni dai burina ka taimakeni nasamu wannan karin girman.


sir malik yace "karka damu fu'ad ,kaima ai mutum ne me kwazo sosai kuma gashi kana da matukar mutunci da girma acikin idanuna dan hk baxa kata'ba neman alfarma agurona na hanaka ba, ka kwantar da hankalinka i wil know what i am supposed to do for you.


"akwai abubuwa na musamman danake son namaka bayan karin girma ni dai burina ka kwantar da hankalinka zuwa wani lokaci.. kirane yashigo wayarsa yayi sauri ciro wayarsa cikin aljihun wandonsa yana dubawa tare da cewa "excuse me sir zan daga kira.


"karka damu fu'ad ka amsa wayarka kawai


"hello .


daga can bangaren doctor " yace hello kana yasoma yiwa fu'ad bayani abinda ke faruwa da yarinyarsa, a matukar razane fu'ad yace "what?


"yarinta daga school meyasameta?


yayi masa tmbyr ajere cike da matsanancin tashin hankali "kaga ganin nan zuwa yanzu ya katse kiran me gidansa dake dubansa tun fara wayarsa yace"meke faruwa fu'ad ?


"kira nasamu daga hospitar wai anyi rushed din yarinyarta daga school zuwa hostopital "ok maza maza ka tashi kaje yanxu "ya mike tsaye cike da girmanawa yana me d'an rankwafawa "nagode sir.


*******


bayan sun kammala da meeting ,tahir da ma'aruf har ma da matakin me'ad suna tsaye abakin get din company kowanensu fuskarsa a dagule ala'mun 'bacin rai tahir ne yasoma magana cike da matsanancin 'bacin "wai ku meyasa wani lokacin kuke behave wani iri haka ?
" koda yaushe Ina kokarin nusar daku amman kamar masu kwalkwaluwar kifi bakwa fahimta, kwata kwata bakwa d'aukar shawarar da nake baku da mahimmanci akan yar rainin hankali matar nan ,abinda nake fad'a maku kenan kullun amman bakwaji
muna cikin meeting wayarka tayi kara ka d'auka kayi magana kuma ,taganka lokacin daka d'auki wayar , fine tarigada takamaka red-handed sai kuma tace maka kabata wayarka kuma ka mika mata saboda kai dolo ne "common woman.. common woman for that matter dayake kaima dakikin ne kmr yadda tace shine kabata wayar bayan tagama wulakantaka sai kabata wallahi idan nine bazan bata ba komai za'ayi sai dai tayi amman wallahi kaji na rantse bazan bayar ba "abin mamaki ma sai lokacin da kake mika Mata wayar kamar wani dolo "wai so.. sorry ma..." a common woman for that matter tahir yakarasa mgnr cike da matsanancin fushi yana furzar da iska ta bakinsa ..


ma'aruf yace" wani irin banzar magana kenan kake kokarin fad'a min hka ,da yake maka dadi abakinka?


"misali lokacin da madam ta
umarceni nabata wayar ban bata ba mekake tunanin zai faru dani?


"babu wani abinda zai faru da kai malam dan nasan babu abinda zata iya yi..


"tahir babu abinda zai faru kace ? inji cewar ma'aruf.


"wallahi bazata iya aikata komai ba duk cika baki ne kawai irin na mata.


"really? inji cewar ma'aruf


tahir yace "yes.


"tahir kace babu abinda zai faru ko,? "amman bari nagaya maka wata mgn dabakasani ba,shekara da shekaru ina zaune zaman banza batare da nasamu aiki yi ba ni kadai nasan halin tashin hankali dana ciki a dalilin rashin samun aikin yi dakake kokarin ganin na aikata abinda zai sa wannan bazar matar takoreni a aiki .


tahir yace " sai akayi idan takoreka ?


"baka da hankali na zauna tsawon lokacin ina zaman jobless daga baya naxo nasamu aiki sai nayi focub akan aikina it's possible "nasan ka fahimci inda na dosa "yadda kake magana kamar wani d'an me arkizi alhalin ubanka ba kowa bane a kasar nan, bai ma da aikin a hanunsa ballanatana kace "a'a oo bari kayi masa magana yasamammin aikin Akarkashinsa dakake kokarin zagina , haka kawai na kwabsawa kaina a koreni abanza bazai yiwu ba wallahi gara dana bata na huta .


mataimakin me'ad ne ya kwashe da wata mahaukaciyar dry har da buga kafasar daya a kasa .


ma'aruf ya dube tahir yace "karamim dan iska ina fatan ka gamsu da maganata?


tahir had'e rai tare da cewa " jima mana Karka nemi raina min hankali ta hanyar zagar min uba "babana yanabawa mutane maching din haya domin su dinga yi aiki suna kawo masa deliver, idan kabar aikin nan ,zan masa magana ya siya maka kaje katayin aikinka cikin kwanciyar hankali babu tsamgwama balle wulakaci...i wil ask my dad to buy you a motorcycle on an installment plan yakarasa mgnr yana hararar, ma'aruf ya
had'e rai kamar zai fashe , zuciya taxo masa iya wuya mudarsir ya sake kwashewa da wata dry yana dafa kafad'ar ma'aruf "kayi hakuri ma'aruf nasan abinda tahir ya fad'a bai kai har cikin zuciyarsa ba ,kar kabari wannan maganar ta sake dagula maka lisafi ,how could his dad give you a job?


"wani irin magana kake fada kenan mudansir? inji cewar tahir
"wallahi ni har cikin zuciyata na fad'a masa haka, "ya daina daukar wulakacin daga wannan matar ,yasa a zuciyarsa ko babu taimakonta zai yi rayuwa .


mudarsir yace "kai kai malam dakata "babanka na bada aiki me daraja meyasa kaxo kake aiki a karkashinta?


"amman ku natsu kuji abinda zance muku yanzu duk wannan rawar jikin da kuke da zafin rai nifa ban d'aukar lamarin matar da girma ba ballanatana har ya tsaya min arai daga baya yaxo yana damuna "ba dai tamaka take da matsayinta ba,wanda yasa take jujjuya mu tare da gayamana duk abinda yazo bakinta ba?
"kubarta tayi iskancinta son ranta tagama mu kuma sai musan ta inda zamu bullo mata "zamu 'bata mata rayuwa ta yadda zuwa gurin aikin ma zai gagareta "listen friend inji cewar tahir "me ya faru ne haka?
" tun sanina da kai mudarsir banta'bajin ka fad'i maganar arziki ba ko shirya planing yadda mutun zaiyi arziki a duniya ba, sai dai yadda rayuwar mutan zai tagayyara ,yadda mutun zai daidaice da lalacewa ko raba mutun da rayuwarsa da makancinsu kawai ka iya.


"yanzu dai mekake tunani zamuyi yanzu akan wannan matsalar?


mudasir yace "inada master akan makarci ba "ba dai takamarta rike biro ba? nasan abinda zanyi akan wannan matsalar ta yadda aikin ma zai bar hannunta.


"ma'aruf yace wannan tsarin yayi sosai gsky ni zanbaka had'in kai sosai duk abinda zakayi kayi ni zanbaka hadin kai ta πŸ’―ta yadda zamu kai ga ci .


"ku tsaya kubani minti goma ina da abinda zan fad'a "if it eventually happen ls, i might be asked replace her post saboda shine abinda nafi bukata.. kar daga baya, bayan komai ya kankama kuzo kuna min bakinckin kar abani ,ni dai idan za'a bani matsayinta nasa hannuna har ma da jikina gbdy gurin aiwatar da abinda za'a yi mata sai dai ni dai bazan biku inda za'a yi aikin ba duk abinda ake ciki kwa sanar min inji cewar tahir yana dryr mugunta, nan dai suka maganar akan mudasir da ma'aruf ne zasu je inda za'a raba me'ad da aikinta ....


********
kallo daya zakayi masa ka tabbatar da cewa ba cikin natsuwa da walwala da kwanciyar hankali yake ba, tunda ya yashigo asibitin bayan kiran daya samu na gaugauwa daga doctor.


idanuwansa kawai ya tsurawa tilon diyarsa yana kallonta kirjinsa na tsananta bugawa da karfi "me ke shirin samun diyarsa dhaka ,da har ta fice cikin haiyacinta bata gane kowa?


"yana son yasan kan matsalar yarinyarsa da dalilin kamuwa da wannan ciwon domin yasan ta inda zai shawo kan abun. "babban abinda ya d'aga masa hankali shine bai wuce har zuwa wannan lokacin me'ada batakaraso hospilata din ba, ya jima zaune akan dayan gadon yana fuskarta yadda diyarsa ke kwance iskar oxygen na taimakawa numfashinta, yaji an banko kofar da karfi an shigo, a sukwane ya dago tsumammun idanunsa ya watsa mata ita kuwa ko kallon inda yake zaune batayi ba, takarasa gadon da diyarta ke kwance .....


mmn sudais ceπŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—
'YAN CINKI
πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–
πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—


~NA~


*AYSHA A BAGUDO*


~DEDICATED TO~
MRS ADAM
( YAR MUTAN KAGARA)


page 11 to 15


..."wayyohlly Allah yarinyata ! wayyo tillon diyata farincikina " me yasa me ki kuma?


"NASREEN dina ki bud'e idanukin ga momy'nki tazo, dan Allah karki min haka "what's it's?
" please NASREEN talk to mummy .


"mummy is here now, please open ur eyes and look at me .. gabadaya ta rud'e had'e da gigicewa ,cikin haka wata nurse tashigo d'akin sanye da kayan aikinsu na likitoci takaraso bakin gadon ta tsaya tana duba yanayin lafiyar yarinyar.


"madam please don't disturb her she need rest .
tsam me'ad ta mike tsaye ,jiki a sanyaye tana duban inda fu'ad ke zaune yana dubanta , tasoma takowa ahankali ta iso har in dayake, "honey what did doctor say?


shi dai fu'ad zaune kawai yake a gurin tare da tsura mata tsumammun idanunsa yana kallonta cike da matsanancin takaicinta acikin zuciyarsa, har ta iso gareshi ta samu guri kusa dashi ta zauna tamkar kazar da kwai ya fashewa a ciki tana sake tambayarsa abinda likita yace.


ya kalleta a kaskance a wulakance sannan yace "what did doctor say fa kike tambayata ?


ta kad'a masa kai tana tsareshi da kyawawan idanunta batare da tace masa komai ba.


a matukar harzuke yace "ke ..ina kike tun safe da'ake ta faman kiranki a waya baki d'auka ba?


tayi sororo tana dubansa kirjinta na wani irin mahaukacin bugu..


"ko zaki ce ba'a kira wayarki bane da kike kallona kmr wace akayiwa karya ?


"wai ke wace irin uwar banza ce ke , da bakinsa ciwon kanki dana yarinyarki ba?


"nace wace irin uwar banza ce ke..?


ta ware idanunta a waje saboda jin furucinsa gareta, dan bata taba jin yayi mata irin haka ba a tun iya zamasu tare . duk da furucinsa yayi mugun ta'ba zuciyarta amman haka ta danne ta rarrashi zuciyata domin batason su nuna hali agaban nurse gashi yarinyarsu na bukatar natsuwa , ahankali muryarta gurin cewa.


"please honey don't say that to me ,you should know there must be a reason for me not to have picked my calls ,i was in a meeting ..


"meeting .....ya fad'i hkn a fusace kana yashiga girgiza kansa cike da matsanancin takaicinta, sannan yacigaba "so the meeting was important that you couldn't see the call from ur daughter's school and call them back.


"banzar kwalkwaluwarki bata gaya miki abinda ya dace kiyi ba ,bayan kin ga kira daga teacher din yarinyarki, "meyasa bakiyi tunanin ki kira wayar daga baya ba kiji meye matsalar , alhalin kinsa yarinyarmu na tare da lalura wanda at anytime za'a iya kiranmu a waya ?


zaune tayi aguri daya tamkar wace aka dasa tsabar tashin hankali datake ciki.


"wallahi kwata kwata me'ad baki da hankali ballantana abinda ake

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads