Showing 24001 words to 27000 words out of 163596 words
Chapter 9 - YANCNKI Book Complete by Aisha Bagudu.txt
nasan fu'ad ba sauraranta zaiyi ba ,dan shi bashi da lokacin mace ,mata nawa suka nuna suna son shi Amman yaki?
********
bangare me'ad kuwa zuciyarta ce ke mugun buguwa a tun sanda tashiga bayan motar tare da hasko mata kyakkwar fuskarsa "tun datake bata ta'ba had'uwa da saurayin daya tsaya mata arai ba kmr shi, sai dai daganin zai yi jin kai da girman kai tattare da isa.
zaune suke su uku sajida misna hailat , sun mugun tsurawa TV plazma ido dake manne da bango suna kallon batakashin da'aka tafka tsakanin 'yanta'ada da ma'aikan sack a dapemu express way dake jahar lagos "barkanmu ,a yau anyi musayar wuta tsakanin 'yansanda ,da 'yanta'ada an samu nasarar harbe wani dan ta'ada me hatsari, acp aliyu rano da jamiansa su sukayi nasarar harbe nabel wanda ya kasance babban dan ta'adar da jamian tsoro suka dade suna nemansa a fadin jahar nan.
"yeeeeee babana yazamo zakaran gwaji..... sajida tasoma murna har da tsallenta "nasan kwanan nan za'ayi wa babana k'arin girma...murna take sosai tare da rungume misna dake kusa daita "gsky na taya dad dinki murna sosai inji cewar misna , hayaniya ce ta kaure atsakaninsu kowanensu na fad'ar albarkacin bakinsu.
me'ad tashigo hadadden parlour'n gidan wanda ya k'awatu tamkar da tayis akayi ginin ,gashi an zagaye shi da manya furanin.
hannuta rike da karamar jaka wace bata wuce a sakalata a tsintsiyar hannuta ba tana juyi sanye cikin doguwar rigar " kawayena yau na had'u da wani saurayi kuma ko wallahi kyakkyawa gaske ne kalar launi danafi so.. takaraso garesu tana murmushin jin dadi "kunji aunty dan allah da wata magana ana labari da d'umi d'uminsa ke kuma kina labarin wani saurayi , "dan Allah malama kiyiwa mutane shiru had'ad'd'e ne fa sosai, Allah ina gaya muku duk fadin garin nan babu me kyawumsa ta karasa fad'ar hk tana sake juya jikinta .
"haka zakice tunda zuciyarki ta yaba dashi ba ,da baki yaba dashi ba duk kyawunsa sai kin nemo makusansa" kmr kinsani kuwa inji cewar misna .
"wai ina miki wasa ne suhailat, ko dake nake maganata? ta fad'i hkn tana tsaki sannan ta fuskanci sajida da misna.
"ku kuma daku fa nake mgn amman kuka min shr , ba ma zaku saurareni ba ,kuna can kallon kwazon da acp yayi "ke dai bari me'ad Allah ina cikin jin dadi yau ,ina ma mama tana raye ta dinganin irin cigaban da baba yake samu, wannan furunci da sajida tayi yasa me'ad kasa cigaba da tsayuwa a gurin ta nufi hanyar d'akinta tana magana "Allah ya jikanta sai dai ki shiyawa jinyar dad dinki bayan kingama tayasa murna k'arin girman da zai samun saboda 'yanta'ada sun harbeshi .
da sauri sajida ta mike jikinta na rawa tabiyo bayanta atare suka shiga dakin "da gaske an harbi dady?
"ke baki lura ba, bakiga ya dafe hannunsa na dama ba?
"ina tunanin anan aka harbe.......
ai sajida bata jira jin karashen zance ba, tayi waje aguje tana kiran layin dad dinta, tayi sa'a ya d'auka "hello dady..
"sajida kina lfy?
" ina lafiya dady kana ina?" yanxu me'ad ke gaya min wata mgn da gaske ne 'yan ta'ada sun harbeka?
"gaky ne sajida ,duk boyewar dana yi ashe ta lura, to dai ki kwantar min da hankalinki, yanzu haka an cire min harsashi , mu had'u a gida, kashe wayarta tayi tare da bud'e murfin motata tashiga ta bar gidansu mead a guje.
mmn sudais ce[11/3, 8:25 AM] El~hajj: ππππππ
'YAN CINKI
ππππ
ππππππ
~NA~
*AYSHA A BAGUDO*
~DEDICATED TO~
MRS ADAM
( YAR MUTAN KAGARA)
page 42 to 44
......Ahankali malik ya sauke kwayar idanunsa akan NASREEN dake kwance ajikinsa ,wacce bacci yasoma kok'arin d'aukarta amman son jin labarin had'uwar iyayenta ya hanata runtsawa .
shiru malik yayi yana dubanta batare da yacigaba ba, ya d'auki sama da minti goma a zaune kawao yana kallon NASREEN cike da tausauawa, yarinyar tana bukatar kulawa takowani bangare, amman tarasa shirun da NASREEN taji yayi yawa ne yasa ta, bud'e idanunta dake runtse taki sunansa "Uncle malik continue now.... kacigaba ina son jin komai, domin kai kad'ai ne zaka iya 'bata lokacinka ka gaya min.
"NASREEN ...ya kira sunanta a sanyaye "na'am unlce "kwalkwaluwarki bazata iya d'aukar sauran labarin ba.. "zan iya uncle am getting to 10yrs now babu abinda zaka fad'a da bazan fahimta ba.. ina jin tausayin dad dina dayawa, ina son nasani wani abu akansa takarasa maganar tana meida kanta bisa cinyarsa..
naunayen ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa "daga bangaren fu'ad da me'ad babu wanda bansan halin dayake ciki ba, akoda yaushe muna tare da fu'ad, haka me'ad duk inda tasanya kafa ina biye daita sai dai a iya nan zan tsaya ... ya d'auke kanta akan cinyarsa ya meida kan karamin kushin din dake jingine da kujera, sannan ya mike tsaye yana duba agogon bangon parlour'n karfe tara ta wuce da wasu 'yan mintunoni, wayarsa ya ciro daga gaban aljihun gaban rigarsa yana kokarin neman layin fu'ad, sai gashi ya fito "yauwa zo kaji da wannan yar rigimar taka, ta matsa,lallai sai taji haduwarku da me'ad, ni dai nayi kok'arin sanar daita kad'an daga cikin had'uwarku sauran kuwa na barta da bagudo takarasa mata yakarasa fadar hk yana murmushi, murmushi fu'ad yayi shima sannan yakaraso inda take kwance kmr ruwa , ya komata ya zaunar daita tare da yi mata makari da pillow ta bayanta "kinji abinda uncle malik yace ?
"ni ..ni naji amman babu ruwana dashi tunda yaki yacigaba dabani labarin, takarasa mgnr muryarta a shagwabe kmr zatayi kuka,kissing din goshinta yayi "don't cry my bby rabu dashi kinji bby nah ni da kaina ma sai nabaki, ai zaki fi son nawa ko?
ta gyda masa kai kawai batare da tace komai ba fu'ad ya fuskanci malik "yanaga kana kok'arin tafiya batare da kaci komai ba?
"kai rabani da cin abincin nan, yanzu ina ci idan naje gida sai nayi bayani daya bayan daya, an dinga yi min qausetion's kenan ,gara kawai idan na koma gidan naci gbdy, ok muje na taka maka "baby nan ina zuwa just give me w minti .
har waje fu'ad ya rako malik suna sake tautaunawa akan sha'anin rayuwa, da hakuri da rayuwar ita karon kanta ...
koda fu'ad ya koma parlour'n bai iske NASREEN ba ,dan hk kai tsaye ya nufi d'akinta ,inda ya isketa kwance cikin blanket dinta, ya yaye blanket din tare da d'aura hannunsa kanta "my bby kin sha maganinki? "yes dady .
"ok kiyi bacci abinki Allah ya baki lfy me d'aurewa .
"ameen babana, shiyasa nake sonka.....
"i love you more yacigaba da zama yana dubanta tana matukar bashi tausayi yana jin kmr ya ajiye komai ya bata kulawar data dace, ita kad'ai garesa kmr yadda ya kasance, a zahirin gasky baya son yarasata duk da kasancewarta mai karancin lfy yana sonta hk... tsawon lokaci yana zaune yana tunani har sanda bacci ya d'auketa sannan ya yunkura ya tashi ya nufi d'akinsa ya kwanta lamo akan gadon yana tunani ya saka wancan ya kwance wancan, runtse idanunsa yayi sosai yana kiran sunan Allah, ahankali ya bude idanunsa wanda suka kad'a sukayi jawur saboda tuno abinda yake yi masa cikin rayuwarsa, a filli yace "nayi dana sanin aurenki me'ad dana san hk zaki zamomin arayuwata da ban yi kuskuren aureki ba...hawaye ne yaji suna sauka masa akan kuncinsa ,cikin sauri ya sharesu, lokacin ne wayarsa ta d'auki kara, ya kai hannunsa ya d'auka akan bed side ya manna a kunnesa batare daya duba ba.
sautin muryarta yaji ta doki dodon kunneshi ,yayi Shiru tare da janyo pillow ya manna akirjinsa ya rungume tsam sbd d'and'anon dadin muryar "hello hello fu'ad kana jina !! ta sake maimaitawa akaro na biyu.
"uhmm ya'akayi kira adaidai wannan lokacin ko kin manta ina iyali ne ?
"am sorry for disturbing you , but ina son ka saurareni fu'ad kaji abinda za....
saurin katseta yayi ta hanyar cewa "sauraran me zanyi miki, karki meidani wani shasha mana ,ta yaya kike kokarin manta dangantakarki da me'ad mana ,karki manta har yanzu me'ad matsayin matata take, dan me kike kokarin sanyo damuwa acikin wace nake ciki....?
" fu'ad ka saurareni mana, haba fu'ad ya dace ace nasamu kar'buwa a wajenka a daidai wannan lokacin, na d'auki sama da shekaru goma ina dakon soyayyarka batare dana fayace maka ba .
" wannan damace tazo mana, kabari mu dama mana dan Allah ... karka ki amsar soyyayata saboda dan adam daraja garesa, idan ka amince zaka aureni zan ajiye komai har aikina domin na baka farinciki dakarasa.
"dakata dakata malama enough is enough don't talk any rubbish.. "kinsa yadda zaki bani faricikin any not ki fahimtar da me'ad tabi abinda nake so domin a zauna lafiya?
" ni dai ka ajiye mgnr wata me'ad kawai ka amince da au..
"ok baxaki iya bata wannan shawarar ba amman zaki iya shigowa gidanta amatsayin kishiyarta ko...?
"ka fahimceni fu'ad ba ...
"babu wata fahimtarki da zanyi idan ma aure nake da bukata ,bake zan aura ba.... bake ya dace na aura ba, ina da ido nasan inda mata suke okay, dan haka ki shafa min lfy if not zan gayawa me'ad da kaina tasan yadda zatayi dake ya katse kiran yana fitar da numfashi sama sama.
"meyasa kayi haka?
zuciyarsa ta kismamashi hkn, "m e yasa baka amshi tayin soyayyarta ba?
take yabawa zuciyarsa amsa da, bazan k'ara wannan kuskuren ba bazan sake kuskuren auren ya'yan masu arziki ba.......
a ranar fu'ad baiyi ishashen bacci ba, juyi kawai yake ga tunanin ciwon NASREEN ga kewar iyayensa dake addabarsa uwa uba matsalar me'ad da sabuwar matsalar dake shirin kunno kai, har karfe daya ta buga fu'ad bai san yadda zai yi da al'amura dake kokarin kusowa rayuwarsa ba. ahankali tunanin haduwarsa da me'ad ya dinga zuwa masa daki har zuwa lokacin da sajida ta bar gidansu me'ad agigice zuwa gidansu taga lafiyar mahaifinta .
"koda sajida ta koma gida hankalinta yayi matukar tashi saboda ganin raunin harbin da d'anta'ada yayi masa, kuka take sosai tana "furta sannu dady ..shi kuma yana rarashinta da kyar dai yasamu tayi shiru.
ita kuwa me'ad bayan ta tagama kimtsa kanta tattare da tunanin sabon fuskar data tsaya mata arai ta nufo hanyar parlour tana kwallawa me aikinsu kira " ummi ummi!! har takaraso parlour'n shiru babu kowa hatta misna da suhailat basu gurin, nan ranta ya soma baci tashiga kai kawo ta sake dawowa cikin parlour'n tattare da matsancin damuwa tasamu guri ta zauna tare da d'aura kafar daya kan daya tana girgizawa tare da cizon yatsanta ummi dake d'akin suhailat tana mata guga tayi saurin ajiye Iron ta fito da gudu tana haki, cikin rawar murya tace "aunty gani me'ad ta d'auke kanta cikin isa tace, "ummi ina son tambayarki...
ummi ta d'aga kanta da sauri cikin tsoro jikinta yana rawa tace "kiyi duk irin tambarki da kike so.
me'ad ta sake d'aure fuska kana tace "wai shin nan gidan ubanki, ko kuwa da gadonki acikin wannan gida..?
da sauri ummi ta sake d'ago fuskarta ta kalli me'ad lokaci guda, kuma tayi saurin d'aukewa dan wani irin kallon da me'ad ta watso mata, sannan cikin rawar muryar tace babu ko daya sai dai kawai cin arziki danake yi acikinsa.
"okay a she kinsan cin arziki kike yi amman kike neman kifi ya'yan gida sakewa, ki km fisu iko ko?
ita dai ummi tayi shiru kawai tana kallon kasa dan daman hk halin me'ad din yake duk wanda yake kasanta ,sai yayi hakuri, in kuwa ba hk ba zai rasa aikinsa acikin kankanin lokaci. me'ad ta girgiza kafarta cikin isa da iko "daga yau duk sanda na sake kiranki, kikayi banza dani wallahi kinji na rantse in har baki rasa aikinki ba, zaki had'u fushina jahila kawai dabba mummuna.......
mmn sudais ce
[11/3, 8:25 AM] El~hajj: ππππππ
'YAN CINKI
ππππ
ππππππ
~NA~
*AYSHA A BAGUDO*
~DEDICATED TO~
MRS ADAM
( YAR MUTAN KAGARA)
page 45 to 46
........."Wallahi Ba kiga yadda na tsanaki ba, ji nake kmr na kasheki ta had'e hannunwanta duka biyu al'amun da gaske zata iya aikatawa abinda ta furta .
da sauri ummi taja baya tare da furta " Dan Allah aunty kiyi hakuri Insha'allahu bazan sake ba,zan kiyaye ....
"Kar ma ki kiyayye kiga yadda zanyi dake .
"Kiyi hakuri ta sake furtawa jikinta a sanyaye "Dan Allah malama banason long talk tashi ki bani guri kazama kawai.
Ummi ta mike jiki a sanyaye babu laka ta fito, idan da sabo tarigada ta saba da wulakancin me'ad.
Me'ad taja dagon tsaki lokaci daya taji gabanta yayi wani irin mahaukacin bugu da karfi , tayi shiru tana tunanin abinda ya sata jin hk, take fuskar fu'ad tasoma yi mata gizo acikin 'kwal'kwaluwarta ,runtse idanunta tayi kawai ta d'auki wayarta tare da mikewa tsaye ta haye sama inda mahaifiyarta take zaune da system agabanta tana tura sakonni, shigowarta d'akin yasa mom dinta d'agowa tare da cewa " yauwa gara da kika shigo, yanzu nake son aikawa akira min ke, me'ad takaraso jiki a sanyaye ta zauna kusa daita "gani sweet momy dina,ina matukar alfahari da kasancewarki mamana "uhmmmmm dan kinga abbanki baya kasar ba,?
"kai momy wai meyasa kike kishi da dad ne?
"nifa gbdyanku ina sonku domin banida abin so fiyye daku a duniya ku ne komai na.
"kinga bason zance karya ina file din da hjy maryam tace ta tura dazu da safe?
tsam tayi da ranta sannan tace" yana cikin jakata "okay je ki zo min dashi yanzu akan aikinsa nake.
cikin mintina kad'an me'ad ta fito daga d'akin mom dinta , ta nufi d'akinta tasoma duba jakarta amman abun mamaki babu diary dinta ballanatana file din dake ciki, gabanta ne ya sake fad'awa , lokacin da 'kwal'kwaluwarta ta hasko mata ko dai ta yarda dashi agurin batakashin da ya rutsa daita gurin cirar kudi.. "tabbas in har bata ganshi ba definitely acan ta yar, ta furta hkn a fili tana cigaba da bincike gefe da gefen jakarta sannan cikin sauri ta fito da niyyar komawa gurin, har zata fita sai taga kmr shigarta batayi ba, basani ba, ko zata sake had'uwa da wannan kyakkyawan fu'ad , Dan haka takoma cikin d'akinta .
ta fito cikin wani koren voyal dinki doguwar riga har kasa ba D'an kwali a kanta ,sai koren mayafin data yane kanta dashi, takalman kafarta suma duk kore ne, ta cigaba da tafiya cikin yanga, ta isa inda aka tanada domin ajiye motocin gidan, ta tsaya tana karewa motocin kallo ,4mart itace wace zuciyarta tabata umarnin shiga .
Tun kafin ta kunna motar me gadi ya zabura ya mike tsaye, yasoma kok'arin bud'e mata get, ahankali tasanyo hancin motarta wajen gidan..a natse take tukin m .
kai tsaye ta d'auki hanyar isa inda suka had'u da fuad ,cikin kankanin lokaci ta iso ,tasamu guri tayi parking din motarta ,tana bin gurin da kallo abubuwan da suka faru a d'azu da safe ne suka shiga dawo mata, tun daga kan sanda ta d'aura idanunta akansa ,har zuwa lokacin data nutse a tsakiyar faffad'an kirjinsa...fuskarsa , ajinsa, jin k'ansa da komai nashi sunyi mata ,ta dad'e bata ga halitar da kai tsaye aganin farko ya mamaye zuciyarta ba .
fitowa tayi daga cikin motar ahankali tana dube dube, duk da zuciyarta na tabbatar mata bazata gansa ba adaidai wannan lokacin ,dan haka tasoma duba inda suka had'u, bata jin ATM dinta domin tasan cikin kankanin lokaci zata mallaki wani ,tafi bukatar diary din dake d'auke da manya sirrinkan rayuwarta tare da file din momy dinta, da shi kanshi fu'ad ,Saboda idanunta na matukar kwad'ayin sake ganinsa .
ta kasa hakuri tsayuwa guri daya, tayi tafiya me nisa dan har ta kusan shiga alimoshi local government, amman bata ga ko mai kama da fu'ad ba da diary dinta , sannan ta dawo gida cikin wani irin 'bacin rai ,cikin sarsarrafa ta shiga parlour'n, yau kam gabadaya a sama take jin kanta, kuma duk wanda yayi kok'arin shiga track dinta zai had'u da 'bacin rainta.
a daidai tsakiyar parlour'n suka ci karo da mahaifiyarta "ke kuma daga ina haka kika yi wani wujiga wujiga dake?
me'ad ta dan tsosa tsakiyar kanta batare da tace komai ba, "dake fa nake magana kina jina?, kinsa banason wannan fitar ta babu gaira babu dalili ko.
takarasa mgnr tana jan tsaki sannan tace "ina file din danace kin kawo min?
"uhmm ammmmm daman shi naje nema ,daxu da safe ko da direbanta ya kawo na shirya zanje injin ciro kudi sai na kar'ba na saka acikin diary dina ,amman narasa komai nawa ina tunani agurin bata kashin nan ya subuce acikin jakata ,"yanzu hk gurin na koma ko zangani amman .....sai tayi shiru ta kasa k'arasa maganarta sakamakon wani irin kallo da uwar ta jiho mata ....
"abinda kike kok'arin cewa baki gani ba, ko ba abinda zaki ce min kenan ba?
me'ad tayi saurin d'aga kanta "kinsan ko file menene kika yarda shi? "
file ne dake tattare da mahimman bayane akan kudad'en marayun ya'yanta, amman kalli yadda sakacinki yasa aka rasashi , keda zaki ajiye abu a gida amman kika fita dashi, nan fa suhailat tafiki kaifin baseera "am really sorry momy zanyi kokari na nemo.. " a ina zakigani?
" zan sake komawa gurin ko Allah zai sa nagani takarasa mgnr tana narke fuska alamun shagwaba.
"ke bar shi kawai zan sake tuntubarta ko tana da wani copy "thank you my mom .... hjy khadeeja ta shige d'akin mai gidan . Ranta babu