Showing 141001 words to 144000 words out of 163596 words
Chapter 48 - YANCNKI Book Complete by Aisha Bagudu.txt
*la yahlamul gaibi illalah* ban taba wata muamula da wani dan adam ba nayita ta sigar munafurci ba, babu muhmuni aduniya da zaice ba'a saba masa tunda aka sabawa manzon allah kuma akwai lokacin da aka 'sabawa manzon allah fushi ya bayyana akan fuskarsa" kai dan adam kai waye ko kai akwai abinda za'a maka dole zuciyarka tasoso babu wani muhmumi da aduniya
wanda dan adam baya saba masa .
wallahi ko shi waye tunda aka taba maaikin Allah ka manta a daifa aka jefi manzon allah ka manta aka dauki tunbi aka zazzagewa manzon allah wanda yafi kowa girma dan asalin girma wanda daraja nemansa take amman yaji babu dadi har yarsa take kuka ,dan haka malam isa duk abinda kasani na rayuwa babu wanda ban sani ba, sai abinda ubangiji bai sanar ba, kasan kowani dan adam akwai gwargwadon abinda Allah yake sanar dashi koda jahili ne kai ko mahaukaci ne akwai wata ilhama da ubangiji yake bashi yakeyi cikin haukansa ballanatana mai hankali wannan yaron dai idan nace ga abinda yayi min kowani aibunsa nayi karya Allah ne yake halittar so azukatan dan adam haka yake halitar ki, to ina son kasani Allah ne bai halitta min kaunarsa acikin zuciyata ba ,ba dan yakasance a yadda yake ba, shi kansa safwan danake son ta aura ban taba cin kwansalarsa soyayya ce kawai da amintar mahaifinsa wannan shine.....
Mmn sudais ce
[11/3, 8:31 AM] El~hajj: 💗💗💗💗💗💗
'YAN CINKI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~NA~
*AYSHA A BAGUDO*
~DEDICATED TO~
*hajiya maryam jikar kulu*
Page 89
......numfasawa malam isa yayi had'e da sauke naunayen ajiyar zuciya,still yana duban dady dake fuskantarsa .
A hankali malam Ibrahim shima yashiga janyowa dady ayoyi da ingantatttun hadisan dake raunata zuciyar d'an adam da duk inda ya kai ga kangarewa ,
take jikin dady yayi mugu mugun sanyi ,idanunsa suka kad'a sukayi jajir, nadama ta shigesa mara misaltuwa, sosai sukayi Masa ruf da dugu gurin lalasa zuciyarsa har suka samu zuciyarsa ta sauko gabad'aya ya amshi wa'azinsu da hannu biyu biyu wanda ad'azu yaso yayi musu taurin kai .
cike da matsananncin nadama dady yace "shikenan na yarda na amince ta koma garesa su cigaba da rayuwar aurensu, amman kusani bafa zan ta'ba son fu'ad acikin zuciyata ba.
saboda shi wannan son halitta ne da Allah ke hallatawa bayinsa acikin zukatansu ,to ni sam sam ba'a halitta min soyayyar fu'ad acikin tawa zuciyar ba . sannan koda ina son fu'ad wannan soyayyar ba zatayi tasiri ba, sakamakon abinda diyar cikina tayi min akansa, ta fifita shi akaina, tayi sa'insa dani akansa.. to ta yaya kuke tunanin zuciyata zata iya soyuwa da soyayyarsa?
"kar kace haka alhaji akwai kyautatawar dake saka shakuwa mai ilhama har ta zamo soyayya mai karfi ,yaran wannan lokacin daban suke akan makauniyar soyayya ....
zasu iya komai akan abinda zukatansu ke so, hakuri zamuyi dasu tare da yi musu addua , kama godewa Allah da ban d'an iska dan shaye shaye takawo maka gida ba, sam sam wannan yaron bash wani laifi ko aibun da za'a ki bashi mata ya aura, saboda yana da nagarta data dace illar dai rashin sonsa da bakayi ,amman dai kayi hakuri a hakan ma mun gode kwarai da gaske daka fahimcemu .
,Allah ya k'ara sanyaya zuciyarka, su kuma Allah yabasu zaman lafiya mai d'aurewa ,abu na karshe da zance anan shine kayi hakuri ka rage kiyayyar yaron acikin zuciyarka, domin annabi muhammadu saw yace idan zaka ki mutun ka kisa kad'an saboda wata rana zai iya zama masoyinka, haka zalika idan zaka so mutun kaso shi kad'an saboda wata zai iya zama makiyinka. mlm isa na gama fad'ar haka suka mike tsaye atare shi da mlm Ibrahim suka yiwa junansu misabaha sannan suka fice suna sake tautaunawa akan lamarin dady atsakaninsu .
bayan tafiyarsu shiru dady yayi zaune agurin kwakwaluwarsa na dawo masa da abubuwan da suka faru a baya da kuma wad'an da suka faru a yanzu, bai ta'ba tunanin zuciyarsa zata raunana a daidai wannan lokacin ba, sannan bai ta'ba sanyawa ransa zai amince da komawar me'ad ga fu'ad ba, ya dad'e zaune agurin yana tunani yana girgiza kafarsa daya ,zuciyarsa tayi masa nauyi , yasoma tunanin ta yadda zai fahimtar da safwan ya fahimcesa batare da wata damuwa ko tashin hankali ba ,gabadaya zuciyarsa tagama karanto masa ya nasanar masa da komai kawai Amman sai bayan me'ad din ta koma gidanta ,da wannan shawarar yasamu natsuwar zuciyar daya yunkura ya Mike tsaye yashige d'akinsa.
bangaren me'ad kuwa ita sam batasan da zuwan baki gidan ba, tana kwance lamo akan gadonta kiran Dubai max-zoniya,ta lullu'ba cikin laulausar bargo ,iya kanta ne kawai a waje idanunta na kallon saman d'akin tana tunanin mai tattare da kewar mijinta da tilon diyarta mara ishashiyar lafiya,"ko a wani hali nasreen da fu'ad dinta suke ?
Ta lumshe idanunta ahankali sakamakon gefen kanta dayayi mata nauyi kmr kowani lokaci idan ta zafafa tunaninta akan fu'ad da nasreen.
idanunta sun kad'e sunyi jajir tsabar kukan datake akan rashin sanin madafar rayuwarsu da rashin sanin takamaiman halin da fu'ad da nasreen suke ciki .
Suhailat ce tashigo d'akin kawo mata abinci ta tsaya daidai saman kanta "ya dai ?
"Lafiya aunty ko wani gurin ke miki ciwo ?
Kallon kanwar tata tayi inda take ganinta dishi dishi ,"wallahi hailat da ba Dan kar nayi sa'bo ba Dana ce nagaji da rayuwar duniya, da abubuwan dake faruwa dani ,narasa me ke damun zuciyar dady...
Komai ya tsaya min banasamun sukuni da walwalar zuciya, bazance miki when Dana tsinci kaina cikin farinciki ba ..suhailat ta ajiye tiren hannunta akan bedside sannan tace "Kiyi hakuri aunty ki d'auki wad'an nan abubuwan dake faruwa dake amatsayin kaddararki, da sannu komai zai zo ya wuce ,kin kuwa samu abban nasreen a waya kuwa ?
Lumshe idanunta tayi ahankali tana jin yadda bugun zuciyarta ya k'aru saboda zance suhaila "ban samesa ba saboda duk kwanakin nan bana samunsa a waya ,suhailat abubuwa sunyi min yawa ina jin tausayin kaina ,suhailat kiyiwa iyayenmu biyayya, kada kiyi kuskuren bujircewa umarninsu arayuwa,kalleni dai kiga yadda na dawo , na isheki misali arayuwa , maseefa iri iri sun afka min adalilin sa'insar danayi da mahaifina akan aurena da fu'ad ,kina ganin dakace fu'ad ya wulakantani arayuwa yau me zance ?
ba kowani nmj bane kmr fu'ad, domin kuwa da irin wasu mazan ne wallahi tallahi da yanzu fu'ad ya manta ya sakeni ,ni kaina bansa fu'ad yana tsananin kaunata ba, sai a yanzu da komai yagama cakud'e mana ..."haka ne aunty ni kaina ban ta'ba ganin nmj irinsa ba ,shiyasa tun baya nake fahimatar dake kika kasa fahimta "
"ba laifina bane suhailat, ko a wancan lokaci har da zigar sajida gareni, a tunanina ita din masoyiya ce, ashe ita da wata manufar take min ingiza mai kanto.
Suhailat tace "Allah kyauta ta wani bangaren kuma abinda tayi miki yayi amfani domin yasa kin dawo haiyacinki ,tunda gashi har kin fahimci kuskurenki arayuwa, tana gama fad'ar hk ta juya ta bar d'akin.
hannunta ta kai kan wayarta tashiga dealing number'sa bugu biyu ya d'auka ji tayi tmkr an mata bushara da gidan aljanna dan dadi alokacin dataji sautin muryarsa cikin dodon kunneta, yau kusan kwana uku kenan yaki daga wayarta wanda batasan dalilin hakan ba, muryarta a sarke tayi masa sallama cikin sanyayyiyar muryarta tare da fashewa da wani irin marayan kuka mai ta'ba zuciya.
"my love .....ya furta muryarsa a matukar tausashe"yayinda hannunsa ke rike da biro, idanunsa na duban file din dake gabansa Wanda yake ganin fuskarta aciki tana zubar da ruwan hawaye.
lumshe idanuna tayi wasu ruwan hawayen na dada kwaranya akan kuncinta "honey me yasa kayi min haka?
"me yasa ka nisantani da kanka da NASREEN alhalin kasan kune farincikin rayuwata ?
"ganinku kusa dani kad'ai yana rage min tarin damuwar danake ciki "is okay love kukan ya isa hk its it's not my fault "
"yanzu dai ina ka kai min yarinyata ? ta katseshi tana goge hawayenta,shima shareta yayi ya cigaba da sauraron kukanta dake narkar masa zuciya.
" kada kayi fushi dani fu'ad komai yana da lokaci har ya zamanto tamkar ba'ayi ba, nasani dady ya Nuna maka abubuwa dayawa wanda ni karan kaina bana jin dadi Abinda yake maka, amman banida yadda zanyi, bani da zabi daya wuce ka taimaki rayuwata kabari nayi mahaifina biyayya a karo na farko..
karkaji haushinsa da zafafa kiyayyarsa kmr yadda yake maka....
ka taimaka ka dawo gareni ka dawo min da sanyin idaniyyata farincikin rayuwata "i love both of you, a halin yanzu damuwa tayi min yawa har tana daf da illatani, kayi hkr fu'ad ka taimaki ruhin daya sadaukar da komai gareka, har yanzu ina matukar sonka raba zuciyar me'ad da fu'ad abu ne mai matukar wahala .
"I love you ... and I know you love me,and you still care about me ,pls come back to me karka barni ni kad'ai cikin wannan halin ...
"yaya kike son nayi da rayuwata me'ad?
"abubuwan kullun gaba sukeyi ,abu yaki ci yaki cinyewa ,shin ba'a soyayya da aure ne nayi dake ?
"a tunanina duk duniya babu wanda yakamaci dady yaso sama dani Amman ki duba kiga abinda yake min but babu komai, bazan ji Haushinsa ba sannan bazan zafafa kiyayyarsa ba saboda ke..
"tunda yayi silar zuwanki duniya ai yagama min komai, agurina har yanzu dady matsayin uba yake gareni ko yaki ko yaso.
zance nasreen kuma kisawa ranki tagama zama cikin gidan nan matsawar ba maslaha muka samu atsakaninmu ba, wanda hakan nike fata.
" ina sonki me'ad, son da bansan ina yi miki shi ba sai a yanzu da bama tare, ji nake tmkr ana fixgar raina .......
Cikin wani irin kuka ta katse kiran ,tana gunjin kuka taji an turo kofar dakin ta d'ago idanunta ahankali dake cike da ruwan hawaye ta sauke su akan mahaifinta ,da sauri ta gyara zamanta tasanya hannuwanta duka tana goge hawayenta har tsakiyar d'akin dady ya k'araso yana dubanta cike da matsanancin tausayinta.
hannuwansa duka ya ware mata alamun tazo garesa .
Da sauri ta duro daga saman gadon kmr wata karamar yarinya ,madadin ta rungumesa sai ta durkushe kasa ta d'aura hannunwanta bisa kafafunta tana gunjin kuka tana rokonsa yayi hakuri ya yafe mata, ya barta ta koma gidan fu'ad, "dady fuad shine rayuwata ,dady kar ka rabamu yayi saurin runtse idanunsa saboda d'acin kalmar Amman take ya kawar da bakincikinsa ya kamota ya rungumeta cike da tausayawa "Allah yayi miki albarka me'ad hakika nayi nadamar abubuwan daya faru Allah yayiwa rayuwar aurenki albarka..
a matukar firgice ta d'ago tana dubansa tana son ya gasgata abinda taji ya fito daga cikin bakinsa mafarki take ko kuma a zahirance take jin wannn furucin daga bakinsa jin ya sake maimsitawa tayi saurun zamewa ta durkushe agabansa tana kuka mai tattare da murmushin farinciki had'e da mamakin abinda taji yana cigaba da fitowa daga bakin mahaifinta "kiyi farinciki ki daina mamaki na yarda na amince ki koma gidan mijinki yanzu haka NASA a sanar masa yazo ya d'aukeki a duk lokacin dayaso, cikin haka mumy da suhailat suka yi wuf suka fad'o d'akin Wanda daman suna la'be tun sanda sukaji shigowarsa d'akin suma murna suke suna kukan farinciki mumy kuka me'ad kuka suhailat kuka hatta dady sai daya goge hawaye sannan ya juya ya barsu rungume da juna suna murna ..
lokacin da fu'ad ya samu labarin abinda ya faru har da rawa yayi acikin office dinsa ,yana furta kalmar alhamdullahi, Allah na gode maka da kawo min karshen matsalata , sannan yakira wayar me'ad, ta d'auka tana kuka mai had'e da zallar farinciki shi kuma yashiga rera mata waka.
" it's god miracle that he made me meet you dying over you, i have learnt to live the relation wit you my makes world colourful ..haka yayita rawa yana murna yana rera mata wakar soyayya ,dariya tayi sosai kasancewar tana kallonsa dan video call ne..
a ranar fu'ad yabiyo jirgin karfe bakwai, karfe tara daidai a gidan surukinsa tayi masa, sam kunya bai sanya dady ya had'u dashi ba ,shima bai wani damu da had'uwar tasu ba.
yace me'ad ta taso taso muce gidanmu plz ..yana kai mata kiss a goshi "laulausar murmushi tayi masa wanda ya bayyana wushiyarta "tun yanzu kabari zuwa gobe mana "ok babu damuwa ai sai muyi baccinmu kawai anan.
ta sanya hannuwanta duka ta rufe idanunta ya janyota ya zaunar daita bisa cinyarsa ya cire hannunta ya d'ago habarta yana kallon kwayar idanunta "kunya na meye ne hk?
" ke da har tsarabar zaman gida kika samu ya k'arasa fadar yana kwashe mata da dry..
ta murmush tana 'boye fuskarta a kirjinsa tare da dan duka kirjin "banason haka fa "ni kuma kinga abinda nafi so kenan, samun cikinki yayi matukar min dadi, tashi muje kar dady yaji shiru ya canza ra'ayi "to ai ni ban shirya kayana ba tukun .
"muje kawai kayan sazo daga baya dan wallahi bazan sake barin ki kara ko minit goma acikin gidan nan ba ,yana gama fad'ar haka ya mike tsaye daita hajab dinta daya gani akan abun sallarta ya d'auka yasanya mata.
ya kamo hannunta suka fito daga cikin d'akin, ta kofar baya suka biyo suka shige motarsa suka bar gidan, sai a mota takira mumy take sanar mata su sun wuce.
mumy tace " a sauka lafiya ni ai fu'ad din yayi min daidai gara dayazo ya tattaraki ko na huta da wannan kukan naki ..
me'ad ta sa dry "kai mumy.. "kai mumy ko gasky, Allah dai ya kiyaye gaba, fu'ad dake tuki yayi mata ala'mun tace yana gaishe da mumuy, ta kashe masa idonta daya sannan ta isar da sakonshi .
mumy tace "kice masa ina amsawa d'an albarka, Allah yayi muku albarka, har suka iso gidansa daya mallaka a watani biyar da suka gabata, me'ad na kan layi suna magana da mumy inda take sake nusar daita zaman takewar rayuwa .
tafkeken gida ne mai girman gaske wanda yaji komai da komai ,zagaye da shuke shuke da wutar lantarki daya sake fito da kyawun gidan ,ahankali take bin harabar gidan da kallo har sanda yayi parking agurin da'aka tana da domin ajiye motoci, batasani ba sbd hankalinta yana can gurin kallon tsarin gidan daya ninka gidan ubanta a komai .
fu'ad ya fito daga cikin motar ya zagayo ya bud'e mata ya kamo hannuta ta fito tana sake kallon gidan da shi kanshi mai gidan .
ta bude baki kenan zatayi mgn ya had'e bakinsu guri daya saboda yasan tambayar da zata masa.
sai daya tsotse miyon bakinta son ranshi sannan ya zare bakinsa yana dubanta "kar ki yi mamaki me'ad ni kaina wani lokacin ina mamakin faruwar abubuwa ,amman duk wannan ba abun mamaki bane ,sbd Allah ya wuce haka yanzu dai sai dai mu godewa Allah saboda fu'ad dinki ya taka wani matsayi na daban, alokacin da abubuwa suka tsananta gareni alokacin abubuwan alkhairi da wadata suka dinga kusowa cikin rayuwata .
ya janyo hannuta zuwa cikin babban parlour'n gidan tayi sororo tana kallon tsarin gidan lumtsuma lumtsuman kujeru masu kalar brown colour zagaye da parlour'n,haka labule su ma kalar kujerun duk wani nau'in kayan kawa na rayuwar duniya yana cikin parlour'n, kama daga standin ac fan zuwa ac tv plazma manya speker a gefen tv hagu da dama, dstv centertable manya manya flowers ,daga gefe can hada'dd'en dining table ne.
wani irin sanyi dadi da farinciki ne ya lullu'beta alokaci daya ,yau tazo mata da abubuwa dayawa na tarin farinciki juyowa tayi ta rungumeshi tsam ajikinta tana kuka har da shesheka "yanzu ba lokacin kuka bane me'ad kuka yakare sai dai kuma jin dadi muje muyi wanka mu huta nagaji over gashi gobe nake son komawa, muje ko d'an tausa nasamu kiyi min.
tunda sukayi aure basu ta'ba samun natsuwa irin na wannan lokacin ba bayan sunyi wanka sunci abinci dayayi masu oder suka kwanta ,tana kwance akirjinsa tana mulmula yakira sunanta "my love "yes honey massage plz.
daga tayi masa tausa komai ya sauya atsakaninsu ranar dai sun gurji juna cike da farantawa, sai fatan Allah ya kiyaye gaba.
washegari ta dameshi da tambayar ina nasreen?" ina ya kaita?lokacin daya sanar mata inda take yayi mamakin ganin yadda bata ce komai ba, jirgin karfe bakwai suka bi zuwa akwai ibon inda yake aiki yanzu .
nan ma wani sabon mamaki tayi ganin inda yake rayuwa ,da idanu take binsa da kallo tmkr wani sabon halitta, ya zagayo bayanta had'e da zagaye hannuwansa da kungunta ya d'aura kanshi bisa kafad'arta "nasan abinda kikewa tunani sannan nasan yadda kike ji acikin zuciyarki, kina jin wani abu mai dadi aranki, kmr yadda nake ji bazan manta ba innata tasha gaya min wata rana zanyi mamaki irin lakhairun da zasu zomun har su zama tsani na rayuwata, amman bansan sai byn ranta wannan arziki zai zo min ba, mead a kullun na tuna irin wahalar da dawainiyyar da inna tayi dani ,na zauna nayi kuka.
a halin yanzu tunanin abubuwan da zan mata nake wanda zai zama sadakatuljariya gareta nakeyi ya karasa mgnr yana maida hawayen dayaji suna kokarin rabowa daga cikin kwarnin idanunsa "itama kusan taji yanayin dayaji most especial da tuna lokacin inna da in da sukayi rayuwa, babu da rashi na talauci yayi musu katutu yau ga yadda Allah ya maida jikanta mafi soyuwa gareta ,Allah kenan...
rungumeshi tayi ajikinta wanda hkn bai hana hawayensa gangarowa "kayi