Header Ads
Showing 87001 words to 90000 words out of 163596 words

Chapter 30 - YANCNKI Book Complete by Aisha Bagudu.txt

Ads the beginning of article before Image

02 Jun 2024

1303

Ads at the middle of Article

fu'ad yayi saurin riketa ya rankwafar da tunkunyar ruwan zafin ya kelaya a kasa, amman Me'ad bata hakura ba tayo cikin kitchen d'in da gudu ta wawuri doguwar wuka ta biyo Najma ....


Najma tayo hanyar waje tana ihu inda shima Fu'ad ya biyota ya riketa gam sai ga Sajida tashigo gidan a matukar firgice takaraso Me'ad ta tsaya tana haki wallahi sai na kasheki .....
cikin kidema Sajida ta sake motsosu zuciyarta na wani irin mahaukacin bugu take tambayar Me'ad abinda ke faruwa "sajida nashiga uku wai agabana Fu'ad yake rokon wannan yarinyar da ta taimaka ta aureshi.


"ke Me'ad Sajid ta furta da k'arfi jikinta na wani irin rawa zamuyi mummunar sa'bawa dake, ta yaya zaki dubi wannan abar kice Fu'ad d'ina danake burin mallaka matsayin miji zaice yana sonta wannan maganar ma ai karyace wallahi bazata'ba zama gaskiya ba, takarasa mgnr cikin daga murya .....


tunda Sajida tasoma mgn zuciyar Me'ad ta tsaya cak ta daina aiki na wunci gadi sakamakon sakon da kunnuwana suka jiyo mata daga cikin bakin Sajid, idan dai kunneta ba karya ya jiyo mata ba fu'ad dinta taji ta furta cikin yanayin na tashin hankali "to me hkn yake nufi itama sonshi take ko shine yake sonta kmr yadda yake son auren najma?


kusan minti goma tana tsaye jikinta na kyarma har lokacin tsaye kawai take bisa kafafunta babu wani wadatacen numfashi dake kai kawo ajikinta har sanda taji sautin muryarsa cikin kunnuwanta suna mata kuwa "kina mamaki jin abinda tace ko?


"kina mamakin jin furucinta ko akaina ?


"tabbas nasan zakiyi mamaki jin hk , har zuciyarki tayi kokari tsayawa ta daina aiki.. "kwanakin baya na tab'a gaya miki wata mgn alokacin da kika fasa wayata nace "idan kikaji wace nake waya daita zuciyarki zata buga sabida tashin hankali abun..to bakowa bace wace muke waya daita adaidai wannan lokacin face aminiyarki Sajida dake tsaye agabanki ayanxu , babu daren da zai zo Sajida bata kirani ba sannan babu garin da zai waye Sajida bata kirani ba sakoninta kuwa basu kirguwa acikin wayata domin son mallakar abinda yake mallakinki wanda ke , kike k'ok'arin bazantarwa bisa wani bazan dalili naki , gata nan ki tambayeta batace tana sonta ba , zata ajiye aikin da ke kika gagara ajiyewa dan dai kawai ta aureni gata nan ..
"Kin raina albashina Amman ni ban rainasa ba har ina yunkurin kara aure har biyu dashi..
Me'ad ta juyo zuciyarta kmr zata tarwatse ta fito daga cikin kirjinta, jikinta ne dauki rawa kar kar idanunta Kan kallon Sajid.


Sajida ta kalleta ido cikin ido tace "tabbas gsky fu'ad ya fad'a miki tunda muka had'u dashi a wancen lokacin naji ina mutuwar sonshi wanda Allah ne ya jarabeni da sonshi ada na boye amman a yanzu bazan iya boyewa kowa irin son da nake masa ba.
cikin rawar murya Me'ad tace "so fa kikace Sajida me yasa zaki min haka? "Ki rasa Wanda zaki so sai mijina?


"na aminta dake kece mafi kusancin abunda na yarda daita a duniya na kuma aminta daita "why why why sajida zaki min hk "so fa kikace kikayiwa fu'ad anya kuwa kina cikin haiyacinki?
"anya cutar hauka da mantau bata kama kwawaluwarki ba da zakice kina son mijina fu'ad? "Cikin kuka ta matso kusa daita tare da kamo hannuta"kice karya ne sajida bakya son mijina..


"Ta yaya zance banason shi aminyata?
"Alhalin ina son mijinki fu'ad so kuwa me tsansni son da ni kaina bazan ce ga daga inda ya fara ba balle insan inda zai tsaya, ina sonshi bazan ji shaka ko shayin furta shi akoina ba ko gaba kowaye saboda so ba karya bane, kuma bazan miki karya ba wallahi ina son fu'ad mijinki so na hakika wanda nake fatan zai kai mu gayin aure..


"sajida me'ad ta furt da karfi tana dafe kirjinta tare da furta kalmar inna lillahi wa inna ilaihi rajiun cikin matsancin damuwa sannan ta juyo tana fuskatsrsa idanunta cike da ruwan hawaye tace "da gaske ne abinda kunnuwana suke ji ayanzu "dan Allah fu'ad kace karya ne bakason yarinyar nan da tun sanda na fara sanyata cikin idanuna naji na tsaneta fiyye da komai sannan ka karyata min kallamar wannan maciya amanar abota ....


"uhm duk ina sonsu kuma aurensu zanyi kmr yadda na aureki ,aduk abinda ya faru kece silar faruwarsa"wallahi fu'ad bazaka ta'ba auren wannan yariyar ba haka zalika bazaka auri wannsn maci amanar ba takarasa mgnr tana juyowa tare da damk'ar wuyan sajida "mijina sajida mijina kike so?
" daman abinda ke ranki kenan shiyasa kullun kike hanyar zuwa gidana da sonji halin dayake ciki .......?
"shiyasa kullum kike adduar samun miji irinsa ta a she sonshi kikeyi ta d'auketa da wani gigitaccen mari wanda yasa taga gilmawar wasu taurari ko numfashi sajida ta gagara yi yau zan kasheki so that nima na hakura da duniyar gabadaya.


a gigice fu'ad yayi kanta yana kiran sunanta "wai kin haukace ne ko me da zaki dinga neman kasheta "eh na haukace maciya amana kawai sai Allah ya saka min na barku da fitowar Rana da faruwarsa .. ..
ta sake dauke sajida da wani Marin gabadaya tagama birkicewa kallo daya zaka mata ka tabbatar da cewar bata cikin hankalinta ta wujijiga sajida da karfi wacce gabadaya numfashinta yagama tsayawa ,tsaye kawai take bisa kafafunta ,sannan tayi wani irin jifa daita , sajida tayi luuuuuuu zata fad'i kan dutse cikin zafin nama fu'ad ya banbare najma dake makale ajikinsa ya kai hannunsa zai tarota ,a matukar tsawace tace "kar .......kar ta 'bata fu'ad Wallahi idan ka sanya hannunka ajikinta zan aikata abinda sai kashiga uku .... cak ya tsaya jikinsa na rawa. Yana kallo Kan sajida ya bugi da dutse kara daya tayi bata sake motsawa ba .


Ta wawuri wukarta da subuce ta rike gam kana tace "ke kuma karamar yar iska tayi mgnr da iyakacin karfinta har sai da najma ta zabura ta zura aguje tsabar tashin hankali data riski kanta ciki ."tsaya Dan ubanki tambayarki zanyi kafin na yankaki da hanuna, kuma kinsa idan na yankaki na yanka banza saboda babu abinda za'a yi kasancewarki mara galihu, ina son ki gaya min yaya kike jin mijina aranki kema kina son shi ne kmr yadda wannan sumammiyar ta fad'a....?


Najma tayi saurin girgiza kai idanunta cike da ruwan hawaye "ki bud'e baki stupid ki gaya min kina son mijina zaki aureshi kamar yadda yace "wallahi tallahi aunty banason shi ko kad'an Dan bamu dace da juna ba
Ni iyayena talakawa ne Dan haka zan auri irina bazan ta'ba auren mijinki ba duk runtsi ..
"yi min shiru Dan ubanki munafukar Allah kasheki zanyi in kuma kikaga ban kasheki ba to kwanakin ne bai cika ba tana gama maganar ta zabura ta sake yin Kan najma rike da wukar tayi mata yanka yafi biyar a hannunta Amman Dan azabar naci take rike daita sai alokacin fu'ad yayi karfin halin daka mata tsawa da cewar "kawo wukar nan tunda naga abun naki ya zama iskanci ga wata kin sumar kina kokarin kashe wannan ,yana mgnr yana takowa zuwa inda take tare da kokari son kwace wukar hannunta "fuad kada kazo wajena Dan kai nayi nufi ba wannan munafukar ba zan kashe kowa a huta Dan bansa amfanin badi babu rai ba bata sauraresa ba ta sake nufar najma cikin zafin rai ta sameta a gefen kafad'a ai kuwa nan da nan jini yasoma zuba.
fu'ad yayi saurin dosar wajenta bai tsaya wata wata ba ya fixge wukar yayi jifa daita saman zink sannan ya wanketa da wani mari ta fashe da kuka tare da durkushewa kasa bisa gwiwowinta " Dan abinda ya faru daita ko acikin mafarki bata ta'ba zaton zai faru ba fu'ad yayi mata wannan cin fuskar akan wasu banzaye ahankali cike da matsanancin sanyi jiki yakarasa gareta inda take durkushe tana kuka yasanya hannuwansa duka ya d'agota yana share mata hawaye, rungumeta yayi ajikinsa tsam yana Dan dukan bayanta Amman ina kuka take sosai , yayinda har lokacin sajida ke kwance sume akasa babu alamun numfashi atare daita ,cike da bakinciki mara misaltuwa tasoma kokarin barin jiknsa "fuad ka cuceni ka cuci rayuwata , "me na maka dana cancanci wannan wulakanci da tozarcin ?"yar aikina da aminyata kake yunkurin aure alokaci daya.."duk Akan aikina wanda shine rufin asirinmu ..."am really sorry love I didn't mean to hurt you Amman.....


"Banason jin komai daga bakinka daman ka gaji dani har kana wulakantani tare da yunkurin sakina, am ready for it now "ka sakeni domin zanfi bukatar saki akan na zauna ka auri wannan abar da tare da wannan maci amanar "bazan iya sakinki ba me'ad da zan sakeki da tuni a wuce gurin ni dai plz ki natsu ki dawo haiyacinki koda ban auri sajida ba kibarni na auri najma bawai ina son yarinyar bane hk kawai take bani tausayi..


suman tsaye tayi agurin jikinta na sake d'aukar rawa kmr wace aka jona mata wutar lantarki idanunta sukayi wani irin canzawa "dont don't repeat it coz it's not possible, how can this possibly ka auri wannan to ka kaita ina bakagani fu'ad juya ka kalleta up and down she's not your type Amman tunda zuciyarka ta aminta bari na aunata barzahu takaraso inda najma ke tsaye tana kirma tana gama karasowa ji kake tasssss tassss saukar mari dama da hagu tasoma neman abinda zata buga mata. idanunta ne ya sauka akan wani karfi wanda duka daya idan tayiwa najma dashi tabbas zata tashi aiki .
gadan gadan tayi gurin karfin ta d'auka fu'ad yayo kanta "plz me'ad karki buga mata.....
gocewa tayi bata bari ya kai hannunsa jikinta ba , da sauri ta nufi Kan najma daidai lokacin da direban nasreen yasanyo hancin motarsa cikin gidan idanunta ya sauka akan abinda momy'ta ke shirin yi da sauri tun direban bai gama daidaita motar ba ta sanyo kafafunta waje ta kwaso aguje tana "furta momy karki buga mata plz ai bata gama rufe bakinta ba me'ad ta daga karfen sosai da iyakacin karfinta zata bugawa najma..
nasreen ta tsaya cak tare da rufe idanunta saboda tsoro ta saki wata razananniyar kara sai gata tana kokarin yin kasa da sauri me'ad ta saki karfen hannunta wanda a sauka akan kafar najma itama ta saki kara har da fitsari.
aguje me'ad da fu'ad sukayo Kan nasreen fu'ad ne yayi nasarar isa gareta ya tallafota zuwa jikinsa ya rungumeta yana kiran sunanta, itama me'ad jikinta na rawa take kok'arin amsarta daga hannunsa "barmin yarinyarta karki k'arasa kashe min ita ........


Mmn sudais ce
[11/3, 8:29 AM] El~hajj: 💗💗💗💗💗💗
'YAN CINKI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗


~NA~


*AYSHA A BAGUDO*


~DEDICATED TO~
FAIZA HAMMADU BARAU
(YAR NUMAN)


Page 76


........ wani irin k'ara ta saka tare da d'aura hannuwanta duka saman kanta "shikenan tawa tasameni nasreen Dina zata mutu tabarni ...."wayyohlly nasreen ki taimaki mamanki ki tashi karki ki mutu kubarni cikin wannan halin damuwar danake ciki ,idan kika mutu wazan kama naji dadi? "wayyohlly Allah,"nashiga uku nah ... "help me to carry her to hospital this man, ka tashi ka wani zauna kana kallonta saboda kasan idan ta mutu baka da hasara zaka kuma samun madadinta ni kuwa fa wazan kama...?
a rud'e fu'ad ya d'auki nasreen da bata numfashi ya sa'bata akafad'arsa yasoma tafiya daita cikin sauri sauri, me'ad ma ta mike azumbur ta biyosa abaya rike da gefen rigarta tana wani irin kuka me ta'ba zuciya.
A haukace ya isa inda motarsa take parke ya bud'e gidan baya ya kwantar daita, me'ad tayi saurin shiga ta d'aga kanta ta zauna ta meida kanta saman cinyarta tana wani irin kuka jikinta banda kirma babu abinda yake ,shi kuma ya zagaya cikin sauri yashiga gaban motar ya zauna ya kunna motar yana mai danna hon da karfi ........
me gadin gidan da tun sanda rikicin yasoma faruwa akan idanunsa yashige d'akinsa ya boye ya leko ta window, ganin motar fu'ad ne yayi saurin fitowa ya bud'e masa get sannan fu'ad ya figi motar aguje ya bar gidan .
wani irin gudu yake shararawa akan titi wanda yaja hankalin mutane dayawa kansa ,domin duk wanda yaga irin gudun dayake sai ya tsaya yabi bayan motar da kallo, cikin lokaci kankani ya isa asibiti tun bai gama daidaita tsayuwar motar ba me'ad ta fito jikinta na rawa tana ihun kiran nurse....nurse!! shima ya fito a kid'ime batare daya tsaya rufe motar ba, ya sake d'aukar nasreen dake kwance babu alamun numfashi atare daita.
sautin muryar me'ad yasa
wasu daga cikin likitoci fitowa da hanzari suna tura gadon marasa lfy domin sunsa duk me irin ihun nan hk a matukar bukace yake da taimako,batare da 'bata lokaci ba aka kwantar da nasreen.
kai tsaye d'akin likita aka nufa daita aka akwantar daita akan gado sannan aka soma bata taimakon gaugawa ,likitoci kusan guda biyar ne suka rufa akanta domin k'ok'arin dawo da numfashinta ,wanda da kyar aka samu numfashinta ya dawo daidai sai dai bata farka ba.
Yayinda fu'ad da me'ad gabadayansu sun fita haiyacinsu ,sai zariya suke suna kai kawo a reception, most especial me'ad da hawaye yaki tsayuwa acikin kwarnin idanunta, kuka take sosai kmr wace akace mata tarasa nasreen din, ahankali fu'ad ya waigowa gefen datake zariya tana kuka ya tsura mata ido yana duban yadda gbdy ta gama birkicewa ta hargitse ta dawo abar tausayi ,matsalarta kenan a duk sanda nasreen ke cikin wani hali gbdy zata rasa sukuni da kwanciyar hankali Amman ta zauna domin kula daita da lfyr ce bazata iya ba ...
ahankali ya d'auke idanunsa akanta had'e da Jan tsaki... shi kansa cike yake da matsanancin fargabar abinda likita zai fito ya sanar musu,cikin hk suka hango fitowa wata nurse daga d'akin da'aka kwntar da nasreen ,gbdy sukayo kanta "how is she?
suka furta atare cike da matsanancin tashin hankali?
"she's feeling better now ta basu amsa atakaice cike da tausaya musu sannan tacigaba da mgn "doctor is already attending to her, Dan haka kusamu natsuwa ku kwantar da hankalinku InshaAllahu babu abinda zai faru da yarinyar ku....."you said doctor is with her inji cewar fu'ad?"haka ne likita nabata kulawa just keep praying for her, everything will be fine okay.
sannan ta barsu tashiga wani d'akin opposite dinsu.
suna nan tsaye ta sake dawo ta wucesu cikin sauri tashige d'akin .
me'ad ta k'arasa jikin bango ta d'aura kanta tana wani irin kuka ..., sai alokacin abubuwa suke dawo mata daki daki , "sajida aminiyarta, aminiyar datafi yarda daita a duk cikin aminanta, wai itace yau aka wayi gari take son mijinta har take burin mallakar aurensa, wannan wace irin cin amana ce ...?
"Sajida kin cuceni kin ci amanar yarda da amince dana miki ,kin cuceni kin yaudareni, kin ha'inceni.. Amman nasan Allah bazai barki haka ba ,da yarda Allah sai allah ya nuna miki illar cin amanar wanda ya aminta da dake , matukar yarda da na miki ta tsakani da Allah ce sai Allah ya nuna miki atafin hanuna, saboda daidai da rana daya ban ta'ba tunanin zaki yi min hk ba ,na yarda dake kin cutarda dani ...na aminta dake kin ha'inceni "me na miki kika za'bi ki min haka?
"Duk duniya ki rasa wanda zaki so sai mijina..kuka take sosai tana maganar ashe har maganar ta fito fili batasani ba .
Tausayinta ne yashiga ratsashi ,da bin lungu da sako na sansar jikinsa , jiki a sanyaye yak'araso zuwa inda take ya kai hannunsa ya dafa kafad'arta, da sauri tayi wata irin juyowa tana kallonsa cike da zallar tsana da 'bacin rai sannan ta cire hannunsa tayi jifa dashi "karka sake kai hannunka jikina mayaudari maci amanar kauna.......abinda ta iya fad'a kenan ta bar gurin zuwa harabar asibiti tana kuka kmr wata zautaciya..." yau tazo mata da abubuwa daban daban wanda kowane daga cikinsu akwai d'aci da muni gareta, mijinta ke son me aikinta da aminiyarta.... alhalin tana raye bata mutu ba wannan abu da matukar ciwo .."why fu'ad ?"ban cancanci hk daga gareka ba ,bansa zaka min haka ba ,Amman tunda wannan shine besty solution dakake ganin zaka d'auka akaina I will live you for them wallahi na hakura da kai nabar musu kai ta karasa mgnr tana kuka ahankali ta durkushe kasa tare da d'aura kanta saman gwiwowinta tacigaba da kuka .....


Can gidan kuwa najma taci kukanta kmr ranta zai fita da kyar tasamu ta yunkura ta mike tsaye tana d'ingisa kafarta da k'arfe ya saukar mata kai, tasoma tafiya jikinta na karkarwa ,kai tsaye hanyar cikin gidan ta nufa inda tashiga ta d'auki kayanta kwaya daya dake cikin bakar leda ajiye, har lokacin hawaye take sharewa ita bakincikinta bai wuce yadda zatayi da rayuwata ba ,domin a matukar tsorace take da halin data ga me'ad din take ciki , gara ta gudu tun bata dawo gidan ta kasheta ba , kmr yadda tayi niyya ba.
ahankali ta fito harabar gidan inda idanunta ya sauka akan sajida dake kwance kmr gawa, nan da nan hankalinta ya sake tashi sai lokacin ta tuna yadda akayi take kwance cikin wannan halin, girgiza kanta tayi tana takaicin hali irin nata nacin amanar aminiyarta datayi, ta isa inda me gadi yake tsaye tare da direban nasreen yana labarta masa abinda ya faru akan idanunsa, ta nuna musu inda sajida ke kwance"ku taimaka mata Dan Allah karta mutu mushiga uku ,duk da ni dai tafiya zanyi yanzu .
sai lokacin hankalinsu ya kai gareta ai kuwa da sauri me gadi yaje dibo ruwa shi kuma direba ya isa gareta yana dubanta atsoroce, daidai lokacin da me gadi ya kawo ruwa

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads