Header Ads
Showing 111001 words to 114000 words out of 163596 words

Chapter 38 - YANCNKI Book Complete by Aisha Bagudu.txt

Ads the beginning of article before Image

02 Jun 2024

1309

Ads at the middle of Article

bayanin inda malamin dayayi masa aikin yake,kai tsaye gidan bokan da akewa lakani da malami wanda ko kusa bai dace da amsa wannan sunan ba ,saboda mugun aikinsa da kuma irin ta'asar dayake aikatawa, rashin imani had'e da rashin tausayi sune abubuwan da suka baibaye zuciyarsa , bashi da maraba da irin bokayen nan na kan tsaunaka ,domin kuwa kallo daya zaka yi masa ka tabbatar da rikakken matsafi ne ,koda suka isa sun iske dubbanin jama'a tundaga kofar gidan har cikin gidan masu neman biyan bukata ,mutane na ganin rundunar polisawa na k'ok'arin shigowa kowa yashiga hankalinsa wasu ma tuni suka arci na kare kar a had'a dasu .
batare da bata lokaci ba suka samu nasarar shiga inda boka yake ta,asa da wata mata kafin yi mata aiki a matukar firgice ya tashi daga jikinta yana kwaso kayanta Dana shi ya rufe jikinsa dashi ,ita kuma ta kudindine jikinta tana kirma, basu tsaya wata wata ba suka damko wuyansa sukayi hanyar waje dashi tsirara haihuwar uwarsa, ya turje yaki tafiya ,yana neman ba'asin dalilin dayasa zasu shigo har cikin gidansa suka mashi ,wannan mutsu da gardamar da yayi musu yasa suka rufeshi da dukan mutuwa tunin ya bada had'in kai .
Aka fito dashi nan mutane suka ihu, masu guduwa nayi masu runtse idanunsu nayi ,daya daga cikin police yashig Janshi a kasa ,kai tsaye office dinsu suka nufa dashi , lokacin da'aka tambayesa game da aikin da yayiwa su mudansir bayi musu ba Amman lokacin da'aka nuna masa mudansir muryarsa kawai ya iya ganewa da abubuwan da suka faru atsakaninsu Wanda mudansir din ke kara yin bayani akansu ,hkn ya k'ara tabbatar masa dashi din ne mutumin dayayiwa aikin asiri da allurai ga shugaban aikinsa.
Cikin tashin hankali jami'an tsaro suka shiga yi masa tambayoyi daki daki shi kuma yana basu amsa, inda yace asirin zai karye Amman sai sunje ma'aikanta da office dinta saboda abubuwan da'akayi amfani dasu suna dayawa .kuka tahir yakeyi sosai tmkr ransa zai fita ya durkusa kasa gaban boka yana kuka yana rokon boka daya fad'i gsky mutun nawa ne suka zo yin asiri gurinsa duk rashin eimanin boka sai da tausayinsa yakamasa,yayi kmr ya fadi gsky sai kuma ya fasa yaki cewa komai dan a wannan stage din kowa ta kansa yake babu wani zance taimako .


Gabadayansu aka tasa keyarsu zuwa company, suna isa aka tsaidasu agaban tafkeken get din ma'aikanta mutane nata wucewa suna kallonsu ,yayinda tsirarun jama'ar company da suka San abinda suka aikata sukayi caaa suna kallonsu tare da Allah wadai dasu ,Allah sarki tahir yayi kukan dayasani har hawaye suka daina fitowa daga cikin idanunsa ,
bayan an gama kare musu kallo sannan aka shiga dasu cikin company kai tsaye office din me'ad akayi dasu ,boka yayi shiru yana kallon office din hankalinsa a matukar tashe gbdy yama rasa ta ina zai fara.


A zafafe daya daga cikin polisawan yayi magana cikin zafin rai da d'aga murya "what are waiting for?
ganin bokan na nuku nuku tare da zare idanuwa"kayi abinda yakawo mu mana cikin rawar murya yace "yalla'bai kujerar datake zama za'a nuna min batare da 'bata lokaci ba aka nuna masa ya isa yashiga sarakulensa ,sai ga allurai su bayyana Wanda bazasu lisafu ba ,ba chairman da me'ad ba, hatta polisawa sun razana da ganin wannan tashin hankali ,boka ya cire gbdy allurai sannan ya dinga bin koina acikin office din yana ciro layu Wanda bil adama bai isa yaganewa isanunsa ba, sai dai a irin wannan lokacin.
duk wani abinda akasawa me'ad a office dinta da cikin ma'aikatar sai da aka ciresa sannan aka tasa keyarsu zuwa caji office inda daga nan za'a gurfa nan dasu agaban kotu ....


Tun daga wannan lokacin komai ya daidaita ga me'ad tasamu natsuwar zuciyar cigaba da yin aikinta yadda yakamata, sai dai duk abinda za'a yi ta daina tsoma bakinta aduk abinda bai shafeta ba, alamuran aikinta kawai tasanya agaba , matsalarta daya ahalin yanzu fu'ad ne......
tayi iya yinta ta ciresa aranta Amman abun yaci tura, kullun soyayyarsa k'ara wanzuwa take acikin zuciyarta, shiru tayi tare da yin tagumi da hannunwata duka ,tana tunaninsa cikin hk akayi knocking din kofar office dinta, naunayen ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa"come in cikin murya tkmr mara kuzari ,sannan ta dukar da kanta domin cigaba da ayukan dake gabanta.


"Turo kofar yayi ahankali ya shigo fuskarsa a daure babu alamun murmushi ko kad'an sannan ya meida kofar yayi key ,sanye yake cikin wani had'ad'en suit Wando da Riga black sai long selve pinky daga cikin rigar hannunsa daure da agogon fata baki ,yayinda gashin kanshi ke kwance luf luf tmkr ta jinjuri..


Kamshin turarensa daya kai wa hancinta ziyara yasa tayi saurin d'agowa a matukar firgice idanunta ya sauka akansa take gabanta yayi wani irin fad'uwa t "fu'ad ta furta jikinta a matukar sanyaye while zuciyarta na wani irin harbawa da sauri sauri ta tsura masa idanunta yayi bala'in canza mata .
ahankali ya fara taku zuwa inda take , tare da tsura mata kyawawan idanunsa masu shegen kyau da rikitarwa, tana can kallonsa ya kamo fuskatarta da hannunwasa duka cikin sarkewar murya yace "oh my goodness god I really missed you so much love sannan ya mikar daita tsaye ya kamo hannuta ya zagayo daita zuwa Kan doguwar kujera me zaman mutun uku ya zauna had'e da zaunar daita akan cinyarsa, yasanya hannunsa daya ya d'ago ha'barta ya Sanya kwayar idanunsa cikin kwayar idanunta ,wani abu taga ya fito daga cikin idanunsa yashiga nata me kama da kibiyar so ..tayi saurin lumshe idanunta batare datace masa komai ba.. sai lokacin murmushi ya bayyana akan fuskasa "am here for you love na baro duk wasu mahiman aikina saboda nazo gareki domin muyi sharing farincikin abinda yasameni ayau, kasancewar nasan duk duniya you are the first person dazatayi murna wannan abinda daya sameni yakarasa mgnr yana kissing din lips dinta ,sannan ya ciro wata farar envelop acikin aljihun wandosa ya mika mata "amsa ki bud'e ki gani an yi min double promotion a wajen aiki tare da transfer zuwa cross river.....
Da kyar ta tattaro natsuwa tasanyawa jikinta tace "Allah yasanya alkairi Amman karka kara tako kafafunka zuwa inda na......."shiiiiiiiiii ya fad'a yana zare karamin hijabin datake sanye dashi, cikin sauri ta turesa yayi baya kad'an zata mike ya fixgota ta fad'o saman fad'ad'den kirjinsa ,ya rungumeta tsam had'e da matseta ajikinsa yana kissing wuyanta ,tasoma mutsu mutsun turesa Amman yaki sakinta sai ma kissinh dinta hungrily daya cigaba da yayi,Tare da k'ok'arin had'e bakinsu guri daya , yayi yayi ta bud'e bakinta taki da kyar yasamu nasarar bud'e bakin tare cafko laulausar harshenta yasoma tsotsa yana rike da fuskarta da hannu biyu ,wani irin kissing dinta yakeyi tun tana iya jurewa har itama tasoma meida masa martini, suka shiga romancing din junansu cikin wani irin shauki ,fu'ad bai barta ba har sai dayasamu natsuwar dayake bukata daga gareta . Adaidai wannan lokacin kira yashigo wayarta.


"Ture fu'ad din tayi kad'an ,ta janye jikinta tana sauke numfashi da ajiyar zuciya atare ,sannan tasoma k'ok'arin d'aukar wayar ..cak taji ya kamo tsintsiyar hannuta ya amshi wayar ya ajiye a gefensa yana kallonta yana busa mata iskar bakinsa Wanda ke sake dilmiyar daita tafkin kaunarsa.
a natse ya kai yatsan hannunsa kan lips dinta yana wayo da yatsansa har zuwa saman kirjinta yana mgn "ki bud'e envelop din nan ki duba matsayin da mijinki ya taka acikin D'an kankanin lokaci, abinda mahaifinki yake da burin gani kenan, ya ganki cikin farinciki Wanda nasan wannan arziki bashi kike bukata ba sannan duk duniya babu wanda zai iya baki wannan farinciki byn Allah daya haliceki sai ni.." "me'ad yakira sunanta a raunane while bakinsa na daidai wuyanta yana aikin busa mata Iskar bakinsa Wanda ke kashe mata sansar jiki ,ahankali jikinta ya dinga sakewa yana narkewa tsigar jikinta suka mike tsaye yrrrrrr , zuciyarta ta ding beating da tarin kaunarsa "ban manta halaccinki gareni ba ,sannan ban kasance me manta alkairi ba ballanatana na manta naki, da kikayi min Wanda sadaukarwa ne gareni , Nasani kin yi hidima dani da rayuwata gabadaya ,kuma nagode da hkkn ya k'arasa mgnr yana mai mikewa tsaye tare daita ya manneta ajikinsa suna fuskatar juna ,wani irin d'auke numfashi yayi da sauri saboda kirjinta daya tokare nashi kirjin, ahankali numfashinsu ke tsarkewa da juna yana juyewa zuwa wani shauki na daban me zafafa damkon kauna da karfafafa soyayya.
"me'ad ki kular min da kanki duk da kince kin daina sona Wanda ni nasan karya ne hkn bazai ta'ba kasancewa ba muddin ina raye ......
"Idan kuma hasashena bai zamanto gaske ba ,kiyi k'ok'arin ki dawo da soyayyata sabuwa fill acikin zuciyarki saboda babu kalmar rabuwa acikin tsarinmu kmr yadda kika sha Fada min abaya, Dan ko kin barni ni bazan barki ba sai dai mubi juna ......
yana gama fad'ar hk ya kamo fuskarta yayiwa lips dinta light kiss "bye take good care of yourself for me before na dawo a fafata ya juya yasoma tafiya yana taku kmr bai son taka kasa , tabi bayansa da wani irin kallo kirjinta na dukan uku uku har ya bar office din idanunta na Kan kofar ta kasa d'auke idanunta akan kofar daya fita.
ahankali cike da matsanancin sanyi jiki ta k'arasa tayiwa kofar key ta dawo ta d'auki hijabinta ta saka sannan ta d'auki farar envelop din daya bar mata ta koma mazauninta ta zauna tana sauke ajiyar zuciya sannan ta bud'e envelop din inda ta ci karo da wata farar takadar tasoma dubawa a natse .
gyara zamanta tayi sosai saboda abinda idanunta yagani fu'ad ne ya kusan taka matsayin MD na companies din dayake aiki tare da Karin albashi na dubu dari duhu da hamsi Akan 150k dayake amsa a watanin baya da suka gabata,sababbin motaci guda biyu da gida....runtse idanunta tayi hawaye suka gangaro bisa kuncinta ahankali ta furta "Allah kenan babu yadda bai iya da lamarinsa ba ,abinda suka dade suna jiran zuwansa, azahirin gsky tayi matukar farinciki ,duk da batare zasu ci wannan samuwar datazo masa ba wunin ranar kusan cikin farinciki da annashuwa tayisa ........


**************
Asabar din karshen wata march ,kofar gidan tshohun commissioned of police na Nigeria makil yake taf da dubban jama'a dake cikin garin lagos da wajenta , suka sheida d'aurin aurin khalid Ismail money mis road da sajida Aliyu a lagos state central mosque a kan Sadaki mafi kankanta.....


Mmn sudais ce
[11/3, 8:30 AM] El~hajj: 💗💗💗💗💗💗
'YAN CINKI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗


~NA~


*AYSHA A BAGUDO*


~DEDICATED TO~


*AUNTY BASEERA WANNAN PAJIN NAKI NE , INA MATUKAR GODIYA BISA GA SOYAYYARKI , ALKHAIRINKI,KULAWARKI GARENI ALLAH YA BARMU TARE*🤝🏻🤝🏻🤝🏻


Page 82


........tana tsaka da bacci ,tayi wata irin zabura ta mike zaune akan gadonta tana zare idanuwa ,gumi na karyo mata ta koina a sansar jikinta tmkr ac dake cikin d'akin ya daina aiki . kirjinta ne yashiga mahaukacin bugu da karfin gaske, yayinda kunnuwanta ke sake jiyo mata abinda ya farkar daita daga baccinta,sautin muryar maroka tacigaba da jiyowa suna tashi ta koina ,a kofar gidansu maroka ke yin kirarin Amman ji take timkr acikin d'akinta sukeyi ,tayi wata irin zabura ta mike tare da hantsilowa daga saman gadon jikinta na wani irin kyarma......
ta fito daga ita sai rigar bacci iya cinyarta .
tana k'arasowa parlour'n nan tashin hankalinta ya karu sakamakon fuskokin mutanen daban daban tagani makil acikin parlour'n suna cike da matsanancin farinciki, wanda hkn yasa tayi tsaye turus tana binsu da wani irin kallon mamaki yayinda hankalinta ke k'ara tashi ,sakamakon yadda marokan ke maimata kirari Tare da ambato sunansa Dana mahaifinsa da kakanninsa "yeeeeee kuwa jama'a ku sheida an d'aura auren sajida Aliyu da khalid money mis road jikan sani gilo... Allah ya sanyawa aurensu albarka ,"hakika khalid kashigo gidan girma tare da sa'ar mallakar 'yar gata shalele agurin mahaifinta , hjy sajida ikon Allah yarinya irin arziki wacce ta taso cikin arziki ,hjy sajida kiyi min arziki ki sha min arziki ,arziki nke so daga gareki ,ina son kujera hajjin bana da sabuwar mota yar yayi , take dady yace an bashi ,"khalid kaima irin arziki ne wanda ya gada tun daga kan ka kannin kakaninsa, ka nuna halin girma khalid banda makodo domin gadon gidanku ......ai kuwa aka kashe dariya.


"shin gaskiya ne abinda kunnuwanta suke jiyo mata daga bakin maroka nan ko kuwa har lokacin mafarki take yi? Tayiwa kanta tambayar tana mai kai
hannunta ta muntsini gefen kuncinta taji ko mafarki take ko kuwa a zahiri ne abinda ke faruwa an d'aura aurenta da Khalid .. .....
jin zafin da taji ne yasa ta fahimci a zahirance ne ba mafarki ba ,take jikinta ya d'auki kar karwa .......
wata daga cikin makociyar ce tayi bud'a " eyyyyyirrrrrr "ga amarya nan ta fito ,nan hankalin mutane gabadaya sukayo kanta kowa ka kalli fuskarsa agurin cike take da tsantsar farinciki da annashuwa.
cikin haka sai ga aunty nadiya ta fito daga cikin d'akinta rike da Wasu kaya zumar zuwa ta tasheta a bacci tasanyata tayi wanka tasa batare dasanin komai ba .
da sauri sajida tak'aro gareta "aunty yaushe duka wannan abun ya faru batare da sanina ba... ?
"Wai ma auren wa aka d'aura yanzu ?
aunty nadiya takamo hannunta cikin nata tace "ki natsu sajida ki dawo cikin natsuwarki mu ... ..
Tayi saurin katse aunty nadiya ta hanyar cewa "bazan ta'ba dawowa cikin natsuwata ba har sai naji zahirin gsky abinda ya faru plz auntu ki gaya min auren wa aka d'aura ?
"saboda 'kwa'kwaluwata tashiga rudu da gigita akan abinda kunnuwana suke jiyo min daga waje .
Aunty nadiya ta kamo hannuta cikin nata "muje d'akinki muyi magana .
fixge hannunta tayi da karfi daga cikin na aunty nadiya jikinta na rawa, hawaye na bin kuncinta "duk abinda zaki gaya min ki gaya min shi anan ,anan nake son jin komai tak'arasa mgnr tana durkushewa kasa bisa gwiwowinta ,itama aunty nadiya kasa tayi kmr yadda sajida tayi had'e da raunata muryarta Dan kar mutane su fahimci yadda auren yakasance "kukan ya isa hk sajida ,aurenki da Khalid aka d'aura yanzu..
wata irin gigita tayi daga tsugunnen datake tare da d'aura duka hannuwanta bisa kanta" shikenan abinda take tantama gaske ne ya ta faru takare ...
take jinta da ganinta ya d'auke na wuncin gadi tashiga kallon jama'ar dake tsaye akanta suna mamakin abinda ke faruwa...


cikin HK tawagar angwane suka sanyo kai cikin gidan bisa al'adar jahar Lagos ,byn d'aurin aure ,ango zashigo tare da abokansa domin gaida dagin amaryasa, sannan suyi hoto da amarya,suna shigowa parlour'n idanunsa ya sauka akan durkushe tana kuka, Sam khalida bai yi tsamanin ganinta hk ba, saboda a tunaninsa ya d'auka zata hauka yi fiyye da hkn.


aunty nadiya najin shigowarsu ta mike tsaye ta koma gefe guda cike da jimami, shi kuwa khalid da sauri ya k'arasa inda take zaune tana zare idanuwa ya tsuguna agabanta tare da baza babbar rigasa ya rufeta dashi dan kar abokansa su karewa yanayinta kallo, yanayin da shi kad'ai ya cancaci ganinsa..
idanunsa ya tsura mata yana kallon yadda hawaye ke bin kuncinta gabadaya ta gigice ta fita haiyacinta, kallo dayan dayayi mata ya gane kalar tashin hankali datake ciki, matsota yayi sosai kmr zai shige cikin jikinta muryarsa a kasalance yakira sunanta"sajida tashi ki koma d'aki, ki suturta min jikinki ,ki daina mamaki da hukunci Allah, kinga yadda alamarin ubangiji yake ko?
nayi magana da harshen malaiku Allah ya amsa ....


tayi masa shiru kasancewa bata cikin hankalinta ,Dan kwata kwata bata San abinda yake fad'a ba ,maganar duniya yayi mata Amman ko gezo batayi ba agurin, ta dawo tamkar mutun mutumi yayinda abokansa suka shiga tsokanarsa ... bai juyo ya sauraresu ba yacigaba dayi mata mgn ,kusan minti goma ya lura da tasoma dawowa cikin haiyacinta, Dan haka yasanya duka karfinsa ya cici'beta ya rungumeta bisa kafad'arsa Wanda take parlour'n ya haigitse da ihun jama'a..aunty nadiya kanta sai dataji kunya ta kamata "aunty nadiya ina ne d'akinta ? Inji cewar Khalid
Da sauri tayi gaba shi kuma ya biyota abaya hannuwansa duka rungume daita ..
bud'e yaga d'akin da aunty nadiya ta nuna masa sannan ta juya byn ta mika masa ledar hannunta Wanda kayan sajida ne aciki ,agefen gadonta ya ajiyeta yaje ya kulle kofar ya dawo ya tsaya a tsakiyar d'akin yana karewa d'akin kallo .
d'akin neat ,koina kamshin turarenta yake fitarwa ,ya Jima tsaye yana kallon d'akin da take rayuwa aciki Wanda ya nika NASA sau dubu ........
ahankali yasoma taku zuwa inda take zaune tana tsiyayar hawaye gabadaya tashin hankali datake ciki bai barta ta iya furta daidai da kalma daya ba ,kuka take sosai tmkr karamar yarinya, ta kasa goge hawayenta, gabadaya komai ya cakud'emata daga wannan sai wannan ajiye zuciya ta sauke bata jin jure wannan auren shima, domin wannan auren daidai yake da nisantata da fu'ad dinta "why why why !!! Dady why did you do this to me gabadaya duniya tasoma mata dumi ,jikinta yayi mugun sanyi ga matso idanunta hawaye masu zafi suka sulalo bisa kuncinta. hannunsa ya kai ya

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads