Showing 60001 words to 63000 words out of 163596 words
Chapter 21 - YANCNKI Book Complete by Aisha Bagudu.txt
yayi kusa daita cikin sanyayyiyar murya yace "sorry love Allah yayi miki albarka ya biyaki dukkan abinda kike nema duniya da lahira magana yake mata Amman bata San abinda yake cewa va.
Gani yayi kmr bata cikin haiyacinta, ya tabata jikinta yaji zafi rau, tashi yayi ya hada ruwan zafi sosai daidai yadda bazai koneta ba ,ya dawo ya dauketa duk jikinta a sake, sata yayi cikin ruwan zafi ta fasa ihu tare da sakin marayar kuka ta kamkameshi ajikinta har da kiran sunan dady .
"Ki zauna zakiji sauki, girgiza masa kai tai alamun bazata iya ba,"ya Allah ya furta cikin zuciyarsa, anya kuwa ba ciwo yaji mata ba?
Cikin muryar kuka mai cike da ban tausayi tace" Dan Allah kabarni hk bazan iya ba ,zan mutu idan naciga da zama cikin ruwan nan .."ok shikenan bari na gyara miki jikinki kai kawai ta iya daga masa.
Ahankali ya dinga mata wayo yana tsomata cikin ruwan zafin har ta daina jin radadin sannan ya gyarata da kyar ta iya wankan tsarki ,daukota yayi, ya cire bedsheet din daya baci yasa wani duk da ba iyawa yayi ba haka yasa ya Dan gyagyra ya kwantar daita ya mata rufa da blanket ya kwanta kusa daita yana shafa mata kanta zuwa bayanta, kuka take har lokacin Dan ji take kmr kara mata wani azabar yake da hannunsa a haka har bacci ya dauketa Wanda da gani bana jin dadi bane, shi km ya zame jikinsa yaje yayi wanka yadauro alwala ya fara nafilfili nagodewa Allah daya mallaka masa mead amatsayin matarsa ta sunna, addua yayi tayi musu da samun zaman lfy a tsakaninsu Dan farinciki dayake ciki bazai misaltu ba shirin bacci yayi ya kwanta kusa daita tare da kankameta ajikinsa kmr Wanda zaa kwacewa ta hk bacci shima ya daukeshi cike da matsanancin farinciki.
A satin sam fu'ad bai bar mead ta sarara da bukatarsa ba ,gurzarta yake kmr yasamu tuwo, Allah yagani shi nmj ne da yi daya biyu baya isarshi ita kuma sam ba hk take ba, ta dai yi hakurin barinsa yaci angoncinsa a tunaninta da bai saba yi bane yasa yakeyi kmr zai cinyeta.
Aurensu da wata daya fuad yace inna ta dawo gidansu tinda 3 bedroom ne amman Sam inna taki yarda tace "banda abunka fuad ina ni ina zama tare daku,?"kudai kuyi zamanku lfy Allah kade fitina kubarni nan ni dai ka dinga zuwa ina ganinka.
*BAYAN SHEKARA DAYA*
Me'ad ce kwance a cinyar fuad yana shafa gashin kanta, "Na tabbatar da cewa nafi kowane namiji sa'ar abokiyar xama, Yanzu nake Ζara tabbatar da cewa yar halak na aura, tunda muka yi aure babu wanda ya taba jin kanmu, muna rayuwa mai cike da farin ciki, duk yadda aka yi kokarin xuga ki a kan ki rabu da ni,amman baki yarda da hakan ba, dole na gode miki me'ad na kuma cigaba da kula da ke har karshen rayuwata.
Murmushi me'ad tayi tare da shafa kwantaccen sajen da ke kewaye a fuskarsa, na gode da yadda na samu kyakkwan yabo daga wajenka fuad, insha Allah babu Wanda xai ji kanmu har abada, soyayyar su suka ci-gaba da yi mai cike da ban sha'awa ,har zuwa lokacin da suka samu haihuwar nasreen , Wanda tun daga lokacin suka Dan fara samun rashin jituwa atsakaninsu adalilin rashin kulawa da yarinyar, ganin hk yasa inna ta dawo gidansu da zama domin cigaba da kula da yarinyar, daga nan komai ya daidaita, inna ce komai na yarinyar Sam me'ad batasan meye kula daita ba, abinda ke had'ata da yarinyar shan nono shima idan tana gida ,idan zata aiki kuma, sai dai ta tsiyaya mata nono ta ajiye mata ta kama gabanta ,idan kuma tana gida system ne agabanta bata da wani lokacin kowa ,dan idan ta zauna tana daddana system sallah kadai ke tadata, sannan duk wanda ke zaune kusa daita yazama bawa koda kuwa fu'ad ,Dan ta dinga aikesa kenan ,shi kuma tsakani da Allah baya kin mata a ganinsa duk cikin soyayya ne .
Zamansu da inna gwanin dadi da kulawa saboda tsananin kaunar me'ad din datake, komai mead ,aiki idan taga yayi mata yawa zagewa take ta tayata, ita kanta mead na tsananin son inna da bata kulawa Sam bata kaunar abinda zai bata mata rai ,duk abinda zai faranta mata shi take, saboda yadda take kula daita Dan wani lokacin har abincin yi musu take kafin su dawo aiki , sosai mead ke jin dadin zama tare da inna ,bata da mataslar komai ko ta fannin mijinta da kowa illa ta rashin lafiyar yarinyarta saboda tana girma ciwonta na sake bayyana ajikinta, zamansu tare da inna bai d'auki wani dogon lokaci ba, zazzabi kwana daya da yini tal yayi sanadin barinta duniya ,acikin dare inna tace ga garinku, mutuwar da ta kusan haukata fu'ad da mead, sun yi kukan da tun sanda sukazo duniya basu yi irinsa ba ,aka shirya inna zuwa gidanta na gsky.
Bayan rasuwar inna mead tasha daukar masu aiki sai dai ,abun baya zuwa koina, take sallamarsu saboda bala'I datake musu duk abinda sukayi sai taci gyaransu .
Har takai ga rokon ummi mai aikinsu ta gida momy tabata, itama zuwa wani lokaci tace kallon mijinta take da sauransu ta tattarata ta meidaita ,a haka da yau ta canza wannan mai aikin ta kore wancan har nasreen ta girma.
Wannan shine takaitaccen had'uwar mead da fu'ad .
Back to the story
Mmn sudais ce
[11/3, 8:27 AM] El~hajj: ππππππ
'YAN CINKI
ππππ
ππππππ
~NA~
*AYSHA A BAGUDO*
~DEDICATED TO~
MRS ADAM
( YAR MUTAN KAGARA)
Page 65 t0 66
......nasreen kwance akan gadonta lullu'be cikin bargo mai taushi, tana sharar baccinta ,hankali kwance take fitar da numfashi yayinda me'ad ke zaune a gefenta tana gyangyadi , minti daya minti biyu zata bud'e idanunta, taga halin datake ciki, can dai taja naunayen ajiyar zuciya sannan ta bud'e idanunta gabadaya tana furzar da numfashi tana girgiza kai tare da furta "fuad kenan ....
Amman babu komai , komai zai zo qarshe, ba dai gobe Monday ba?" zan sa ido inga yadda gobe zata kasance garemu " how could you ask me to stop my work?
"For what.?
" ai abinda ba zai ma ta'ba yiwuwa bane yake fad'a idan nabar aikin sauran abubuwan da aikin nawa yake taimakawa agidan fa ?
"Shi nawa yake amsa albashinsa da har yake kokarin cewa na ajiye aiki na zauna gida, ta taja tsaki,ba laifinsa bane zan je d'akinsa yanzu nasamesa muyita tak'are .
Jin motsin fitowowarsa yasa ta yunkura ta tashi had'e da kai hannunta saman sumar nasreen ta shafa ahankali sannan tak'arasa mikewa tsaye tana gyara zaman rigarta ta fito daga d'akin .
lokacin da fito parlour'n da niyyar nufar d'akinsa jikinta ne yayi mugu mugun sanyi sakamakon ganinsa kwance datayi akan doguwar kujera cike da matsanancin damuwa, amman sai ta kau da abinda ta gani atattare dashi tashiga aika masa da wani irin kallo kana tasoma takowa zuwa inda yake kwance tana kiran sunansa cikin d'aga murya"abban nasreen!!!
Duk kiran da take masa yana jinta sarai yayi mata banza tamkr bada shi take ba har taka'raso ta zauna kusa dashi ta shafa hannunsa zuwa wuyansa... "fuad still shiru yayi mata sai numfashinsa da yayi saurin d'aukewa dan ji kmr ta jona masa electric ne ajikinsa, ahankali ta kwanto jikinsa har nonuwanta na ta'bo fuskarsa ta saita fuskarta danashi tana shakar numfashisa domin son tabbatar Da baccin yake da gsky ko dai wani shirin ya fito mata dashi....
saurin sake d'auke numfashi yayi saboda zuciyarsa datayi saurin bugawa adalilin jin abinda yafi kauna atare daita sun kawo masa ziyara wanda take yanayinsa ya sauya,lokaci daya zuciyarsa da joystick dinsa tasoma harbawa ....
Ta d'ago daga jikinsa tana yatsina fuska da tsaki "yanzu kai har kaga gurin bacci?" koda yake kana sane fa kakeyi kmr kana bacci alhalin nasan ba baccin kakeyi ba 'amman no problem I will give you as you want it...takarasa fad'ar
tana mai gyara zamanta zuwa kwanciya a gefensa.
"Nasan cewar kana da kafuri taurin kai, Amman idan kace kana da taurin kai nima mahaukaciya ce ,gurin taurin kai har ya zarta naka ,kaima kasan da wannan, kasan halina fa ,kasan halin wacce kake zaune daita ba sai na sake gaya maka ,nasan Kana sane kake wani baccin manufurci saboda bakason akawo karshen matsalar nan dake kasa saboda mugunta ,kasane kake yin abubuwa iri iri so that ranar monday sai gidan ya saura daga ni sai yarinyata ko Dan dai ka 'bata min rai ?
" to wallahi baka isa ,Dan ba yarda zanyi ba ,shine ka wani zo ka kwanta Dan da gari ya waye ka lalla'ba ka shirya da wuri ka wuce aiki batare da nasani ba .."so that I will not have any choice than to stay at home with our child...saboda kasan zuciyata ba zata iya d'aukar barin yarinyata a gida ita kad'ai ba,that's why you are playing different prank, am really ready for you..." wallahi tallahi kaji na rantse da Allah kowa zai gaya min zance ni yakamata na zauna tare da nasreen a gida bazanji ba infact I will not listing to any body ,kai koda kuwa ubana ne zai tako kafafunsa gidan nan adaidai wannan lokacin wallahi bazan yarda ba...
"kai ko inna ce zata ta fito daga cikin kabarinta tabani hakuri bazan hakura ba ,kai kuma daman kasan ina da wannan taurin kai fiyye da naka both of us must iron out the issue on ground before everything could have mess up.
shine kazo kana wani baccin gulma baccin tsiya, baccin munafurci, kai yanzu bacci ne agabanka?
"bansan yaushe ne kake son komai namu yazamo daban Dana sauran mutane ba ...yanzu kai abun alfaharinka ne nasreen tazo tasameka shame shame anan wai kai ubanta kana bacci alhalin ana bukatar solutions ga rayuwarta, ka bud'e idanunka kaga yadda ni bacci ya kaurace nawa idanuwa ....
"But no problem na godewa Allah da yasa yarinyata ta samu bacci ,ni kuma daman ina da lokacin kowani irin wahala coz am ready for trouble tare zamu kwana anan har garin Allah ya waye, bazan baka chance din tashi da wuri ka gudu aiki ka barni da yarinya a gida ba, kana farkawa daga wannan tsinanen baccin naka da kakeyi da kwayar idanuna zaka samo cin karo dashi zaka san dani kake zance zan tabbatar maka da me'ad din dakasani tana nan bata canza ba ,in dai akan wannan matsalar ne bazaka ta'ba samun yadda kake so .
"You know me and I know you uhmmmmm wallahi yau bazan runtsa ba ballanatana bacci ya d'aukeni sai mun samu maslahar wannan matsalartamu tukun .
shi dai fu'ad juya mata baya yayi yacigaba da kwanciyarsa, can wuraren karfe 3 na dare ,wani naunayen bacci ya kawo mata ziyara bata San lokacin data bingire agurin tasoma sharar bacci ba ,shi kuma lokacin yasamu damar mikewa tsaye da kyar yana mika had'e da salati yana dubanta yace "wahalalliyar mata kawai, wa yagaya miki ana yiwa bacci wannan salon iskanci?
"" muna nan mu zuba inda ke zamuga wanda zai ci riba, wallahi matukar nine mijinki ,kuma ni nake rike da igiyoyin aurenki sai kin zauna gida kin kula da gida da yarinyarki zance zuwa aiki nayi cancelling dinsa inga dinsa kuma banga uban da ya isa yasani janye raayina ba yakarasa fad'ar hk tare da shigewa d'akinsa.
ba ita ta farka ba sai gurin asuba ta bud'e idanunta wayam taga babu fu'ad babu al'amunsa, Dan haka kai tsaye ta nufi dakinta..
Washegari bayan tayi duk wani abinda ya zama al'adarta ce sallah, wanka ,girka abinda zasu ci, ta tsaya kan wanka nasreen da shirinta ta bata abinci taci ta koshi da bata magungunanta ,sannan ta zauna ta kamo tafukan hannuta cikin nata suka zauna a gefen gado tashiga karanto mata aduoi iri iri na neman tsari da lafiyar jikinta ,ta tofa cikin ruwa ta bata tasha sannan tacigaba da yi mata addu'a yadda zan fita na barki cikin gidan nan lfy ,hk zan na dawo na sameki gidan nan lafiya lau cikin koshin lafiya da kuzari kina wasanki koina batare da wata damuwa ba albarkacin Annabi Muhammad s.a.w.
"mugun ji da mugun gani Allah bazai sa naji ba ,na godewa Allah dayasa zuwa wannan lokacin kina raye sannan muna raye dake, ina sake godewa Allah , Allah yacigaba da karemin ke ya raya min ke yabaki ingantacciyar lafiya mai daurewa, duk maganar datake da adduointa a kaikaice nasreen take kallonta tana furta ameen acikin zuciyarta har sanda me'ad tagama ta sakar mata murmushin tare da kokarin mikewa tsaye nasreen tace "a'a momy ,are you going out?
Tace " me zan miki idan kina bukatar wani abu just tell me?
"Ni kawai banason kije koina stay with me mummy..
" what do you mean by that ?
" today is Monday nasreen zan tafi aiki am going to work.
" but momy....
"Uhmmmmm nasreen karki damu dad'ynki na gida and he is going to take good care of you .
"Guses what?
Nasreen ta narke fuska tamkar zatayi kuka Dan ita tafi son mom dinta ta zauna gida kmr yadda sauran iyayen friend's dinta keyi..
"Karki damu bby nah, zan dawo aiki yau da wuri ni dake zamuyi kallo a zeey world muna cin popcorn da chocolate tak'arasa mgnr tana dry tare da mikewa ta kamo kanta ta bata kis a goshi "be good for dady dont disturb my husband "bye bye my dear Ta rataya jakarta na dubanta kmr tasamu pictures "love you bby, say bye to mummy nasreen ta d'aga mata hannu tana mata bye bye..
"bye my love ...
Mead na fita daga d'akin nasreen ta sake bata rai sosai tamkar zatayi kuka,ta rungume duka hannuwanta, a kirji ta jingina bayanta da abun gado tana turo baki gabadaya ranta in yayi dubu to abace yake , zamewa tayi ta kwanta batare datasan abinda ke mata dadi.
Me'ad kuwa kai tsaye keyn motarta ta d'auka a inda ta saba ajiyewa a parlour'n, ta nufi kofar fita, ta kai hannu da zumar murd'a handle din kofar, sai me?
ba sai kofa taki bud'ewa ta sake murd'awa still the same cike da matsanancin mamaki tashiga jan kofar tana kiran "a'a .... da iyakacin karfinta tana mamakin yadda hakan ya kasance,cikin hk taji sautin muryarsa daga bayanta yana cewa "kamata yayi kiyi tsale da fukafikinki ki tsallake ki bi ta cikin kofar ne ki wuce daga gidan ,ba wai ki tsaya 'batawa kanki lokacin ja ba .
cak ta tsaya tare juyowa ahankali tana dubansa rike da key'n kofar a hannunsa yana takowa zuwa inda take tsaye tmkr an dasata..
" a she baki da kunya me'ad?
Sannan bakisan abinda ake cewa kunya ba a al'adar hausa fulani..,"anya ma kuwa ke kina daga cikin cikakkun jinsin hausa fulani kuwa, wad'an da suka San darajar aurensu data ya'yansu?
"No no bazaki kasance haka ba coz you're so shameless and now how dare you dress up and go to work?
"What about your daughter whom you abandoned to?
" ,I mean yarinyarki da kika Haifa acikinki wa kike tunani zai kular miki daita?
"Dan Allah fu'ad ka ajiye wannan maganar agefe saboda mu rigada muyita before bai kamata kana dawo mana da hannun agogo baya ta katseshi ta hanyar fadar tana cika tana batsewa .
"Oky kya fadi hk mana tunda Ke ba uwar arziki bace, Dan duk uwar arziki datasan ciwon kanta bazata fadi hk ba .
"Kai ke Sam ba uwa bace wallahi, idan kuma uwace ke kina daga cikin asararrun iyaye, wallahi tallahi ita kanta nasreen datasan irinki ce uwarta daba ta roki abar kartazo duniya ...
"Fu'ad.......ta kira sunansa a zafafe tana tsuma sai kuma tayi shir tare da ciza lips dinta.
"Ki fad'i maganarki kai tsaye ba sai kin kira sunana ba .
Sai Dataja numfashi ta sauke kana tace "Plz it's too early on a Monday morning...
"Really ? Ya fada yana dage mata girarsa daya tare da rike kugunsa da hannu daya yana dubanta.
"Ina rokonka da had'aka da girman Allah, just give me the key and let me be on my way to work.
"Key gashi a hannuna ki amsa mana ki fita nagani ,which kind of woman are you?
"What sort of mother are you?
Your daughter is sick and the doctor said someone has to be with her for thirty days ...but you are expect me to stay at home with her ..
" me kake magana akai fu'ad?
" ko ince me kake kokarin cewa?
" nice zan zauna a gida har na tsawon kwanaki 30 domin in kula da yarinyarmu ko me?
"No karki zauna ki kula daita ,ki zauna gadin gidan ne ,da wata shashar tambayarki.
Cike da izza da jin kai tace " I will be home stay with her not go to work ?
"Exactly abinda nake bukata kenan, ki zauna gida ki kula da yarinyarki ,your common sense didn't tell you that as a woman, you need to stay at home and take good care of her.
"For what reason? Ta fad'a a matukar fusace tana matsoshi kmr zata shige jikinsa....
"For what reason fa ki kake ce? "To for matsayinki na shashar mace kuma uwa, kinsa Allah wallahi ba zaki wannan tsinannen aiki ba.... shima ya fad'a a matukar fusace suna fuskarta juna kowanensu na shakar numfashin juna zuciyoyinsu na wani irin bugawa da karfi at the same time suna kallon cikin kwayar idanunsu cike da zallar 'bacin rai....
"Me kake nufi dani ne fu'ad?
"Fu'ad you are the one you will stay indoor with your daughter and