Header Ads
Showing 30001 words to 33000 words out of 163596 words

Chapter 11 - YANCNKI Book Complete by Aisha Bagudu.txt

Ads the beginning of article before Image

02 Jun 2024

1287

Ads at the middle of Article

ina zaka bayan gasu can, cangurin fa sukayi, ba itace me kaya ruwan d'aurawa ba?
"eh itace "mead dan Allah ki tsaya ita kuwa tafiya kawai take tana jan hannun sajida, "gsky fu'ad kyakkywa ne ajin farko amman me zai hana ki tsaya ki saurari wancan wata killa abokinsa ne fa.
"kinga da ala'mun magana yake son yi dake.


me'ad tayi mata banza sai janta take har suka shiga lift "ki daina turani mana, shi Wanda kike so ma bai san kina yi ba, ba gara ki tsayawa me binki ba, watakilla ma abokinsa ne ya taimaka ya janyo miki hankalinsa ,aguje malik ya biyosu yana ihun" jimana dan Allah ki tsaya minti daya abunki zan baki ta cikin lift sajida ta d'agowa fu'ad hannu wanda ya sake juyowa "sannu tana dariyar da za'a iya kiranta na farinciki "kibari mana sajida kina magana zai ta binki ne ya d'auka muma irinsa ne.ta fadi hkn ne a tunanita ko Malik sajida ta dagawa hannu, sajida tayi murmushi tana sake daga masa hannu.
" haba sajida meye hk ne? Karki manta fa watan gobe ne za'a yi bikinki.


"kinga bangane mgnrki ba nifa fu'ad nake d'agawa hannu ba wancan me bin namu ba "stop it sajida.. .." ki daina kallonsa dayawa da fa sadakin wani akanki "ki kyaleni nayita kallonsa tun yanzu kafin aurena bayan nayi auren shikenan... me'ad tayi shiru kawai takasa cewa komai har sanda lift ya tsaya suka fito da sauri me'ad janye da hannun sajida .
malik kuwa sai kokarin saukowa yake daga step domin ya iske su akasa .
yayinda fu'ad ke tsaye a inda suka barshe yana kallonsu batare da yayi yunkurin motsawa ba....


mmn sudais ce
[11/3, 8:26 AM] El~hajj: 💗💗💗💗💗💗
'YAN CINKI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗


~NA~


*AYSHA A BAGUDO*


~DEDICATED TO~
MRS ADAM
( YAR MUTAN KAGARA)


page 47 to 48


.....yana nan tsaye a gurin da suka barshi har sanda suka dawo suka samesa, malik ya dafa kafad'arsa yana fidda numfashi sama sama sannan yace "abokina kaga me'ad dina ko?" gsky yarinyar ta had'u iya had'uwa ,dan Allah abokin ka taimakeni ka tayani yakin shawo kanta,dan zan iya rasa raina akanta yakarasa mgnr yana kwashewa da dry....


on expecting malik yaji sautin muryarsa " Allah yasa ka mutu yanzu in har sai na tayaka yakin neman amincewarta sannan ya juya yasoma takawa ahankali ya bar malik tsaye, sake da baki yana kallon bayansa sai dai fuskarsa kunshe da dry ..kana ya juyo yana fuskartata kabeer "kungani ko zargina fa yana neman tabbata fu'ad son yarinyar nan amman miskilancinsa ya hanashi fahimta, amman ni nan zansashi ya fahimci ya fad'a tarko dan bazan bari yarinyar ta subuce masa ba.." tabbas zanceka hk yake,yana sonta, itama yarinyar da ala'mun ta kamu da matsanancin sonshi inji cewar sudais.


kabeer ya numfasa kana yace "kar dai ku manta da halin fu'ad, tunda bai ce yana sonta ba ku yanzu meye naku a ciki ?balle kai malik da kabi ka hakikance akan yariyar , ka dai bi ahankali kar ka je ka jefa kan cikin wahala shi dai fu'ad bai aikeka ba har gara ma kayiwa kanka yaki neman au...shigowar wasu costumer's ne yasa kabeer katse zance yaso garesu tare da kiran daya daga cikin yan dake kula gurin..


bangarensu me'ad da sajida kuwa tunda suka shiga mota babu wanda yayi kokarin yin magana kowace da abinda zuciyarta take kismamata akan fu'ad, har suka karasa gida jiki a sanyaye suka shiga parlour'n inda suka iske hjy Khadija zaune tana kallon labarai "momy sannu da gida.


"sannunku yammatana har kun dawo ?
"ina siyayyar da kuka fita yi?


sajida ta zauna jagwab akan kujera tana fuskantar momy "me'ad ta hana mu yi taba amsa da hkn tana runtse idanunta.


"bangane hausar ta hana ba?


" nan sajida ta gaya komai amman banda sunan fu'ad. momy taja numfashi da ajiyar zuciya atare sannan ta dubi inda me'ad take tsaye tana cizan lip's dinta "karki soma janyowa kanki tashin hankali kinsa dai an gama maganar aurenki da safwan jiran dawowarsa kawai ake... tun da momy tasoma mgn tayi yunkurin barin gurin dan zuciyarta baxa iya sauraran maganganunta akan safwan ba, wanda a halin datake ciki yanxu ta manta dashi balle wani magana da'aka tsayar a tsakaninsu.


dare yayi sosai yanayin garin yayi sanyi baka jin sautin komai da sautin komai sai na iskar garin dake kad'awa ahankali yana bin jikin bil'adam ciki kuwa har dasu sajida da me'ad da idanunsu ke bud'e ,babu wani ala'mun bacci acikinsu juyi kawai suke akan gado suna tunani rai daya wato fu'ad, sosai sajida ke zurfafa tunaninta akansa sam bata tsamaci kyawunsa da nagartasa ta Kai yadda tagansa ba,a zahirin gasky bacin me'ad tasoma furta tana son fu'ad ba, da tsab zata rusa zance aurenta da emran ,tayi yakin neman soyayyarsa tare da aurensa, amman kashi ....me'ad tayi mata tawayar da baxata iya kai kanta garesa ba ...... sam ranar sajida bata samu runtsawa ba, har gara ma me'ad ta runtsa da taimakon mafarkinsa daya kawo mata ziyara.
abu fa kmr wasa kullun mee'ad ta kwanta sai tayi mafarki fu'ad yana romacing dinta wani lokacin har saduwa daita, saboda zurfafa tunaninsa datake.


parlour'n gidan momy ta fito sanye cikin doguwar rigar har k'asa da madaidaicin hijab ,tana gyara zaman takardun dake rike a hannunta tare da kiran sunanta "mead..me'ad!!
ummi tayi saurin cewa "tana d'akinta bata fito ba tukun.
kai tsaye hanyar d'akin momy ta nufa tana cewa karfe takwas fa har tayi me'ad amman har yanzu kina kwance, koda tashiga d'akin kwance ta isketa akan gadonta kmr yadda tazata ,ta lullu'be jikinta da blanket me taushi , momy tak'araso har inda take kwance tare da zame bargon data lullu'ba dashi "me'ad kitashi mana karfe takwas fa tayi "uhmmmm momy bacci nake ji tayi mgnr tana mika ...ki d'aure ki tashi ....
tashi zaune me'ad tayi idanunta a runtse "maza tashi mana wannan fa shine karo na biyu fa dana dana shigo tashinki bazan sake dawowa ba kin san dai kina da interview yau ko?
nima na shirya zuwa aiki momy ta juya abunta idan kingama ga abincinki can har ta kai bakin kofar taja ta tsaya tace "me'ad ...."na'am momy ya sunan yaron ?
da sauri ta bud'e idanunta sosai sannan tace sunan wa kenan momy ?
"sunan yaron dakika jarabar so har kika kwana kina marfakinsa.


runtse idanunta tayi ta sauko daga kan gadon zuwa kan doguwar ta kishingid'a ,sannan tace fu....... ad "uhmmmm idan na dawo mayi magana akanshi ,sai na dawo dan gsky na kusan makara ki hanzarta tashi.


goshinta ta dafe tana tunanin, "yanzu son fu'ad hk zai mata ?


ta dad'e zaune kafin daga baya ta mike tashiga wanka shap shap ta fito sanye cikin riga da siket na atamfar super exclusive me zanen fuluwa ja da baki a had'e wanda ya d'an kamata ajiki kad'an, kanta babu d'an kwali kasancewar bata fiyye son d'aurawa ba sai karamin bakin mayafi data yane kanta dashi ta fita cikin takunta na yanga da nuna ita yar wani ce ta shiga motarta oil and gas dake cikin apapa.


koda ta isa ta iske dubbanin mutane suna jira amman da zuwanta kiran waya kawai tayi sai gashi an bada umarnin tashigo kai tsaye batare da bata lokaci ba ta fito wanda fitowarta sai days bugar da zukatan tarin mazan dake zaune agurin ciki kuwa har da fu'ad dake tsaye rike da takardun neman aiki, zuciyarta taji tayi wani irin bugawa da karfi ahankali ta d'ago idanunta kmr ance ta waiga gefen hannunta na dama taganshi tsaye shi da wani da batasan kowaye ba, kallo daya tayi masa taji zuciyarta ta sake bugawa kmr yau ta fara ganinsa ,duk da bawai yau ta fara daura idanunta akanshi ba, sai dai kusancin na yau ya sha bambam da sauran lukuta wani irin kyakkyawan kallo take masa, yau gashi a gabanta ba daga nesa nesa ba, shima gabansa ne ya fad'i sakamakon ganinta dayayi a aininhin shigarta ta hausa fulani.


ahankali take daga kafafunta har zuwa office din alhj Ibrahim wanda yake shugaba ga maikatan kuma aminin mahaifinta, bayan sun gaisa ya tambayeta lafiyar mutanen gidansu, tace "duk lfy atakaice sannan akabata aiki wanda zata dinga daukar albashi me tsoka batare da wani interview ..kusan minti biyar tana zaune alhj ibrahim ya d'ago yana dubanta sannan yace "ko akwai wani abu ne, shiru tayi na minti biyu kana tace akwai "ina sauraronki ya fad'a tare da meida idanunsa kan tarin takardu dake gabansa "akwai wani danake son ka taimakawa kabashi aiki a ma'aikatar nan.


"yana ina?
" shine kika tsaya jan maganar abinda zaki fad'a da confidence ai ba mutun daya ba diyata ko mutun goma kike son a d'auka za'a d'auka masengen sa ta aika yaje ya shigo da fu'ad, wanda shigowarsa yayi daidai da tashin da alhj ibrahim yayi, yakaraso shigowa sanye da suit da bakin glass frada a idanunsa take office din ya gauraya da kamshin turarensa kafafunsa rufe cikin cover shoe baki ,taja masa kujera tana nuna masa gurin zama amman yaki zama "ka zauna zaka samu aiki karkashin jagorancina matukar shi kazo neman ,idan kuma kaki zaka karad'e garin nan batare da kasamu aiki ba saboda mu 'yan alfarma gama maganarta keda wuya ya juya kawai batare yace mata ko uffan ba, ta mike da sauri tabi bayansa tana kiran sunansa "fu'ad ka tsaya zan saka abaka aiki me mahimmaci .
amman ina ko juyowa baiyi ba har ya isa inda sudais ke tsaye yana jiransa ya rike hannunsa "zo mu wuce kawai ya iya furtawa "ka tsaya mana bakaji tana kiranka bane ?
kana ji fa taimakonmu zatayi "banason duk wani taimako daga gareta kazo muje kawai idan km baxaka ba na wuce.... ya fixge hannunsa cikin nasa "to bazani ba shekara nawa ina neman aikin bansamu ba yau zamu samu amman kake girman kan banza ...


fu'ad ba tsaya ba ballanatana ya juyo gareta yacigaba da tafiyarsa shi kuma sudais yakarasa gareta "ranki ya dad'e kiyi hakuri hk halinsa yake, shegen girman kan tsiya shi ba... "dakata karka soma furta kalmar 'batanci garesa, daya tsaya har kAi zaka iya cin albarkansa tana karasa fad'ar hk ta juya fuuuuuu zuwa inda tayi parking din motarta ta figa aguje, mutane kuwa sai zagin fu'ad suke akan wasa da damarsa da yayi.


tana barin oil and gas kai coffter coffe ta zarce inda suka saba had'uwa da sajida ,dukkaninsu shiru sukayi suna kallon junansu bayan labarin da me'ad tabata akan abinda ya faru atsakaninta da fu'ad. "me zai hana ki hakura dashi, tunda yaki saurararki.


"i can't sajida ina son shi bansan ina son shi ba sai yau dana yi masa kallon gani ga shi, ni dai ki tayani adduar samun shi kawai dan matsawar ban auresa ba sai dai na mutu babu aure ..
"all the same inji cewar sajida "what?
"no babu komai suka cigaba da zance fu'ad batare da sun kai coffen da'aka kawo musu bakinsu ba tsawon lokaci suna zantawa sannan suka mike atare daga nan gidansu sajida suka nufa ,trafic ya kamasu suka tsaya inda malik shima yana d'ayan gefen hagu bai lura dasu ba sai danja tabasu damar wucewa sannan ya gansu, nan fa yashiga binsu akan lefan dinsa .


kmr ance sajida ta kalli mudubin gefenta ta hangosa yana daga musu hannu, leko da kanta tayi domim tabbatar dashi din ne "me ad duba madubin gefenki kiga wannan d'an jagaliyar fa mu yake bi inji cewar sajida "kai dan Allah tayi mgnr tana dubawa ,"tabbas mu yake bi amman nasan yadda zanyi maganinsa k'ararsa zan kai gurin uncle ya jefa min shi cikin magark'ama ayi masa dukan tsiya haba dai ke kuwa kamar shi yace kar fu'ad yasoki takarasa mgnr tana dry a daidai lokacin da suka iso kofar gidansu sajida shims yaja ya tsaya tare da parking din mashin dinsa suna fitowa daga cikin motar ya iso garesu yana cewa jimana me'ad. nasan kinsani amman kike pretending kamar bakisani ba ...dau dau ta d'auke shi da mari "how dare you calling my name? yayi saurin dafe kuncinsa yana kallonta.


"me ma yasa kake bina? "kasan ko ni wacece?
"dan jagaliya irinka kake bibiyata "waye ubanka a duk fad'in garin nan ?


jiki a sanyaye yace" daman bawani abu bane amman idan baki tunani ba, ni ne malik wanda muka had'u agurin ciro kudi ..


"and so what?
"jibeka kawai wani wawa dashi ,ko iya fitar da maganar bai iya ba,da muka had'u sai akayi yaya?


"daman kin yar da diary dinki ne shine fa na amsa gurin abokina fu'ad dan nasan shi ba bazai ta'ba biyoki domin yabaki ba ,shi nake ta ajiyarsa kullun ina son nabaki amman bakya saurarata..


"inna ilaihi wa inna ilaihi rajiun ta furta acikin zuciyarta ...........idanunta a kansa


mmn sudais ce
[11/3, 8:26 AM] El~hajj: 💗💗💗💗💗💗
'YAN CINKI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗


~NA~


*AYSHA A BAGUDO*


~DEDICATED TO~
MRS ADAM
( YAR MUTAN KAGARA)


page 49 to 50


....kallon kallo suka shiga yi atsakaninsu duka uku sajida me'ad malik, shiru me'ad tayi tana kallonsa batare da ta sake yunkurin cewa dashi komai ba ,sai dai gabadaya nadama tattare da kunyar abinda tayi masa a yanzu ya kamata tare da raunata wani shashi na gangar jikinta," ta wulakanta mafi kusanci ga zuciyarta bisa ga mummunar d'abi'arta...."me yasa tayi saurin marinsa?


"why why why!!! me'ad?


"why did you slap him..?


tana nan tsaye jikinta na rawa har malik yakaraso zuwa inda take tsaye jikinta nacigaba da kyarma ya miko mata diary dinta ......nadama ce fal dankare da zuciyarta "hakika ta cuci kanta ta cuci rayuwarta ba zata ta'ba yafewa kanta abinda ta aikata masa ba matsawar yayi silar rasa fu'ad dinta....."ki amsa ko nabawa kawarki ne?
jin sautin mgnrsa yasa tayi saurin dawowa cikin haiyacinta domin natsuwar tasoma barin gangar jikinta, kallo daya zaka mata kagane kalar damuwar datake ciki.
sai daya sake mgn sannan jiki a sanyaye tasanya hannuta ta amshi diary dinta, shi kuma ya juya tamkar wanda kwai ya fashewa aciki yasoma tafiya , har ya kai gurin mashin dinsa yana shirin hawa yaji sautin muryarta ahankali "tsaya dan Allah sannan tasoma kok'arin takowa zuwa inda yake, jikinta a matukar sanyaye .


muryarta na rawa tace "dan...dan girman Allah kayi hakuri ta furta hkn tana mai runtse idanunta kasancewar wannan shine Karo na farko data bai wa wani mutun hakuri ,bayan iyayenta da suka kawota duniya "kayi hakuri ta sake maimaita kalmar muryata a raunane tare da bud'e idanunta fess akansa tana kallon yanayinsa da gbdy ya sauya, a yanzu dayake gabanta ganin take tamkar fu'ad dinta ne tsaye a gabanta cikin matsanancin damuwa , "hakika nayi abinda bai dace ba ,da rashin kamata gareka,
tun ranar farko dana soma ganinka a gidanmu nayi tunanin kmr nasan fuskarka amman alokacin na kasa tuna inda nasanka, sannan lokacin dana ganka tare da fu'ad a boutiq shima ban tantance alakarku dashi ba amman dai kayi hkr dan Allah.


" babu komai ,komai ya wuce Allah ya kiyaye na gaba, hk daman rayuwar take ,da nabi shawarar fu'ad da ban jawo wa kaina wulakanci ba, domin babu abinda ya kai wulakanci kmr a tsinkaka ta hanyar mari..... ...amman babu komai "me'ad yakira sunanta ,nasan kina mutuwar son abokina fu'ad duba ga yanayin nadamarki bayan kinsa alakata dashi, amman shi mutun ne me matukar kamewa ,kai tsaye hk bazai ta'ba fuskantarki ba ....


"nasani ....nasan da haka amman ko zaka iya taimaka min plz takarasa mgnr muryarta na craking ?
domin zan iya yin komai akansa ,"da fari dai ka taimaka min da number wayarsa tare da sake bashi hakuri.
"sajida plz ki matso kusa mana ki bashi hakuri kema bawai ki wani ja kin tsaya kina kallonmu ba.


"me zance masa me'ad?


"me kike son nace masa after kingama aikata son ranki ?
"i think kin bashi hakurin kuma yace ya hakura.


"eh amman ni dai kice masa wani abu dan Allah har yanzu akwai damuwa a tattare da shi.
"dole kuwa kiga damuwa atare dashi me'ad , bashi ba koni kika karewa kallo zakiga ala'mun hk atare dani "ta yaya daga ambatar sunanki zaki maresa?
" tun ranar farko daya kira sunanki na gaya miki definitely wannan mutumin yasanki wani guri amman kika nuna min sam ba hk bane yanzu wa gari ya waya?


" komai sai kin saka zafin rai aciki, sosai sajida tayi mata fad'a ta inda take shiga bata nan take fita ba har sai da malik ya nuna abar zance ya isa hk "kuma har ga Allah komai ya wuce daga karshe ya karanto mata number fu'ad bayan tayi tsore, tace yabata nashi yabata sannan ya wuce .


" a she dai mutumin kirki ne nake masa wani irin kallo ta furta hkn tana kallon bayansa .. .......
juyawa sukayi zuwa cikin gidan suna shiga d'akin sajida tasoma neman layinsa amman kiran duniya tayi bai d'auka ba haka takarar da wunin ranar akan kiran layinsa bai d'auka ba.


shi kuwa malik a sanyaye ya karaso gida, duk da har cikin zuciyarsa yana jin abinda me'ad tayi masa ya wuce, amman gangar jikinsa takasa hakurin hk, ganin yanayinsa yasa sudais dake bawa kabeer labarin abinda ya faru a oil and gas a safiyar yau din nan ya karaso gurinsa yana tmbyrsa, shima kabeer yazo ya tsaya dayan gefensa "lafiyarka malik?
" me yasameka duk ka dawo wani iri hk? yayi masa tmbyr ajere. naunayen ajiyar zuciya ya sauke tare da gaya musu abinda ya faru har zuwa Number wayar fu'ad daya bata, dan basa boyewa junansu komai, daga karshe yace "karsu sanarwa fu'ad saboda ya sha ja masa kunne da gargadin

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads