Showing 54001 words to 57000 words out of 163596 words
Chapter 19 - YANCNKI Book Complete by Aisha Bagudu.txt
wani kwaso shirmen jikinki kinzo kina kara gaya min maganganu banza, sai danazo na fuskanci mahaifinki nagane irin kuskuren danayi ,ba dai aiki ba,to bazan nemanba ,km Zan aureki da rashin aikin nawa domin na tabbatarwa mahaifinki ko babu aiki zan iya kula dake yadda yakamata .
wai mgnr tawa ahlin gidanku suka meida abar dry, wanda wannnan abun daaka min ina da tabbacin safwan yana da hannu aciki kuma shine ya ziga babanki akan hk.
"Fu'ad ka daina magana hk mana, domin magana cikin fushi bashi da fa'ida, sannan ni ina da tabbacin babu ruwan safwan cikin wannan matsalar, "ai magana ce ta gsky idan tazo a fadeta baka da aikin yi, ko kana da? Ta jiho masa tambayar tana kallon cikin kwayar idanunsa wani irin kallo yayi mata ..
"Kuji wawiya da wata wawiyar magana ya furta hkn adaidai lokacin da ruwan sama ya sauko kmr da bakin kwarya,yacigaba "ai ban tabasanin cewar ke din shasha bace sai yau, tun farko da kika nacewa sona aikinsa bana aiki ko baki sani ba ? Shima yayi mata tmbyr yana tsare gira da kamewa "oho zuwa yanzu soyayya da mutuntakan dake tsakaninki da safwan zai iya sa ki mance hk ba..?
"Bari kiji nagaya miki abinda bakisani ba nasan komai tsakaninki da safwan, tundaga farko har karshe ko last week da kuka fita yawon celebrating din birthday dinki ina sane...nasan kunyi soyayya dashi ...,a yanzu kuma yaudararki yake,da furuncin ya janye batun aurenki, kina sona zaki aureni amatsayin danake. .ki tabbatar da kin rabu da safwan rabuwa ta har abada, idan ba hk ba kisawa zuciyarki fu'ad ba rabonki bane na wata ne ,yana gama fadar hk ya juya yasoma daga kafafunsa.
jikinta na rawa tabiyo bayansa tana kiran sunansa fuad ka tsaya dan Allah ...
Bai tsaya ba har sanda ta isa garesa ta riko hannunsa ya juyo a fusace yana dubanta "idan na tsaya na miki meye?"narigada nagama magana period sannan ki tsaya daga nan domin idan kikayi gangancin biyoni,har kikayi silar shigar innata damuwa zan miki abinda bakiyi expecting dinsa daga gareni ba.
juyowar nan da zaiyi yasanya hannuwansa ya goge fuskarsa sai yaga innarsa tsaye a bakin kofa tana kallonsu ,wacce tun da zu take tsaye agurin juyawa tayi cikin gidan, nan shima yashiga ya samu guri ya zauna agefen gadonta batare daya cire kayan jikinsa ba,inna dake sharar hawaye takaraso garesa ta dafa kafadarsa ahankali sannan tasanya dayan hanunta bisa kansa, inda gbdy ta fashe da wani irin kuka mai cin rai tare da rungume kansa a kirjinta shima kukan yake son yi amman ya dake.
***********
Yadda fu'ad ya kwana bai runtsa ba ,haka mead ta kwana juyi akan gadon ta,duk inda ya juya maganganun mahaifinta ke masa kuwa ya yarda ya amince ya saduda ya amince mead ta haramta garesa, soyayyarsu tazama mafarki mai dadi irin wanda dan adam kanyi, ya farka yana mai cizan yatsar kasancewarsa, tunda har mahaifinta yayi wannan hukuncin, dreams are conceived but not all dream 'a are born alive some are aborted, others are stillborn ya juya ya kalli su jabeer baccinsu kawai suke cikin sukuni alamun basa cikin matsalar rayuwa sannan basu san menen kalmar da ake cewa so ba .
aganinsa babu masu saa aduniya kmr su ,tunda basu zuki gardi da dadin tattare da dacin dake cikin so baz gashi dai sun fisa rawar kai akomai amman basuyi gangancin sanya kansu cikin soyayya ba balle har tazo ta damesu tazame musu kmr cutar cancer, wanda abu ne dake yawo yayi can yayi nan tunda yana faruwa da zuciya ne kawai, amman daga baya sai ta kurda cikin kasusuwan mutun ta gyaraye koina bargo jijiya da jinin jiki har da gabadaya gangar jikin Dan Adam. wayarsa dake wuriri akarkashin pillow'NSA yasoma ruri ,tunin ya gane msi kiransa mead ce adaidai wannan lokacin yaki dauka hk tayi ta kararta tagaji "mai zata ce masa da zai fahimta?
Bazai sake yarda ta luguiguita masa zuciya ba, ya yarda ya amince tunda har mahaifinta yayi furuncinsa garesa bazai bashi auren yarinyarsa ba .
Ta kirasa yafi sau goma amman bai dauka, daga karshe ma yaka kashe wayar gabadaya ya kife kansa jikin pillow tare da lumshe ido cikin halin tausayin kansa, Dan ganinsa ita mead ba abar tausayi bace ....
Mmn sudais ce
[11/3, 8:27 AM] El~hajj: 💗💗💗💗💗💗
'YAN CINKI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~NA~
*AYSHA A BAGUDO*
~DEDICATED TO~
MRS ADAM
( YAR MUTAN KAGARA)
page 61 to 62
washegari har karfe 11:00 na safiyar ranar me'ad bata fito daga cikin d'akin ba, tana kwance akan gadonta tana kuka, tare da tunanin maganganun fu'ad akan safwan,ahankali komai ke dawo mata daki daki, "ita ba rabu da safwan din ne bazata iya ba ,illa tashin hankali dashi fu'ad yake ciki, tana son shi bilhaki da gasky ta yarda ta amincewa zuciyarta ko bai da sisin kobo zata auresa tayi rayuwa dashi,cikin wannan tunanin zazzafan zazzabin da yayi kokarin kamata tun yammancin jiya, ya saukar mata take jikinta ya d'auki kyarma tmkr mazari, shiru shiru momy bata ga saukowarta ba har sun gama break fast,yasa momy cewa suhailat taje ta dubota anya kuwa lafiya take,da har yanxu bata sauko ba?" Duk da week end ce amman bata ta'ba kaiwa wannan lokacin bata sauko ba.
suhailat dake zaune akan kujera tana assign din da'aka basu a makaranta, ta ajiyei litafin hannuta ta nufi d'akin me'ad, da sallamarta tashiga amman shr ,Dan haka tayi kokari k'arasa shiga d'akin ,nan ta isketa can karshen gadonta kudundune cikin bargo tana rawar d'ari da sauri ta karasa" aunty me'ad lfy yau baki fito ba?
cikin dasashiyar murya tace "hailat sake rufa min bargon can sanyi make ji sosai ,a raunane suhailat tace "sanyi aunty? a wannan uban zafin da'ake ko dai baki da lfy ne? dan kusan ruwa jiya da'akayi tadda zafi yayi .
ta kasa ce mata komai illa lumshe idanunta datayi takaraso ta d'aura hannuta akan goshinta zafin daya kaiwa tafin hannuta ziyara ne,yasa tayi saurin cire hannuta wuyanta ta ta'ba nan ma zafi rau kmr an jonata da wutar lantarki.
da sauri ta fita daga d'akin ta gayawa momy ai wata uwar zabura momy tayi tana furta kalmar "inna lillahi wa inna ilaihi rajiun atare suka dawo d'akin momy ta hau saman gadon duk ta rud'e tare da rungumota jikinta"bakida lfy me'ad shine ko waya bazakiyi ba ki sanar?
" sai ki zauna ke kad'ai cikin d'aki idan wani abu ya faru dake fa, me kike tunanin zai samemu..?
me'ad tayi shiru taki mgn sai numfashi take fitarwa ahankali ahankali jikinta na sake d'aukar kyarma "ke suhailat d'auko mukulli mota muje hospital sai sannan me'ad tayi mgn da kyar "no momy kibani paracetamol kawai ya isa ba sai muje koina ba "its just tension...... momy da suhailat suka kmr zasuyi mata kukan halin tashin hankali datake ciki, sannan suhailat taje ta had'a mata ruwan wanka da taimakon momy ta iya yin wanka aka kawo mata breakfast,hadaddiyar jolof din Shinkafa dataji nama kasa zuku zuku byn ta fito daga wanka momy da suhailat suka sata atsakiya da roko da rarrashi sannan suka samu taci hawaye nabin kuncinta sannan suka tsiyaya mata ruwan roba mara sanyi acikin cup ta amsa tasha magani ta koma ta jingina jikinta da abun gadon, ta runtse idanunwata gam zuciyarta na buguwa daf..daf..suhailat ta fita daga d'akin amman sam momy ta kasa fita tabar diyarta cikin halin damuwa dan tasan ciwon diya mace na diya mace ne.
"me'ad momy taki kira sunanta a sanyaye "kibi ahankali karki bari wata cutar ta kamaki , lamarina zaki duba ba dady dinki ba, ku biyu gareni acikinku bana son na rasa ko daya ahannuna....
"akan aurenki da fu'ad ni dai na yarda na amince kuma ina farinciki dashi ,sai dai amatsayina na mahaifiyarki ina baki shawara kiyi addua akan lamarin, matukar rabonki ne fuad zaki auresa.
"sai dai ki duba wani abu guda acikin matsalar nan mahaifinki yafi karfin komai agurinki mead yana sonki yana son farincikinki,sai dai yafi son da bukatar auranki da safwan," me zai hana ki hakura da fu'ad ki auri zabinsa domin zaman lafiyarmu gabadaya...
ta bud'e idanunta da kyar ta saukesu kan mahaifiyarta dake zaune kusa daita, muryarta na rawa ta fara magana "momy me yasa daddy yake kin talakawa ne?
" me yasa dady baya son ala'kar shi da talakawa?" Ni ina son fu'ad ko a yaya yake' a barni na aure shi, ina son shi ko da ba shi da ko sisi, ina son shi ko da baxai ci da ni da komai ba, Ina sonshi ina bu'katar rayuwa da shi.... dukkan farin cikina da kwanciyar hankalina yana tattare da shi, baxan iya rayuwa ba tare da fu'ad ba rabani dashi tmkr rabani da rayuwata ne ,amman idan kunfi son rayuwa babu ni kuna iya aurawa safwan ni takarasa mgnr hawaye na gangarowa bisa kuncinta.
Sauke ajiyar zuciya momy tayi "me'ad babanki, ba shi da wani dalilinsa na 'kin talakawa kawai hali ne wanda Allah yake halittar kowane bawa da shi, shi dai kawai ya fi son ki auri Safwan, Ni kaina idan kika auri safwan xan ji dadi, amma kuma idan baki aure shi ba xan biyewa don zuciyar ki , zan biyewa zabinki zan amince ki auri fu'ad domin kwanciyar hankalin ki a Matsayinki na diyata". Tunda mead ta maida idanunta ta tufe bata sake yunkurin budewa ba illa zamewa datayi ta kwanta akan katifarta, tsawon minti talatin momy na tare daita tana kallon yadda soyayya ke tangaliliya diyarta ..
***********
A ɓangaren fu'ad kuwa gari na karasa wayewa bayan ya kammala karatunsa na Alkur'ani da addu'oinsa, magazine din da aka buga satin da ya gabata ya d'auko ya fara duddubawa, yana cikin karatun ne yaci karo da wasu Companies da suke neman ma'aikata, da hanzari ya tashi ya shirya cikin suit kayan sun yi matukar karbar jikinsa file din takardunsa ya ɗauka ya fita, kai tsaye wajen kakarsa ya nufa yana zuwa ya shaida mata inda yake son tafiya, albarka tasa masa tare da yi masa addu'ar samun nasara.
A ranar wuni fuad yayi yana karad'e Company by Company yana neman aiki, wasu su yi masa alkawarin xasu kira shi wasu kuma su ce ba su da gurbin da za su saka shi, wani lokacin ma yana zaune zai ji an kira wayarsa tare da sanar da shi cewa an É—auke shi aiki, amma daga baya a ce an fasa É—aukar sa saboda wani dalili da shi kansa bai sani.
Haka ya kasance har tsawon sati biyu yana yawon Company duk don ya samu abinda zai dogara da kansa . Yayin da ita kuma me'ad take ta kiransa ,amman gaba ɗaya ya daina ɗaukan wayarta, tun yana rejecting daga ƙarshe ma yayi blocking dinta, duk inda tasan xata je nemansa taje amma bata samu ganin sa ba, gaba ɗaya ya toshe duk wata hanyar haɗuwa da ita domin a wannan lokacin yasanyawa zuciyarsa rabuwa daita , ita din ba daidai take rayuwarsa ba,sai dai yana da yakinin diya ko ta gidan uban waye zai iya mallakarta adalilin nagartarsa ,shi bama mashayi ba manemin mata ba dan me zai zauna a wulakantashi a karo banza.
Yadda gbdy mead ta haukace gurin nemansa amman bata ga ko mai kamaninsa yasa cikin wannan lokacin har ta fara sakawa zucuyarta hakuri dashi tunda tasan shima yana sonta amman ya iya daurewa zuciyarsa, ba don ya daina sonta da kaunarta ba.
***********
A tsakanin wannan lokacin wata shakuwa ta musamman ta sake shiga tsakaninta da safwan bisa karfafa mata gwiwar dayake, "tabbas bata da mijin daya wuce fu'ad kuma duk runtsi duk wuya sai sun auri junansu, yayinda azuciyarsa yake back to sender da adduar, shi ...shine zai mallaketa bawani banzar fu'ad ba.
Wata rana sun fita unguwa tare da Safwan suna tsaye a wani traffic Safwan ya hango fuad tsaye rike da takardunsa jikin wani company dagani a wahale yake dan har ya zazzago da tie dinsa , kallonta Safwan yayi cike da matsanancin tsanarsa aransa yace "matukar ina raye ba kai ba samun aiki arayuwarka, a zahirance kuwa cewa yayi
"me'ad kinga wani kamar fu'ad dinki" kallo É—aya tayi masa ta É—'auke kanta dan alokacin haushin watsar da lamarinta da yayi take ji.
"Mu wuce kawai Safwan kada mu isa garesa"
"Haba ke kuwa ai ayi hk?"ki bari mu je mu gaisa ,ai kema kin kwana biyo baki gansa ba ,plz kizo muje mu gaisa yaushe rabon da ki gansa"
"A'a Ni baxan je ba sai dai idan kai ne xaka je bazan hanaka ba"
"To shikenan bari ni naje mu gaisa da shi gsky"
Bud'e motar yayi ya fita yana fita yaje ya iske shi inda yake tsaye wanda zuwa lokacin ya gansu ya dauke kansa tmkr bai gansu ba ,safwan da fara'arsa ya karasa inda yake.
"Ah!! Malam fu'ad ya gida ya kake ya kwana 2?
" duk maganar nan da Safwan yake yi fu'ad bai tanka masa ba balle ya dago ya. Dubesa, sam safwan bai yi zuciya sai ma kokarin kufular dashi dayayi niyya, yayi kusa dashi sosai ya sake bude bakinsa .
"Malam fu'ad da alama ma kamar neman aiki kake yi na ganka da takardun neman aiki a hannunka ?
" banxa still fu'ad ya sake yi da shi bai ,Dan bashi da amsar bashi..
Matsowa Safwan ya sake yi kusa da shi yace masa.
"Fu'ad kaga a cikin siyasa da wayo na raba ka da me'ad ko?
" kuma Sannan ni ne mutumin da mahaifinta yace akwai alƙawarin aure a tsakanin mu ba tun yau ba, Ni ne mutumin da zan aureta tun farko kafin kaxo ka ruguza min shirina akanta, don haka nan da dan wani lokaci kankani zan aure me'ad, in bar ƙasar nan da ita zuwa hollond mucigaba da rayuwarmu, Sannan kuma idan mun haihu tare da ita, daga baya ƴa'ƴanmu zasu riƙa kiranka da kawu"
A fusace fu'ad ya cakumo wuyan Safwan " Ni kake gayawa wannan banzar maganar ina ruwana da aurenku ballanatana wani d'an ka aureta kun bar kasar nan, idan kaga dama ma dan Allah ka bar duniyar da ita sai me?
"Ai ba tun yau nasan makirci kake shiryawa rayuwarta ba saboda nasan komai kana sonta ,ita km bata sonka, kasani wallahi kayi kad'an hk nan nabar maka ita sai bisa dalilolin da kai karamin tantirin kafi sani..
Me'ad dake cikin mota ta hango su kamar zasu yi kokawa don haka da sauri ta fito daga motar tana faÉ—in "Safwan ba sai da nace maka kada ka fito kazo wajen shi ba,Amman kazo, daga abin arziki sai ya zama na faÉ—a, dan Allah ka rabu da shi kaxo mu tafi"
Wucewa tayi gaba Safwan ya biyo bayanta ,taku biyu yayi ya juyo yanawa fu'ad gwalo sannan yacigaba da take masa baya , bin su yayi da kallo mai cike da taikaici, wani kululun bakin ciki ne ya tokare zuciyar fu'ad ji yayi kamar ya hadiyi zuciya ya mutu, saboda baƙin ciki da takaicin abinda Safwan ya faɗa masa, tambayarka xuciyar sa ya shiga yi, "dama Safwan yazo wajena ne don ya ci min mutunci Saboda ni talaka ne ba ni da abin duniya, hawaye ne suka cika idanunsa, ji yayi jiri na ƙoƙarin dibansa don haka da sauri ya nemi guri ya zauna, yana kallon su suka ja motarsu su suka tafi.
****************
Sajeeda ce da Safwan ke zaune suna tattaunawa, inda Safwan ya kawo mata maganar fu'ad
"Sajeeda na san shirin ki nasan dukkan abinda ke cikin zuciyarki a kan fu'ad kina son fu'ad kamar yadda nake son me'ad, to me zai hana mu bi ta wata hanya ta yadda burin kowane ɗayanmu xai cika cikin sauki, kinga idan kika yi kokari kika xuga zuciyar me'ad a kan ta rabu da fu'ad ba mijin aure bane, bai dace da mace irinta ba,xata iya rabuwa da shi ni na aureta, ke kuma ki auri zaɓin ranki fu'ad.
Batare da bata lokaci ba taji ta yarda ta amince zatayi komai dan rabasu, haka suka rabu da shi tare da alkawarin zata cika masa aikin da ya saka ta.sai dai duk yadda tayi tunanin lamarin ya wuce tsamaninta Dan sai da sukayi uwaka ubanka da sajida da me'ad.
*********
Kabir ne ya kira fu'ad a waya ya faɗa masa cewa ya samo masa wani babban aiki, amma aikin za a fita zuwa ƙasar England ne domin yiwa wani babban company aikin dako , ba ƙaramin farin ciki fu'ad da kakar shi suka yi ba wahalarsu ta kusan yankewa zuwa jin dadi, cikin kankanin lokaci fu'ad ya shirya ........
don zuwa offfice din campay dazasu masa aikin tafiyarsa, atake akayi masa passport, byn kwana uku vizarsa ta fito.
Yana tsaye a airport duk ransa babu dadi yana jin kmr ya fasa tafiyar, saboda yadda yake jin zuciyarsa na rawa rawa....gefe daya kuma soyayyar me'ad ne ya dawo masa sabo fil , kabir daya fahimci halin damuwar dayake ciki ya matso ya dafashi yace "aboki ka kirata mana akalla ko sallama kwayiwa junanku, "a'a kabir barta kawai banason wani karin damuwa, da kyar dai kabir yasamu ya shawo kansa ya amince , har yasoma kokarin kiran layinta,kira biyar yayi wayar nata kara amman sam ba'a d'auka ba adalilin tana bayi tana wanka, cikin hk safwan yashigo d'akin, inda ya iske wayar na ruri, ya duba yaga kowaye, sunan honey dayaga tana yawo ajikin screen din wayar ya kusan bugar masa da zuciya, take ransa yayi maseefar baci har numfashinsa yasoma kokarin daukewa, kmr bazai d'auka ba ,sai kuma yayi tunanin ,wannan ma wata damace garesa Dan hk ya dauka tare da cewa hello mead tana wanka wani abune.......?
Jin sautin muryar safwan da fu'ad yayi yasashi katse kiran da sauri yana furzar da iska mai zafi ta bakinsa sannan ya juya ahankali tare da dafe goshinsa dayaji yayi mugun sara masa .
Kabir ya juyo ya fuskancesa "ya'akayi