Header Ads
Showing 90001 words to 93000 words out of 163596 words

Chapter 31 - YANCNKI Book Complete by Aisha Bagudu.txt

Ads the beginning of article before Image

02 Jun 2024

1307

Ads at the middle of Article

tuni najma ta fice daga gidan .
Ruwa suka zuba mata sosai sannan ta sauke ajiyar zuciya da karfi dishi dishi take kallonsu kanta na jujjuyawa had'e da sarawa kusan minti goma da kwara mata ruwa ta dawo haiyacinta sosai tana sake dubansu dafe da gefen kanta "ranki ya dad'e wai me ya had'aki da hjy ne har hkn ta faru atsakaninku?"gsky zan so ki tashi ki fice daga gidan nan tun kafin ta dawo ta sameki tak'arasaki. maganganunsa tsab suke shiga cikin kunnenta , ahankali tasoma mikewa har ta mike tana bin bango tare da cewa direba "ahuwa taimaka ka kaini gida dan Allah, bazan iya tuki ba ... da sauri ya zaro duka idanunwansa waje "wa ni zan kaiki gida ranki ya dad'e?
Ta d'aga masa batare datace masa komai ba "a'a wallahi bazan iya ba ,,Dan idan hjy ta dawo tasamu labarin ni na kaiki gida kashina ya bushe ,ki dai lalla'ba kija kanki shi zai fi miki alkairi .
Sororo tayi agurin tana kallonsa da mamaki , me'ad kenan jarabar duniya kowa tsoronta yake ji tayi maganar acikin zuciyarta "ita me'ad tayi yunkurin kashewa Akan d'a nmj, nmj da zai iya rayuwa babu ita aduniya. Nmj da tabbas garesa balle alkwari yanzu inda takasheni fa me take tunani zai faru?"ita ba matsiyaciyar me aikinta bace daba gata da galihu bace balle tayi tunanin idan ta kasheta ta kashe banza.
Tafiya take ahankali tana zance zuci har ta iso inda motarta take tashiga ta zauna tana jin yadda gefen kanta ke cigaba da sarawa, wayarta ta d'auka takira direban gidansu ,cikin minti goma sai gashi ya iso yana rusuna mata cike da girmamawa tace "ya kai ta asibintin da take zuwa ...


**********


Sai gurin takwas din dare nasreen ta bud'e idanunta tana wani irin kukan bakinciki, nurse ta shigo d'akin cikin sauri ta ajiye karamin tiren hannunta wanda ke d'auke da kayan aiki akan table tare da janyo wani flat table gaban gadon nasreen wace tana ganin shigowar nurse ta d'auke kanta ta meida gefe tana cigaba da kukanta .
nurse ta meida tiren kan flat table had'e da sanya safar hannu nasreen ta juyo gefenta hawaye na bin kuncinta "nurse ta kirata muryarta na rawa "I don't want to see you don't come near me plz ,I don't want to see ....
nurse ta bud'e baki da hanci tana dubanta kafin daga bisani tace "ki bari nayi treatment dinki mana ,amatukar tsawace nasreen ta mike zaune "go I don't want to see you, sannan ta koma ta kwanta tana Janyo numfashi da kyar.
"What's wrong with you nasreen?
" bakiga halin da kike ciki ba, kina bukatar kulawarmu,
Kibari na dubaki mana ....
"please, go!
Ihu kawai take tana furta go "I don't want to see likita ne ya fad'o cikin d'akin da sauri yana tambayr abinda ke faruwwa "doctor I wanted to treat her,but she asked me not to touch her, nor come close to her .
doctor yayi shiru yana duban nurse din sannan ya meida idanunsa Kan nasreen dake kwance tana kuka har da shesheka ,"ammm ya fad'i hk tare da k'arasawa gadon da nasreen take ya tsura mata ido kawai yana kallonta gbdy ya kasa cewa komai.
yarinyar na mugu mugun bashi tausayi lamarinta na ta'ba zuciyarsa ,waigowa yayi tare da cewa nurse "you can go.
"Ok sir ta fad'a tana cire safar hannuta kana ta bar d'akin .


Doctor ya matso tare da tura table din dake d'auke da magani gefe sannan yasamu guri ya zauna daga gefen kafafunta yana kare mata kallo ahankali ya kira sunanta "nasreen, you will be fine, okay?
"Ammm permit me to take of yourself I will treat you by my self and you will be fine is that clear?


Ahankali ta waigo hawaye nabin kuncinta tace " doctor all i want from you is to kill me ,"give me poison ,i just want to die ,I ,i heter my self banason cigaba da wannan rayuwa ,ina bukatar barin duniyar nan ....sororo doctor yayi tare da bud'e idanunsa yana cigaba da kallonta kirjinsa na wani irin bugawa saboda jin lafazinta "abun mamaki yarinya karamar irinta ke furta wannan kalmar ..
tana son tasha poison ta mutu to akan me kenan ?
"Ina son na mutu doctor bana bukatar cigaba da rayuwa a duniyar nan ta sake maimaitawa tana kuka....
Cike da matsanancin tashin hankali ya furta kalmar "death.?
"Yes doctor I want to die....ta juyar da kanta...
"What ?
Ya sake furtawa yana dubanta a matukar tsorace , kasa tashi doctor yayi daga cikin inda yake zaune illa dubanta da yaciga da yi tare da rafka tagumi .
Shiru shiru me'ad na jiran ganin fitowar likita Amman shiru hkn yasa ta nufi d'akin din da gudu tana kuka shima fu'ad cikin sauri yabiyo bayanta, gbdy kallo daya zaka mata kasan bata cikin natsuwarta, tunda suka zo asibitin batayi yunkurin komawa gidan ba , "to idan ma ta koma tayi me ?
" ne zata koma tayi a wannan gidan ?
Haka tayita zariya acikin asibitin har zuwa wannan lokacin, sannan bata kira kowa daga bangarenta ba ,Dan har gara fu'ad ta lura da yaje gidan ya dawo, Amman ita zuwansa ba damuwarta bace, damuwarta ahalin yanzu bata wuce ta lafiyar tilon diyarta ba .
Zaune suka iske doctor ya tasa nasreen gaba yana dubanta, da sauri tayo gurin nasreen tana kiran sunan "doc......
AI kuwa nasreen ta zabura ta mike zaune tare da dakatar da uwar ta hanyar cewa "go back mummy I don't want to see you, plz go !!!! Shi kansa doctor sai dayayi shock a zaune agurin,wannan abinda me faruwa gaske ne ko mafarki ne ?
A matukar firgice me'ad da fu'ad suka shiga kallon kallo atsakaninsu suna zare ido. da kyar fu'ad yayi karfin halin cewa "did you hear her? Yana kallon kwayar idanun me'ad.
"Did you hear what she said?
Runtse idanunta tayi hawayen bakinciki biyu biyu na gangaro mata, magana take son yi Amman ko tace zatayi maganar bazata fito ba saboda cikin halin tashin hankali datake ciki ,Dan haka ta bud'e idanunta dake cike da ruwan hawaye ta d'aurasu Akan yarinyarta tana mata kallon karta mata .....
Hawaye sha'be sha'be a kwance a kuncinta nasreen ta sake cewa "I don't want to see any of you here, Plz just go...
doctor ya d'ago ya dubesu yana girgiza kai sannan yace "fatan kunji abinda yarinyarku tace ?
"Yanxu dai kuje daga waje tukun am coming to see you guy's.
"Doctor including me ..?
Fu'ad ya fad'a cike da tsantsar mamaki da tashin hankali, yana duban nasreen dinsa.
a matukar fusace doctor yace "you guy's leave plz.."both of you should leave! Me'ad ta nuna kofar fita idanunta na kan nasreen dake kuka ,da hannun doctor ya nuna musu hanya alamun hk yake nufi .
jiki a sanyaye me'ad tasoma d'aga kafafunta still idanunta na Kan diyarta wanda zuwa lokacin tuni fu'ad ya bar d'akin dafe da goshinsa .
bayan fitarsu doctor ya sauke naunayen ajiyar zuciya yana me d'aura hannunsa akan bakinsa "ammmmm nasreen ya furta ahankali,"just calm down okay.
"I understand you Amman meyasa kikayiwa iyayenki hk alhalin suna matsanancin kaunar suga kin rayu?
"No doctor don't say that basa sona wallahi ,sun fi son na mutuwa .........
"Kullun cikin fad'a suke a tun sanda kace cikinsu daya zai ajiye aikinsa ,nan tashiga koro masa komai tun daga farko har zuwa abinda idanunta ya gane mata momy'nta na yunkurin aikatawa "shiyasa ni dai ka taimakeni kabani poison na sha na mutu .......
"doctor ya girgiza kansa kawai sannan yace "ki daina furta wannan kalmar bata da kyau ga duk wani cikakken Muslim ,"ko bakinsa duk Wanda yayi yunkurin kashe kansa da kansa amatsayin kafuri zai tashi agurin Allah ba ?
"Dan haka karki sake furta wannan kalmar bata da kyau okay,?
Ta matso wasu hawayen batare da tace komai ba," ya Mike ya bar d'akin zuwa office dinsa, inda yasa ayi masa kiransu ,da gudu me'ad tashigo office din tana goge hawayen idanunta.


Zaune suke agaban doctor gabadayansu a firgici suke, kowanensu da abinda zuciyarsa ke kismawa Akan wannan kiran da likita yayi musu, doctor ya zuba uban tagumin yana sake tunanin zantuttukan nasreen kalma daya ce tafi kowace kalma muni da daci garesa kmr "doctor give me poison I want to die ......
"Wannan Kalmar tayi matukar gigitashi da tsaya masa arai, tsawon minti goma suna zaune still doctor yaki ce musu k'ala Me'ad ta matsu ta matsu bataji abinda doctor yakirasu dominsa ba ,yayinda zuciyarta ta dinga tsinkewa da rawa rawa ,banda zare idanuwa babu abinda take ,ganin shirun yayi yawa yasa me'ad kasa hakuri tace "doctor, what's exactly happened to my child?
"Ina jin tsoro doctor kar wani abu ya sameta ,I think ba ciwonta bane ..? Doctor yayi shr yacigaba da jimami yana ta'be baki .
"doctor wai meke faruwa ne kabarmu zaune cikin tashin hankali Dan Allah ka sanar mana da abinda ke faruwa da yarinyarmu ?
Inji cewar fu'ad.
Ahankali doctor ya kallesu kana ya dukar kansa na minti biyu sannan ya sake d'agowa yace "do you guy's want to know what is going on?
Da sauri suka had'a baki gurin cewa "yes muna bukatar sani .


"Both of you are not good parent to child ." what ?
me'ad ta furta tare da barin bakinta a bud'e .
Fu'ad yace "har dani kake nufi ko da wannan datake zaune kake mgn ?
Doctor yace "dukanku nake mgn , sannan duk inda aka kira iyayen arziki masu son yaransu da son farincikinsu ,idan irinku suka fito wallahi kamata yayi aka maku ayi muku dukan mutuwa ,ko kuma ad'aureku ajikin kujera har ku mutu .... "what suka furta atare?
" yes I mean it inji cewar doctor yana masu kallon banza "saboda gabadayanku mugaye ne sannan baku da halin kirki you are not a good parent at all...for ten years old girl to be considering death as an option..
"what doctor ?
Inji cewar me'ad gabanta na wani irin mahaukacin bugu "yes she ask me to give her poison because her parents do not like her yet you call yourself parents.
"kai kai doctor it can be possible ya dafe goshinsa yana girgiza kai..numfashi me'ad tasoma ja kmr me cutar asm "um umm uhmm sai kuma kuka ya kwace mata, take kuma jikinta ya sake d'aukar rawa ta juya ahankali tana zabgawa fu'ad harara had'e da kallon banza .
bai kulata ba illa muryarsa cike da in ina yace "doctor can I go see her and talk to her?
"You can't see her right now..
"ah!
Suka furta atare suna duban doctor.
Doctor yace "am telling you you guy's can't see her.


Me'ad ta watsawa fu'ad wata katuwar harara kmr idanunta zasuyo waje "ai kaga abinda kayi ko ,kaga abinda sanadin matsalarka zata haifar ko ?
"Bari kaji in gaya maka wani sabon labari ,wallahi wallahi idan wani abu yasamu yarinyarta bazan yarda ba ,Idan kuma ta mutu heeeeeeeee....."kai dai kayi adduar kar wani abu yasamu yarinyarta kawai ,Dan idan wani abu ya ta'ba lfyrta sakamakon abinda ya faru kasawa ranka kaima mutuwa zakayi......dan wallahi tallahi kotu ce zata rabu da kai ,takarasa mgnr tana kuka "ni nasan wahalar Dana sha akanta tun daga d'aukar cikinta har zuwa yau din nan .."haihuwarta kawai kikayi Amman na fiki son nasreen da bukatar lta araye "uhmmmmm uhmmmmm!!! Tashiga sauke ajiyar zuciya tana kuka tana jijiga kafarta.


"plz can I go and see her plz? "I need to talk to my daughter inji cewar fu'ad da gbdy ya susuce kuka kawai yake son yi ko shima zai ji sanyi aransa, "nasreen dinsa ke adduar mutuwa, tana bukatar mutuwa saboda matsalar shi da mahaifiyarta..wannan wace irin rayuwa ce?
,"ya Allah karka kashe min ita, ina sonta , ya dafe kanshi tare da dukar da kasa gbdy yasoma jin duniyar tana jujjuyawa dashi "wani irin zunubi ya aikatawa ubangijinsa haka,da abubuwa suke faruwa dashi hk?
Zuciyarsa ce tayi saurin kwa'bersa" karkayi sabo fu'ad kai muslimi da kasan da kaddara me kyau ko akasin hk, ka d'auka duk abinda ke faruwa dakai kaddaraka ce tazo da hkn wanda bazaka ta'ba gogewa ba ,a sukwane ya d'ago idanunsa da suka yi jawur tmkr garwashin wuta yana duban me'ad ..


"Ba yanzu bane lokacin kukanka fu'ad, kajira lokacin da yarinyata zata mutu, ranar zaka sha kallon abinda zai faru atsakaninmu," doctor idan duk damuwar nasreen ni ake cewa naji na yarda na Amince, but na yau babu hannu ciki shine musababbin faruwar komai, Amman wallahi nasreen Dina ta mutu sai duniya tasan damu, Dan ina tabbatar maka gidan tv daban daban za'a dinga watso labaranmu.
"just imagine doctor ya fad'a yana mata kallon banza "that was exactly what I was still talking about, "is this the way you supposed to be doing now?
Tayi saurin girgiza masa kai tana zaro idanuwa "see .. both of you can't see her "
ah fu'ad ya furta yana me bud'e baki "yes wallahi bazan bari ku ganta ba ,hk kawai kuje da maseefarku ku k'arasa yarinya mara lfy ......"Dan girman Allah doctor kabarni ni kad'ai naje naganta nasan zata saurareni, after all ina bukatar ganin yanayin jikinta,ina bukatar jin dumin jikin yarinta.."duka acikin babu wanda zakayi ,ku tashi ku tafi plz ina da abubuwan yi ...


Tsam me'ad ta tashi tasoma d'aga kafafunta tmkr wace bata da laka ajikinta,while hawaye na tsiyaya a saman kuncinta har ta iso harabar asibitin, daya wadatu da hasken wutar lantarki tasamu guri daga gefe ta zauna a kasa still tana cigaba da zubar da hawaye , ahankali ta sanya hannuwanta duka ta rungume jikinta tare d'aga idanunta sama tana kallon sararin samaniya, tana tunanin rayuwa kuka take sosai kmr ranta zai fita ,"wayyohlly Allah nah... ..ina zan saka raina naji dadi?
"Ya Allah ka d'auki rayuwata na huta da ganin tarin bakinciki dake kokarin kusanto rayuwata, "Allah na rokeka ka kasheni kafin naga abinda fu'ad yake shirin aikata min ....
tana cikin wannan halin fu'ad ya fito yana dube duben nemanta can ya hangota zaune takure da jikinta tana kuka .
ya runtse idanunsa sannan ya k'araso inda take ya tsaya akanta "mead ya kira sunanta da sanyayyiyar murya "me yasa kika barni kika dawo nan kina kuka? Wannan karon Yayi mgnr muryarsa cike da tausayawa sannan ahankali.
Ya matso sosai kusa daita tare da durkusawa agabanta "why did you left me there and weeping outside ?


Bata kula shi ba tacigaba da kukanta tana goge hawaye, wasu na sake gangarowa ya sake matsota sosai kmr zai shige jikinta, "don't do this to me plz ,the doctor has promised us that she will be fine let's keep praying for her, after all ,we are not god dole mujira hukuncin Allah garemu ...
ya kamo laulausar tafin hannuta cikin nasa "dan Allah ki natsu ki kwantar da hankalinki babu abinda zai sameta "am..am scared I don't want lose her takarasa mgnr tana mai sakin wani irin kuka ..
ta kwanto jikinsa tana kuka yanyota yayi jikinsa ya rungumeta tsam ya manna fuskarta daidai saitin zuciyarsa dake bugawa, yasoma rarrashinta "you are not going to lose her ,okay? " InshaAllahu zamu rayu tare da diyarmu, ki daina kawo mata mutuwa, Dan zamu iya mutuwa mu barta babu ruwan Allah.
Cikin halin datake ciki , ta tuno da abinda yake son shuka mata, ai batare da 'bata lokaci ba ta fixge jikinta daga nashi ta Mike tsaye tana kallonsa kafin daga bisani tasoma tafiya cikin sauri tana kuka ,shima ya biyo bayanta yana kiran sunanta "mead ina zaki, ki dawo idan gida zaki na kaiki. tayi masa banza tacigaba da tafiyarta har takarasa bakin titi tana kokarin tsaida abun hawa "karki soma me'ad..karki soma shiga kowace mota.
"Zan shiga so that idan na shiga ka sakeni ,wanda daman abinda nafi bukata kenan daga gareka tana fad'ar hk ta juya a fusace daidai lokacin da wani me adaidaita ya tsaya agabanta yana tmbyr inda zata.
Tun kafin ta bud'e bakinta fu'ad yayi saurin cewa "ka wuce kawai tare muke daita, idan km kayi k'ok'arin d'aukarta sai dai wani ba kai ba ,yakarasa mgnr ya kamo hannuta da niyyar komawa cikin hospital, tasoma turturjewa" kabarni fu'ad banason abinda kake min, "me yasa kake son kasheni tun kwanakina basu cika ba ..?
"Kece kike son kashe kanki da kanki ,amman karki damu bazaki mutu yanzu ba ,har sai kinga aurena da matana guda biyu.
"Ina ai bazan so ki mutu tun yanzu ba matata, kece fa kikace am your husband for life, har tsufa muna tare ko kin manta da kin furta hkn ?
"Ki tuna idan kuma kin manta gashin na tuna miki,aurena da 'yammatana babu fashi ,zance saki sakanina dake babu shi ,Dan HK muje kisamu natsuwar zuciya.
Ta tattara iya karfinta ta fixge daga rikon da yayi mata ta juya cikin sauri tayi tafiyarta ,sai dai taku daya zuwa biyu yayi ya damketa tare da yin sama daita jama'a kan titi da idanunsu ke kansu suka bisu da kallo, har sanda ya sanyata cikin mota shima yashiga ya kule yana me fuskantarta.muryarsa a matukar sanyaye yace "Keleni me'ad, sannan ki natsu kibani aron hankalinki muyi mgn ta fahimta ."matukar Akan zance aurenka ne bazan ta'ba fahimtarka ba ,ince ba'ayin aure dole?"Dan Allah dan Annabi ka rabu dani da nace ina sonka zan rayu da kai yanzu kuma banayi kaje byn sajida da najma ka k'ara wasu ,ni dai me'ad ban sake komawa aurnka Allah ya had'a kowa da rabon...bata k'arasa ba taji ya buge mata baki "idan kika sake furta wannan kalmar zan zaki had'u da fushina da baki ta'ba ganin ba ,yanzu dai mu ajiye komai har sanda nasreen zata samu lfy aure kuma babu fashi zanyi ,let me tell you

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads