Showing 78001 words to 81000 words out of 163596 words
Chapter 27 - YANCNKI Book Complete by Aisha Bagudu.txt
da kika meida kmr tissue, kullun kika tashi iskancinki akanta kike karewa...bama wannan ba karki damu rayuwata plz.. "ai kin daina sona shiyasa kike wulakantani ,to kibari masu sona su shigo suyi min abinda nake bukata .
durkushewa tayi agabansa tana kuka "waye yace maka na daina sonka ..?
"wallahi ina sonka kai kanka kasan wannan ranar bazata zo ba ,bana ma faran ranar da zan daina sonka, kai ne dai ka daina sona tunda gashi kana kokarin kasheni tun kwanakina basu cika ba "ka gaya me kake son nayi maka ?
"Zan canza wallahi zan dinga baka had'in kai a shimfid'arka sai yadda kayi dani ,komai kake so zanyi maka wallahi bazan sake sa'bawa umarninka ba ....
Kuka take sosai tana rokonsa .
Jin kukan na ta'ba masa zuciya yasashi runtse idanunsa tare da cewa "naji kin fad'i komai baki fad'i batun ajiye aiki ba, ok shi fa tare aka halicceki dashi ko bazaki iya ajiyewa ba?
"No karkace hk honey wannan aikin nawa shine rufin asirimu ni da kai da tilon diyarmu kamin uzuri, "ni dai kayi hakuri dan Allah am really sorry for what I did...
Bai ce mata komai ba yashige bayi ya barta durkushe yana shiga ya sakarwa kansa ruwa, kafin ya fito ta kwashe kayan daya cire ta nufi washing room dashi sannan ta sake dawowa d'akin inda ta iske ya fito sanye da jallabiya "muje kaci abinci "a koshe nake....
"honey...... yaushe rabon kaci abincina ?
"Ka daina cin abincina ka daina mua'mula ta aure dani gbdy kokarin cireni kakeyi azuciyarka ,ka taimaka fu'ad nasan nayi ...plz ki takaita mgnrki hk ina bukatar hutu kina iya fita plz......
tsimi tsimi kmr baita ba ta fito daga d'akin ta nufi nata d'aki tana rike da kugunta tashiga zagaye d'akin"komai fa yana neman tsaya min ni me'ad," yanzu me yakamata nayi na dawo da mijina hannuna? Ina bukatar shi banason rasashi ,ya Allah ka taimakeni karkasa fuad ya juya min baya..
" ko sajida zan kira ta bani shawara akan wannan sabon lamarin dake shirin kuno kai cikin gidana "no no bana tunani zata iya min magani wannan matsalar .
"Ke kanki ki zauna kiyi tunanin zaki iya shawo Kan matsalarki inji cewar zuciyarta gbdy ta kasa zama hawaye take sosai damuwa tayi mata yawa ga matsalar gurin aikinta data rasa dalilin dayasa idan tashiga office dinta take jin zafi ajikinta ga matsalar rashin lfyr nasreen yanzu kuma ga abinda fu'ad yake son Bullo mata dashi.."ya rabbi ka taimakeni ...
***********
Shiru yana zaune a inda tabarshi yana tunanin abubuwan sa suka faru tsakaninsa da sajida, sosai lamarin ke bashi mamaki da daure masa kai "wai yau shine ya sha bakin wata mace ,macen ma aminyar matarsa , ya Jima zaune abun na ta'ba zuciyarsa, lamarin ya maseefar tsaya masa arai, ahankali ya Mike ya fito daga d'akinsa yana cigaba da tunani zai aureta ne kmr yadda me gidansa ke bukata ko kuwa zai dojewa aurenta ne ?
Yana fitowa ya ga wulgawar najma ta nufi d'akin nasreen bai ga fuskar yarinyar ba ,sai bayanta ya hanga doguwa ce Amman ba can ba ,kad'a kansa yayi sannan yashige kitchen coffee ya had'awa kansa ya fito rike da cup din yana kur'ba har yak'araso parlour'n ya zauna tare da d'aukar remut ya kunna tv ya canza channel zuwa CNN yana zaune har 12:00 dot kuma har lokacin zuciyarsa ta kasa samun natsuwa, ya sake mikewa yashiga d'akinsa yana shiga ya iske wayarsa na kara yakarasa cike da sanyi jiki ya d'auka yana duba screen din wayar wata number yagani wace bai Santa ba da kmr bazai d'auka ba saboda bai cika d'aukar wayar da baisani ba Amman dai zuciyarsa ta umarceshi daya d'auka
Mmn sudais ce
[11/3, 8:28 AM] El~hajj: ππππππ
'YAN CINKI
ππππ
ππππππ
~NA~
*AYSHA A BAGUDO*
~DEDICATED TO~
MRS ADAM
( YAR MUTAN KAGARA)
Page 73
.......Sautin muryar sajida yaji ta doki cikin dodon kunnenshi, Wanda hakan ya saukar masa da jin wani yanayi na daban sakamakon tuno moment dinsu na dazu, goshinsa ya Dafe yana me Jan dogon tsaki tare da furta "matsala........
Bangarenta itama naunayen ajiyar zuciya ta sauke lokacin dataji sautin muryarsa sai dai taji haushi abinda ya fad'a ,Amman sai kawar da hakan ta kwantar da muryarta sosai tace "na ta kuraka ko ?
"Am really sorry nima banso hakan ta kasance ba ,na kasa bacci ne sakamakon tunaninka daya addabi ruhina, shiyasa kaga kirana a daidai wannan lokacin,but kai me kakeyi da bakayi bacci ba har yanzu...?
Tayi masa tambayar tana sake kamkame wayar a kunenta tana jin is like suna makale da junansu ..
Fu'ad lumshe idanunsa yayi yana jin wani sabon yanayi a game daita wanda bai San ko na mene ba ,yana bin ilahirin jikinsa tare da kaiwa kowani shashi na gangar jikinsa ziyara , yayinda duk wata kafar gashi dake kwance ajikinsa suka soma mikewa,ahankali har suka mike duka , ya furzar da iska me dumi ta bakinsa "wai meke damuna ne ?
Ya tmbyi zuciyarsa yana shafa sumar kansa sannan yasamu guri ya zauna daga gefen gadon yana bud'e idanunsa , cikin murya me cike da kasala yasoma kira sunanta "sajida .....meye matsalarki dani dakike kok'arin shiga rayuwa?
"I think na gaya miki ki fita harkata ina son matata and bazan iya kara wani aure a halin yanzu ba ,kuma ko auren zanyi not you sajida saboda gbdy bakya daga cikin tsarin matar danake so ....dan hk tun wuri ina umartarki da ki bar rayuwata plz tun tunanina bai soma canzawa akanki ba.
Pillow ta janyo ta manne akirjinta ,tana yadda zuciyarta ke wani irin beting fastly "me yasa kake nacin na bar rayuwarka fu'ad a halin ina sonka fiyye da komai a duniya ?
" me yasa baka sona fu'ad?
"Na mallaki duk wani abinda cikakken nmj yake bukata daga kyakkywar mace ,why why da bazaka soni ba fu'ad..?
"tabe baki fu'ad yayi kmr yana gabanta sannan yace "ina ruwana da wani kyawunki ,wallahi idan za'a jeramin dubunku ba abinda zanyi daku saboda matata fiki komai danake bukata, sannan ba kyau akeyiwa ba ,hali akewa, wallahi in dai nace miki kin tsarinki yayi min zan aureki nayi miki karya sajida , kawai saboda babu kyau wulakanci ne yasa kikaga nake raga miki, domin duk wanda yace yana sonka yagama maka komai arayuwa, to be your last warning sajida da zaki kirani arayuwarki saboda banason hkn sannan bana bukatar mu'amula dake.....
"Haba fu'ad me yasa kake min haka ko dan nace ina sonka....?
"Exactly...abinda kika fad'a haka ne ,saboda kince kina sona yayinda ni kuma bana bukatar hakan ,zanso ki fahimta hakan azahirance , saboda idan kika lura ni dake bamu dace ba duba ga yadda kuke da matata,sannan Baki min ba Dan hk ki barni na karashe sauran rayuwata da matata bana bukatar wata sabuwar matsala ayanxu so Dan Allah kiyi hakuri ki janye kudirinki akaina ni yanzu ba soyayya bace a gabana ..
cikin fushi da bacin rai daba San lokacin daya dira acikin ranta ba tace "haba fu'ad Dan nace ina sonka, ta yaya arziki na binka kake gudu?
"KaSanin bazan ta'ba neman Abu ban samu ba balle abinda zuciyata ta kwallafa rai akai na Jima ina dawainiyya da dakon soyayyarka ,ina sonka kuma sai kazama nawa saboda. Babu ruwana da wata matarka ko dangantar dake tsakaninmu ,bugu da kari dan dady na yana min abinda nake so ,ahalin yanzu babu abinda yafi bukata kmr yaga nayi aure tunda nayi bika ta lallami kaki to zakaga abinda zan biyo baya sbd dole kazama mallakina....
Shima a matukar fusace yace "kin dad'e bakiyi fushi ba ,kuma wannan abinda kikayi yanzu yana cikin abinda yasa bazan so ki ba, idan kina takama da kudi ko wani abu ,to ni banida komai
, ke dadynki ne gatanki ni kuma Allah ne gatana shi zai tsaya min a dukkan lamurana, sannan shine bai doramin sonki ba da ina sonki sajida zan iya aurenki to banasonki ....dan hk karki sake kirana akan wannan banzar issue din ya k'arasa fad'ar hk yana katse kiran ya cillata saman gado ya juya ya kwanta flat tare da dafe goshinsa.
Tsaki taja "har ni zance ina sonshi yaki amincewa, duk da kyau'n da Allah yayi min ga tarin kudi?
"Me matarsa tafini dashi dayake wulakantani akanta ?
"Ai kuwa duk abinda zai faru sai dai ya faru Amman sai na aureka fu'ad koda kuwa zaka mutu byn na aureka......
*********
Daren ranar tarihi ne ya sake maimaita kansa Domin daga me'ad sajida fu'ad duk babu wanda ya runtsa acikinsu kowa da tunani dayake har garin Allah ya waye Dan har gara ma ta kwana yin nafilfili ne .....
*******
Tunda najma tazo gidan take yin abinda ya kawota, tare da kaffa kaffa da kanta ,Dan tasha jin labarin me'ad agurin yayarta ummi, Sam bata da mutucin ga masu aikinta duk kankatar laifi zata iya tozarta mutun akansa, gashi batasan darajar mutane ba acewarta ,shiyasa abinda aka kawota dominsa shi takeyi ,sosai take bawa nasreen kulawa tare da janta ajiki dan har yarinyar ta fara sabawa daita, yau takama ranar asabar , ta tashi da wuri domin killace gidan duk da baya daga cikin abinda ya kawota gidan, sai data share koina ta gyara tazo inda me'ad ke zaune tana tura sakonni a system dinta, sanye cikin wata hadaddiyar Riga da wandon jeans , tayi maseefar kyau cikin kayan sai kamshi ne ke fita ajikinta sam bazaka ta'ba cewar itace ta kawo nasreen duniya ba ,yayinda nasreen ke gefenta zaune tana zuba mata shagwaba iri iri .
Takaraso nesa kadan dasu tare da gaisheta cike da ladabi ,bata ko kalli inda take tsugune ba balle ta amsa mata tacigaba da aikin gabanta.
Najma cikin bakinciki da takacin wanda bata da ikon magana tunda Allah yayi abincinta a wajenta yake dole ta sawa zuciyarta hakuri har ranar da Allah zai yaye mata ahankali tace " nasreen tashi muje ki sha magani .."kawo mata nan me'ad tayi mgnr atakaice batare data dago ba.
Nasreen kuwa d'aura kanta tayi a saman cinyar mamanta tana zuba shagwaba "momy.....
"Yes baby what did you want?
"zanci indomi wit egg..
"Sai ki tashi kije ki soma dafa mata abinda ta bukata ko, ta kuma jifanta da wannan maganar atsawace cikin isa da nuna ita din wata ce me iko Akanta....
Najma ta mike ta tashi duk jikinta yana rawa tayi wajen aiwatar da ,abinda uwar d'akinta ta sata ta fito barandar gidan anan taci karo da wani kyakyawan mutun matashi wanda ba sai an gaya mata ba ,tasan mijin aunty ne Dan haka gwiwa biyu ta durkusa har kasa tace "ina kwana...
Fu'ad yayi kuri da ido yana kallonta cikin tsananin mamakin ganin wannan kyakkywar yarinyar wace shekarunta bazasu wuce shabakwai ba amatsayin me aiki ,sosai ya tsura mata idanunsa cike da tausayawa yasan babu da rashi irin na talauci ne ya haifar da hakan gareta, "Allah sarki rayuwa azahirin gsky talauci bai yi ba ,bai sani ba kodan ya fito daga tsantso talakawa ne yasa yake mugu mugun tausayawa talaka ....
Ita kam kallon da yake mata ne yasa jikinta d'aukar rawa ta mike da sauri ta bar gurin ta nufi d'akin da me'ad ta nuna mata tun farkon zuwanta gidan ,cikin sauri tashiga store ta d'auki indomin data kaita ta sake dawo cikin rawar jiki da sarsarfa a hanyar suka kuma cin karo da fu'ad wanda ke tsaye a wajen data barshi.
Shi kuwa bayanta yabi da kallo yana ta kallonta duk tausayinta ya cika masa zuciya, Da irin rayuwar data samu kanta ta babu, wanda har yasa take aikatau agidan mutane Dan su samu rufin asiri ..
Tana tsaye acikin kitchen din tana dafa indomin zuciyarta harbawa tare da hasko fuskar mijin uwar d'akinta ,tunda take bata taba ganin halittar data d'auki hankalinta alokaci daya ba kmr shi ,ya had'u sosai babu karya ,duk macen data ganshi taga cikakken njm, ahankali damuwarta ke juyewa zuwa farincikin dabasan dalilin faruwar hkn ba .
Bayan najma tagama dafawa nasreen indomi ta kawo mata har inda suke zaune da me'ad ,ta janyo center table ta d'aura mata sannan ta nufi d'akinta cikin sauri ta kwaso magungunanta ta dawo ta raku'be agefe tana jiran tagama tabata magani , tana nan har tsawon minti talatin tsayuwar jiranta, saboda itama nasreen kmr yanayin uwarta gareta gurin cin abinci ,ana ci kmr ba'a son ci,tana kallonta ta ture plate din gefe alamun takoshi sannan cikin rawar jiki ta nufi dispenser ta tara cup ta tsiyayi ruwa ta dawo tasoma balbale magani ta miko mata cikin rawar jiki Dan batason tayi kuskure agaban uwar d'akinta.
nasreen ta 'bata rai sosai tana turo bakinta Dan tasoma gajiya da shan magani saboda makoshinta na mata zafi a duk lokacin da zata sha ," najma bazan shan maganin nan yanzu ba ki bari zuwa anjima am so tired with it..
da sauri najma ta sake matsota "ki d'aure kinji nasreen an san shan magani da wahala amman d'aurewa ake kinji nasreen din ummanta....
me'ad tayi jimmmm Tare da barin abinda take ta D'an juyo ta saci kallonta sannan ta d'auke kanta duk da batason yarinyar sai dai taji dadi sosai da kulawarta ga tilon diyarta.
"amshi ki sha kinji nasreen din ummanta .....
Ta sake girgiza mata kai da kyar dai da rarrashi da komai ta samu ta lallabata sha sannan ita kuma ta tattara magungunanta tayi d'aki dasu.
ta dawo ta d'auke plet Wanda zuwa lokacin me'ad ta bar parlour'n zuwa d'akinta da waya manne a kunneta .
Har zata koma ta zauna kusa da nasreen sai Ta samu kanta da son sake ganin fuskar kyakyawan mijin aunty...
Ahankali ta isa bakin barandar tana lekensa tana waigen bayanta gudun kar me'ad takamata tana kallon mijinta , tana tsaye tana sake tsintar kanta cikin matsanancin farinciki mara misaltuwa, "kai mutumin nan ya had'u fa kmr wani balarabe , anya ma bai had'a jinsi da rabawan asali ba kuwa ?
Tayiwa zuciyarta wannan tambayar tana murmushin jin dadi "kai wasu dai sun marewa rayuwar duniya "shi da matarsa da yarsu masu shegen kyau duk da yadda mutane suke zuzuta nata kyau,ganinsu family din gidan yasa ta raina nata, Dan ko kama kafar nasu kyawun batayi ba ,"ina ma za a had'a?
haka tayita zance zuci tana murmushi kmr wace akayiwa albishiri da samun gidan aljannah.
cikin haka me'ad ta dawo parlour'n ,inda idanunta ya sauka akan najma tana kalle mata fuskar miji batare daya sanin tana tsaye ba..
Gabanta ne yayi wani irin bugawa yashiga dukan uku uku me zata gani yau kuma ?
"Ba dai mijinta take satar kallo ba?
" inna lillahi wa inna ilaihi rajiun tashiga furtawa acikin zuciyarta gabanta na sake dokawa, yayinda ahankali tashiga d'aga kafafunta zuwa inda najma ke tsaye tana cigaba da kallonsa ,me'ad nagama karasowa bata tsaya wata wata ba ta damki bayan wuyanta batare da tace mata uffan ba ta nufin hanyar karamin parlour daita, sannan ta sakar mata wuya tare da ingizata tana aika mata da wani irin mugun kallo a kaskance, wanda take hanjin colin najma tasoma cakudewa ta hau mazurai jikinta na rawa ,take tayi saurin durkushewa kasa ta dukar da kanta kasa tana wasa da yatsun hannuwanta tana jiran jin abinda zai fito daga bakin uwar d'akinta .
adduar take aranta Allah yasa bata kamata tana kallon mijinta ba, kafin kace tuni gumi yashiga tsatsafo mata zuciyarta na bugawa kmr yadda na me'ad ke harbawa ,tsawon minti goma najma na durkushe Amman Dan tsabar wulakanci me'ad bata ce mata komai ba ,baya ga idanun data tsareta dashi Wanda ita najma take jin kmr ta tashi ta zura aguje tabar gidan.
sai data gama kallonta a wulakance sannan ta yatsina fuska tace " ke Dan ubanki me yasa kike kallon mijina?
"na kawoki gidana Dan ki dinga kallon mijina ne?
"Ko daman abinda ya kawoki kenan ki dinga satar kallon mazajen mutane yasa kike yawon aikatau agidajen mutane?
Tayi mata tmbyr tana zabga mata uwar harara. Najma tayi saurin d'ago kanta tana girgiza mata kai ..
"Aiki na kawoki kiyi min ba kallon mijina ba ... ?
"Lalura ce yasa nace akawoki min ke Dan ubanki domin ki dinga kula min da yarinyata, Ba wai kishiga hurumin gidana ba Dan I can't take this nonsense, shara wanke wanke da sauran ayyukan gidan bance kimin ba, kinsa kanki ne non of my business Dan bakurtuwa bace ni zan iya abina , ni dai magani kawai nace kibawa yarinyata akan kaida tare da bata kulawar datace while kudin aikinki kuma momy ce zata dinga bawa iyayenki Dan haka banga dalilin da zai saka ki dinga labe kina kallon min miji ba ko kina son shi ne?
Da sauri Najma ta d'ago ta kalli me'ad cikin mamaki jin furucinta ,"yanzu ita tunaninta kenan ita har ga Allah bawai sonshi take ba ya dai mata kyau ne kawai yasa ta kalleshi .
A matukar tsawace me'ad tace "me nene kikayi saurin kallona, ko karya nake miki ba kallon mijina na kamaki kinayi ba ?
Najma ta sunkuyar da kanta cikin fargaba "wayyohlly Allah ka ceceni meye kaini kallonsa gashi najawo kaina tozarci..?
"Dan ubanki daga yau na sake ganin kin la'be kina kallon min miji sai na miki dukan mutuwa sannan na tattaraki na aikawa iyayenki da ragowar gangar jikinki stupid kawai yara kanana daku sai jarabar iskanci tsiya ,yanzu ma kisawa ranki ba kisamu gidan zama ba ,at anytime zan iya gargad'anki kibar min gida wawiya shasha kawai maza ki tashi ki koma dakinki banason ganin wannan shegiyar fuskar taki..
najma ta tashi duk jikinta yana rawa "kiyi hakuri Dan Allah..
Wunin rana cikin damuwa me'ad ta wuni tana tunanin, ita ba abun ta kori yarinyar ba ace bata da hakuri tacika maseefa,if not