Showing 114001 words to 117000 words out of 163596 words
Chapter 39 - YANCNKI Book Complete by Aisha Bagudu.txt
janyo karama kujerar stood gabanta ya zauna yana fuskantarta hk gwiwowinsu manne da juna, had'e da lalubo tafukan hannuwanta ya rike gam cikin nasa yana murzawa ahankali,abinda yasa kenan tayi saurin d'ago idanunta tana kallonsa, ganin tana kallonsa wani iri yasa ya marairaice murya had'e da karyar da kai ya koma abun tausayi agabanta sannan yace "haba sajida... wani irin damuwa kike son haifawa kanki hk ?
"Kalli yadda zuciyarki take bugawa da mugun karfi akan aurenki da Khalid......." Dan girman Allah ki natsu ni kaina bayina bane, haka zalika ba shirina bane ,komai ya faru ne da izinin Allah, Dan hk ki daina damuwa ,kinsa tun ba yau ba banason ganinki cikin damuwa ,sannan duk duniya babu abinda na tsana irin damuwarki ,banason kina yawon damuwa most especial akaina ,"yanzu fad'a min meye matsalarki ?
D'auke kanta tayi tare da yatsina fuska Wanda HKN ya rigada ya zame mata jiki Dan koda yaushe ba'a rabata da yatsina fuska idan dai tana kallon mutun to hk zata dinga yatsina kmr tana kallon kashi ,ballanatana wannan yatsinawar ta dabance me d'auke da tarin ma'anoni dayawa ce.
dayan hannunsa yasanya ya juyo da fuskarta , inda yashiga nacin tayi masa mgn ko hankalinsa zai kwanta Amman taki sai hawaye kawai take zubarwa tana ihun ya cuceta tare da tsine masa acikin zuciyarta .
"Tashi muje kiyi wanka yasoma k'ok'arin rabata da kayan jikinta Wanda hkn yayi nasarar ta'bo nonuwanta, nan fa ta fixge jikinta tare da mikewa tsaye tana haki tana auna masa wani irin wulakantaccen kallo .
A matukar zafafe tace "out of this room kafin zuciyata tagama dugunzuma akanka ....
"Aikin banza ,karamin yaro da kai ,sai shegen iyayin tsiya da naci" nace bana sonka banasonka dole ne wallahi sai kay dakasani aurna arayuwarka ta k'arasa mgnr tana juya masa baya inda hakan yabashi damar karewa yan madaidaitan bombom dinta kallo sannan ya kwashe da wata uwar dariya "danasani danasani !! ko me naji kince?
"Uhmmmmm abinda baki sani ba , kece zakiyi da kinsani ba Khalid daya rufa miki asiri ba ,Amman har abada Khalid bazai yi dayasani ba ,saboda sunanh ya habbaka ba zina ba ..
"Na d'auka abun naki zai zo da sauki shiyasa kikaga inata lalla'baki Amman tunda wulakanci ne abun muzuba, " nima nan da kika gani tatacce ne wanda zai iya yin fiyye da abinda zaki yi ,sannan ita zuciyarta taki k'arewar dugunzuma tayi bindiga ta fashe Bob.......
sannan wannan yaron da kike rainawa zai shayar dake mamaki ,zakiyi nadamar had'uwarki dashi arayuwarki, sai kin zubda hawayenki Akan wannan yaron ya nuna kirjinsa dayatsansa ,abu na karshe da zan gaya miki shine ki shirya anjima akwai zuwa dinner..
"da wa zaka wani banzan dinner ni ko wa ? " are you sick or what?
"dake zamu je dinne , kuma ki tabbatar da kin shirya kafin lokacin, idan ba haka ba kiga aikin yarinta "to sannu ubna aliyu .. kuma wallahi bazan aje Koin ba, kai kayi kad'an din da zanjewa dinne aikin banza kawai .
Ji kake tassssssss ya dauketa da wani gigitaccen Marin dayasa ta d'auke wuta tana zaro idanunta dake cike da ruwan hawaye ..
"dan girma Allah karki shirya har sanda zanzo sannan ya juya ya bar d'akin cike da matsanancin takaicinta .
cike da tashin hankali ta fad'a Kan gadonta tana wani irin kuka "mari ...marina fa wannan D'an iskan yaron yayi batare da na iya daukar wani mataki akai ba ? "Wayyohlly Allah meke shirin faruwa dani ne ,na baro gidan emran da zummar cika burina Akan fu'ad, gashi ban samesa ba na bige da auren yaro .....
bayan d'aurin auri ango ya zarce da walima a gidan saukar bakin mahaifinsa dake ebutte meta road.
aunty nadiya nata fama da jama'a, kawayenta yan'uwan ta, Dana 'yancin arxiki, mak'ota da abokan arxiki dan ko ta ina acikin gidan jama'a ne makil gbdy hidima ta sha kanta, gidan cike yake taf Ba masaka tsinke musamman lokacin da dangin mahaifiyar sajida suka zo daga Minna Cikinsu akwai ya'yan wan mahaifiyarta da suke uwa daya uba daya , Aysha da jidda wanda suka kasance sa'anni Sajid ne, sannan akwai wasu daga cikin kawayenta misnah mincy hajaracy wanda labarin auren yasame bagatatan duk sunzo duk da ba sajida ce tagayacesu Ba ..
kanwar mahaifinta ce tashigo d'akin ta isketa kwance tana kuka ,tashiga ta kurata Akan lallai sai ta tashi tayi wanka amman juyin duniya Sajida tace bazatayi wani wanka ba ,balle wata kwaliyar banza akan auren yaro karami sa'an Dan cikinta har dare tana kwance taki motsawa duk wanda yayi mata mgn bata sauraransa , Kuka kawai take , sallah ce kawai ke tada ita .
karfe takwas daidai motocin dibar jama'a domin zuwa wajen dinne ta iso , nan ma bakaramin tashin hankali akayi Ba domin tace babu inda zata, Yayinda Khalid yana waje tare da abokansa , Aysha ta fito ta sheida khalid cewar sunyi iya yinsu amman amarya tace bazataje koina ba .
Ango khalid dake zaune cikin motar sanye cikin wani lallausar yadi mai sharara fari sol har kana iya hango farar singlet dinsa da manyan damtsensa masu nuna alamun karfi da cikakkiyar lafiya da mazantakansa na matashin saurayi me jini ajika.
kallon yadi kadai ya isa ya shedawa mutun ki manta tsadarsa, ahankali ya d'ago tsumammun idanunsa byn yagama suraron bayanin aysha yace "yanzu tana ina ?
tace "tana d'akinta yace "aunty nadiya fa?
"tana cikin mutane hidima tayi mata yawa ahankali ,"dady na ciki ne ?
"Yana Amman yana shashinsa gama jin hk keda wuya ya yunkura ya fito daga cikin motar adaidai lokacin da kiran kanwarsa khadija yashigo wayarsa ya ciro wayar daga aljihun gaban rigarsa ya manna a kunne "ya akayi khadija ?
"yaya ku kad'ai fa ake jira jama'a sun cika kowa ya kosa "
"kuyi hkr gamu nan zuwa , da sarsarfa ya taka matattakalar binen da zai kai mutun d'akinta kai tsaye.
tana zaune abakin gado sai faman cika take tana batsewa tkmr wata macijjya Sabod rigimar da'ake ta faman tafkawa daita akan lallai sai ta tashi ta shirya Khalid yasanyo Kai yashigo cikin d'akin ko sallama babu ba ita ba hatta jamar dake fama daita sun yi matukar razana da ganin wannan zakin mazan ma'aboci Haiba da kamala sai dai kallo daya zaka masa ka tabbatar da kuruciyarsa a fili wato bazai wuce 26 yrs da haihuwa ba, Suna ganinsa Suka soma k'ok'arin barin d'akin ...
d'akin ya saura daga ita sai shi bai yi mgn ba illa Idanuwansa daya tsura mata yana kare mata kallo tun kayan daya barta dasu ne ajikinta, yayinda ita ko kallon inda yake tsaye bata ba illa jijiga kafarta daya da take ta faman aikin yi .
ahankali murysrsa ta fito "malama ki tashi kije kiyi wanka "
A matukar fusace ta d'ago had'e da cewa "idan ba'ayi ba.. ?
"nace bazani ba ko dole ne? "duk wani abu agurunki zai iya zama ba dole ba ,amman zuwanki wannan dinne din yana da matukar mahimmanci arayuwata, saboda wannan shine al'amari na farinciki gareni , ya kai hannunsa ya shafi gefen fuakarsa "wai meyasa ma zan damu kaina akan dole sai naje dinne da shohuwa iriki ? ya tmby kansa yana tsareta da idanunsa tare da takowa zuwa inda take .
sauri zaro idanunta waje tare da dafe daidai saitin zuciyarta datake jin yana daf da tsayawa ,while idanunta na kan dubansa a matukar firgice.
"nice tsohuwar ta fad'i hk cikin murya mai rawa ala'mun tana son yi masa rashin mutunci?
"uhmmmmm da ke mecece ba tsohuwa ba ?
"Dan Allah malama ki tashi kije kiyi wanka ki shirya minti goma kacal na baki idan kuma kikayi kuskuren k'ara ko second biyu ne akai , wallahi wallahi sai dai ki iske kanki abayi ina miki wanka da kaina "what ?
ta furta tana yatsina fuska had'e da masa kallon ta'b'ba'be mara hankali.
Yayi mugun tsareta da idanunsa "ko kina da ja ne acikin abinda nace ?
hk kawai ta tsinci zuciyarta kasa amsa masa sannan wani bala'in shakar maganarsa tashigeta ,dan a yadda take ganin takusan zai iya yin fiyye da abinda yace zai yi barin ma lokacin data Tina marin safe ai batasan lokacin da tashi tsam tashiga bayin ta barshi zaune zaman jira fitowarsa .
Dialling number aysha daya kar'ba yayi ,kira daya biyu ta d'auka yace "ta turo masa me make up sannsn ya katse kiran ya nufi barandar d'akinta "Yasan ko ita wacece , amman bai San me yasa yaji sonta acikin zuciyarsa ba..
sai dai zai yi kokari dankwafar da shi wannan son dayake mata domin yasamu damar ajiyeta a mazaunin dayafi bukatar takasance .
Bata wani lokaci ba ta fito inda ta iske mai make up zaune zaman jiranta dogon tsaki taja tare da kokarin sanya kaya ,sannan ta zauna duk ranta a dagule ,an tsara mata make up na garari wanda ya canzata zuwa matashiyar yarinya, tayi wani irin masefaffen kyau, sai kamshi jikinta ke fitarwa har aka gama tana zaune batare da tayi yunkurin mikewa domin halarta zuwa gurin dinne ba ,yatsina fuska tayi had'e da cewa mai make up "Kinga dan Allah kina tafiyarki zan kule d'akina dan babu dan iskan dinne da zanje.....
yarinyar tace to tasoma hanzarta tattara kayayyakinta tasanya ka ta fice... ta mike kenan da niyyar kulle dakin batasan yana tsaye a barandar d'akin Yana fuskartata ba .
bai tsaya wata ba yasoma takowa inda take ya cire links din hannunsa Ya nad'e hannun rigarsa ya sunkuya ya sunkuceta yayi sama daita wanda hkn yayi sanadiyar da d'ankwalinta ya cire ya fad'i ya nufo hanyar parlour'n kasa daita a parlour'n kasa ya iske yan'uwanta da kawayenta suna zaman jira , aiko suna ganinsu sukace me zasuyi ba dariya Ba ,take kowace daga cikinsu ta ciro wayarta tana d'aukarsu hoto tare da mamakin wai wannan wani irin ango ne mara kunya ?
aysha tace "ba takalmi da dan kwali akanta zbatare da tsayawa 'bata lokaci ba yace " kibiyota dashi ai khalid bai direta sajida akoina Ba sai cikin mota abokan ango in banda dry babu abinda suke suna jinjinawa kunjinsa, aysha da me make up suka karaso gurin atare tasanya mata takalmanta akafafunta sannan aka sake d'aura mata d'an kwali ,
ana tada motar ta fashe da wani irin kuka "yanzu banda lalacewa a kalleta ace wanna abun ne mijinta wallahi har gara emran da auren Khalid arayurwa wallahi ba karamin abun kunya dady yaja mata ba .
Kuka take sosai shi kuwa ko ajikinsa ,guri daya hankalinsa yayi mugu mugun tashi yadda ta dinga Surfa masa zagi iri iri ,bai tan kata ba illa daidaita hannunsa da yayi ya bata gwab abakinta, ai da sauri tayi shiru "wallahi kisa sake wata mgn anan zakiga aiki da cikawa Dan HK kinsa irin mgnr da zaki dinga gaya min, ni ba sakarai bane shasha lusari irin wancan,Shanshan tsohon mijin naki yana gama fad'ar hk yayi shru yana jiran ta sake cewa wani abu har suka isa 3 star dake ikeja Awolowo way bata sake cewa kala ba sai kuka take ..
daidai inda zasu zauna direban yayi parking abokai da yanuwa suka nu fosu domin tararsu ,khalid ya sai walkiya suke acikin hasken fitilu daya haskaka gurin ya fito ya zagayo daidai inda take tare da rusunawa kmr zai shige jikinta "to yaya akayi tsohuwar amaryar khalid zaki fito ne ko na sake nad'e hanun rigata?
ai ba shiri ta fito zuciyarta na wani dukan uku uku gabadaya Tasom tsorata da yanayinsa sai nuna mata tashen balagar tsuntsaye yake .....
dariya sosai tabashi ganin yadda hanzarta fitowa ya kamo hannuta cikin NASA ita kuwa ji tayi kmr ta d'aura hannuwanta duka bisa kanta ta rutsa kuka dan bakinciki, shi kuwa sai murmushi yaje ya matso kusa daita sosai "kina ji ko tsohuwar amarya ki saki jikinki da ranki if possible ma kiyi murmushi kmr yadda nima nake yi ko kuma yanzu nayi miki abinda, zai tabbatar miki da kuruciyata a fili.
wayyohhly Allah ta furta tare da kirkiro murmushin dole wanda yaja hankalin masu d'aukar hoto da video kansu ya kai hannunsa yana gyara mata zaman sarkar wuyanta da Goggoronta ,aiko take tashiga zabga masa wata katuwar harara ,batasan sanda bakinta ya subuce ba tace aikin banza kawai duk abinda mutun zaiyi dai ba zai taba burgeni ba, tunda bashi zuciyata take so ba, wata irin damka yayi tsintsiyar hannunta taji tmkr jijiyo hannunta zasu tsinke Dan azaba , yayinda har lokacin masu d'aukar video da masu d'aukar hoto nayi aikinsu , hka zalika jamar dake gurun nayi Da wayoyinsu har sai da suka isa mazauninsu sannan ya saki hannuta, tayi saurin sauke naunauyen ajiyar zuciya tana shafa tsintsiyar hannunta tare da tsine masa..
aranta take mamakin karfinsa..
bayan sun zauna aka soma bud'e taro da addua sannan aka shiga program ...
Mmn sudais ce
[11/3, 8:30 AM] El~hajj: 💗💗💗💗💗💗
'YAN CINKI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~NA~
*AYSHA A BAGUDO*
~DEDICATED TO~
*AUNTY BASEERA WANNAN PAJIN NAKI NE , INA MATUKAR GODIYA BISA GA SOYAYYARKI , ALKHAIRINKI,KULAWARKI GARENI ALLAH YA BARMU TARE*🤝🏻🤝🏻🤝🏻
Page 83
........d'aya daga cikin abokan ango ne ke tsaye bisa kafafunsa rike da abun magana ,yasoma karanto tahirin khalid da makarantar da yayi ,har zuwa kan matakin da yake yanzu, inda yake bayyana kwalayensa da matsayin na mataimakin sajida .
yace "khalid uwar d'akinsa ya aura saboda kankaba da tsaurin ido irin nasa gashin nan sai yanga da yauki ake masa .......
dariya gabadaya hall din ya d'auka tare tafa masa hannu hamza yacigaba da magana kmr hk "sai dai mu agurinmu musan mace bata fi karfin namiji ba, matukar namijin ya amsa sunansa nmj,da kuma yadda namijin yasan kansa dan haka ta wannan fannin zan iya cewa abokina bayi tsaurin ido had'e da kankaba ba ......
aka sake kwashewa dariya "Allah yasanyawa rayuwar aurensu albarka yadda muka taru anan Allah ya hadamu mun zo suna haka .
mc ya amshi abun magana yana dry " ameen sai dai kuma gasky wannan abokin naka baiyi kankaba saboda kowa da irin ra'ayinsa ..
Ita kuwa sajida tun da ta zauna Kan kujerar da
ta ke mallakinta amatsayinta na amarya, hankalinta yasoma barin gangar jikinta, gabadaya tunaninta ya azzara ne akan burin zuciyarta," wannan karon ma irin zaman rayuwar datayi da emran zatayi da khalid kenan,
tayiwa kanta mgnr zuciyarta na kokawa ....
Dan a yanzu har tasoma hasasho yanayin zaman nasu , Dan sam bata ji zuciyarta zata amince ta hakura ta amsa rayuwa dashi amatsayin miji gareta .
a halin yanzu hankalinta a matukar tashe yake tana sake mamakin yadda khalid ya makalewa aurenta dole, yayinda ga en mata nan birjik a gari da suka fita komai ,"ayanzu datasani take da bata zauna ta hakura da auren emran ba, ga kuma abinda karshenta ya dawo ta bige da auren jinjiri "wace irin rayuwa ce hk ?
"wace irin kaddarar ce haka ta giftawa rayuwarta?
gabadaya komai ya rigada ya cakud'ewa mata tarasa nemowa kanta mafuta "yanzu ya zatayi da rayuwarta?
sosai tayi zurfi cikin tunani Dan kwata kwata ita zantuttukan hamza abokinsa baa shi ga kunnunwata ,hankalinta da tunaninta suna can ga fu'ad dinta ,tana jin ina ma wannan ranar ta kasance ranar aurensu ce da fu'ad dinta sanyin idanunta, hasken zuciyarta, lizamin rayuwarta ,bugun zuciyarta...
"ina ma mafarki take, ba'a gaske bane duk abinda ke faruwa daita? har sanda khalid ya lalu'bo tafin hannuta cikin nasa fuskarsa cike da matsanancin farinciki batasani ba ,Yayinda ta koina acikin hall din murya mc ne ya karad'e gurin ,inda yace "ana son ganin ango da amarya a flow, waigowa Khalid yayi ahankali yana dubanta fuskarsa na sake fad'ad'a farincikinsa.
Amman ganin yanayinta al'amun tashiga duniyar tunanin yasa take murmushin dake fuskarsa d'aukewa cak zuwa wani malolon bakinciki da tarin damuwa, ransa yasoma 'baci zuciyarsa tashiga rawa rawa Dan ko ba'a gaya masa ba yasan wani tunani take yi daban wanda ba nashi bane .
"shi kuma wulakancin da bazai ta'ba lamunta dashi ba kenan yana zaune ana tunanin waninsa ,ransa a matukar 'bace ya kai bakinsa daidai saitin kunneta had'e da tausasa muryarsa tmkr bai so yin mgnr yace "ke tsohuwar kawai kiyi maza ki dawo cikin haiyacinki da natsuwarki ana bukatar ganinmu yanxu Dan kin wani shantake atunanin iska .... tunanin abinda bazai ta'ba fissheki ba .....
yana gama fad'ar hk ya mike tsaye tare daita yana kirkiro fara'r dole zuciyarsa a dagule, alokacin shi kad'ai yasan tashin hankali da zuciyarsa take ciki ..
Ahankali yake rike da hannunta yana tafiya ,ita kuma tana biye dashi abaya masu d'aukar hoto da masu d'aukar video suka matso kusa dasu sosai suka shiga aikinsu ,na d'aukarsu har sanda suka sauko daga mazauninsu zuwa tsakiyar hall ,inda mutane suka sake rud'ewa gurin d'aukarsu hoto, sauti na musamman aka sakar musu Amman sajida tayi tsaye ta kasa motsa koda D'an yatsanta ne ,ganinta sam bata ga wani abun rawa ba......
Idan ma rawa zatayi ta rasa Wanda zata tsaya yi rawa dashi sai Khalid ..?
"Ina wannan abun kunyar ba da ita za'a yi ba ,ganinsa take agabanta tmkr mazuru ne agaban zaki ....
Duk da ransa a matukar 'bace yake ,Amman ya d'aure yayi k'ok'arin sanyawa zuciyarsa da gangar jikinsa jarumta