Showing 51001 words to 54000 words out of 163596 words
Chapter 18 - YANCNKI Book Complete by Aisha Bagudu.txt
sai dai al'amarin damuwata ya danganceta..kina saurarata kuwa?
"Ina jinki sajida sai dai maganarki tasanya kuzarin jikina yin rauni .
"karki damu da furucina nasanki, nasan halinki da zurfin ciki duk wuya duk runtsi akayi sirri dake baza ta'ba jinsa akoina ba shiyasa nasanyoki cikin abinda yashafi sirrikan rayuwata.
Taja numfashi ahankali ta fitar tana mai karya kwana wanda kai tsaye inda tasan fu'ad yake zama tare da abokansa ta nufa daga nesa kad'an da gurin tayi parking ta tsura masa idanunta sosai kmr zata fixgosa gareta, yana zaune tsakiyarsu kabeer suna hira wanda ba kasafai yake sanya bakinsa ciki ba.
kallonsa kawai take bata ko kifta ido, ga wani irin kalar murmushi datake masa wanda ita kanta batasan tanayi ba balle wanda ake dominsa, tsawon lokaci tana zaune tana kallonsa taji an hura mata iska a idanunta, tayi firgigib ta dawo haiyacinta tana duban misna dake zaune a gefenta ," misna a yau nake son shearing wani abu daya danganci rayuwata dake "waye wancan dake zaune tsakiyar maza uku din can sanye da t shirt fari da bakin wando?
tayi mata tmbyr tare da d'auke idanunta akanta ta maida kan fu'ad da bai san wainar da'ake toyawa ba .
Ahankali misna tace "Idan dai har idanuna nagani kmr yadda nayi zato fu'ad din me'ad ne zaune.......
"yauwa yar gari sai dai kinyi kuskuren kiransa da fu'ad din me'ad ne ,kice fu'ad din mai raboz saboda shine mutumin da zuciyata ta kamu da matsanancin kaunarsa, shine mutumin daya hanani walwala da sukuni, shi mutumin da tuaninsa ya dusashe tarin soyayyar emran acikin zuciyata ,har nake ganin duk mazan duniya mata ne shi kawai ne tsayayen nmj... "what ..kina mafarkine sajida?
"Idan mafarki kike maza ki farka "karki manta halakar dake tsakanin iyayenku daku kanka, "meyasa zakiyi hk sajida?
"Gsky banji dadin furuncinki ga abinda aminiyarki take so tmkr ranta ba .."nasani misna amman ya na iya da rayuwata, me'ad ce silar faruwar komai "itace ta nuna minshi daga kallo dayan dana masa narasa gane kaina,"yanzu dai ki taimakeni ta yaya kike ganin zan mallakesa shine abinda nafi bukata daga gareki?
Naunayen ajiyar zuciya misna ta sauke da karfi "azahirin gsky ni banida wani taimako da zan iya miki daya wuce kiyi hkr ki hakura dashi domin shine zaman lfyarmu da kwanciyar hankalinmu kafin mead tasan da wannan zance.
"haba haba sam wannan abu baiyi min dadi ba,aminan juna daku kuna son abu daya......."ki hakura dashi sajida ,a gsky banji dadin yadda kikace saboda shi kika kasa zama da emran ba domin emran masoyinki ne na hakika wanda samun irinsa ke wuya .
"shawara nake bukata daga gareki bawani zance emran ba " matukar shawara kike bukata daga gareni ki cire soyayyar fuad acikin ranki ki fawwalawa Allah komai shi yasan yadda zaiyi da al'amarinsa ,babu mamaki akwai manufar da Allah yake nufi daku ,da har yasa kuka kamu da son mutun daya, mutun dayan kum wanda ya kasance bakowa ba face talaka ...
Sajida ta daina sauraron misna ta meida hankalinta sosai gurin cigaba da kallonsa har sai dataji zuciyarta tasamu natsuwar datake bukata sannan taja motarta ta gabansa suka wuce amman bai san ko su waye ba kasancewar glass din motar baki ne, ta sauke misna a gidansu sannan ta koma gida cike da tunanin misna.
"An kuwa zata iya rabuwa dashi?
"idan ta rabu dashi tayi yaya da rayuwarta?
"kenan rayuwarta zata zamo abar tausayi babu emran babu shi babu budurcinta...... ina da sake.
Zuwan fu'ad biyu amman me'ad batayi kokarin sanar masa da sakon mahaifinta ba ,yanzu ma tsaye suke a harabar gidansu tayo masa rakiya motocin safwan suka sanyo kai cikin harabar gidan, tundaga nesan daya hangosu kirjinsa ke bugawa har zuwa sanda suka isa inda aka tanada domin ajiye motoci ,bayan an yi parking,ya yunkura da kyar yasamu ya fito sanye cikin riga da wando sai yar saman suit dake saman farar longselve, ya kirkiro dariyar dole yakaraso zuwa inda suke alokaci daya zuciyar fu'ad data safwan ta buga rasssssss atare batare da suncewa juna komai ba sai me'ad ce ta bud'e baki tana murmushi "fu'ad ga yayana safwan....safwan yayi saurin runtse idonsa sbd zuciyarsa dake na wani irin harbawa kmr zata fasa kirjinsa dan ji yayi kmr an diga masa ruwan dalma, sannan ta juya ta kalli safwan tace "yaya safwan ga fu'ad Dina....ahankali ya bud'e idanunsa ya daura akan fu'ad daya tsareshi danashi idon kana jiki a sanyaye suka mikawa junansu hannu domin gaisawa " mlm fu'ad ya gida da aiki?
"Lfy fu'ad yace atakaice saboda ganin irin kallon kasan dayake masa mai had'e da maxurai da rainin wayo da murmushi ahad'e.
Hannunsu na sarkafe cikin juna safwan yace "gsky kanwata kin iya zabe ..."allah ko yaya? "Kwarai kuwa...da gaske, kin kuwa gaya masa sakon dady ?
Numfashi taja ta sauke da kyar kana tace"Abinda nake shirin yi kenan kashigo "ok kiyi kokari ki sanar masa idan da wata matsala ki hanzarta sanar min "ok yaya na gode da kulawarka .
"No karki damu kanwata any for you ya juya zuciyarsa na farfasa, ya nufi cikin gidan kmr zai kifa tsabar duhun da zuciyarsa tashiga har yayi dayasanin zuwansa gidan bayansa fu'ad ya tsurawa idanu duk bai jiyo ba yana iya ganin yadda numfashinsa ke fita da karfi.
byn shigarsa cikin gidan fu'ad yayi mugu mugun tsareta da ido "kikace wannan mutumin yayanki ne ?
"eh tabashi amsa tana kallon cikin idanunsa.
"Uwa daya uba daya?
" no D'an aminin kuma mai gidan dady ne,"wani abu ne ?girgiza mata kai kawai yayi "yanzu dai kaji da kunnenka dady nason ganinka ya kenan?
"Ok badamuwa zuwa yaushe yake son ganina?
"anytime you are free ,"ok mubarshi nest week saboda gabadaya satinan zanyi busy kema bazaki samu damar ganina ba har sai nagama abinda nake, jin hk yasa ta narke masa fuska kmr zatayi kuka "har next week fa kace , kasan kuwa yadda nake ji idan nayi kwana daya ban sanyaka acikin idanuna ba ?
"Ji nake kmr ana fixgar numfashina ni dai kasan yadda zakayi, ko kazo ko sau biyu ne naganka ,ko kuma ni na sameka inda kake.
Murmushin yayi sannan yasoma rarrashinta sai daya samu ta dawo normal sannan ya wuce.
Kwanakin nan gbdy acikin kunci da damuwa mead tayisa sakamakon rashin ganinsa Dan hk randa yazo da zumar ganin mahaifinta tana ganinsa bata tsaya wata wata ba ta rungume shi ajikinta tana farinciki ,saurin d'auke numfashinsa yayi saboda jin diran nonuwanta bisa kirjinsa atare sukaji tmkr
Wani irin abu yana masu yawo a gabadaya ilahirin jikinsun me kama da shocking wanda take ya haddasawa nata kirjin bugawa yayinda shi km a take kwakwaluwarsa ta d'auki caji , cikin wani irin murya yace " my love you kinzo min da wani irin salo mai tsayawa a zuciya, kar da kisa nayi abun kunya a gidan siriki, a yadda yayi maganar bakaramin rud'ata yayi ba ....jin yanayinsa nason canzawa yasashi zareta ajikinsa yana fitar da wani irin numfashi da kyar da sauri ta ita kuma ta fita daga cikin parlour fuskarta cike da fara'a, itama wani irin kalar numfashi take ,a yanzu ji take ina ma amatsayin mallakinsa take.
"tun bayan fitarta fu'ad yafara jin caji ajikinsa, ahankali yake jin wani feelings na bijirowa a gangar jikinsa ,lips dinsa na kasa ya ciza da matukar karfi kmr zai datse harshensa, sannan yayi saurin batsar da abinda yake jin yana masa yawo ajiki kana yacigaba da zaman jiranta.
Cikin wasu yan mintunoni da basu wuce biyar ba ta sake dawowa karamin parlour'n dayake zaune zaman jiranta "taso muje zuwa ga babban parlour'n dady inda anan dady zai ganka ,bakinsa d'auke da sallama yashigo cikin hadadden parlour'n ,inda suka iske parlour'n empty babu kowa cikinsa sai k'aran tv plazma dake manne da bangon parlour'n yana aiki acikinsa hannunsa ta kamo zuwa kan kujera "ka zauna yanzu dady zai shigo, gyaran murya yayi mata batare da yace komai ba illa idanunsa dake yawo a sansar jikinta, ta juya cike da rausaya ta nufi cikin gidan tana daddana number safwan kira daya ya dauka "ya'akayi ne kanwata?
"kazo yanzu ga fu'ad yazo dan Allah nafi son duk abinda za'a yi kana nan domin nasan zakayi controlling din dady . Tunda tasoma mgn numfashinsa ya nemi dauke amman yayi saurin sanyawa jikinsa jarumtar cewar"ok karki damu gani zuwa just give me some mint.
byn kmr minti 30 sai ga dady yashigo parlour'n yana dingisawa fu'ad naganinsa yayi saurin mikewa tsaye cike da girmamawa yana mai gaishe dashi "uhm kawai dady ya iya cewa sannam ya zauna tare da cewa "kana iya zama.
fu'ad ya Zauna zuciyarsa na d'ardar dan ganin yadda mahaifin me'ad ke kallonsa kasa da sama wanda hkn yake nuna alamun bai yaba da ganinsa ba .
yayinda me'ad tasake dawowa parlour'n tare da tsayawa a bakin kofar shigowa ta tsurawa fu'ad ido dady ya yi gyaran murya kana yace "me za'a kawo maka?
shayi ko lemo ko... "no no dady ba sai an kawo min komai ba ,nagode "uhmm kasha wani abu mana kai kuwa ?
cike da in ina fuad yace "to ruwa ma kawai ya isa .
"ruwa fa?
mahaifin me'ad ya fad'a yana jinjina kai .fuad yace eh shi kawai ya isa.
kai kuwa "ya zakazo gidan masu abun kace ruwa kawai zaka sha any how mead kawowa bakonki abinda ya bukata ta juya, jiki a sanyaye ta nufi kitchen dan sam bataji dadi irin tarban da dady yayi masa ba, byn fitarta dady ya fuskanci fu'ad yana tsare idanu tun kafin yasoma magana safwan yashigo cikin parlour'n cikin sallama sanye cikin kananun kaya wad'anda suka mugun amsar jikinsa sai kamshi dadden turarensa yake bazawa ya gaishe da dady sannan yakarasa ya mikawa fu'ad. Hannu"barkanmu da warhk?
Shima fu'ad Hannu ya mika masa suka gaisa sannan ya samun guri ya zauna shima yana fuskantar fu'ad , yasanya hannunsa daya yayi tagumi yana cigaba da kallon fu'ad "me yafi shi har da me'ad ta zabesa ta barshi?
kyau ilimi tattare makudan kudaden da shi kansa bai san adadinsu ba, duk yafi wannan dake zaune a gabanshi..
"a ina kake da zama sautin muryar dady ta karade parlour'n zuwa cikin dodon kunne fu'ad "ina zaune a gbegulori dake kan titi capito road "uhmm anan kake zaune tare da iyayenka?
"eh ana nake tare da kakata dan tun daga haihuwata mahaifiyata ta rasu byn wani lokaci shima mahaifina ya rasu yanzu dai ina tare da kakata nake zaune.
"ayya ina mai jajanta maka Allah ya jikansu.
"Ameen na.. na gode dady. Cikin hk mead tashigo ta ajiye tire dake dauke da nauikan abinci ta juya tanayiwa safwan alamar ya taimaka komai yazo karshe sannan tabar gurin.
Dady yacigaba"da dukan alamum kakarka tana riritaka dayawa ?
fu'ad yayi muushin jin dadi tare da sakin jikinsa kad'an dan da adirice yake ,sannan yace azahirin gsky hk ne Sabod tana matsananci sona sosai "ya isa me kakeyi ahalin yanzu aiki ko karatu?
"gsky babu abinda nake ahalin yanzu ina dai kan neman aiki a tun bayan dana gama digri Dina Amman har yanzu ban samu ba shiyasa na yanke shawarar soma sana'ar kasuwancin..
"idan na fahimci maganarka baka Da aikin yi, kai mutun ne dakayi karatu amman baka da tsayayen aikin yi, safwan kana ji fa da sanar da bai kai ga samu ba yake neman diyar babban gida ko dai baiyi karatun bane?
"a'a dady digre gareni nasan zuwa yanzu nasan abinda kake son kace amman na rantse maka da Allah zan kular maka da me'ad sosai fiyye da yadda kake tsammani "uhm kace kayi karatu geo ko history ka karanta? "aa kasuwanci na karanta zaka iya kallon abun wani iri Amman muddin me'ad na tare dani kusan babu abinda bazan iya mata ba, ko maye zanyi domim na bata farinciki da.....
"ya isa hk malam dady ya katseshi yana mazurai da "Karka cikani da wannan surutain banza da wofi "meye matsayinka? "kai fa ka kasance yaro ne mara zuciyar neman na kansa wanda kakarsa ke ciyar dashi tare da bashi kudin kashewa, yayi gantali yayi can yayi gantali yayi nan rayuwar kenan wadan nan takalman da kayan jikinka da machine din dakazo dashi da kudin wa kasiya? mu dubi komai a zahirance mana sannan musa gsky a hurumunta mana "ta yaya kake tunani zan dauki diyata me'ad nabawa mai matacciyar zuciya irinka?
"na d'auki diyar dana fi so na aurawa ga wanda gabadaya rayuwarsa sipili ce a tunaninka hkn zai yiwu?
fu'ad da kansa ke sunkuye ya dago a matukar firgice yana duban dady kamin yayi magana dady yace "ysushe kasan me'ad? "karkari tsawon wata shida.
ran fu'ad ya sake kaiwa kololuwa gurin tashi ganin ga safwan zaune amman yaki takawa dady burki gashi dady bashi alamun saida zancesa hkn kuma still safwan na kallonsa A wulakance yana masa murmushin da bai san ko na mene ba, ya bude bakinsa da kyar yace "yallabai ni dai nasan idan kabani auren yarinyaka zansata farinciki "me kake bukata atare da mutun adali ince na natsuwa nagarta mai kamun kai mara shaye2, to duk ina cikin abinda na lisafa maka, ince duka matsalar akan ta rashin aikin yi ce? "ka zuba ido kagani nan gaba da kayan aiki zakaganni ,zan tabbatar maka da kai.. "meye abun tabbatarwa yaro byn gaka agabana da shirman rayuwarka zaka tabvatar min da kanka ko me?
dady yakarasa mgnr yana murmushi safwan kaji fa, "wai shin wani shirin wasan kwaikwayo akeyi anan ne ko me?
"wai tabbatar da kansa yake son yi wa uban me'ad yakarasa mgnr yana dry "babban magana kenan "mai yawo a gari babu aiki yake son tabbatar da kansa shi dai safwan bai ce ta tafar ba illa dryr dayake ta kunshewa saboda gabadaya maganganun dady sun matukar yi masa dadi da sanyaya ransa.. "kasani diyata me'ad nada alkwarin auren wani akanta attajiri Wanda ya fika a komai na rayuwar duniya dan hk kwarya tabi kwarya a gidan baka da matar aure period mgn ta karshe kar na sake ganin kafarka gidana..
fu'ad yasoma kokarin mike tsaye "sai anjima yallabai nagode da lokacin daka bani wani irin kallon kaskanci dady yake binsa dashi yayinda har wannan lokacin fuskar safwan kumshe take da dryr mugunta.
jiki a sanyaye fu'ad yakarasa mikewa yana gyara rigarsa ta baya sannan yasoma daga kafafunsa kmr kazar da kwai ya fashewa aciki ya nufi inda yayi parking din machin din kabeer daya aro, ya hau ya zauna amman ya kasa tadashi sai dai ya kwantar da kansa kan mashin din, bai yi auni va sai jin danshi yayi akan fuskasa ya mika hannunsa ya shafo hawaye ne, shi kansa yayi makakin dalilin zubarsu akan mead ne da zai rasa ko kuma akan tozarcin daaka masa ne ?
yafi minti talatin a haka kamin yasoma kokarin tayar da machine ,masu gadi suka bude masa kofar get ya fita, ya yarda bazai samu me'ad ba har abada. shi ba aure yadamu dashi ba da wuri kasancewarsa saurayi da bai taba aure ba, km ba shashanci yake ba balle ya tancance yanada bukatar mace yanzu ko aa, me'ad din kawai yake so, soyayyarta ce tasanyasa son yin aure a halin yanzu.
meyasa mead tayi masa hk ?"me yasa ta boye masa akwai alkwarin auren wani akanta? tayi masa wasa da zuciya da hankali har ya iso gida bai san inda hankalinsa yake ba kuma tmbyr dayake son yayi mata kenan "hakika tayi masa wasa da zuciya, dan bazai iya cewar ta yaudaresa ba ,dan ya yarda da son datake masa na gaske ne, sannan na tsakani da Allah ..
Da yammacin ranar sai ga mead tazo gidansu sakamakon abinda safwan yagaya mata daya yayi masa, da kunneta km taji lokacin da safwan kebawa dady hkr da kokarin shawo kansa daya amince da auren albashi sai su tsaya masa yasamu aiki,inda ta lsamu fuad zaune kofar gidan inna ,yana kallon sararin samaniya, da yadda hadari ya hado agarin,a zahirin gsky zaka dauka yana nazarta yanayin zuwan ruwan saman ne, amman sam abun ba hk yake ba tunanin rayuwa yake, tunani yadda rayuwa take shirin tagaliliya dashi yake, har sanda takaraso garesa bai sani ba sai jin laulausar tafin hannuta yayi saman nashi, wanda hkn yasa shi juyowa ahankali tare da sauke naunayen ajiyar zuciya ganin itace ,sai dai ganinta ya zafafa mikin dake cikin zuciyarsa, atake ransa ya sake dugunzuma, ya cire hannunsa daga nata yana mai basarwa sannan muryarsa a dakile yace"mai ya kawo gareni?
"Dan Allah kibar nan tun raina bai gama dagulewa akanki , banason kusancina dake."to saboda meye fu'ad? "Saboda kin kai ni ga mahaifinki ya tsarkafeni da sarkafaffun tmbayoyinsa marasa maana da tushe , ya bata amsa a matukar fusace yana mai maida idanunsa sama jin har ansoma yayyafi.
"karkayi wannan maganar fu'ad daman irin tambayar da iyaye sukayi kenan , kasa kanka amatsayin mahaifina ka duba Alamarin....dan Allah dan Annabi malam ya isa hk kawai kin gayuaceni zuwa gidanku dan aci mutuncina akaremin tanadi da tozarci ,shi kuma wannan tantirin safwan din yana zaune agurin yana min dariya "ka daina magana ta shirme mana safwan mutumin kirki ne karka tuhumaishi acikin wannan matsalar "oho ni kuma mutumin banza wanda bayada aikin yi, dan jagaliyar titi daya fada soyayya da yar babban gida, in da kace masu kudi kawai suke da alhakin da yancin fadawa soyayya ,da soyayya tayi karanci a duniya, fuad ka daina daga murya mana kana jawo hankali mutane garemu.
"Gara na daga sautin muryarta ansa kece kebibiyata har kikayi silar da yau aka tozartani, banki kowa yafito yasani ba, kece kika tallata min kanki akan soyayyarki ina zaman zamana cikin rufin asirin Allah "dan Allah karkayi magana cikin fushi har da kake wani shir...datse harshenta tayi da karfi takasa karasawa.
".Kwarai kuwa dole kice hk tunda kina son kare gidanku da ahlinki, an wulakantani sam baki damu ba suna kina sona kin