Header Ads
Showing 45001 words to 48000 words out of 163596 words

Chapter 16 - YANCNKI Book Complete by Aisha Bagudu.txt

Ads the beginning of article before Image

02 Jun 2024

1291

Ads at the middle of Article

san abin yi "a'a khadeeja koma waye shi sai dai ta hakura ,sbd ni bata ta'ba sanar dani tana son wani ba byn emran,wanda itace da kanta ta kawo min amatsayin mijin aurenta, kuma zuciyata ta aminta dashi," kan wani dalili take son maidamu kananun mutane.?


likita ya dafashi alamun rarrashi yana cewa "ka kwantar da hankalinka ranka ya dad'e,ka natsu ka binciketa da kyau idan har batason shi wanda ta kawo din yanxu ,sai a hakura mana , "itace dai zata hakura da koma wani d'an iska ne . "Alamarin na soyayya mafi yawa masu kwalkwaluwa irin tasu su kan d'auketa da tsananin sai daga baya komai ya daidaita, kamata yayi kasamu lokaci kayi zaman sirri daita domin sanin kowayeshi yaron, "wallahi kaji na rantse sajida bata da miji daya wuce emran koda mutuwa ce sai dai ta dauke ad'akinsa Amman...


wata irin zabura tayi hjy Khadija ta rikota da sauri,wanda hkn yayi nasara katse acp ya tsura mata ido, shi kansa dady sai dayayi dayasani furuncinsa,saboda yadda yaga gbdy ta sake firgicewa, likita yayi kok'arin 'ban'bareta da kyar daga jikin momy yana fad'a tana sakin momy ta sake Sumewa alamarin daya d'aga musu hankali kenan kuka kawai suke har da acp ,momy tace wannan wani irin maseefa ne ? A zuciyarta.


" Ga zance me'ad dake soyayya da d'an talaka ,wanda har yanzu mahaifinta bai sani ba ga lamarin sajida.


likita yana bata taimakon gaugawa yace "ban so ka dinga fad'ar irin wand'an maganganun ba,yallabai, irin wannan lamarin rarrashi da nasiha yake bukata da kwantar da hankali yakarasa mgnr yana mata allurar bacci sannan yacigaba "koda zata farka Insha Allahu zata dawo Normal"Allah yasa suka amsa gbdy,lamarin na sake d'aure musu kai.


Cikin ikon Allah kmr yadda likita ya fad'a koda ta farka tasamu natsuwar zuciya , bugun zuciyarta datake jin ya tsananta ,yayi k'asa sosai yasoma dawowa daidai, sai dai kallo daya zaka mata kasan tana cikin matsanancin damuwa. Lokacin da me'ad ta gama taimaka mata tayi wanka da sauransu ta matsa da tambaya.


"waye shi wanda kikarasa sajida ,da har yayi silar kwanciyarki hospital?tayi mata shiru taki cewa komai "to mai ma zata ce mata,tace akan fu'ad tashiga wannan hali ko mai? Ai ma abun kunya ne ita da aminyarta sun kama da soyayyar mutun daya kmr wani almara.
Tsawon lokaci me'ad na tare daita tare da son jin damuwarta amman sam sajida taki gaya mata komai"wato ni ban san ciwon kaina ba kenan danake gaya miki sirrukana da abinda ya shafi rayuwata ba ko ?


"shikenan sai kicigaba da rike damuwarki ke kad'ai mu km zamu cigaba da tayaki da addua, Dan ni tuni zuciyata ta soma zargin kin fad'a soyayya da wani mafi kusanci damu.


"ba karya kika fada...."ina ma zaki bar min shi da har karshen rayuwa bazan manta dake ba?tayi mgnr cikin ranta tana mai runtsa idanu.


Kwananta biyar a hospital likita ya sallamota duba da ganin samu saukin jikinta,domin tayi kokarin tsaida zuciyarta gurin soma cire fu'ad cikin ranta, ta sake maye gurbin gurin da emran kai tsaye gidansu me'ad aka wuce daita bisa umarnin mahaifinta daya bayar.
Kowa a gidan attention dinsa na kan sajida da bata duk wata kulawa tare da sanyata cikin nishadi, hkn nayi mata dadi sosai sai dai har lokacin tunaninsa yaki barinta.


*******
Yau me'ad da kanta tashiga kitchen sa'baninta lokutan baya,ta had'a dinner mai rai da motsi da taimakon ummi sannan tashiga wanka har ta fito ta tsaya gaban mirrow hankalin sajida na kanta tarasa dalilin da hk kawai take jin babu aranta, a game da wanka data shiga, ahankali me'ad tayi shafinta ta shirya cikin wasu had'ad'd'iyar doguwar riga swiss less ruwan zuma tana fesa turare a kowani lugu na jikinta kararrawar shigowa gidan tayi k'ara sannan wayarta ta hau ruri tabbacin fu'ad dinta ya iso kmr yadda sukayi dashi, daman tun a safiyar yau kai tsaye takira masu gadi ta gaya musu tana da baKo su barshi yashigo, tayi taku d'aya biyu taji sautin muryar sajida cikin rauni dayasa ta tsaya batare data juyo ba "fu....fu'ad ne yazo . ?"uhmmm ta bata amsa dashi tana gyara mayafin jikinta "ok ki gaida min shi "zaiji ta sanya kai fice daga d'akin ,mead na fita ta mike tashige bayi saboda kukan daya tunkuro mata mai had'e tari ,tana shiga ta fashe da wani tsumammen kuka.


Me'ad na k'arasawa farfajiyar gidan,ta d'aura kyawawan idanunta akansa sai ta nemi daburcewa , kasancewar wani azababben kyawun dataga ya kara mata, suka dubi juna da wani irin kallo mai kwantar da zuciya, kafin kowannensu ya saki murmushin mai d'auke da boyayyar ajiyar zuciya.


Gaba tayi ya biyota abaya yana kallon kugunta dake juyawa ahankali wanda yasoma tayar masa da boyayyen tsumin shaawarsa da bai san yana daita ba ,da sauri ya d'auke idanunsa zuwa yanayin tsarin gidan , adaidai wani karamin parlour'n baki ta tsaya tare da kaucewa tabashi hanya yashigo parlour'n cikin kodaddiyar shadda mai hasken sararin samaniya gilashin idanunsa fari ne dan siriri, wanda ya fiddo da zahirin cikar kamalarsa na cikakken d'a nmj wanda rayuwa ke yayi ,matsalarsa dai rashin aiki da kudi, ita kanta tana da tabbacin da zai kasance mai aiki a hannunsa, matan da zasuyi rubibinsa suna dayawa da wata killa ma bata had'u dashi ba me'ad tayi nisa sosai a kallonsa, yayi murmushi yasoma busa mata iskar bakinsa a idanunta tayi firgigib ta dawo haiyacinta .


"kallon ya isa hk me'ad ,sosai taji kunya abinda yace, ta wuce ciki suka zauna cikin kananan leather da suka yiwa qaramin parlour'n nasu qawanya.


Tace "sannu da zuwa honey ya hanya? Yayi murmushi tare da lumshe idanunsa kmr bazai amsa ba sannan yace "lfy . tayi D'an jim tana kallonsa sannan suka gaisa gbdy suka kasa boye soyayyar dake zuciyoyinsu sun jima suna bayyanawa juna sakonni zuciyoyinsu daga karshe ta gabatar masa da abinci da abun sha amman Sam yaki ci komai "iya ganinki kad'ai me'ad ya isheni ....taji Dadin wannan furuncin nasa sosai har kasa boye farincikinta.


Sajida takira mahaifinta dayazo ya d'auke da kansa, Dan bazata iya tuki ba, ta gwammaci zaman kadaitan gidansu akan tacigaba da zama tare da mead, wacce bata iya boye son fu'ad ako gaban waye,nunawa take, da yammanci ranar tana kwance tasoma jiyo jinia, ta tabbatar da mahaifinta yazo, har cikin gidan yashigo sun dade da dadyn su mead suna tautaunawa akan yadda bikinta zai kasance ,sannan daga baya yasa akayi kiranta nasiha da rarrashi sosai dady yayi, har gaban motar dazata shiga ya kai ya bude mata da kansa yana sake rarrashita ,dady na tsaye har sai daya ga wucewarsu sannan ya koma cikin gida yana girgiza kai.


********


Soyayya fa mai karfi tashiga tsakanin me'ad da fu'ad, cikin salo mai ban mamaki basu iya sati basu sanya junansu a ido ba ,kullun yana kan hanyar zuwa gidansu idan kuma bai zo ba, suna makale a waya, duk wannan wainar da'ake toyawa babu wanda ya sanarwa dady har safwan dan koda ta tmbyesa ko ya sanar masa "cewa yayi bai samu had'uwa da dady ba,gashi tafiyar gaugawa tasameshi American sai ya dawo tukun.


Bata damu ba, tacigaba da bawa fu'ad kulawa, fu'ad shi din yasan me Nene so? yasan darajar abinda yake son,ya km iya tafiyar dashi ta hanyoyi daban daban, ta yadda duk wanda zata so shi,zata so shine da dukkanin zuciya, ruhi da gangar jiki koda taki Allah shi ba dan bariki bane, amman ga matar dayake so, mugun dan soyayya ne kmr ba indiye dan irin kalaman dayake furta mata azahiri da cikin waya idan ka ganshi a zahiri rantsewa zakayi kace bashi yake fad'arsu ba ,sbd tsare gida da rashin son raini ,Dan hk ne bai sha wahalar sake yiwa zuciyar me'ad kamun kazar kuku ba, bata da wani tunani sai na fu'ad ,bata da wani ra'ayi sai nashi bata da wani buri sai na mallakarsa matsayin abokin rayuwarta har karshen rayuwa.


Gbdy ta mance da wani safwan dake can wata kasa tattare da dakon soyayyarta ,a wani zuwa ne da fu'ad yayi tana zaune gabansa cikin less mai taushi fari sol da zanen silver ,dinki bakaramin kama jikinta yayi Dan har saman dukiyarta yana iya hangowa, shr yayi zuwa wani lokaci sannan yakira sunanta muryarsa a kasalance "mead, na zauna nayi tunani mai yawa akan lamarinmu dake, ni talaka ne sannan d'an talakawa gaba da baya, wanda yake karkashin kulawar kakarsa ,da bata da komai ,bata aje ba sannan bata bawa kowa ajiya ba,gani zaune babu aikin yi ina sonki sai dai bansa yadda zanyi ba idan batun aurenmu ya tashi .


Maganganunsa sun mata ciwo matukar da hk muryarta a d'an zafafe tace "duk nasan da hk fu'ad nace ina sonka.


Ya langwabar kansa tare da tsura mata idanu kmr zai cinyeta sannan ya bude bakinsa da kyar yace "zaki iya zama dani cikin halin babu, sannan bazan iya rayuwa babu innata a kusa dani ba saboda nayi aure, Dan tayi min komai arayuwa, byn kasancewarta kaka gareni uwa ce mai tattare da matsayin uba, ta taka matsayin komai gareni zaki iya tallafawa rayuwata data innata?


Ta lumshe ido cikin wata sabuwar kaunarsa dake mamayarta ta km lullu'be zuciyarta "kada ka damu baka da matsala dani fu'ad soyayyarmu had'in Allah ce ba dan wasu kyale kyalen duniya ba, kacigaba da tafiyar da rayuwarka hk ina sonka hk , ina girmamaka sbd dattakonka,ni fuad din kawai nake so bawani abu nasa ba ,ina matukar sonka ta yadda har bazan iya waiwaya ba, in hango hierarchy dinsa ,yake gani wanda shi so baya la'akari dasu.....sai byn data furta hkn kunya ta lullu'beta Dan ganin irin yadda jikinsa yajike yake tsuma km ya zubawa dan karamin bakinta idanu dake motsi yana fitar da kalamai masu sanyi garesa, tacigaba "ni dai fatana da burina ka rikeni amana ka yardani nima in yarda da kai, Allah yardadamu yabamu ikon mallakar juna idan kayi min wannan, ni km nayi maka alkwarin zama da kai muddin rai cikin kowani irin hali ,akwai ko babu dadi ko akasin sa....da sauri ya mika mata hannunsa tun kafin takarasa.


"shake my hands my love..nagode da soyayyarki gareni, ina rokon Allah ya fiddani kunyar soyayyarki..yabani ikon fita hakkokinta yabani ikon sanin mahimmantata fiye da duk wani alamarin da dan adam ke burin samu suka had'e hannuwa guri daya kmr masu kulla alkwari.
Ta lumshe ido jikinta na tsuma saboda had'uwar tafukan hannuwansu ,domin ji wani abu na fita daga cikinsu zuwa nata naunayen ajiyar zuciya ta sauke tana sake damke hannunsa cikin nata sannan tace "sai batu na neman aiki fu'ad kabani CV's dinka a samomaka aiki, ina bukatar ganin cikin office honey, ka yarda ka amince min....


Murmushi yayi "kibar wannan issue din, nima ina kan nema da kaina wanda ya amshi takarduna ina sa ransa samu, ki min addua yakarasa mgnr yana saka yatsun hannuta cikin bakinsa, bai tsaya bata lokaci ya fara tsotsarsu domin kwantar mata da hankali, aiko take abinda yake bukata daga gareta ya kau Dan jikinta ya d'auki kyarma dan ji tayi kmr yana zarar ranta da kyar tasamu ta kwaci hannunta fa fad'a jikinsa .


************


An yi bikin sajida na ban mamaki sannan aka kai amarya gidan mijinta dake cikin ajawo estate, 'yan kai amarya mutun Hudu basu tsaya ba ,suna kaita suka juyo bayan kowa ya fita ne ta d'auki jakarta tashige d'aki ta kulle kanta har gari ya waye sannan ta shirya ta fito ta zauna cike da jin haushi emran ita fa fu'ad take so, zuciyarta ta kasa hakura dashi gbdy ango yarasa gane kan amaryarsa, duk yadda yayi daita taki haushinsa take ji, da ganin bai iya komai ba ,komai yayi bai iya ba fu'ad ne ya iya kwata kwata baya burgeta tana zaune emran yashigo yana fara'a wai shi me amarya ya samu gefen kujerar da take zaune ya zauna tare da zura mata ido baya ko kiftawa.


ita kuwa ko kallo bai isheta ba ta juya masa baya dama tagaji da kallon dayake mata kawai sai ta mike tashige dakinta .
yasha mamakin abinda ya faru shi daman tun kafin bukinsu yaga ta canza tmbyr duniya yayi mata taki amsa masa .


Satinta daya a gidan
da yamma emran yashigo yace taxo yana son ganinta, bata kulashi ba dan bai isa ba shi km ya dawo parlour'n ya zauna yana jiranta ya jima yana zaune a parlour'n amman bata fito ba hkn yayi maseefsr 'bata masa rai ya tashi ya koma cikin d'akin yasameta a kwance a inda ya barta batare da niyyar tashi ba ,ya daka mata tsawa da cewar sajida wai me ke damunki ne da har zan dinga miki mgn kina jina byn ba dole nayi miki ba ?


"wai ma me kike nufi ne tun sanda aka kawoki gidan nan kin kasa zuwa ki gaida iyayena, dan baki d'aukesu abakin komai ba,
sannan ko ruwan zafi baki tab'a dafa min kin kawo min nasha ba balle kiyi min girki irin na mata da miji ki kawo naci to kisani bazsn dauka ba..


sajida dake kwance jin yayi shiru yasa ta tashi zaune tana yiwa emran wani kallon tsana tace "amman emran kabani dry dan ina jin kana da matsalar kwalkwaluwa, banda hk ka dubeni da kyau kace wai ni zan maka girki ashe zaka mutu da yunwa bakaci ba,dan ni ba yar aikinka bace kuma ba tun yau ba kasani ko ruwan zafi ban iya daurawa ba, idan kuma ka manta na tuna maka saunawa me'ad na sanar dakai sajida bata iya komai ba?


Dan hk ko ruwan zafi dazaayi wanka dashi ban iya dafawa ba ,kai ko gas ban iya kunnawa ba balle km yin girki dan hk ka nemi wace zata dafa maka abinci sannan zance inje ingaida iyayenka ai basu na aura ba su dan girman kai tinda nazo gidan basu zo ganni ba balle su girmamani amatsayina na matar d'ansu, kaga nima bazanje in gaidasu ba don neman gindin zama bazanje koina ba kaji ko?


idan km sai naje ne sai dai ka sakeni nakara gaba..


"au haka kikace ko?


Emran ya fad'a cikin 'bacin rai "Kwarai na fad'a itama ta mayar masa tana cewa dama kasakeni naje nayi yakin neman auren fu'ad shi kawai zuciyata ke muradi ba kai ba ta fada aranta.


bai kuma cewa komai ba yasanya kai ya fita yana mamakim abinda ya canza masa sajidarsa ,shi ba zance rashin girkinta ne yafi damunsa kmr yadda take nuna kiri kiri bata sonshi yanzu.. idan rashin girki ne ya Dade dasanin hkn, km har yayi tunanin nema musu me aiki amman kwata kwata yarasa meyasa ta tsiro masa da wannan halin to ko dan taga yana maseefsr sonta ne?


amman yasan yadda zai yi mata momysa zai gayawa watakilla yasamu kanta .


yana fita sajida taja wani dogon tsaki ta koma ta kwanta lamo tana tunanin fu'ad.


Mmn sudais ce[11/3, 8:26 AM] El~hajj: 💗💗💗💗💗💗
'YAN CINKI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗


~NA~


*AYSHA A BAGUDO*


~DEDICATED TO~
MRS ADAM
( YAR MUTAN KAGARA)


Page 57 to 58


.........Emran na fita kai tsaye bangaren ummansa ya nufa bakinciki duk ya cika masa zuciya,umma ta sarawa d'an nata lokacin daya gaya mata irin abinda sajida take masa .


Umma da kanta taje bangaren sajida domin yi Mata fad'a saboda tana mutuwar sonta kmr yadda emran dinta ke sonta, Amman abinda sajida tace ya kusan sumar umma dake zaune cewa tayi " hjy ai ba nice kawai mace ba a duniya , idan yaji haushi kuma bazai iya da halina ba ya sake aure tunda yana da kudin da zai iya auren ko mata nawa ne,Dan ni ba ruwana ,abinda nake son ya gane kuma ya fahimta banzo gidansa Dan in yi masa biyayya ba,ko wani bauta, shima yasan da wannan, in karya ne ki tmbayeshi gashi nan zaune agabanki .


Umma ta girgiza kai cike da bakinciki sannan tace "shikenan babu komai tunda da kanki kikace yayi miki kishiya zakuwa ayi da yardar Allah, Dan kuwa zan tabbatar da d'ana emrana ya auro santaleliyar budurwa yar gidan mutunci.


"To ni hjy manene zai dameni ,byn nima har yanzu amatsayin budurwa nake babu nmj daya ta'ba takani , ni da zaki taimakamin ma da kinsa wannan d'an naki ya sallemi na huta...
emran ya yunkura ya mike jikinsa na rawa zai d'auketa da wani gigitaccen mari, hjy tayi saurin taresa "kul karka soma ... akwai abinda yafi duka ko mari zafi arayuwar d'an adam, shi yafi cancanta kayi mata ba mari ba Dan ko ka mareta bazaka huce ba.


Gabadaya jikinsa kyarma yake "yanzu har sunzo gurin shi sajida,?wulakantashi da iyayensa zagaye dakin yasomayi zuciyarsa na masa daci da tafarfasa, ita dai umma bata sake cewa komai ba ta tashi ta fita tana jin zafin abinda sajida tayi mata, sai dai tayi kanta alkwarin duk runtse sai ta aurawa emran mata har biyu sai dai idan shine baya so.


Kwana hudu tsakani abinda daya faru da daddare suna bacci kaddara ta fad'o gidan, domin barayi ne sukayiwa gidan diran makiya, saboda jin labarin emran yashigo da wasu makudan kudi masu yawa xshiyasa sukazo dan su amshi rabonsu, gabadaya mutanen gidan suka tara a falo daya, duk sukace kowannensu ya kwanta flat a kasa ,kowa ya kwanta amman banda sajida saboda jin itace diyar acp , taki kwanciya babu yadda emran bai yi daita ba amman taki, babbansu yace" da kyau yar kanwata kinfa burgeni sosai, dan kina da zuciya mai dakiya ke matar 'barawo yakamata kizama bana na maikacin BBC ba , amman duk da hk za'a shafa miki bakin fanti da iya rayuwarki idan kika tuna zaki ji zafi, ke ba iya ke ba har ya'yanki sai bakin fenti ya shafesu, yakarasa mgnr ya kalli wani baki mummuna daga cikin yaransa yace "kai shigar min daita turakar

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads