Showing 105001 words to 108000 words out of 163596 words
Chapter 36 - YANCNKI Book Complete by Aisha Bagudu.txt
dasu sannan ayi musu azaba me rad'ad'i har sai sun gaya muku malamin dayayi musu wannan aiki, if possible ma a asakasu a under ground har sai sun fad'a Dan babu yadda banyi dasu ba, alokacin Dana kamasu suna tad'in Dana takurasu ne ma sukace tare da tahir akayi komai "
Acp yace"Karka damu kana zaune zamu zo maka da good news. "Okay nagode sosai tare da mikawa acp hannu sannan suka juya suka bar office din .
Wani irin kuka me'ad take kmr ranta zai fita chairman nacigaba da bata hakuri"ba kuka yakamata kiyi ba illa ki godewa Allah da asiri ya tono if not ,hk kina ji kina gani aikinki zai bar hannunki "nagode nagode har bansa kalar godiyar da zan maka ba ,a yau na k'ara sani duniya ba'akin komai take ba, nasan watakilla sunyi min hk ne saboda yadda nake takura musu akan aikinsu ,kuma fa ni ina yi musu hkn bada wata manufa ba sai Dan su tsaya akan aikinsu kar ya subuce musu Amman babu komai nagodewa Allah daya nuna min su a tafin hannuna ......
Tun daga wannan lokaci chairman ya nemi manyan mutane wad'an da yasan suna muamula da mahaifin me'ad Sannan ya nemi mahaifin sajeeda domin shine kan gaba a komai agurin mahaifinta,domin a zauna da shi a bashi hakuri a roke shi gafara a kan laifin da me'ad tayi masa.
sunje kmr yadda Chairman ya bukata sai dai da kyar alhj ediris ya yarda me'ad tashigo masa gida .
Bayan sun gama gaisawa suka soma magana akan abinda ya kawosu"alhaji jabir yace "alhj ediris abinda ya kawo mu akan batun yarinyarka me'ad ne..
Dady yayi sauron katse masa maganar ta hanyar cewa "ni bani da wata yarinya me'ad arayuwata ,yarinya daya gareni kuma sunan suhailat Dan hk kayi wata mgnr ban da wannan"
da sauri me'ad tashiga Jan gwiwowinta tana kuka "Dan girman Allah dady kayi hakuri ka yafe min ,kayi hakuri wallahi nayi nadama ka daina cireni acikin ya'yanka ...kuka take sosai tana bashi hakuri "Dan Allah ku bashi hakuri ya yafe min wallahi na tuba bazan sake ba, ku gaya masa duk abinda yake so zanyi masa bazan sake ketare zancesa ba, na tuba dady nabi Allah da manzonsa nabinka ka taimakeni ka taimaki rayuwata banida kamarka ,kaine ubana, bani da wani uban dayafika kamin komai arayuwa ka inganta rayuwata ka gatantani kayi min komai ,kayi hakuri nasan ban kyauta maka ba .....
"Banice yakamata nayi maka abinda nayi ba .....,Amman banida yadda zanyi ,bani da yadda zanyi da kaddara data gitta akaina, kayiwa darajar Allah kace ka yafe min ko al'amurana zasu daidaita jikin jama'ar dake gurin yayi sanyi hk ma dady karan kanshi .
Sai dai yayi shiru yana aikin jijiga kafarsa, nan kowa yashiga topa albarkacin bakinsa, wannan yayi nasiha yayi shiru ,wani ma yakama da kyar dai akasamu jikinsa yayi sanyi gbdy , ya sauke naunayen ajiyar zuciya Wanda ke nuna ya sauko.
mahaifin sajida yace "me'ad matsa kusa da mahaifinki sosai ki sake rokosa gafara kinji " cikin rawar jiki ta sake tsugunna har Ζasa ta roke shi gafara, bai yi gardama ba yace zai yafe mata amma tare da sharad'in kowa yayi tsuru tsuru agurin suna kallonsa tare da mamakinsa "
Mahaifin sajida ne yayi karfin halin cewa "wani sharadi ne wannan ?
"Sharadina shine zan raba aurenta da fu'ad saboda ni fu'ad din ne gaba daya bana sonta dashi ......."na tsine shi na tsani naga suna tarayya da 'yata , indai har tana buΖatar yafiyata to tabbas sai ta rabu da fu'ad..
kuma rabuwa ta har abada idan har ta amince da haka zan yafe mata kuma za ta zauna a gidana ta ci-gaba da rayuwa tare dani kmr can baya amma fa batare da auren fu'ad ba..
Mmn sudais ceππππππ
'YAN CINKI
ππππ
ππππππ
~NA~
*AYSHA A BAGUDO*
~DEDICATED TO~
JIDDATULKHAIRI
MARUBUCIYAR
MATAR DATTIJO
Page 80
......'kwa'kwaluwarta ce ta tsaya ta daina processing na wani lokaci kafin daga baya ta cigaba da bugawa, ji take mgnrsa ba iya cikin kunnuwanta kad'ai suka tsaya ba har cikin zuciyarta take jin komai ,ta sake matsowa sosai kusa da mahaifinta wasu zafafan hawaye suka shiga gangarowa akan kuncinta.
Tafukan hannuwanta ta d'aura a saman kafafuwansa dady Cikin mataanancin kuka, gabadayan idanunta dake zubar da ruwan hawaye ta tsurawa mahaifinta tana kallonsa tana son ya karyata mata abinda taji ya fito daga cikin bakinsa, yace "mata wasa yake mata ba gaske bane ,saboda d'acin kalmar tafi kowace kalma muni da zafi me ta'bo zuciya da wuyar mantawa , Amman sake maimaita kalmar da dady yayi ya tabbatar mata da iyakacin gaskiyarsa yake nufin raba aurenta da fu'ad a.
take ta dinga furta kalmar "inna lillahi wa inna ilaihi rajiun "shikenan ta faru dani takare ta fad'i hk acikin ranta cikin matsanancin tashin hankali" yaushe ne zan sake samu 'yancin da rayuwa mai dadi kmr rayuwarta ta baya ?
,tun kafin jamar gurin suyi yunkurin mgn tashiga fad'i" shikenan shikenan !!! dady naji na amince na yarda da wannan sharad'in naka matukar zaka ya femin , domin ni yanzu nafi son farin cikinka a kan farin cikin kowa, duk abinda kake so shi zanyi ,bani da za'bin daya wuce naka ..
Tana mgn tana kuka zuciyarta na rawa da gargadinta a kan abinda take shirin aikatawa rayuwata ..
"tana son fu'ad tamkar ranta, kuma bata jin cewa xata iya ci-gaba da rayuwa ba tare dashi ba,Amman a halin yanzu ta za'bi farincikin mahaifinta akan ta cigaba da zama dashi ,zata cigaba rayuwarta babu shi acikin duniyarta , ta gwamaci ta yiwa mahaifinta biyayya a karo na farko ko rayuwarta zata daidaita ,koda kuwa rabuwa da fu'ad din zai zama silar barinta duniya.....
a yanzu ta yarda ta fad'a kowane irin yanayi ne matuΖar dai mahaifinta zai yi farin ciki ya amshita amatsayin diyarsa sa'banin shekarun baya ,da ya fita lamarinta ......
"xata yi k'ok'arin k'arasa fitar da ragowar soyayyar fu'ad daga cikin xuciyar tayi rayuwarta da iyayenta da tilon diyarta.
Kanta a sunkuye ta cigaba maimata mgn "Daddy na yarda ..,dady na amince duk Abinda kake so a halin yanzu zan yi, ba ni da wani buri a rayuwata sama da na faranta maka, sama da na kyautata maka nayi maka biyayya a kan duk abinda kake bukata daga gare ni, duk abinda kake so xan yi maka shi Daddy....
Takarasa mgnr tana wani irin kuka me ta'ba zuciya kuka take sosai tmkr ranta zai fita gabadaya duniya ta cukud'e mata waje daya bata ta'ba hk tashin hankali irin wannan da take ciki yake da muni da ciwo ba ,ta d'auka rashin son da dady yakewa fu'ad zai tsaya a iya hk ne ,ta d'auka rad'ad'in tuni ta tsaya a wancan lokacin ,ta d'auka ko darajar samun nasreen atsananinsu zai sauk'ak'awa zuciyarsa kiyayyar fu'ad .....
Amman da kalamansa na yanzu ta fahimci komai ya sauya agareta ,ta gane ita din ba kowa bace, tasoma fahimtar talaka marashi da galihu ya fita kwanciyar hankali sau dubu.
yanzu wakilla najma datake kallo mafi kaskancin gani akanta tafita kwanciyar hankali da walwala .
"yau din tazo mata da tashin hankali da rud'anin rayuwa maramisaltu "ya zatayi da kaddarar data gifta mata da rayuwarta gabadaya? Parlour'n ya d'auki shiru ,gabadaya jama'ar dake zaune acikinsa sun rafka uban tagumi, ban da sautin kukan me'ad bakajin sautin komai acikin parlour'n .....
Yayinda Mahaifinta yaji dadin jin kalaman daya fito daga bakin 'yar tasa, a nan take ya fahimci me'ad dinsa ta sauya ,ta samu natsuwa, ta k'ara hankali fiyye da lokutan baya, sannan da gaske take nufin nadamar abinda tayi masa a baya ,sannan a halin yanzu yasan ko zuwa gaba yace mata "ga abinda yake son tayi masa tayi batare da sa'bawa umarninsa ba.
cike da matsanancin farinciki da jin dadi yace "me'ad na yafe miki duniya da lahira Allah kuma yayi miki albarka, Sannan amatsayina, na mahaifi gareki ina umartarki daki baro hotel din da kika kama ki dawo gidan ubanki da zama .
Alhaji gali yayi saurin sauke hannunsa dayayi tagumi dashi tare da numfasawa yace " yanzu alhj ediris wannan d'ayen hukuncin daka yanke kana ganin abune me bulewa, raba ma'aurata da rana tsaka alhalin suna son junansu..? "Ni aganina hkn bai kamata ba ,idan shi yaron laifi yayi maka kamatayi a nemeshi ya baka hakuri ba rabashi da matarsa ba alhalin tana son shi ...
Da sauri me'ad ta d'ago idanunta da har wannan lokacin basu daina tsiyayar ruwan hawaye ba tace "No.....dady kubar hukuncin da mahaifina ya yanke akaina kawai kada ku tursashi ,ni koda ina son fu'ad zan iya rabuwa dashi, ballanatana ahalin yanzu babu d'igonsa sonsa ko daya araina ni dai ku taya sake bawa mahaifina hakuri, nagode nagode da kulawarku gareni ,yadda kuka tsaya kuka gyara tsakanina da mahaifina, ina muku adduar allah ya biya muku bukatunku na alkairi, nagode nagode har bansan irin godiyar da zan muku ba ..
jikinsu yayi mugun mugun sanyi babu wanda ya sake yunkurin cewa komai bisa lafazin bakin me'ad ,hk kowanensu ya tashi jiki a sanyaye suka soma mikawa juna hannu suna sallama da juna tare da k'ok'arin barin parlour'n,a tare suka fita har me'ad kowane yashiga motarsa itama tashiga nata motarta da niyyar d'auko nasreen daga school sannan .
kasa tukin tayi ta gangarawa gefen titi tayi parking tare da d'aura kanta saman sitiyari ta fashe da wani irin gigitaccen kuka, gbdy tasoma datasanin barin gidan mijinta datayi
...kuka take sosai yayinda zuciyarta ke sake bud'ewa a wajajen ,da duk ciwoka suka samu muhalli, jikinta yayi mata sanyi,zuciyarta ta dinga tsinkewa har take jin tmkr batayiwa kanta adalcin rabuwa dashi ba,"ina Zata sake samun madadinsa?
"Ina Zata samu jarumi jajjirtaccen miji irinsa ?
bata San lokacin data d'auka tsaye agurin ba zuciyarta ke mata zafi had'e da tsinkewa ahankali take sake jin ciwon abinda fu'ad din yayi mata , sai da taci kukanta ta koshi sannan ta tada motar tabar gurin .
a kan hanyarta ta dawo gida bayan ta d'auko nasreen, yarinyar take tambayarta abinda ke damunta "momy me ke damunki da alamun kina cikin damuwa koma nace kmr kinyi kuka ko..?
"Bby banyi kuka ba idona ke min ciwo ,hk gefen kaina kmr zai fita kimin addua kinji bby .... ta k'arasa mgnr tana meida hawayen da yayi k'ok'arin zubowa .
nasreen ta d'aura hannunta akan na momy'nta dake Kan giyar mota sannan muryarta a raunane tace " momy allah ya baki lfy ,but ki daina damuwa,Dan Nasan damuwa ne akan auren dady ko?
" but momy ina tabbatar miki dady ba zai auri daya daga cikinsu ba ,saboda dady najin mgnta ba zai yi abinda banaso ba ,nagaya masa banason yayi miki kishiya da aunty sajida da najma. ..
girgiza kanta kawai me'ad tayi "yaro duk inda yake yaro ne ... hanyar da nasreen taga me'ad ta d'auka ne sa'banin masaukinsu yasa ta sake fuskantarta sosai "momy ina kuma zaki kaimu ba hotel zamu ba ,? Tayi uwar tmby jikinta na rawa rawa "Dan Allah karki kaimu gidan grandpa yacika fad'a dayawa sannan kuma bayason dady'na nima...."short up there my friend I don't want here any from you just keep your mouth short ...tacigaba da tukinta batare da ta sake kallon inda take ba .
yayinda nasreen ta sakar mata kukan ita baza taje gidan grandpa ba, gara ta kai ta gurin dadynta.....
kukan datake yana ta'ba zuciyarta kuma batason kukanta saboda ,da zaran jikinta ya d'auki zafi shikenan .. ciwonta zai tashi Amman babu yadda ta iya da rayuwata ,hkn datayi shine kwanciyar hankalinta da samun natsuwarta ,duk ita tajawo komai daya faru dasu sai dai bata bakinciki da hukuncin da mahaifina ya zarta akanta ...
har suka shigo harabar gidan kuka nasreen take, taki fitowa daga cikin motar sai da me'ad ta zagaya ta fito daita tashiga turturjewa ita sam bazata shiga cikin gidan ba "Dan Allah momy karki shiga dani banason gidan ....plz momy .
alhj ediris dake saman barandarsa tsaye idanunsa ya sauka akansu sai yau yagama k'arewa yanayin yarinyar kallo , kyakkywace kmr me'ad dinsa ,sai dai kusan yanayinta na ubanta ne ,abubuwa kad'an ta d'auko na uwarta ....
Haushi ne yakamashi ganin yadda ake dambe daita akan bazata shiga gidansa ba, to me hkn yake nufi kenan...?
Ransa a matukar 'bace ya saki wata razananniyar tsawa tare da cewa "ki barta anan kishigo abinki idan bazata shigo ba ,wata irin gigicewa nasreen tayi tare da kwakume me'ad ajikinta "Wayyohlly Allah momy tsoro nakeji .....momy momy tsoro nake ji ki fita dani daga gidan nan tsoro nake ji .....
ahankalin me'ad yayi mugu mugun tashi take hawaye ya balle mata yashiga gudana a saman kuncinta, ahankali ta rungumeta ajikinta tashiga shafa mata kanta zuwa bayan ",cool down my baby nothing wel happen to you, just trust your mom....ki saki jikinki babu abinda grandpa zai yi miki he really loves you rarrashinta ta dinga yi yayinda har lokacin idanun dady ke kansu, ya kasa d'auke idanunsa akansu jiki a sanyaye me'ad ta yunkura tare da d'aukarta ta rungume kasancewar nasreen din bata da wani girma gashi babu kiba sai zallar farin fata da tsagwaron kyawun data d'auko daga iyayenta. .....
suna shiga cikin gidan me'ad ta kwantar da nasreen akan doguwar kujera 3 siter tana shafa kwanta yarinyar ta runtse idanunta gam batason ganin kowa har lokacin bata daina furta "tsoro take ji ba a fitar daita daga gidan .
Me'ad tasamu guri ta zauna a gefen kujerar da momy ke zaune ta zuba uwar tagumi tana zubarwa da hawaye saboda duk abinda ya faru acikin kunnenta akayisa "Sam bataji dadin furucin dady ba ,Amman tasan tana yin wata mgn nata ne zaiyi zafi .
me'ad ta kai hannunta zata cire tagumin datayi kenan suhailat tasanyo kai cikin parlour'n dawowarta kenan daga exam dinta karshe daga shi za'a turasu bautar k'asa.
da sauri ta k'araso ta rungume me'ad tana murnar ganin sai dai ganin yanayinsu ya sanyayar mata da gwiwa tayi tsuru tsuru tana kallonnsu zuciyarta na wani irin bugawa "aunty me'ad momy lfy na ganku wani iri ko wani abu ne ya faru da dady byn fitata?
Kuka momy ta fashe dashi sannan tashiga koro mata duk abinda ya faru .
wata irin zabura suhailat tayi tana furta kalmar inna lillahi wa inna ilaihi rajiun sai maimata kalmar take hankalinta a matukar tashe cikin tsananin rud'u ,tana duban me'ad da wata irin gigitaccen duba muryarta a sarke tace " me ya zanyo kikayi mummunar wannan tunanin anti?
Me'ad ta cije le'benta alamun damuwarta ta kai makura "ai kinga irinta ko anti?" kinga irin taurin kan naki ba ?
"gashi zaki yi sanadiyar kashe auren dake kad'ai kika San irin wahalar da kika sha akansa .
"watakilla da kinyi hakuri kin zauna ad'akin mijinki da yanzu duk hkn bata faru ba, Dan nasan ko bade dady zai yafe miki wallahi tallahi matsawar aurenki ya mutu ki sani kin yanki tikitin zawarci na shekara Goma sha.... ko fiyye da hakan ga dai karamin misali nan akan aunty sajida banda sauran mata da basamu sani ba ,me'ad tayi saurin runtse idanunta saboda sunan sajida da suhailat ta ambata.
Suhailat tacigaba da mgn " kin guji mijinki Dan zai k'ara aure ke yanzu a tunaninki idan aurenki ya mutu mara mata ne zai zo yace yana sonki zai aureki?
Sam ki canza tunani ki koma kibawa dady hakuri ya janye wannan furucin NASA ...suhailat takarasa maganar da sheshekar kuka Wanda ya k'ara dama lisafin me'ad har ta kasa kuka illa girgiza kai kawai datake kmr wata kadangaruwa.."take ciwon so yashiga dawainiyya daita a zaune datake ahankali ta sake runtse idanunta gam fu'ad zuciyarta tasoma hasko mata ," ta yaya zata iya rabuwa dashi ? Anya kuwa bata yaudari kanta ba ? Ta bude idanunta tare da zubawa suhailat ido gbdy ta kasa mgn suhailat ta sauke wata ajiyar zuciya mai bayyanan ne ciwo akirji "bari naje nasamu dady Dan Allah ya sausauta rayuwarma guda na wace ,idan da sauran zama tsakaninku sai rabo yazo ya kasheshi azo ana kuka.....
ganin ta yunkura ta Mike me'ad tayi saurin meidata mazauninta "kiyi hakuri suhailat karkije ni kad'ai nasan kunci Dana shiga a sanadiyar fushinsa gareni, yau nasamu da kyar ya sauko har ya sake amincewa dani amatsayin diyarsa, Dan Allah karkiyi abinda zai sa a sake maimata tarihi fu'ad dai ni na kawoshi nace ina sonshi a yau kuma nace banasonshi .....
dan kowa ya d'auka wata halaka ko dangantaka bata ta'ba shiga tsakaninmu ba ..
tana gama fad'ar hk ta mike hawaye nabin kuncinta tashige d'akin momy ta fad'a kan gado, ta kwanta ruf da ciki ta fashe da wani irin gigitaccen kuka "na barka bari na har abada kai din ma baka cancanci na sake butulcewa mahaifina akanka ba ,kai din maci amanar kauna ne gareni Allah yasa rabuwarmu tazama alkairi a rayuwata Allah ya had'a kowa da rabonsa na alkairi.....
**********
Bangaren mahaifin sajida kuwa daga gidansu me'ad kai tsaye gidansa ya nufa ana k'ok'arin bud'e masa get idanunsa ya sauka akan Khalid da wasu daga cikin security's din bakin get ke dambe dashi na lallai sai an barshi yashiga gidan ,ai kuwa ana k'arasa bud'e masa ,atare suka shiga gidan .bayan direbansa yayi parking a inda aka tanada domin ajiye motoci da sauri ya fito batare daya rufe murfin motar ba ya k'araso bakin kofar da mahaifin sajida yake ,ya bud'e masa kafafunsa yasoma sanyowa waje