Header Ads
Showing 147001 words to 150000 words out of 163596 words

Chapter 50 - YANCNKI Book Complete by Aisha Bagudu.txt

Ads the beginning of article before Image

02 Jun 2024

1326

Ads at the middle of Article

ta Mike tsaye jikinta na rawa Dan haka kawai ta kasa samun natsuwar zuciya.
Suka fito atare cikin sauri suka nufi parlour'n bakinsa inda nan tashin hankalinsu ya ninku sakamakon Suna shiga sukayi mugun gani da dady kwance cikin jini male Male ta hanci ta baki gbdy jikinsa jini ne .


mumy da suhailat suka fasa ihu atare sukayo kansa suna girgiza shi da kiran sunansa, Amman ina babu numfashi ajikinsa cike da matsanancin tsoro suhailat tayi saurin ta juya ta nufi hanyar fita tana kuka ta bar mumy durkushe gaban dady.


Biyu biyu suhailat ta dinga taka matattakala har tashiga d'akinta, ta d'auko wayarta jikinta na karkarwa ,tasoma neman number likitan dady ,sannan ta juyo tana tafiya cikin sauri sauri doctor na d'auka tasoma masa bayanin cikin kuka yace "okay gashi nan zuwa sannan ta juya a matukar gigice ta koma parlour'n dady wanda zuwa lokacin mumy ta kwance d'aurin da'akayi bakinsa .
suka tsaya cirko cirko akansa suna kuka .


cikin minti goma doctor ya k'arasa yayi parking din motarsa yashiga bangaren da suhailat tagaya masa suke.


Mutuwar tsaye yayi lokacin da idanunsa ya sauka akan dady dake kwance murya suhailat ce ta dawo dashi daga buguwar zuciyar data samesa alokaci daya yakaraso ya ajiye kayan aikinsa yana cewa mumy ta matsa yasoma duba dady da numfashinsa ke daf da ficewa daga gangar jikinsa, taimakon gaugawa yasoma bashi sannan yace dole sai sun dannga da hospital.
Cicibo dady sukayi suka sanyashi abayan motar likita momy tashiga bayan motar itama ta zauna ,suhailat kuma tashiga motar gida direba yajata sukar bar gidan.


Suna isa hospital akan d'ora dady akan gadon marasa lafiya dake tsaye abakin emergency zaman jiran karasowarsu , sauri sauri aka shiga turasa zuwa d'akin likita.


Likitoci guda biyar ne tsaye akan dady yayinda mumy da suhailat suke zariya a tsakanin dakin da aka shiga dashi suna kuka kmr ransu zai fita,cike da tashin hankali suhailat ta kira me'ad ta sanar mata da abinda ya faru cike da tashin hankali itama sanar da fu'ad , yace ta shirya su biyo jirgin safe.rabar kwana tayi zaune tana kuka da kiran suhailat domin jin yanayin jikinsa .


Da kyar likitoci suka samu numfashin dady ya dawo daidai , Amman kwanta kwata bai San waye akansa ba, har washegarin da mead da fu'ad suka iso.


tana ganin halin dady yake ciki ta sake rushewa da wani sabon kuka.
Fu'ad ya matso kusa daita ya tsaya yana duban dady daya zamato tmkr matacce akwance bai San Wanda ke kansa ba , kallon second biyu yayi masa ya d'auke Idanunsa saboda kunburin daya ga fuskarsa yayi ga kuma hawayen na bin gefen fuskarsa gbdy ya jike pillow da kansa ke kai.


"mead kiyi hakuri kukan ya isa haka bari naje naga likita , na dawo kai kawai ta iya d'aga masa.


Zaune fu'ad yake yana tambayar doctor abinda ke damunsa , doctor yace "waye kai tukun saboda abinda ke rubuce a file dinsa sirri ne "karka damu doctor nima kmr D'an cikinsa ne kasanar min ,batare da bata lokaci ba doctor yasanar masa da komai cewar "anyi amfani dashi ne ta karfi da yaji wanda har sai da mukayi masa d'inki agurin sannan jininsa ya hau sosai Wanda muke tunanin Allah yasa cutar shayewar barin jiki bata kamashi ba.


Tunda doctor yasoma bayani tsigar jikin fu'ad ya dinga mikewa ,hankalinsa yayi mugu mugun tashi matuka ,yashiga tunanin su waye suka aikata wannan aika aika ga dady ?


"Sannan meye hadinsu dashi da har suka yi masa hk adai bayanan likita da yayi masa ya nuna dady bai ta'ba aikata wannan harkar ba ,ta karfin tsiya aka yi masa.


Tashi fuad yayi zumbur jikinsa na rawa ya fito daga office ,bai koma dakin da aka kwantar da dady ba ,kai tsaye inda yayi parking din motarsa ya nufa yashiga ya bar hospital din .


Sannu ahankali yake tukinsa har ya kai inda danja ya tsaidasu ,ya tsaya yana kallon ayarin motocin da suka yi jeri kwatsam idanunsa ya sauka akan matukin motar dake kusa dashi kmr a mafarki tabbas bazai mance da wannan fuskar ba duk da dadewar da yayi bai ganta ba ,yau shekara Goma kenan rabonsa daita ,daman yana kasar ne ?
Yayiwa kansa tmby adaidai lokacin da aka basu hannu fu'ad ya bi bayan motar da kallo take number motar tashiga kwalkwaluwarsa gidan dady ya nufa yasamu ganawa da mai gadinsa , bai samu wani isheshen bayani ba ,domin mai gadin cewa yayi "shi dai aikinsa abakin get ne kawai ya bud'e ya rufe bazai iya karar da abinda ya faru acikin gidan ba haka direbobin gidan duk sukace basu San komai ba haka ya baro gidan jikinsa a matukar sanyaye .


Daga nan babu inda fu'ad ya nufa sai ofishin 'yansanda ya yi musu bayanin abinda akayiwa surukinsa sannan yace yana bukarar ayi duk wani bincike agano ko suwaye suka da hannu gurin keta ma surukinsa hadi, yansada suka karbi wannan case din sannan fu'ad ya wuce hospital ya koma inda ya iske me'ad da suhailat da mumy sun yi jigun jigun sunci kuka sun koshe...


Yau kimanin sati daya kenan sai ankwatar sai antayar da dady, sam Sam baya motsa jikinsa an dai samu ya bud'e idanunsa yana kallon kowa Amman babu bakin magana cikin kankanin lokaci labari ya karad'e gari , Akan abinda yasamu dady .haka jama'a suka dinga zuwa duba shi mahaifin sajida ma yazo ,hatta ita kanta sajidar zuwanta biyu basu dai hada da me'ad ba .


Bangaren fu'ad kuwa hukuma ya matsawa sosai ta hanyar sakar musu makudan kudi domin asamu agano wad'an da sukayi laifin,a cikin kwanaki aka kama mai gadin gidan da direbobin Wanda kai tsaye basu fadi gaskiya ba ,sai da suka ci dukan mutuwa sannan mai gadi ,ya fadi wadan daya ga sun shigo gidan a wannan ranar har ma da yanayin daya gansu aiko police suka rufeshi da duka saboda batawa hukuma lokaci dayayi ,fuad ma kmr ya rufeshi da duka saboda Bakinciki.
daya gaya masa tun wancan ranar wata killa daya yanzu an dade da kama safwan.


Numbar motar safwan fu'ad yabawa yansada suka amshi number sannan suka baza jami'an tsaro domin kamo shi wannan da'ake zargi da wannan laifin .


A labarin da yansada
suka samu akan safwan, bakaramin hatsabibi bane yanzu ,abinda yasa yan sandar da case din ke hannunsu basu isa garesa ba ,suna dai kewaye dashi kasancewar har lokacin zarginsa Suke shiyasa ma suka kyaleshi ,Amman duk wani shige da ficensa da yadda yake kokarin gyara passport dinsa domin barin kasar suna sane .


Yau dai sunyi shirinsu domin kamo safwan bisa ga hujojin da suka samu na tabbacin shi ake zargi da aikata wannan laifin domin CCTV camera ta hasko musu komai daya faru,barin safwan a doron kasa kuskure ne babba ,domin duk Wanda ya aikata wannan babbar laifin to kuwa dashi da abinda yake gidansa sai sun zama turbaya.


Abdul shine shugaban tawagar ,yayi shirinsa sosai ya lodi duk abinda zai isheshe rigima dashi da yaransa ya nufi gidan kai tsaye.
Sun samu shiga cikin gidan safwan da taimakon fu'ad inda suka iske safwan zaune a parlour'nsa hannunsa rike da tabar wiwi tablet din dake gabansa giya ne kala daban daban ,gefe daya kuma taleburin caca ne da suke bugawa , garam sukaji an bud'e kofar a matukar zabure suka juyo gabadayansu a firgice safwan yayi ido biyu da fuad tsaye yaci kananan kaya espector Abdul ya dubi daya daga yaransa daya Dane window zai haura Abdul ya dubi mai shirin haurawa yace "kana haurawa zan tarwatsa kanka yanzun nan .


Safwan ya tafa masa yana dry Weldon gsky kayi mugun burgeni fa ,action dinka yayi ,sannan ya kalli inda fu'ad yake tsaye ya zuba hannuwansa duka cikin aljihun wandosa yana dubansa, yace "you again ?


"Lallai zaka san kacika mai shishigi cikin lamarina da gano ka inda nake ,har ma ka iya taso keyar yansada kazo gidana adaidai wannan lokacin, wad'an nan police din guda biyu baza su iya min komai ba, abinda zan aikata muku yanzu sai yafi wanda dalilinsa ya kawoku.
Yanzu abinda nake so da kai shine ,tunda ka kawo kanka gareni ahalin ina cike da bukatuwa da nemanka domin na sabautaka Kan shishigin dakamin na tsawon shekaru...


"Hukuncinka anan zan saka ayi maka abinda akayiwa surukinka wanda ya hassalaka har yayi nasarar tabo qunjinka ya hautsina tunaninka da kwalkwaluwarka ya kasa jurewa ,Zan lalata maka rayuwa da kaina "s k ,targent ku kamomin wannan mai dikakkiyar zuciyar na koya masa hankali, atare sukayi Kan fu'ad dake tsaye kmr wasu mayunta zakuna. .......


mmn sudais ce[11/11, 12:36 PM] El~hajj: 💗💗💗💗💗💗
'YAN CINKI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗



~NA~


*AYSHA A BAGUDO*


~DEDICATED TO~
*HUSAINA,D'ANLARABAWA (YAR PARTY ABBA GIDA GIDA)*🤩🤩


page 91


....wani irin kallon kaskanci fu'ad ke musu alokacin da suke takowa zuwa garesa, yana jin wani irin kwarin gwiwa attare dashi ,gaba d'aya yagama shiryawa yadda zai yi dasu idan sukayi kuskuren kai hannunsu jikinsa .
cigaba da kusanto shi suka yi suna mammatsa yatsun hannuwansu , sai dai tun kafin su k'araso garesa suka ji an kuraye gidan da harbe harbe, suna waigawa ta window, suka ga 'yan sanda runduna guda kewaye da gidan suna ta faman harbi, suna kuma k'ok'arin shigowa ciki.


wani irin mamaki ne yakama safwan,iya tunaninsa wad'an nan polisawan guda biyu ne kawai sai shi fu'ad din, a she ruf da dugu akayi masa bisa dole ba dan yaso ba yayi saranda da fasa niyyarsa ta farma fu'ad ta karfi da yaji...


ahankali ya kalli fu'ad da murmushi ya bayyana akan fuskarsa yace "ka tsira daga wannan tarkon nawa, sannan ka sake cin narasa akaina ,amman wallahi muddin ina raye sai na halakaka, bazan bari a yanke min hukunci ba,har sai na kasheka kafin kaga tawa mutuwar saboda nasan daga nan kisa ne hukuncina , yana gama fad'ar haka yayi baya da hannuwansa duka ya ciro wata karamar pistol da niyyar harbin fu'ad, sai fau!
wani d'an sanda ya harbe hannunsa, sai ga bindigar hannunsa ta fad'i kasa jini ya tsirtu yashiga tsiyaya, ya rike hannun had'e da sakin wata k'ara, take police suka zagayeshi yana makarkatar zugin ciwo, suka damke su baki d'aya, sai mota babu abinda ke bakin fu'ad sai godiya ga allah daya kubutar dashi daga hannun wannan bakin azalumin bawan mara imani.


haka dai suka isa police station aka shiga dasu baki d'aya domin tantance masu manya laifi .
andai samu safwan dumu dumu da laifin aikatawa dad'y fyade ta hanyar luwadi da kuma safarar kwayoyi zuwa kasashen duniya ,azabar da'a gana musu ta rana d'aya yasa safwan yace" ya tuba bazai sake aikata makamancin abinda ya aikata ba, amman duk da hakan bai hana shi samun hukunci daga hukuma ba, domin har kotu za'a turasu, safwan ya kalli fu'ad ya girgiza kanshi yana zubda hawaye a zuciyarsa yace "karshen rayuwata tazo kenan yana ji yana gani aka tura su zuwa kotu ,sai yanxu yake bakincikin halin daya tsinci kanshi yasan dai mafi kaskancin humunci shine d'aurin rai da rai .
fu'ad wanda tunda abun ya faru ya kasa samun sukuni har sai dayaji zance zuwa kotu ya sallami polisawa ya fice byn ya sake musu kyauta ta musamman bisa kokarinsu.


tun sanda me'ad tasan abinda ya faru da mahaifinta ta gaza samun kwanciyar hankali, taki kwantar da hankalinta fu'ad ne ke ta faman aikin rarrashinta data kwantar da hankinta komai ya rigada yazo karshe ,domin rayuwar safwan tazo karshe sai dai wani ikon Allah.


bangaren dad'y kuwa har lokacin yana karkashin kulawar likitoci, sai an kwantar sai antayar dashi ko d'anyatsan bai iya motsowa , magana yake son yi domin yiwa fu'ad godiya bisa kokarinsa garesa dan duk halin da'ake ciki yana ji ,amman babu bakin magana ,sai hawayen nadama dake tsiyaya daga ciki kwarnin idanunsa yana d'iga akan pillow da kansa ke kwance akai .
Allah sarki bai ta'ba tunanin hk zuciyarsa take ba, hakika ya zalinci ruhin dake tattare da alkhari.


tuni an tura su safwan kotu har an yanke musu hukunci kisa bakidayansu .haka akayi wannan shari'a kowa yayi farincikin da hakan wannan shine karshen safwan da mukaranbansa .


shi kuma dady yacigaba da samun kulawar data dace ,dan har an daina saka masa pampers din da'ake saka masa,a wannan lokacin likitoci suka fahimci barin jikinsa d'aya yasamu matsala dan har lokacin babu baki, ga wuyansa ya karkace bakinsa ma ya juye ala'mun dai cutar shanyewar jiki takamashi..
gabad'aya ragamar rayuwar gidan dad'y takoma hannun fu'ad da me'ad, duk wani abinda za'a bukata a gidan fu'ad ne wanda hkn ke sake saka dad'y jin kunya, kukan nadama kam yayi shi har babu adadi, a she ba ragamar diyarsa kad'ai fu'ad zai dawo ya dauka ba, har da ragamar gidansa. ...


**********

tafi suke cikin mota domin zuwa gidansu emran kmr yadda khalid yayiwa sajida alkwarin kaita gurin emran da mahaifiyarsa ta rokesu yafiya abinda tayi musu bayan sun isa gidan, aka tarbisu hannu biyu biyu batare da bata lokaci ba khalid da suka samu guri suka zauna yasoma zayyano labarin Abinda ya kawosu tun daga farko har karshe take sajida ta nemi gafararsu, mahaifiyar emran ta gafarta mata emran dai shiru yayi yana dubanta ya kasa cewa komai, arayuwa babu halittar dayake so kmr sajida,saboda itace first love dinsa dole ce kawai yasa ya rabu daita, amman ya zai yi da rayuwa haka Allah ya kaddaro masa ba zai yi rayuwa daita ba .
shi kuwa khalid wannan kallon da emran keyiwa sajida gabad'aya ya damesa zuciya ta dinga harbawa had'e tasoma masa, barin lokacin da sautin muryar sajida ta sake karad'e parlour'n inda take cewa "dan girman allah emran kace wani abu ,tun dazu kayi shiru kaki cewa komai, ni nasan na cutar da kai arayuwa ,kayi hakuri ka yafe min kmr yadda hjy tayi.. ..


wata uwar harara khalid din ya sakar mata wanda yasa take tayi dif da bakinta tmkr ruwa ya cinyeta tsabar tsoro .
ahankali emran ya bud'e bakinsa da kyar yace "na yafe miki Allah ya yafemana gabad'aya khalid nagama jin haka ya mike tare da dubanta itama ta mike sukayi musu sallama suka wuce ko acikin mota ma cika ya dinga yi yana batsewa,ko kallon Inda take baiyi ba illa tsakin da yayita ja yana dukan kan sitiyarin mota, ita kuwa sai murna take yau dai ta rage nauyi dake kanta amman data hankalta da yanayinsa tuni tasha jinin jikinta tashiga tai tayinta .


kai tsaye gidan mahaifinta ya nufa daita, sun ji dadin ganin juna yaushe rabon data sanyashi acikin idanunta tun randa khalid ya d'aukota bata sake ganinsa ba ,sajida na rike da hannun mahaifinta tmkr wata yarinya gani take kmr sun yi shekara da shekaru basu had'u ba, gabad'aya ta share khalid a yanzu ta mahaifinta take yi dady yayiwa Khalid "sannu da zuwa idanunsa na kan tilon diysrsa ..
hakika aure yakin mata, domin inba aure ba babu abinda zai hana alhji aliyu ya dawo da diyarsa kusa dashi saboda har yanzu yana begen ganinta kusa dashi ,
to amman babu yadda zai yi tunda ta wuce minzalin zaman gida. bayan sun gama gaisawa suka shiga hirar daga baya alhji aliyu yabada umarni akawo musu abinci aka jibge musu kayan tande tande da lashe lashe aiko sajida ta zage tana ci duk dubawar dazatayi idanun mahaifinta yana kanta wani nishadi take ji tmkr am mata bushara da gidan aljanna har suka gama tashiga d'akin aunty nadiya tabar dady da Khalid lokacin data dawo parlour'n
Khalid ya basu gurin domin ta zanta da mahaifinta shi kuma ya koma mota zaman jiranta, bayan fitarsa hira tabarke sosai atsakaninsu inda mahaifinta yake tmbyrta labarin aikinta "uhmmmmm ajiyar zuciya ta sauke "ai dady khalid yaki sam sam bashida ra'ayin matarsa taje aiki ni nama hakura da aikin nan "haka ma yayi daidai Allah yayi miki albarka ki cigaba dayiwa mijinki biyayya gidan aurenki shine rufin asirinki, yanzu zan baki check na million biyu ya janyo check book dinsa dake gefensa yasoma rubutu "ki rike a hannunki kada ki damu mijinki da bani bani, idan kuma da wani abu da kike so ki gaugauta sanar min ba sai kin tambayesa "nagode sosai dad'y Allah ya kara girma Allah ya barmin kai cikin koshin lfy "ina da burin yin business sai dai sai nagaya masa tukun idan ya amince zan sanar maka.
cike da murna da farinciki suka rabu da mahaifinta kmr karsu rabu.


akan hanyarsu ta koma gida taga basu d'auki hanyar gidansu me'ad ba ta dan juyo ta kalleshi gabad'aya tasa dalilin fushinsa, ta kai hannunta kan hannusa tace "yana ga ka d'auki wata hanyar ba gidan me'ad zamu ba? "ko mum
fasa zuwa gurin su me'ad ne? ta sake tamvayarsa zuciyarta na dokawa,
yayi mata banza ta sake yin magana "bazamu ba ya fad'a a hassale sannan yacigaba da mgn dan bazan lamunce kije kina wani 'bare 'bare ba da tsigar neman yafiya ba.
"kan bala'i ta furta acikin zuciyarta wanda bata san hkn yafito fili ba.


birki taji ya ya ja sannan ya gangara gefen titi yayi parking batare daya kashe motar ba "kan bala'i a ina kenan?
"wannan kalmar ta zamo ta farko kuma ta karshe dazaki furtata muna tare, dan bazan d'auki kina d'auke da gudan jinina kina kiran bala'i ba..
"kuma karya nayi bakiyi 'bare 'bare bane, har da wani kashe murya shi kuma tsohon maye sai wani tsura miki ido yayi yana kallonki kmr zai cinyeki, yasan yana sonki meyesa ya sakeki?


kirjinta ya dinga dukan uku uku jikinta ya d'auki rawa hankalinta yayi matukar tashi

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads