Header Ads
Showing 39001 words to 42000 words out of 163596 words

Chapter 14 - YANCNKI Book Complete by Aisha Bagudu.txt

Ads the beginning of article before Image

02 Jun 2024

1292

Ads at the middle of Article

daya ta zauna "dad sannu da zuwa ya hanya ?


mahaifin safwan ya amsa da kulawa sannan ta waiga inda safwan wanda tun shigowarta idanunsa ke kanta yana kallonta saboda wani irin azababben kyau dayaga takarayi masa sai dai ta rame kad'an Wanda bai San dalilin faruwar hkn ba ,sautin muryarta ce ta dawo dashi "yaya ina yini?


ya lumshe idanunsa na second biyu sannan ya bud'esu fess akanta kanwata kin yini lfy?
tayi masa wani irin kallo mai bugar da zuciya sannan tace lfy atakaice.


sun jima a parlour'n dad dinta ya dubeta yace ki kai yayan naki lambu ya huta mana , babu mutsu me'ad ta mike shima yabi bayanta cikin matsananci farinciki yayinda ita kuma ba'a son ranta ba Dan dai babu yadda zatayi ne.


wani parlour'n ta kai shi al wanda duk gidansu babu irinsa an maserfar zuba abun duniya agurin ,an zuva komai wanda me rai yake burin mallaka.


bayan ya zauna tasa aka gabatar masa da abubuwa sha kmr yadda tasaba sannan ta sake tashigowa batare da wani abu ba ta zauna shiru batace masa komai ba gbdy sai yaji baya bukatar cin komai dake gabansa illa matsowa da yaayi ya saita bakinsa daidai kunneta "ina sonki mead dayawa amman banji dadin yanayin dana ganki ba at least kinsa ina bukatar kulawa daga gareki. .tace har da gaske kana sona har yanzu ka mayar da akalar soyayyata ga wata in har kana son farincikina .
A matukar firgice ya tsura mata ido yana kallonta Kafin daga baya yace "no no hkn ba zai yuwuba "saboda me ?"saboda bana sonka yanzu sannan karka kazamanto me yawan wahalar da kanka wajen sake tadda zance aurenmu domin ahalin yanzu zuciyata bata gareka , ta kamu da soyayyar waninka ,da sauri safwan ya kalleta cike da matsanancin mamaki abinda take fad'a masa yayi shiru ya kasa cewa komai illa jikinsa dake rawa..


"kaji abinda nace amman har yanzu ka kasa Cewa komai, ko magnata ta kurmanta da kai ne?
. "ko daya kawai mamaki kikabani shin kin manta matsayina a gidan nan dama duniya gbdy?


"sam maganganunki a yau babu girmamawa balle nuna tarbiya, "dan Allah ki gyara maganarki sam banji dadin yadda kika min ba saboda har yanzu ina sonki me'ad kuma banga abinda zai hanani aurenki ba matukar ina raye.
da sauri me'ad ta kalleshi cikin mamaki tayi wata dry na rainin hnkl " amman baka kyautawa xuciyarka ba sannan bakayi tunani me kyau ba, karkayi takamar dan mahaifinka me gidan mahaifina ne bazai sa nagaya maka abinda ke cikin zuciyata ba, idan kuma kayi kuskuren aurena girmamawa zai yi wahala ka samu romon da maxa dayawa in sunyi aure suke samu ba sai nagaya maka ba dan nasan kaima agidanku akwai irina safwan kake ko wa kake ;? ina son nagaya maka wallahi ban ta'bawa yiwa kowani mahaluki karya ba ko shi waye to kaima bazan ma karya ba, safwan har ka aureni bazan maka biyyaya aure ba sannan bazakayi min kulle ba, duk abinda nake so shi zanyi agidanka,kuma ba lallai ne na dinga maka girki ba idan taka ma har Wanda nake so sai na kawoshi gidanka kuma nayi duk abinda nake so dashi ,idan har kaga zaka iya to kana iya turo a karasa mgnr aurenmu da kai ,idan km ka janye niyyar aurenka akaina sai mucigaba da muntuncinmu , tayi shiru tare da mikewa tayi hanyar kofa, har ta zira kafarta daya a kofar parlou'n sannan ta tsaya batare data jiyo ba tace zaka iya fitowa ka tafi tunda na sallameka ..


tana gama fadar hk ta juya shi kum safwan da bita da kallo sannan ya saukar da numfashi ckin sanyi jiki ya tashi ya nufin parlour'n zuciyarsa cike da tunaninta tabbas yasan yana son me'ad so kuwa me tsanani har yana ji aransa matukar bai aureta ba tabbas akwai Matsala dan wannan abun datayi masa mugun burgeshi tayi shifa bai ga dalilin da zai bar wani me'ad dinsa ba alhalin yana raye bai mutu ba ,babu wannan nmj a duniya kuma kowaye sai ya nemoshi da karfinsa da dukiyarsa .


ita kuwa me'ad byn tafiyarsu ta shige part dinta ta sake wanka tasanya kaya marsa nauyi sannan ta fito paloun mom dake zaune ita kadai tana kallon labarai a CNN jin takun me'ad tana saukowa daga step " momy kallon kike ke kad'ai a parlour'n ina suhailat ?


momy tayi dry ai daman yanzu zan kiraki dan ina son naji yadda kuka yi da safwan.


me'ad tayi saurin kallon momy tace "waye km hk an?
da sauri momy tayi saurin kallo me'ad cikin mamaki da tsoro, cike da in ina momy tace " me'ad me ye nufinki?


batare da ta kalli momy ba tace "nufina bawai wuce ya nemi wata ya aura ba danni har abada ta fu'..


"yi min shr me'ad kada ki meidamu kanana mutane tare da meida hannun agogo baya dan wallahi tallahi baki isa ba a wannan karon mune muka haifeki dole muyi duk yadda muke so dake wallahi baki isa kiyi mana mugunta ba dan hk ki meida hankalinki cikin jikinki tun kafin mahaifinki yaji .


"momy kingama ?


me'ad ta fad'a batare data kalleta ba, bata jira abinda momy zata ce tacigaba "mom ni babu ruwana da dady yasani dan nafi son hk, kowa fa takasan yake yi yanzu dan hk baxaku matsamin ba, dan kawai kun kawoni duniya, ku dai yi hkr zanyi shawara da zuciyata idan na rarrashita akan fu'ad taji zata iya rabuwa dashi fine then zan iya auren safwan ,amman idan taki hakura sai dai kuyi hakuri, duk yadda nayi da zuciyata zan gaya muku tana gama fadar hk ta mike zata fita momy itama ta mike cikin bacin rai da fushi ta riko hannunta har sai datayi kara.


"momy cire min hannuna zakiyi dan kawai banason safwan ?


momy dataga ala'mun fa yarinyarta tayi zurfi sai ta kwantar da murya "kiyi hkr me'ad ki zauna muyi mgn nasan zaki fahimci mamanki.


me'ad ta kurawa momy ido tana saukar da numfashi momy "kema kiyi hkr ki barni da zabin raina sannan mgnr da zamuyi ,mayi idan na tashi daga bacci tana karasa fadar hk ta mke ta koma samanta momy tabita da kallo cikin takaicin domin ita kad'ai tasan bala'in daza'a yi idan mahaifinta yasan tana soyayya da talaka abunda shi ya tsana kenan had'a hanya da talaka arayuwarsa .


me'ad kuwa gadonta ta haye tayi kwancinyarta tare da rufe idanunta fu'ad fess take gani acikin idanunta har ga Allah wani irin so take masa me tsuma zuciya da wuyar bari ..hk tayita tunaninsa har bacci ya dauketa bayan ta tashi momy tashigo d'akin tayita rarrashita amman furrr taki yarda da zabin iyayenta "momy tun farko banason safwan ke dady kuka matsa min ,ta yaya yanzu nasamu wanda nake ku nemi hanani aurensa.


"Ba hanaki aurensa mukayi ba ki tuna alkwarin dake tsakani Dan allah yarinyata ki duba lamarin nan "momy kema uwa ce nasan kinsa abinda ake kira da soyayya tunda nasan ba hadaku akayi da dady ba, ku kuka ga junanku ,ina rokonkanki momy ku barni da fu'ad wallahi akansa zaku iya rasa takarasa mgnr tana kuka . ..tsakanin uwa da 'ya tuni itama ta sauko taji zabin diyarta yayi mata, zata bata damar ta auri zabin zuciyarta..


Ranar da kyar safwan ya runtsa kwana yayi yana zubawa cikinsa giya da tunanin abun yi, "tabbas yakamata ya d'auki mataki nemo kowaye ke kokari kawo rayuwarsa nakaso ,tun da sanyi safiyya ya baza yaransa domin bincike akan wanda mead take so .
Tashin farko bincike ya zo masa akan yadda bai so ji ba ,domin duk wani abinda ya danganta da fuad da rayuwarsa sai daya zo masa daki daki ya sha mamakin" wai Dan talakawa me'ad take kokarin neman gujewa aurensa ,aransa yace" idan kinsa wata ai baki San wata ba ,nasan dai babu ta yadda za'a mahaifinki ya yarda ki aureshi, balle shi karan kanshi yaron bai sonki ,gbdy safwan yazaba yaransa a gari domin cigaba da kawo masa rahoton komai akan fu'ad.


******
ranar monday da misalin karfe 1:00 na Rana kabir yazo gidansu fu'ad domin zuwa office din Alhaji Abubakar aminin mahaifinsa Wanda zai samarwa fu'ad aikin da kaninsa ,a shiryensa yake zaune a kofar gida yana zaman jiran karasowar kabir yana hangosa yashiga cikin gidan inda yakewa inna sallama "inna mu za fita akan zance neman aikin kiyi min adduar samun nasara kansa ta dafa "InshaAllahu zaayi nasara zaka samu wannan aikin ina jin hk ajikina sai dai Wani tsananin rabo"allah yasa ni na wuce, "a dawo lfy Allah ya tsare, "ameen ya fice daga dakin .


kai tsaye company da alhj Abubakar ke tafiyar da aiki suka nufa akan lefan din fu'ad suna isa suka iske jama'a wanda dayawansu neman abunyi ya kawosu, batare da bata lokaci ba suka nufi office Alhaji Abubakar inda suka iske shi yana sallah sai mataimakinsa sukagani suka gaisa ya nuna musu gurin zama "ku zauna ga guri nan ,suka zauna har zuwa sanda ya idar yakaraso garesu inda kabir yayi saurin cewa dady barka da Warhk "a'a kabir har kun iso?ya fad'i hk tare nufar hanyar office dinsa dake cikin wanda suke zaune da sauri kabir da fu'ad suka mike sukabi bayansa atare suka shiga kabir yasamu guri ya zauna akan daya daga cikin kujerun gurin tare da jawa fu'ad shima ya zauna "ai kuna da sa'a duka takardun mutun biyu din da ka kawo sun samu aiki,Amman D'an bani minti 2 ya fadi hk sakamakon wayarsa dayaji ta d'auki kara ya zagayo ya zauna mazauninsa tare da d'aukar wayar ya manna kunnesa abinda yaji ne ya kusan bugar masa da zuciya "safwan almustapha maitama ne ke mgn da kai daga nan office din jakandancin na kasuwancin Nigeria, naji ance wani mai suna fu'ad yazo neman aiki gurinka ko ba hk ba ?
"Haka ne ranka ya dade.
"To kasani bashi aikin da zakayi yana daidai darasa kujerarka da matsayinka gbdy. .." a,a ranka ya dade ba zayi hkn ba InshaAllahu yadda kake so hk zaa yi,"idan kabi umarnina ka tsira da aikinka kit safwan ya kashe wayar .


shi kuma alhj Abubakar yashiga goge gumin dake keto masa, bayan yagama goge gumi ne ya fuskanci kabir "yauwa kabir batun aikin abokinka a gsky babu shi a halin yanzu ,Dan bazai samu aiki akarkashinmu ba sakamakon wasu dalilai da ba sai na bayyana maka su ba .
"Kmr yaya dady?"da fari kace zasu samu ,yanzu km ka..fu'ad ya dafa kafad'arshi yana mai mikewa tsaye "karka damu abokina da rashin samunka aikina ka d'auka komai mukaddari ne bani da rabon samun aiki anan ne... yana karasa fad'ar hk ya juya.
"Amma fu'ad...."nace karka damu kayi facing din na abdulrashid


alhj Abubakar da zuciyarsa ke cike da matsanancin tausayin fu'ad yacigaba da mgn sai zance aikin kaninka shi yasamu aiki, maiduguri zashi ,zuwa wata mai zuwa ,wannan aikin mutane dayawa na nema Amman acikin sa'a yasamu kad'an jira takardar tabbatar da samun aikin domin zata iya zuwa a kowani lokacin .


fu'ad yataso daga inda yake zaune yana tunanin dayasa zancen samun aikinsa ke neman shan ruwa, ya kwankwasa glass din office inda kabir ya d'ago yana dubansa cike da tausayawa, alama yayi masa da zaije kasa ya jirasa, shi ma da kai ya amsa da badamuwa .


Fu'ad ya sauka kasan maikatan ya isa inda yayi parking din maching dinsa yana waige waige a gurin hannunwasa duka zube cikin aljihun wandosa ,karaf idanunsa ya sauka Akanta tana tuki cikin karewa, itama tun daga nesa ta hangosa tayi saurin ware idanunta bakinta na furta" fu'ad Dina ...... sai dai tun kafin takaraso inda yake taga ya haye maching dinsa tare kunnawa yayi gaba aiko itama tabishi abaya..........


Mmn sudais ce
[11/3, 8:26 AM] El~hajj: πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—
'YAN CINKI
πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–
πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—


~NA~


*AYSHA A BAGUDO*


~DEDICATED TO~
MRS ADAM
( YAR MUTAN KAGARA)


Page 53 to 54


.... gudu yake sosai akan titi tana binsa abaya ,yasamu ya karya wata kwana wacce zata fitar da mutun kai tsaye oshodi Express , anan machine dinsa ya tsaya cak yaki tafiya, sai ma hayakin dayasoma fita daga cikin salansar , dan hk ya sauko daga kan machine din ahankali tare da tsaida shi yana dudubawa, har sanda ta iso garesa tayi parking had'e da fitowa daga cikin motarta zuwa inda yake " abun yayi min kyau ba kad'an "gashin nan cikin minti uku kacal nazo na sameka ,"me km yasamu machine dinka ta tmbyta tana dukursowa ta karkashinsa tana kallon fuskarsa cike da matsanancin kaunarsa ,ya mike tsaye tare da rike kugunsa da hannunsa d'aya yana waige waigen ta inda zai samu makaniki kusa ganin babu alamun hk yasa da dungule hannunsa daya ya naushi iska yana furzar da huci mai zafi daga bakinsa ,ita kuma ta matso kusa dashi tana fuskantashi tace"wato fu'ad lokaci yayi da zan baka gudumuwa ,ta hanyar ajiye wannan machine din naka, mai kama Dana masu ACA'ban abbatuwa .


Yana jinta sai dai yayi mata banza batare da ya ko kalli inda take ba har sanda ta maida idanunta akan machine din "uhmmmmm Allah sarki machine dinmu kenan "ko tun yaushe kake dawainiya damu? Kana
Ta matso kusa dashi har suna iya shakar numfashin junansu "kana ji ko fu'ad,Kafin yanzu yaci ace ka kalli duniyar wata ,duba yanayin morar machine dinka dakayi, tazarar dake tsakanin duniya da wata Mil dubu biyu ne da talatin da biyu da d'ari takwas da sha uku ,ta sake matso shi sosai tamkr zata shige jikinsa wanda hakan yahaddasawa zuciyarsa bugawa da karfi yaja baya kad'an "meye hk kike kuqarin yi ?
Sharesa tayi kmr bata manufarsa ba tace "bari na tmbyeka wani abu ra'ayinka ne hawa machin ko me ?


"kinsan acikin duniyar rayuwata ba son takura balle shishigi, Dan hk ki kama gabanki kawai ya wuce yasoma tafiya dan yasan machin dinsa ya rigada ya tashi daga aiki ,da sauri ta biyo bayansa "wai abun yayi maka rashin dadi ne ko me daka wuce kabarni tsaye?


Sake banza yayi daita yacigaba da d'aga kafafunsa batare daya kalli inda take ba "kana jina ko zan sai maka lafiyayyiyar mota kiran zamani saboda kafi karfin ka dinga hawar wannan kwarababben machen din , shi km wannan machine sai ka kyautar dashi amman kafin nan zan saka kanikawa suzo su d'auka domin gyara .
yayi saurin juyowa yana fuskantarta har hucin numfashinsa ya bugi hancinta ,tayi saurin lumshe idanunta kirjinta na mahaukacin bugawa kusan minti biyu suna tsaye suna kallon kwayar idanun juna sannan a kasalance muryarsa ta fito "anan garin aka haifeni na tashi na girma, nasan kowani lugu da sako dake nan unguwar, akwai makanikai idan ina bukata zan nemesu da kaina, "batu na mota km kibar abunki saboda fu'ad bai bukata komai daga gareki .


"no karkace hk mana bayan da dukkanin alamun rayuwarka na bukatar ha.....a matukar tsawace ya katseta ta hanyar cewa "Kimin shiru anan kafin na d'aukeki da maruka ...


"Mari fa kace?"kina mamakin faruwan hknne ? Yayi mata tmbyr yana tsare gira ," Tayi saurin girgiza kanta alamun a,a "ok na d'auka kina mamaki ne kiga aiki da cikawa wawiya kawai sannan ya juya yacigaba da tafiya tayi saurin shan gabansa tana sauke naunayen ajiyar zuciya tareda rike kugunta da duka hannuwanta "ok muje na saukeka a gida tunda baka bukatar taimakona "nagode kije abunki kawai....
"Haba fu'ad me yasa kake min hk, Allah fa shi yasan abinda yake nufi daya had'amu ,kayi hakuri kabari na saukeka..a fusace yace "banaso ko dole ne?


Ta. runtse idanunta ahankali tana jin d'aci da rad'ad'in ,wulakanshi gareta, kusan second biyu tana tsaye agurin tana experience din abinda rayuwa kan zowa mutun batare daya shirya ba ,ko a mafarki bata ta'ba expecting zata tsinci kanta cikin soyayya da irinsa ba ,ta d'an Jima tsaye domin ita kad'ai tasan halin tashin hankalin data tsinci kanta sannan tasoma kok'arin bud'e idanunta taga wayam babu shi babu alamunsa agurin ta kara gaba da sauri ta fito titi still bata ganshi ba ,sai ma cin karo datayi da wasu yara kusan su 6 tsaye abakin titi mutun uku makafai yayinda 3 suka kasance masu ido, da alamun titi suke son tsallakawa , tsawon minti uku tana tsaye tana dubansu yayinda mota ko d'aya batayi kok'arin tsayawa domin basu damar tsallakawa ,sbd idan ba lura kayi da kwayar idanunsu da sukayi sama ba, ba bazaka ta'ba cewa marasa idanu bane ,cike da matsanancin tashin hankali ta karasa zuwa inda suke tsaye tare da d'agawa mota ta karshe dake shirin kunno kai hannuta take motar ta tsaya cak, sannan tasoma tsallakar dasu d'aya byn d'aya, wanda hkn ya faru ne a idanun fu'ad ,ahankali shima ya fito daga inda yake zaune yana jiran ta wuce ya kama gabansa, yak'araso inda sauran yaran ke tsaye, sai waigawa tayi tagansa rungume da yaro daya, d'ayan km rike a hannunsa
bayan sun gama tsallakar da yaran, tasoma kok'arin iskeshi inda yaja ya tsaya rungume da hannunwasa duka a kirji yana kallonta tmkr ranar yasoma ganinta ,tana k'arasowa ta tsura masa idanunta tana kallonsa kmr yadda yake kallonta gabadaya kowanensu zuciyarsa cike take taf da shaukin juna "me yasa kake kallona hk ?
"Na canza maka ne ko kuwa har yanzu kana jin haushina aranka ?tayi masa tmbyr ajare tana sake kallon kwayar idanunsa da suka soma canza launi "a halin yanzu

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads