Header Ads
Showing 108001 words to 111000 words out of 163596 words

Chapter 37 - YANCNKI Book Complete by Aisha Bagudu.txt

Ads the beginning of article before Image

02 Jun 2024

1308

Ads at the middle of Article

sannan gangar jikinsa ta bayyana inda gbdy security's suka caaaa akansa kowanensu na rusunawa cike da girmamawa shima Khalid yakaraso yayi kmr yadda sukayi mahaifin sajida yabishi da kallo yana tunanin inda yasansa Amman duk tunaninsa yayi bai gano inda yasan yaron ba ,juyowa yayi ga security ganin K'arin bayani yake nema daga garesu yasa suka shiga rige Rigen gaya masa abinda ke tafe da Khalid ya jinjina kai yana sake karewa yaron kallon tsab yaro ne karami sosai Dan nesa ba kusa ba yasan sajida ta girme masa zatayi kani kusan na uku dashi hannun mahaifin sajida ya d'aga musu alamun suka gamansu sannan yace wa Khalid "biyo yaro ,yana gaba khalid na biye dashi abaya har cikin wani rantsentsan parlour'n dayaji kayan more rayuwar duniya yace ya zauna yana zuwa ,shi kuma yak'arasa ciki ,Khalid ya zauna tare da yin balance yana murza tafukan hannuwansa tsanyi ac Dana murna na ratsashi tmkr Wanda akayiwa albishiri da an bashi auren sajida.


Mahaifin sajida nashigowa parlour'n sautin muryarta yasoma jiyowa cikin fad'a "Dan iskan yaro kawai ko me zanyi da kai ?
"me zan ci da kai yaro karami da kai sai tsaurin ido ,okay Dan kaga ranar farko kayi nasarar shigowa, shine yau ma ka kwaso jiki kazo Allah yasa suyi maka dukan mutuwa su karairaka useless kawai, tana ganin mahaifinta tayi saurin waske tana susa tsakiyar gashin kanta sannan tayi masa sannu da zuwa ,ya amsa ransa a sake sannan yashiga d'akinsa bayansa tabi da kallo tana adduar Allah yasa bai ga Khalid ba .
shigarsa d'akin bai fi minti goma ba ya sake fitowa ya nufi inda Khalid yake bayan ya bada umarnin akawo masa abun motsa baki . Yashigo bakinsa d'auke da sallama, Khalid na ganinsa ya sake rusunawa had'e da amsa sallama ,mahafin sajida yasamu guri opposite din Khalid ya zauna
yana fuskantarshi, tsawon minti goma yana zaune yana kallon Khalid tare da nazarinsa ,me aiki tashigo rike da tire ta janyo karamin stood ta ajiye tiren akai ta juya .
"meye ne sunanka mahaifin sajida ya fad'a yana gyara zamansa?
Cikin rawa murya yace "Kha..Khalid ismail money mis road ne sir.." dady ya maimaita sunan saboda yasan Ismail mony mis road, ya jinjina kai kana yace
"malam Khalid ga abun motsa bakin nan kasoma dashi tukun muyi mgn "
"a koshe nake dady "kai kuwa kasha ko kad'an ne "ok na gode sosai ,yasa hannu ya tsiyaye tattaciyar ruwan inibi acikin cup ya cur'ba kad'an ya ajiye cup, yana sake gyara zamansa shima ya fuskance mahaifin sajida kmr yadda yayi masa kuri da ido . "Kace Khalid Ismail mony mis road kai din D'an cikinsa ne ?
"Eh ....."ikon Allah"
" me ke tsakaninka da sajida diyata?
Batare da 'bata lokaci ba Khalid ya zayyane masa komai ."ka tabbatar kana sonta ?
Khalid yace "sosai ma dady sai dai ita din ce kmr take raina ni a cewarta na...."ka manta da duk wani raini kai dai ba dai kana sonta ba kuma kana da inda zaka ajiyeta ba ?
Khalid ya girgiza kansa alamun Eh " to ka turo min mahaifinka muyi magana ta kunne da kunne dashi yana gama fad'ar ya Mike "kayi k'ok'arin ka ci duk abinda aka kawo maka sannan ya juya ya fita daga parlour'n, ai ko babu kunya khalid ya zauna ya take cikinsa ,Dan yana son cin irin abubuwan Amman mugun son kudinsa daya gada Gurin mahaifinsa baya bari fitowa yayi yana d'ad'd'agawa security's kafad'u ,a zuwan shima yanzu wani ne acikin gidan.


*************
Sajida fu'ad zaune agaban me gidansa, yayinda fu'ad sai faman cika yake yana batsewa tare da zabga mata harara ,saboda ya tsani yadda take zuwa kawo complain dinsa ga uban gidansa, daya zame masa tmkr uba garesa.
Cikin murya kuka tasoma mgn "sir Malik ka taimakeni kar zance aurenmu ya rushe gbdy narasa gane Kan fu'ad aka. " dakata dakata !! Munafuka ta yaya zaki gane kaina, muguwa azaluma maci amanar kauna?
sir kana kallon yarinyar nan katuwar muguwar makira ce ta bugawa ajarida, kwata kwata batasona da matata, sannan son datake ikirari tana min karya ne.......
"Saboda zaka fadi hk ?
Inji cewar sir Malik "na karyata hkn ne saboda ina dalilina ,Dan da ace son gsky sajida take min da ta tausayawa rayuwata ta gaya min inda matata da 'yata suke....
Kallonta sir malik yayi "ke kinsa inda matarsa take ne ?
Tayi saurin girgiza masa kai alamun eh "
"Kaji ko Amman tana kallona agari ina yawo bulayin nemanta ta kasa gaya min to ni kuwa me zanyi dake sajida?
"Bari nagaya miki wallahi wallahi bana sonki kuma ban taba jin digon sonki a zuciyata ba ,na dai amincewa aurenki ne saboda yanayin da kike k'ok'arin ganin kin sanyani ciki alhalin ni ba ma'abocin hkn bane . Sannan baki son matata sajida.."karka ce wallahi ina .."short ya buga Mata tsawa "ta ina kike sonta?
" tambayarki ki gaya min baya ga zuga min ita da kike okay kin d'auka ban sani ba ?
"Kisani bazan ta'ba aurenki ba ,ke ko mutuwa me'ad tayi bazan aureki ba ..."karka fad'i sir malik yayi saurin katse shi " wallahi wallahi aaaaaaaa karka rantse "wallahi bazan aureta ba wannan shine maganata takarshe daita yana gama fadar hk ya Mike ya bar parlour'n, durkushewa tayi agurin tana kuka "Dan Allah kataimakeni kace masa ya dawo duk abinda yake tunani ba hk bane ,wayyohlly Allah kuka take kmr wata karamar yarinyar "ki kwantar da hankalinki zan rarrasheshi zan sa yayi kaffaran rantsuwar da yayi InshaAllahu ke dai ki cigaba da addu'a idan da rabo sai ayi da wannan maganar ya kwantar mata da hankali ta wuce.


********


Bayan mead ta dawo gida da sati daya , fu'ad yasamu labari tana gidansu ,Dan haka yayiwa gidan diran makiya , inda ya iske dady a parlour'n farko na gidan ya hakince acikin kujera , yashigo bakinsa d'auke da sallama , zuciyarsa babu wani fargaba ko tsoro ya gaishe da dady cike da girmamawa ,Wanda iya sallamar kawai dady ya amsa shima aciki , ya samu guri ya zauna batare da anyi masa izini ba .


parlour'n ya d'auki shiru kusan minti talatin dady bai tambayi abinda ya kawosa ba, hk zalika shima fuad bai yi mgn ba har sanda nasreen wacce tagaji da jiran , tasanyo kai cikin parlour'n Dan shigowar mahaifinta ya faru ne akan idanunta da gudu tashige jikinsa tana murnar ganinsa "I miss you my special dady.....shima rungumeta yayi tsam ajikinsa yana sauke naunayen ajiyar zuciya kana yace "I really miss you too my special bby how are you doing ?
"Am fine dady wani irin sanyin dadi ne yake jin yana ratsashi , yayinda zuciyar dady kad'an yarage batayi bundiga ba ,tsabar takaici da taanarsa ga fu'ad..


ahankali sautin muryar nasreen ta fito "dady kazo tafiya damu ne ?
"Yes my bby jeki momynki ta fito mu wuce gida "gidan ubanwa kenan zata da kake mgn a gadarance?
"a'a fu'ad ya fad'a cike da matsanancin mamakin dady sannan yacigaba da mgn "wace irin mgn ce hk dady kake fad'a ?
"gidan mijinta mana zata"


" 'Yarka me'ad ..?


"uhmmmmm 'yarka ce sai dai ni kuma *matata ce ta sunnah* da duk ragamar rayuwarta ke tafin hannuna... " yi min shiru , kasani me'ad 'yata ce kuma ta dawo gidan ubanta bazata sake komawa gidanka tayi rayuwar kunci ba da babu ba ,Dan hk minti biyu kacal na baka ka bar min gida.


"No no dady kar muyi hk da kai ,banason wata mgn ta sainsa tashiga tsakaninmu da kai saboda har yanzu kana nan matsayinka na uba gare...."dakata malam banason zance banza ni ba ubanka bane kasan ubanka, nima nasan iyakacin ya'yan Dana Haifa "


"Okay tunda haka kace ina buΖ™atar *matata* abani *matata* na wuce daita muje tacigaba da rayuwar kuncin da babun da kace.


Nan fa mahaifin me'ad ya fusata " baka isa ba ,wannan zance banza ne ka fad'a, ayau kuma ayanzu zaka sauwakewa 'yata igiyoyin aurenka dake kanta tayi rayuwar 'yanci "
", a matukar fusace fu'ad ya mike tsaye jikinsa na wani irin rawa yana yiwa mahaifin me'ad din wani irin kallon me cike da tsantsar tsama .sannan muryarsa a kausashe yace .


"Wai daddy me kake nufi dani ne,?
" me nayi maka ne daddy me na tare maka arayuwa, kake min irin wannan kiyayyar.?
" shin a rayuwa ba a aure ne ko ba a soyayya ne na taimaka na auri 'yarka domin mu rufawa juna asiri, after ina sonta, kuma ita ma kasan tana sona, ka bani *matata* kawai mu koma gida mu je mu ci-gaba da rayuwar aure da ita"


dady yace" baxan ta'ba barin ka tafi da 'yata koina ba, sannan ina da dalilai da yasa bana sonka , kuma har abada bazan ta'ba kaunar ka ba, saboda ni Safwan nake son tayi rayuwa dashi ba kai ba me digirin zero .......
Ka saketa tun wuri tun bamu had'u a kotu ba taje ta auri Safwan shi ne abinda nake buΖ™ata kuma wannan ne cikar burinna a rayuwa me'ad ta auri safwan.....


Furzar da wani numfashi mai zafi fu'ad yayi sannan lokaci daya ya kwashewa da uwar dry yana furta "Good naji duk abinda ka fad'a amma Ni ina son *matata* kuma baxan ta'ba sakinta ba, kuma ko kotun duniya zaka kai ni ,ka kai ni a shiryena Nike Amman bazan saketa ba , duk runtsi duk wuya duk talaucina muna tare , "dady idan duk duniyar zasu taru akanmu bayan kotun dakace , idan sama da kasa zasu had'u, idan za'a dinga hadari malaiku daga sama bazan saki *matata* me'ad ba, kuma idan har sai na saki me'ad sannan Safwan xai yi Aure,wallahi wallahi wallahi!!! sai dai Safwan ya koma ga Allah bayi aure ba, ko kuma ku yi aure a kan aure" yana gama fadar haka ya juya afusace tare da nasreen ya bar parlour'n, zuwa harabar gidan ,me'ad wace tun shigowarsa gidan ta kasa samun natsuwar zuciya sakamakon nasreen tagaya mata zuwansa " ta fito aguje tana haki ta rike hannun nasreen dake kuka saboda tashin hankalin daya faru akan idanun "sakar min hannun yarinya ..........
ya tsaya tare da juyo idanunsu ya tsarke cikin juna, atare zuciyoyinsu suka buga, ido cikin ido suke kallon juna me'ad ce tayi saurin d'auke idanunta acikin NASA "uhmmm repeat what you just said now?
"Yarki ko 'yata ?ya furta muryasa a kasalance tare da tsareta da kyawawan idanunsa.


"Tambayarki nake kinyi shiru ,okay kema kin San gaskiya ko wannan property din belongs to me, kmr yadda mahaifinki ke kokari motsa kunjinsa akanki Dan hk sakar min hannun yarinyar..durkushewa tayi agabansa ta fashe masa da kuka "kabar min yarinyata ,idan ka rabani da ita mutuwa zanyi ,Dan Allah kabar min ita ..ahankali ya saki hannun nasreen sakamakon wani tunani dayayi ,barin nasreen zai iya taimaka masa takowani fanni, wallahi this time around zai bawa mahaifinta mamaki zai zame masa kadan garen bakin tula....rungume nasreen tayi ajikinta tana kuka shi kuma ya juya ya isa yashiga motarsa ya bar gidan ..


Bangaren dady kuwa sai zariya yake a parlour'n, ya kai gauro ya kai mari "aikin banza akin wofi kawai wannan yanzu har surukin arxiki ne?
" ina fad'a yana fad'a, koda yake tsiya da talauci babu abinda basa saka mutun yayi ,sai dai ka rubuta ka'ajiye sai na raba wannan auren koda kuwa da karfin ikona ne .....


Mmn sudais ce[11/3, 8:29 AM] El~hajj: πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—
'YAN CINKI
πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–
πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—


~NA~


*AYSHA A BAGUDO*


~DEDICATED TO~


*AUNTY BASEERA WANNAN PAJIN NAKI , INA MATUKAR GODIYA BISA GA SOYAYYARKI , ALKHAIRINKI,KULAWARKI GARENI ALLAH YA BARMU TARE*🀝🏻🀝🏻🀝🏻


Page 81


.....kai tsaye fu'ad gida ya nufa zuciyarsa na wani irin tafarfasa,yana shiga parlour'n ya fad'a Kan doguwar kujera 3 siter yana fitar da numfashi me gauraye da zafin ciwon abinda surukinsa yayi masa ,ahankali tunaninsa ya cigaba da gudana lokacin daya sautin kukan matarsa yashiga dawo masa tana bashi hakuri"kabar min yarinyata, idan ka rabani daita mutuwa zanyi ..."Dan Allah kabar min ita ....
runtse idanunsa yayi sosai tare da mikewa zaune da kyar, gabadaya ilahirin jikinsa yayi mugu mugun sanyi, ga wani irin matsifaffen ciwon da kansa keyi akan furucin mahaifinta ga tashin hankali daya barota ciki , da kyar ya iya bud'e idanunsa ya Mike tsaye yashiga zariya acikin parlour'n dafe da goshinsa , yana tunanin mafuta " ya Allah ka kawo min hanya me sauki da komai zai daidata gareni ,Allah kar kasa wannan bawa naka yayi nasara akaina ......."ya dade yana zurfafa tunaninsa ,bai San lokacin daya d'auka tsaye agurin ba, kafin daga bisani, ahankali ya d'aga kyawawan idanunsa ya saukesu akan wrist watch din dake d'aure da tsintsiyar hannunsa, karfe shadaya ta wuce da wasu 'yan mintuna, tsaki yaja "hk kawai wannan tsohon na neman hadasa masa ciwon kai na babu gaira babu dalili ,a sukune yasoma tafiya zuwa d'akinsa yana 'bal'bale botiran gaban rigarsa yana shiga bathroom ya k'asara cire kayansa gbdy ya watsa Kan kujera .


Bathtub yashiga ya tsakarwa kansa ruwa, take yaji wata natsuwa ta musamman ta saukar masa tare da bin ilahirin sansar jikinsa ,ahankali kuma yake jin hankalinsa na kara kwanciya ko babu komai yasan halin da matarsa da 'yarsa suke ,bugu da k'ari yasan inda suke Wanda a duk lokacin dayake da bukatar ganinsu zai gansu, wanka yayi shap shap ya fito kugunsa daure da towel fari ,while dayan hannunsa na rike da wani karamin towel yana goge sansar jikinsa dashi ,byn yagama goge jikinsa white boxer and white singlet ya saka yabi ilahirin jikinsa da turaren daya zame masa jiki ,sannan ya fad'a gadonsa zuciyarsa na matukar bugawa da karfin gaske.


"Dole duk runtse muna tare dake me'ad ,ko baki min halicci komai ba arayuwata bazan iya sakinki ba ,da zan sakeki da tuni bamu kawo wannan lokacin ba ,"ka saketa ko mu had'u a kotu maganar dayake tayiwa fu'ad yawo kenan acikin kwalkwaluwa ..dogon tsaki yayi inda zuciyarsa tashiga hasko masa kamannin safwa yayi saurin runtse idanunsa ya d'aura hannunsa akansa tmkr me shirin yi kuka yace" i a m mad iam stupid matukar nayi kuskuren sakin me'ad wa wani katon banza da wofi ..ina sonki matata duk kece silar fad'awarmu cikin damuwa ga wani tashin hankali na shirin afka mana. wayarsa ya janyo ya fara dialling number me'ad domin yaji muryarsa sannan ya kwantar mata da hankali Amman har 5 missed calls bata d'aga ba, tsaki yaja yayi jifa da wayar akan gadon "matsalar kenan taurin kai .
rungume hannunwansa yayi a saman kirjinsa yana kallon saman d'akin ,yayinda zuciyarsa ke hasko masa ita ji yayi hannunwansa daya rungume akirjinsa bazasu wadatar dashi ba ,yasa ya janyo pillow ya matse akirjinsa yana jin tmkr itace rungume ajikinsa, ahankali yana tunaninta ke fixgarsa ya kai hannunsa ya janyo bargo ya lullu'be jikinsa wani irin tsuma jikinsa ke yi tmkr zaki ga joystick dinsa sai mikewa take alamun tana bukatar abincinta wani tsakin yaja mtsssss hade da sanya hannuwansa duka ya dafe saman joystick da kyar yasamu bacci 'barawo yayi awon gaba dashi cike da matsanancin kaunar matarsa ......
Washegari ya tashi tattare da kuzari da farincikinki yashiga bathroom yayi wanka ya fito ya shirya zuwa office ,gabadaya ya nemi tarin damuwarsa ya rasa sai zallar farinciki dake dawainiyya dashi ,haka ma a office aikinsa yake gudanarwa cike da kwanciyar hankali ,a cewarsa matsalarsa ta kau damuwarsa tak'are tunda yasan inda iyalinsa suke Dan shi Sam bai d'auki mgnr dady da wani mahimmanci ba ......


********


Alhj Ismail money mis road ya samu zuwa gurin mahaifin sajida bisa nemawa D'ansa auren diyarsa , inda har an tsaida magana me karfi atsakanin ,sannan an saka ranar aure nan da wata daya kacal me zuwa, mahaifin sajida ya hana Khalid sanar mata ko kusanta inda take har sai an kawo masa ita amatsayin matarsa ,haka zalika ya hana aunty nadiya ta fad'a mata ko yin wani abinda zai sa tagane .
Anata shirye shiryen aurenta batare da saninta ba ,itama bata lura da yadda aunty nadiya ke zariya zuwa kasuwa ba ,lamuran gabanta kawai tasa agaba, na yadda zata mallaki fu'ad yazamo abokin rayuwarta, Dan har wata abokiyar aikinta datasan da mgnrta da fu'ad din ,tayi mata alkawarin Zata kaita gurin wani hatsabibin malaminta yayi mata aiki akansa, ta yadda da kansa zai kawo kansa gareta farinciki sajida tayi sosai sannan tace" banason na mallakesa ta wannan hanyar kafila ......"ai kuwa yadda yake da taurin kan nan da nuna isa ,bazaki ta'ba mallakarsa ba sai kin sa an rankwafar miki dashi tukun kisamu kansa "shikenan kafila zan bi shawarki but ki bari na sake tuntu'barsa zuwa nan da two weeks kafin muje nan suka bar mgnr zuwa sanda sajida ta fad'a...


**********
Me'ad tacigaba da zuwa gurin aikinta, sai dai har yanzu wannan lokacin bata iya shiga office dinta, dama cikin ma'aikanta gabadaya Dan chairman ya canza mata wani office kafin sanda za'a gama binciken su mudansir, Amman har lokacin jikinta bai daina mata tirin zafi ba Dan haka ta dawo zaman mota.


Bangaren su mudansir kuwa, idan ka gansu ba zaka ta'ba ganesu ba ,adalilin dukan mutuwar da policewa suka yi musu, iya azaba an azabtar dasu saboda rashin fad'ar gsky da sukayi, kowane daga cikinsu kanshi yayi wani irin kunburi saboda azabar duka ,bama zaka iya tantance waye mudansir tahir ma'aruf ba acikinsu ,sai da mudansir yaga suna daf da mutuwa sannan yayi

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads