Header Ads
Showing 18001 words to 21000 words out of 163596 words

Chapter 7 - YANCNKI Book Complete by Aisha Bagudu.txt

Ads the beginning of article before Image

02 Jun 2024

1283

Ads at the middle of Article

daya numfasa sannan yacigaba.


"kaine shugaba ga iyalinka, you will remain the head forever .


fu'ad ya gyara zamansa cike da jin dadi abinda boss dinsa ya fad'a kana yace" gabadaya ni ne nayi kuskure ,kuskurena bai wuce na aureta danayi da wannan mugun halin nata ba ,saboda tun lokacin da muke soyayya daita nayi realized tana son controling dina, har zuwa sanda mukayi aure , wanda lokacin komai yayi warse ,saboda sai tana zaune sai kaji tace "na miko mata remut ko na d'aura mata ruwan zafi zatayi wanka ,ko ta aikeni ,ni kum abinda nayi believe shine duk cikin soyayyar da mukeyi ne , a she wulakantani take son yi shiyasa ta nacewa aurena.


"sai dai zuwa yanzu idanuna sun bud'e, idanun da zan nuna mata sai tayi mamaki " dan bazan sake yarda da wannan iskanci ba ,yanzu hk idan na koma gidan zan tabbatar mata da nine mijinta ,abinda nake dashi shi zamuyi manage muci tare koda kuwa 10k nake makig a duk wata gud ,
ko 100k idan bata yarda da wannnan tsarin ba wallahi sai dai tayi gaba dan bazan iya cigaba da zama daita ba na gaji ..


"matakin da kake son d'auka, shine daidai amatsayinka na mijinta, domin barin dakayi tana taimakawa acikin al'amura rayuwar aurenku, shi yasa ta rainaka dayawa ,kaga mata sam ba'a sake musu dayawa sai su nemi su rainawa mutun wayo, sannan karka zauna komai mace ce zatayi agida, Duk k'ank'atar albashinka kayi amfani dashi ,karkayi kuskura ko omo wanki ne matarka ta dinga siya da kudinta ,domin karshen abu wulakanci ne da iko har ma da gori sai ta maka ."sai abu nagaba da zan sanar maka, ka d'auki kowani irin mataki kanta ,amman ban da matakin sakinta saboda nasan kana son matarka har yanzu ...


fu'ad yayi shiru yana sauraronsa har sanda ya dasa aya sannan ya d'an rutsuna tare furta "thank you so much sir Allah ya bar girma .


"karka damu fu'ad allah ya shigemana gaba" ammen ya amsa tare da mikewa tsaye .


a mota ma tunani yake yana tuki yana tunanin abinda zai je y iske agidan ..


mmn sudais ce
[11/3, 8:25 AM] El~hajj: πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—
'YAN CINKI
πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–
πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—


~NA~


*AYSHA A BAGUDO*


~DEDICATED TO~
MRS ADAM
( YAR MUTAN KAGARA)


page 31 to 35


.........diraving kawai yake cike da matsanancin tashin hankali ,yayinda gefe guda na zuciyarsa ke wani irin harbawa, saboda jin bugun zuciyarsa yake tun daga tsakiyar 'kirjinsa har ilahiri sansan jikinsa. wanda hakan ya haddasawa gefen kansa sarawa da 'karfi, gaba d'aya ji yayi jikinsa ya mutu, tu'kin ma na neman gagararsa.


A hankali ya gangara gefen titi yayi parking tare da dai-daita tsayuwar motarsa ya rungume sitiyarin motar had'e da d'aura kansa bisa hannuwansa yana fitar da numfashi me tattare da hucin zafi.


tun daga nesa Sajida wace daga gidan me'ad gidan misna ta wuce, ta hango motar fu'ad parke a gefen titi cike da matsanancin mamaki ta soma rage gudun motarta har sanda ta iso daf da inda motarsa take .
tayi parking ta fito da hanzarinta daga cikin motarta ,hankalinta a matu'kar tashe ta doshi inda yake, tana kare fuskarta da tafin hannuta saboda hasken ranar daya dallare mata idanu , jiki a sanyaye ta 'karasa jinkin motar ta tsaya tare da kai hannuta ta k'wank'wasa glass d'in motar, wanda hakan yasa fu'ad 'ko'karin d'ago idanunsa domin ganin kowaye.


A hankali ya sauke kyawawan idanunsa a kan fuskarta dake cike da mamakin ganinsa a gurin , runtse idanunsa yayi sosai yana jin wani irin d'aci a ransa mara misaltuwa ....


da hannunta tayi masa alama yayi warning glass din motarsa, sai da ya furzar da iska me zafi ta bakinsa sannan yayi 'kasa da glass din, kana ya mai da kansa kan sitiyari kamar yadda yayi da farko , shi kad'ai yasan irin rad'ad'in da zuciyarsa take ciki a kan wannan matsalar dake shirin kunno kai cikin rayuwarsa da al'amuran gidansa.


sautin muryarta yaji ta doki dodon kunneshi "lafiya Abban NASREEN kayi parking a gefen titi haka?


"idan ma wani abu ne ke damunka, kamata yayi ka samu ka qarasa gida first, domin samun natsuwar zuciya saboda tsayuwarka a nan is very very risking.. ta 'karasa mgnr tana zagayo wa d'ayan gefen tana me k'wank'wasawa alamun ya bud'e mata .


da 'kyar ya samu ya danna wani abu a cikin motar domin bata damar shigowa ba tare da yace mata komai ba saboda kansa dake cigaba da sarawa.


ta bud'e murfin motar jikinta na rawa tare da janye jakar briefcase d'insa dake kujera me zaman kanta, ta zauna tana masa fari da ido muryarta a sanyaye tace " sannu Abban NASREEN na san duk damuwar nan taka ,baza ta rasa nasaba da matsalar kawata ba?
,"amman ka yiwa Allah kayi hakuri Insha Allahu komai zai zo da sau'ki, me'ad ce bata d'aukar shawara na rasa abinda ke rud'arta....


A hankali ya d'ago idanunsa tare da waigowa gefen da take zaune ,idanuwansu suka tsarke cikin juna, suna had'a ido kowanensu ya kafe d'anuwansa da kallo zuciyoyinsu na ayyana musu abubuwa da yawa .


kallon cikin kwayar idanunsa ta cigaba da yi tana jin wani abu na yawo a jikinta ,had'e da hango wani irin tashin hankali kwance a cikinsu , a hankali ya soma kokarin motsa bakinsa " kika ce kin rasa abinda ke rud'ar ta ?


ta d'age masa girarta d'aya tana sake masa fari da ido muryarta a sanyaye tace "eh Abban NASREEN ni dai gsky bansani ba, amman idan kasan abinda ke rud'arta ka taimaka ka gaya min ?


" girgiza kansa kawai yayi ba tare da ya sake cewa daita komai ba, ita kuma ta bishi da mayataccen kallo tana yaba kyawun halittarsa, ganin yadda jikinsa yayi matukar amsar kayan dake sanye ajikinsa ya kara hura wutar soyayyarsa acikin zuciyarta ,ji take tamkar ta shige jikinsa ta rumgume shi sannan ta rarrashsshi a kan tarin damuwarsa .


A hankali ta sauke nannauyen ajiyar zuciya tana furta" hamson kenan .....yau dai gani ga ka kyakkyawan mutumin da zuciyata ta dad'e da kamuwa da matsanancin sonshi, kyakkyawa son kowa 'kin wanda ya rasa ..." am very sorry da abinda kaji yana fitowa daga cikin bakina , domin na dad'e ,ba tun yau ba nake son amayar maka da abinda ke cikin zuciyata, "a gaskiya fu'ad na dad'e da afkawa cikin duniyar kaunarka ,idan ba zaka damu ba zan so ka bani damar kawo farin ciki cikin rayuwarka.


" fuad ina tsanin sonka tun a ganin farkon dana maka a rayuwata, wasu dalilai ne suka hana ni fahimtar da kai tsantsar 'kaunarka gareni, amman yanzu ga dama ta samu ," ka natsu ka saurare ni ,ina son ka aure ni na maye maka gurbin da k'awata ta kasa cikewa a gidanka.


bai san sanda yayi saurin dafe kanshi ba cikin matsanancin 6acin rai sakamakon jin abinda ke fitowa daga cikin bakinta, wani tsaki ya ja da 'karfi kana yace "kin zo ne ki 'kara min damuwa a kan wanda nake ciki ko me?


"calm down my hamson i thoueght you feel of fended that I m disturbing you, wanda ba haka bane, ni nasan abinda nake yi, gaba d'aya nasan halin da kake ciki , nasan kana cikin damuwa fu'ad, dan haka nake neman alfarma da ka bani dama na nuna maka kalar tawa soyayyar plz....


A matu'kar firgice ya sake juyowa ya kalleta "me take nufi da shi da rayuwarsa gaba d'aya?


"lallai duniya abin tsoro, haka mutane cikinta, "me yasa sam wasu matan basu da tunani da hango abinda zai je yazo?


"ita din fa tamkar yan uwan junane suke da me'ad, tare ya sansu komai nasu tare tun daga kan sutura da komai, amman take furta wad'annan zantuttuka gare shi ,ba tare da wata shakka ba ko tsoro , "kai tur da mata masu irin wannan hali...


kusan minti goma suna zaune haka tana gaya masa zantuttuka masu sanyi da shiga jiki ba tare da yayi yun'kurin sake cewa da ita komai ba, illa zuciyarsa dake bugawa cike da mamakinta ,duk wata kalmar soyayya da zata fito daga cikin bakinta sai tayi silar bugar masa da zuciya, har zuwa sanda zuciyarsa ta kawo masa mafitar da zata tunzura zuciyar me'ad dinsa akan wulakacinta garesa zaiyi amfani da sajida ko hakan zai kawo cigaba arayuwarsu , take ya amince da shawarar da zuciyarsa ta bashi na ya amince mata kawai ko dan koyar da ita darasin dake cikin duniya .


"sajida ta kira sunansa cikin sanyayiyar muryarta me tsananin dadin sauraro "plz Abban NASREEN kace min wani abu mana, da alamun akwai abinda kake son cewa gareni ....


"zaki iya maida ni gida yanzu i think bazan iya 'karasawa da kaina ba ?
yayi mganar muryarsa can 'kasa, jikinta na rawa tace " me zai hana bari na kira Hakim direbana yazo ya same ni a nan, domin ya biyo ni da tawa motar .
kansa kawai ya iya d'aga mata tare da juyar da kansa gefe yana kallon gefen titi , dan kwata-kwata baya son cigaba da dubanta, yana jin idan ya cigaba da kallonta komai zai iya faruwa a tsakanin su ,saboda kyawun surarta, jikinta me matu'kar kyau da hargitsa lissafi ga shi tana cikin irin shigar da yafi son mace ta kasance ciki, doguwar rigar atamfa, java gold me adon flower's ta yane kanta da 'karamin mayafi baki ,doguwa ce sosai kamar me'ad dinsa, sai dai ba fara bace sai jikinta irin karuwan jikin nan gareta kirjinta cike yake bammmm da ruwan nono , dan wani lokaci yanayin jikinta na sauyawa musamman idan tana cikin farin ciki, ba dai wani tsagwaron kyau gareta ba amman akwai kyawun halittar jiki, a kallo d'aya mutum zai iya afkawa cikin tafkin 'kaunarta, katse shirun sa tayi ta hanyar cewa kad'an yi ha'kuri yanzu zai 'karaso.


kasa amsawa yayi saboda wani abu da yaji yana yawo a gaba d'aya ilahirin jikinsa me kama da shocking wanda ke haddasawa kirjinsa dokawa, cikin mintunan da basu wuce goma ba sai ga Hakim ya 'karaso a kan okada ,tana hangosa ta bud'e murfin motar ta fito a dai-dai lokacin da ya 'karaso gareta yana me rusunawa, ta mi'ka masa key'n motarta bayan tayi nesa kad'an daga jikin motar fu'ad "ka biyo mu a baya, abinda ta iya cewa kenan ta juya wanda a lokacin har fu'ad ya samu damar komawa d'ayan bangaren sannan ta shiga ta zauna mazaunin direba taja motar a guje Hakim ya biyo bayanta kamar yadda tace.


fu'ad yayi shiru yana sauraron abinda take fad'a masa a kan matsanancin 'kaunar da take masa, amman ya kasa furta mata dai-dai da kalma d'aya domin maida martanin maganar data ishe shi dashi ,saboda bacin ran da yake ciki dan gaba d'aya haushi tare da mamakinta ne ya addabi zuciyarsa .


A bakin get din gidan taja ta tsaya tare da yin hon,me gadin ya taso da sauri ya bud'e musu tasanya hancin motarsa ciki harabar gidan , kai tsaye inda aka tanada domin parking din motoci ta nufa tayi parking tana sake yi masa nacin ya taimaka ya amshi tayin soyayyarta ,a tare suka fito daga cikin motar sannan ta kulle ,ta tsaya a gabansa tana fuskantarsa tare da mi'ko masa key , wanda dai-dai wannan lokacin me'ad dake zaune cikin d'akin ta mi'ke tsaye da niyyar zuwa d'akin NASREEN kamar ance ta waigo zuwa harabar gidan, idanunta suka sauka, a kansu tsaye ,sai dai duhun daren da ya soma shigowa ya hanata gane kowace tsaye a gaban mijinta tana mi'ko masa hannu buga da k'ari fadadden kirjinsa ya kareta , 'kirjinta ne yayi wani irin lugud'en bugawa da 'karfi har sai da ta kai ga dafe dai-dai saitin zuciyarta da taji yana neman tarwtsewa.


A hankali sajida take masa magana wacce ke sake kashe masa jiki "fu'ad ina sonka, bana tunanin zan iya sakacin da nayi a farkon haduwar mu, ka taimaka ka amincewa aurena plz..... tare da d'aura key'n motar a tafin hanunsa tana me shafar tsakiyar hannunsa wanda hakan yasa yayi saurin janye hannunsa "sajida .......fu'ad ya kira sunanta.


"na'am fu'ad dina ..


"zaki iya fita daga cikin gidan nan da rayuwata gbdy tun kafin zantuttukanki su soma tarwatsa min 'kwa'kwalwa?


tayi shiru tare da tsura masa ido tana kallonsa , take hawaye ya soma ciccikowa a idanunta "kar ka min haka fu'ad wallahi... "dakata plz just live now ya nuna mata hanyar fita da hannunsa "bazan damu da duk abinda zaka min ba, saboda darajar son da nake maka ,ka sani duk duniya babu wacce tafi can-canta ka aura sama da ni, na ha'kura da kai ne a wancan lokacin saboda lokaci ya 'kure min ,amman yanzu ina tabbatar maka sai inda 'karfina ya 'kare akanka .....


"ni dai na gaya miki ki fita cikin rayuwata, kar ki sake kuskuren furta min kalmar so, saboda ko nakasance mahaukaci bazan ta'ba kuskuren aurenki ba, "me na tsinta a aurena da me'ad ballantana nayi tunanin auren ki?


"kar kace haka plz, ka jarraba aurena fu'ad ... akwai bambamci me yawa atsakanina da me..


"shout up there yayi maganar a matu'kar harzu'ke wanda yasa me'ad 'ko'karin fitowa daga cikin part dinta "me ye bam-bamcin ki da me'ad?
"yadda me'ad take haka kike .....


" kar kace haka fu'ad wallahi akwai bam-banci me tazara a tsakaninmu..tsaki ya ja a fusace ya matse key'n motarsa ya shige cikin ya barta tsaye a gurin tana kallon bayansa babu kowa a parlour'n sai 'karar TV dake manne jikin bango a parlour'n a hankali dafe da goshinsa ya nufi d'akinsa ya fad'a saman doguwar kujerar three seater guda d'aya da ke ajiye a gefe d'aya yana lumshe idanunsa .


mee'ad ta shigo d'akin cikin sauri tana binsa da kallo bayan taje harabar gidan ba taga matar data kawo mijinta gida ba, muryar ta a fusace ta soma magana "wacece wannan tantiriyar da ta kawo ka gida yanzu ?


"meye ala'karka da da ita da har take da 'karfin zuciyar tu'ko min miji har ma da shigo min cikin gida?


shigowarta da banzaye tambayoyinta gare shi yasa shi mi'kewa tsaye ya nufin hanyar bayi "honey cant to hear what am saying?


" nace wace 'yar iska ce ta kawo ka yanzu ? ta biyo bayansa tana sake tambayarsa ,yayi mata banza tamkar ba dashi take mgn ba,ya shige bayi tare da bugo 'kofar bayin da 'karfi kad'an ya rage bai bugi fuskarta ba, tayi baya da sauri tana dafe bangon d'akin gaba daya hankalinta da natsuwarta ya soma barin gangar jikinta ,idanu ta tsurawa 'kofar bayin tana mamakin abinda ya faru wanda bai ta'ba faruwa ba, a tun had'uwarsa dashi ,sam bai kasance ma nemin mata ba, ko shiga shirginsu asali ma duk macen da ya ganta bata birgesa itama sa'a taci .

fu'ad na 'karasa shiga bayi ya sakarwa kansa da ya ji yana 'ko'karin rabewa gida biyu ruwa, ya kai tsawon minti talatin yana tsaye ruwa na tsiyaya a jikinsa ba tare da ya cire kayan jikinsa ba, sannan ya cire kayan jikinsa ya soma wanka a tsanake cike da 'bacin rai "me yasa na auri me'ad? ya jefawa
zuciyarsa wannan. tambayar .


"me yasa ban yi ha'kuri da tarin soyayyarta gare ni ba ,na tunzura zuciyata gurin aurenta ,ga shi ina cikin tsaka mai wuya da lamarinta ?


"ta yaya zan auri matar da baxata iya bin umarnina ba tare da sadaukarwa gareni ...?" hakika nayi kuskure a rayuwata , tabbas nayi kuskure babba da na aureta a rayuwata ba tare da nayi tunani ba... "a zahirin gasky hakkin NASREEN sai ya kamani domin ban za6a mata uwa ta gari ba abin alfahari ba.


"why why why na aureta?
ya furta tare dunkule hannunsa ya naushi iska , da wannan tunanin ya 'karasa wankansa ya fito ,tana tsaye tamkar wacce aka dasa ta a gurin ,yazo ya wuceta yana goge jikinsa ya nufi wardrobe dinsa ya ciro jallabiyya black colour ya sanya, ya je ya kunna TV kana ya dawo kan kujera ya zauna ba tare da ya kalli inda take ruku6e ba, ya d'auki remote ya kunna AC .


me'ad ta 'karaso in da yake ta zauna kusa da shi sosai , zuciyarta na wani irin tafarfasa ta tsura masa ido tana kallonsa , da 'kyar ta samu ta tattaro kuzarinta tare da kamo hannunsa d'aya cikinsa sannan ta soma motsa labbanta "Abban NASREEN tambayarka fa nake wacece wannan matar data kawoka plz ?
" i have been talking you since, and i really has to do this before everting could have mess up wit us, kawai just tell me who is she?

hankalina ya saka kwanciya saboda ban ta'ba ganinka tare da wata ba, ballanata har ku kasance acikin motarka tare..


"ka fara neman mata ne ban sani ba ko me?


"plz talk to me now hankalina a matu'kar tashe yake..


fixge hannunsa da ke cikin nata yayi a matu'kar fusace sannan ya juyo a hankali yana fuskantarta sosai " me'ad !!! ya kira sunanta har sau uku da muryarsa a sanyaye sai dai da ji kasan yana cikin damuwa da tashin hankali "you really has carryover in your dity life for this idiot matter .


" me'ad lokacin yana neman 'kure miki amman rashin common sense dinki ya'ki bari ki hankalta, nadamar ki ta kusa zuwa gareki ba tare da kin shiryawa hakan ba , lokacin kukan ki yayi me'ad.....sannan watan da na saninki ya kusan tsayawa matsawar baki canza wannan hali da 'kudirinki naki a kaina ba.....wallahi ina me tabbatar miki sai kin yi kuka da idanunki nan

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads