Showing 36001 words to 39000 words out of 163596 words
Chapter 13 - YANCNKI Book Complete by Aisha Bagudu.txt
daya biyu malik ya d'auka, bayan sun gaisa tace "malik kuna tare da fu'ad ne ka had'ani dashi?
" a,a ina gurin kallon ball, na dai barshi tare dasu kabeer a gida.
"Okay idan bazaka damu ba zanyi maka wasu 'yan tambayoyi, amman ina bukatar jin gsky daga bakinka ."uhmmm ina sauraranki?
"Ka ta'ba gayawa fu'ad abubuwa da suka dinga faruwa atsakaninmu da kai har zuwa kan marin danayi maka?
sai daya ja naunayen ajiyar zuciya ya sauke da kyar sannan yace"alahakikanin gsky wasu Abubuwan yasani sai dai batu na mari bai sani ba, dan ban gaya masa ba, wani abu ne ya faru da har kikayi tmby?
"Nothing ,Amman yanzu wani irin taimako zaka min malik akan abokinka?"na maseefar kwadaituwa da aurensa, ina son shi sosai kuma zan iya yin komai akansa matsawar zan sameshi, ka taimakawa rayuwata malik nasamu fu'ad, nayi maka alk'awarin zan maka komai ciki kuwa har da samammaka aiki a karkashin ikona tunda shi yaki amsa daga gareni ..?
Numfashi da ajiyar zuciya ya sauke atare kana yace "zaki iya mallakar zuciyar fu'ad cikin sauki dashi kansa gbdy, bisa dalilin abu daya da sauri ta katse Shi ta hanyar cewa"meye shi malik ka fad'a meye shi zan iya yin komai akansa "meye zanyi fu'ad yasoni?
"Bawani abu bane daya wuce kyautatawa, fu'ad na matukar son kyautatawa ,da km kyautatawa wanda ya cancanta most especial mara shi,ina tabbatar miki matukar kika kasance daya daga cikin masu kula da kyautatawa zaki mallaki zuciyar fu'ad cikin sauki batare wata matsala ba, ni kaina ina miki sha,awar aurensa domin idan kika sameshi amatsayin miji ina me tabbatar miki zaki yi alfahari samun miji kmrsa "shikenan malik nagode sosai da shawararka, km InshaAllahu zanyi kok'arin naga na kasance cikin masu kyatatawa mutane, gobe karka manta kasameni a oil and gas.
" InshaAllahu bazan manta ba Na gode sosai Allah ya mallaka miki zuciyar fu'ad "ameen nima nagode da wannan adduar taka sai mun had'u goben ta katse kiran ta koma gadonta ta zauna inda zuciyarta take bata umarnin me zai hana ta tura masa ko da sakon text message ne tunda yaki d'aukar wayarta hannuwanta duka tasa ta rike wayar tasoma rubutu sako kmr hk.
_Assalamu alaikum ina fatan kana cikin koshin lfy, daman na turo maka wannan sakon ne domin na k'ara baka hakuri bisa ga kalamaina na d'azu danayi amfani dashi ,wanda sukayi silar 'bacin ranka har ka mari kyakyawar fuskar matarka, azahirin gsky naji babu dadin abinda kayi min ,sai dai tarin soyayyar danake maka ta hana rashin jin dadin nawa tasiri ,ina sonka fu'ad har bansan yadda zan misalta maka ba, ka daure ko ba yawa nima kasoni kwatankwacin yadda nake sonka I really sorry for what I did ..sai da safe daga mai sonka Me'ad Ediris Takai_
Tana tura masa ta koma kan ganta, ta kwanta lamo tare da runtse idanunta bawai dan tana jin bacci ba, sai Dan shaukinsa dake dibarta ,gudundune jikinta tayi, lokacin da tunaninsa ya yawaita ajikinta dan har ta fara hango sunyi aure dashi da yadda yake sarrafata akan bed gurin aika mata da zafafan romancing dinsa masu birkita 'kwal'kwaluwa.
A kwancen dayake a d'akinsu sanye cikin jallabiya fara sol hannunsa rike da wayarsa yana brownsin sakonta yashigo ,amman bai bi ta kai ba yacigaba da abinda yake, km ko bayan daya gama bai duba ba yayi kwanciyarsa, ranar dai me'ad bata samu ta runtsa ba duk inda ta juya fu'ad take ganin da hannunsa dake yawo a ilahirin jikinta .
Washegari tun 7:00 malik ya tashi yayi shirinsa ya iso oil and gas, sai dai bai iske me'ad ba dan bata karaso ba tukun, yasamu guri ya zauna zaman jiranta, sai gurin takwas tashigo cikin hadaddiyar motarta kiran toyota Camry ta gabansa ta wuce amman bai ganta ba saboda ba'a cikin irin motocin daya saba ganinta ciki bane, bayan ta isa office dinta da kmr minti 2 tasa ayi kiransa,cikin wasu 'yan mintuna malik ya bayyana a office dinta cike da girmama ya gaisheta, ta amsa da kulawa sannan ta nuna masa gurin zama da hannunta kana ta bukaci takardunsa ,batare da 'bata lokaci ba ya mika mata, bayan ta duba ta mike tsaye "kabani minti 20 "ok badamuwa ranki ya dade. Kai tsaye office manager ta nufa domin neman alfarma.
Acikin awa daya kacal malik yasamu aiki a ibadan karkashin kulawar me'ad amtsayin wanda zai dinga kula da ficen da shigen kud'ad'en kasancewar accounting ya karanta
Lokacin da wannan labarin yasameshi a zaunen dayake a office dinta, yayi matukar murna da farinciki, godiya ya dinga yi mata kmr zai mata sujada, aikin daya d'auki sama da shekaru biyar yana nema sai gashi yasamu acikin awa daya nigeria kenan kayi karatun kagama sai kana da hanyar zaka samu aikiyi..
"Kabar min godiya hk nan ,ka godewa Allah daya nufeka dasamu, sai dai shawarar da zan baka ,ba wuce ka rike aikinka da mahimmanci ba ,domin mutane dayawa irinka na can suna nema kasa danaka basu samu ba , sai abu nagaba ka taimaka min nasamu fu'ad.....
"Angama ranki ya dad'e InshaAllahu zanyi iyakacin kok'arina akan lamari, "ok ranar Monday zaka soma aikinka yanzu zakayi dropping account number dinka, akwai wasu kudin daza'a tura maka domin siyan sutura.
"Nagode nagode!!! ranki dad'e wallahi har bansan irin godiyar da zan miki ba ,hk suka rabu malik na farinciki samun aiki ita km tana murnar zata samu fu'ad cikin sauki tasan idan yaji itace tasammansa aiki zaiyi farinciki wata killa adalilin hk burinta ya cika.
Koda malik ya jewa fu'ad da labarin samun aikinsa ta hanyar me'ad, yace "tayi kokari sosai, sai dai kajira ranar zuwan wulakanci daga gareta, domin wannan aikin daka amsa daga hannunta daidai yake da ka amsarwa kanka wulakanci ne da damuwa, ni dai babu ruwa duk abinda yaje ya dawo sai dai ya kare akanka.
"Wace irin magana ce hk fu'ad?
" gskyar lamarin nagaya maka sai kayi taka tsantsan "Naji ni dai ka min addu'a shi nafi bukata daga gareka bawani dogon sharhi ba ,sai agame da zance me'ad , yarinyar nan ta damu da lamarinka dayawa , ka duba kagani kyau ilimi nasaba duk tana da, uwa uba gata da zuciyar taimako "ai ta taimaka maka dole ka fad'I hk mana , ni dai ina umartarka ka takaita maganarta anan dan kadameni da zance ina da abubuwan yi.
Malik yayi dry sannan yace "ni da zakabi shawarata da ka amince ka aureta komai cikin sauki zaka samu aikin ma dake bulayin nema ba sai kaje ba, kana daga kwance za'a yi maka komai."to baza'a d'auki shawarar taka ba ,idan ka damu da lamarinta har hk ka aureta mana ,ai daman kana sonta.
"Ina sonta bata sona kai take so, da kace ni ta nuna tana sona wallahi ina tabbatar maka babu abinda zai hanani aurenta,"yanzu ma zaka iya gwada sa'arka yana karasa fad'ar hk ya wuce ya bar malik tsaye yana kallon bayansa.
*********
Duk abinda me'ad zatayi domin shawo kan fu'ad tayi, tabi abokansa da duk wani wanda tasan suna muamula, duk inda tasan zata ganshi kafafunta na gurin amman ko kallo arziki bata isheshi ba ,asalima yana ganinta zai bar gurin yakama gabansa, acikin tsakankanin wannan lokacin ne labarin rashin lfyrsa ta risketa, bata tsaya sanya a gwiwa ba ta nemi malik da yayi mata rakiya, shine yayi mata jagora har gidansu inda ta tsaya kallon ruba'b'ben gidan dake shirin zubowa "kace na ne gidansu malik?
"Kwarai kuwa nan ne gidansu "kina mamaki ne?
Shiru tayi batare datace masa komai ba illa tsurawa gidan idanu datayi "yanzu anan fu'ad dinta ke rayuwa tun tasowarsa? A she fili tayi zance batasani ba ,
"Ki daina mamaki ranki ya dad'e nan ne gidansu kuma inda yayi rayuwa acikinsa idan kin mutsu ne mushiga Kigani d'aki na d'aya na biyu nan ne d'akin kakarsa.
Tana gama sauraransa ta juya ahankali Jikinta matukar a sanyaye tashiga cikin parlour gidan me cike da duhun tsiya ,hannunta rike da karamar jakarta da kyar take ganin inda take sanya kafafunta duk rana ce ba dare ba ,yayinda malik ke biye daita da manya manya fararen lododi guda biyu ,taja ta tsaya abakin kofar shi km malik yayi sallama tare da kutsa kanshi cikin d'akin sannan itama tayi sallama tashiga "a'a Malik kai ne hk da rana tsaka ?"to marhabun lale ku karaso ciki mana inna ta fad'i hk tana mai mikewa ta shimfid'awa me'ad dadduma ,Dan shi Malik tuni ya ajiye lododin hannunsa yakarasa inda fu'ad yake.
Duk wanda yasan d'aki marasa shi hk d'akin yake bawani shararrun kaya ne acikinsa ba illa wani D'an madaidaicin gadon, sai kayan miyar dake ajiye gefe guda mai nuna alamun na siyarwa ne, gefe daya km wata katuwar akwati ce ajiye kallo daya tayi wa d'akin tasan d'akin marasa shi ne kmr yadda gidan yake sai da ga dukkanin Alamu yana samun kulawa ta hanyar gyara da tsaftaceceshi .
cikin ladabi tamkar ba ita ba, ta durkusa har kasa kanta a sunkuye cikin sanyi murya"inna barkanmu da warhk ya gida da me jiki.. inna ta amsa cikin sakin fuska da kulawa batare datayi tunanin inda tasanta ba saboda ganinta tare da Malik .
ahankali me'ad ta juya inda fu'ad ke zaune Wanda ke aikawa malik da uwar harara sanye cikin gajeren wando da T shirt fara sol gashin jikinsa kwance luf Luf tmkr na jarirai ,ta gaida uban gayyan da ko kallon inda take bai yi ba " ina yini ya jikin ? abunda me'ad ta fad'a Kenan taja bakinta tayi shiru.
ya d'an d'ago kad'an yace lfy atakaice shima dan inna tayi masa ala'mun da kafarta ne ,me'ad ta sake yin wani kayataccen murmushi sannan tayi shr.
Malik yayi gyaran murya sannan yace "inna ga surakarki budurwar fu'ad tazo duba lfyrsa ..inna tayi dry "kace kishiya ce shine har da bata gurin zama ,shi kuma jairin sai wani cika yake yana batsewa kmr ba yanzu nagama fama dashi gurin shan magani. Me'ad ta sunkuyar da kanta alamun kunya .malik yace " har yanzu fu'ad bai bar gudun magani? " ina fa har tsoron rashin lafiyarsa nake saboda hkn.
Mead ta dago da niyyar ta saci kallonsa ,karaf suka had'a idanu atake kirjinsu ya buga, tayi saurin d'auke idanunta Dan bazata iya cigaba da kallon surar jikinsa inna na gurin, sai dai muryarta a sanyaye tace "inna me yasa aka barshi a gida ba'a kai shi hospital ?
"Wannan za'a kai hospital inna ta nuna fu'ad daya yatsina fuska alamun damuwa inna tacigaba "mutumin dake gudun magani balle allura idan kika ganshi kuzarin jiki kawai garesa amman laulauyi garesa sai ki kishirya, murmushin jin dadi mead tayi ganin tasamu karbuwa agurin inna .
sun jima shr sannan inna ta mike tayi waje ,shima malik yace "bari nabawa masoya guri, tsaki fu'ad yayi batare daya tanka masa ba .
Yana fita fu'ad ya gyara zamansa cikin rashin jin dadi fitar da inna da Malik sukayi dan ba'a son ransa ba, dan babu yadda zaiyi ne.
me'ad ta matso zuwa inda yake ta tsuguna tare da cewa "fu'ad...
Sam bai kalli inda take ba hasalima cigaba da danna wayarsa dake rike a hannunsa yayi, tayi kusan minti uku sannan tayi kokari kai hannunta da zumar Kwace wayar hannunsa ya kallota a fusace tana dakatar daita da manya idanunsa domin bayason kusancinsu a yadda yake Dan shi kadai yasan abinda tafiya acikin jikinsa tsawon minti 2 yana tsare daita da manya idanunsa kafin daga baya yasoma mgn kasa kasa "karki wahalar da kanki da wata banzar kalmarki ko gaya min uzirin abinda ya kawoki,domin ina tabbatar miki sam banyi murna ganinki kusa da innata ba ,ni a bangarena bai zama lallai dole sai na soki ba ko yin wata muamula dake ba, dan haka ki daina wani rawar kafa dan sam ba birgeni zakiyi ba, dani bakowace mace ce zata iya yaudareni ba ..
me'ad datayi masa kuri da idanunta tana kallonsa ta saukar da numfashi tace" na jinka fu'ad sai dai abinda nake son kasani tunda nice naganka kuma na aminta da kai, zan iya d'aukar komai tare da shanye duk wasu kalamanka gareni sannan zanyi komai dan ganin na mallakeka amatsayin uban ya'yana koda dukiyata zatakare da numfashina..
wani irin kallon banza fu'ad yayi mata irin na sama da kasan din nan sannan yace "iska na wahalar da mai kayan kara .
"Ina tabbatar maka wannan iskar bazata wahalar da mai kayan kara ba ,domin zamu kasance cikin inuwa daya koma nace bargo daya . tana gama wannan mgn ta juya cikin fushi tayi ficewarta shi kuwa fuad daya bita da kallo ya saukar da numfashi cikin sanyin jiki ya mike daga inda yake zuciyarsa cike da tunaninta tabbas tana matukar burgeshi muttaka, har yana jin idan bai sameta ba komai zai iya faruwa dashi .
bayan tafiyarta tashi yayi ya sake yin wanka yasanya kananan kaya marasa nauyi ya tsaya fesa turare inna tashigo hannunta rike da bakar leda mai dauke da ruwan roba da Malta Amman taga wayam babu yarinyar dazu babu alamunta cikin sauri tace " kai fu'ad ina yarinyar da malik?
Kafadunsa ya daga mata alamun bai sani ba sannan yasanya kai yayi waje inda machin dinsa ke parke.
tuki take cikin 'bacin rai tana ciza yatsan hannuta gbdy ta kagara taje gida domin ta samawar kanta mafuta akan lamarinta da fuad wani irin taka birki tayi dan karfi gudun kada ta buge abinda tagani a gabanta.
a matukar fusace ta fito daga cikin motarta tayo waje inda tsohuwar take tattakawa ahankali saboda tsufa datayi Dan har ta d'an rankwafa "haba matar nan wannan, wani irin mugunta ce hk wato ke kin gama cin kuruciyarki A cikin tsiya shine zaki ja min masifa wato idan na bugeki kika mutu a kamani ko? to in har hk kike nufi ki sani idan na bugeki na kad'e banza dan dake da kuda daya ne agurina dan hk ki matsa kafin nabi ta kanki da mota..
tsohuwar ta d'ago da kyar ta kyalleta tace yarinya kiyi ahankali ahankali domin an yi wasu kafin ke kuma basu ta'ba cin riba ba kinga kema baxaki ciki riba.
me'ad taji wani irin 'bacin rai ya turnukota sai dai lokaci daya shawarar da malik yabata ya fad'o mata "fu'ad na matukar son kyautatawa da kyautatawa marashi kenan irin wannan kyautatawa yake nufi?
"bugu da kari mgnr tsohuwar ta kashe mata jiki murus,Dan HK tasoma nadamar abinda ta aikata da farko ta matso sosai kusa tsohuwar tare da rage sautin murya kasa sosai"inna dan girman Allah kiyi hkr nayi nadamar abinda na aika miki, ni kaina bansa abinda yasa wani lokacin nake reacting hk ba, amman kiyi hkr idan magana ta 'bata miki ,muje na tsalakar dake ta kai hannu zata ta'ba tsohuwar tace "dama kin bar shi yar nan zan iya tsallakawa, sai dai naji dadi da kikayi saurin gane kuskuren abinda kikayi ,ita duniyar ma guda nawa take?" ku dunga d'auka da mai kudi da talaka duk abu daya, saboda Allah da yayi mai kudi shi yayi talaka ba kuma dan baya son shi ba.
"Haka ne inna na gode sosai amman kiyi hkr kibarni na taimaka miki tayi saurin komawa cikin motarta ta kirgo kudi wanda zasu kai kimanin dubu goma ta dawo inda tsohuwar take ta riko hannuta tasanya mata kudin "inna ki amshi wannan dan Allah karki aa"kai yar nan har da wata hidima to nagode kwarai da gaske Allah yayi albarka, Allah yayi miki abinda kike so Inshaallahu zaki gama da duniya lafiya. "Ameen inna na gode.
fu'ad da fitowarsa kensn abun ya faru akan idanunsa duk da bai ji tautaunawarsu ba ,Amman ya ji dadin taimakon datayiwa matar har sanda ta tsallakar daita dayan bangaren tsohuwar na dariya tare da d'aga mata hannu ta koma tashiga cikin motar ta figa a guje yana kallon sannan ya taka mashin dinsa yacigaba da binta abaya batare da tasani ba ,har inda ta sake tsayawa saboda hango wata makauniya rike da yar jagoranta wace bazata wuce kamin shekara takwas ba ta mika musu sadakar dubu daya bayan ta tsaya sun tsallaka abu kmr wasa hk ta dinga taimako mutane wanda abin yacikasa da mamski "daman tana da zuciya irin hk me kyau ?"gsky idan har tana da irin wannan halin na taimakawa marasa karfi ta cancanta tazamo abokiyar rayuwarsa, adaidai jection din bankole suka rabu shi yayi titi dopemu road ita kuma kai tsaye gida ta nufa inda ta iske sunyi bakin da suka dade suna expecting zuwansa, wato safwan almustapha maitama daga kasar hollond, mahaifin safwan baban mutun ne a kashen duniya gbdy ,sannan me gidan mahaifin me'ad ne a can baya kafin yayi rites . Safwan ya dawo daga kasar Holland ne da niyyar abubuwa guda biyu, na farko cima burin auren mead daya kwalafawa ransa tun shekarun baya, sai abu na biyu cigaba aikinsa amatsayin shugaban shashi na kasuwancin Nigeria.
jin ana jera mata sannu ne yasa mom dinta yin saurin fitowa dan tayiwa yar tata gargadi kada ta kawo musu wargi .
me'ad ta kalli uwar cike da mamaki "ni wai momy meyasa kike min hk ne?" narigada na gaya miki na canza mind dina akansa yaje gaba ya auri matarsa ni matar fu' ... momy tayi saurin rufe mata baki "karki sake me'ad kiyi ganganci, karkiyi wasa da damarki,domin damar mutun sau daya take zuwa masa arayuwa, ina shawartaki karki bari taki ta subuce miki.
me'ad tayi wani irin murmushin sannan tace, karki damu momy da subucewar wannan damar ni dai fu'ad nake so simple as that tana gama fad'ar hk tashiga cikin parlour'n mahaifinta wanda sai bakinsa masu mahimmanci yake tara acikinsa ,ta samu gefe