Header Ads
Showing 15001 words to 18000 words out of 163596 words

Chapter 6 - YANCNKI Book Complete by Aisha Bagudu.txt

Ads the beginning of article before Image

02 Jun 2024

1629

Ads at the middle of Article

na wuce ina da abin yi ,kinsa ba tun yau nake warning dinkin akan maganar abinda kudinki yake acikin gidan nan ba, amman bakijin magana ko, ni fu'ad bansaki yin abu dole acikin gidan nan ba , duk abinda nagadama na kawo kiyi hkrn amfani dashi ,idan kin siya wani abu cikin salary dinki wannan matsalarki ce dan ban saki ba .


"kai kasani butulu kawai wanda bai san mutunci ba ,kuma wallahi dole ka ajiye useless work dinka, ka zauna ka kula da yari.... motsin bud'e kofar parlour'n yasa ta katse maganarta tare da juyowa ahankali ..


mmn sudais ce
[11/3, 8:24 AM] El~hajj: 💗💗💗💗💗💗
'YAN CINKI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗


~NA~


*AYSHA A BAGUDO*


~DEDICATED TO~
MRS ADAM
( YAR MUTAN KAGARA)


page 26 to 30


........idanunta ya sauka akan k'anwarta suhailat , take tayi saurin wayancewa tasoma shafa sumar kanta tamkar babu abinda ya faru tsakaninta da fu'ad .


muryarta a tsarke tace "a'a suhailat yau kece a gidanmu?


"eh wallahi aunty me'ad ina kwana , ta bata amsa tare da gaisuwa a had'e sannan ta tsura mata ido tana dubanta fuskarta d'auke da tambayoyi .


fuskar me'ad d'auke da murmushi tace " lfy ya kike ?


"lafiya ?


"abban NASREEN ina yini.


"lafiya yabata amsa atakaice yana duban me'ad a wulaqance..


"ammmm gsky yar halak ce ke, yanxu nake maganarki araina ta fad'i hkn tana me sanya hannuwanta duka ta dafa kafad'ar suhaila tare da yin gaba daita ,sannan ta d'an dawo gurin kofar zata ta hana fu'ad fita batare da suhailar ta lura da hkn ba .


"idan kika yi kuskuren ta'ba ko. ...
ai tun kafin yakasa tayi saurin barin gurin ,wanda zuwa wannan lokacin suhailat tayiwa kanta mazauni.


fu'ad ya d'aura hannunsa kan handle din kofar ya bud'e tare da ficewa daga parlour'n zuciyarsa tamakar zata buga, yana Allah wadai da halinta .


me'ad ta karaso kusa da yar'uwata ta zauna tana shafa fuskarta "hailat kinyi kyau fa sosai fuskarki sai sheki take, meye sirrin ne?


"haba aunty ai ke zancewa haka kullun kina cikin hutu da AC, gida ac mota ac haka ma office , ga albashi me tsoka da kike d'auka duk wata gabadaya kin zama big madam takarasa maganar tana kwashewa da dry..


"uhmmm ke dai bari hailat wani jin dadi kenan?
"ni da nake cikin damuwa, kullun zuciyata cike take taf da fargaba rashin lafiyar NASREEN..


wannan maganar da me'ad tayi yasa hailat
gimtse dariyarta, lokacin daya zuciyarta ta tunatar daita abinda ya kawota gidan, nan take yanayinta ya sauya , muryarta a matukar raunane tace " oh Allah aunty me'ad to yanzu ya jikin nata hope she's getting better ?


" wallahi ina matukar tausayawa rayuwar yarinyar nan but Allah zai bata lfy ..


"ameen ameen fatanmu kenan, arayuwa babu abinda muke so da kwallafa rai akansa kmr NASREEN, NASREEN zuciyarmu ce, domin munajinta tmkr duniyarmu da komai namu.


"suhailat, me'ad takira sunanta jiki a matukar sanyaye, sannan fuskarta cike da matsanancin damuwa "in fact you are my angle right now ,i was so happy when you come in, you have to help me out on my daughter, for God's sake, "dan Allah yar'uwata na rokeki ki taimakeni , kema Allah zai duba lamarinki, wannan matsalar tana neman kawo mis understanding atsakanina da fu'ad, dan haka kiyi hkr ki zauna mana tare da NASREEN wallahi idan kika taimaka mana bakaramin dadi zanmuji ba..


" a'a aunty me'ad .....meyasa kike magana irin haka?


" ni da zan koma school yau din ne ,saboda zamu fara jarabawa on monday ,gsky i can't wait for that. ..


me'ad ta saki baki tana dubanta cike da tsantsar mamaki, idan wani yace mata suhailat zata iya dubanta tagaya mata, zata karyata, sai gashi agabanta ta furta hkn, tsawon minti goma idanun me'ad na kan suhailat tana kallonta batare tayi kokarin d'aukesu akanta ba, sannan ahankali ta had'iye abinda taji ya tsaya mata a makoshi.


" aunty me'ad ke me zai hana ki zauna ki kula da yarinyarki, idan kuma bazaki iya zama ba ki nemi me aiki wace zata dinga kular miki daita mana, domin samun kwanciyar hankalinku.


"a gaskiya banji dadi yadda nazo naji kuna sa'insa da abban NASREEN akan wannan matsalar ba, kece fa uwa, ke yakamata ki ajiye naki aikin domin bawa tilon diyarki kulawar data dace .


"kada ki sanyawa zuciyarki d'agawa ko girman kai da nuna isa ke yar wani ce ,idan abban NASREEN yace bazai ajiye aikinsa ya zauna ya kula daita ba , karki manta shi nmj ne, idan kuka rasa NASREEN a halin yanzu kice zakiyi hasara bashi ba, domin kuwa shi zai iya zuwa ya k'ara aurensa har ma ya haihuwa ,amman ke fa ?


"kika sani ko ita kad'ai Allah ya nufeki da samu arayuwarki, a zahirin gsky gara ki ajiye aikinki na wani lokaci ,ki samu damar kula da yarinyarki ,sannan kiyiwa mijinki adalci arayuwa, kiyi masa biyayya data dace, kibi umarninsa, duba ga yanayin yadda kuka tsinci kanku kafin aureku, a gasky nayi matukar mamakin,domin idan akace zaki kasance irin wannan matar ga fu'ad bayan aurenku zanyi mamaki ..


"sunan ya aureki ne amman baki bashi farincikin daya dace, abinda kikeyi masa koni karamar k'anwarki bazan ta'ba aikata hkn ba." wallahi aunty me'ad ki natsu kisan ciwon kanki, kina wulakanta mijinki saboda bashi da komai ba ko?
"to kisani yadda kike wulakantashi , wata nan can tana neman irin shi batasamu ba , karki jawowa kanki maseefa da hannunki, idan kikayi kuskuren rasa fu'ad arayuwa wannan aikin fa da kike takama dashi babu abinda zai miki sai k'arin bakinciki ..


me'ad ta sauke naunauyen ajiyar zuciya batare da tace mata koma illa idanun data zuba mata .


"aunty me'ad idan kinga bazaki iya ajiye aikinki ba ,why not ki d'auki house maid kamar yadda na fad'a miki a tun farko?


" how can you say that suhailat?


"yanzu abakinki za'a ji na sake d'auki me aiki ,kod'ai kin manta irin abinda ya faru dani akan me akina ta karshe ?


"sunan na d'auki me aiki amman bani da kwanciyar hankali da walwala ,kullun zan fita aiki ina fargaba fita ,kwata kwata masu aiki basu min abinda nake bukata ta hanyar kulamin da NASREEN , banci Allah ya taimakeni da yanzu NASREEN dina bata raye a duniya ,a sanadin over dose din magani da me aiki ta dura mata, dan haka bazan iya sake d'aukar me aiki ba arayuwata .


"yauwa idan baki manta ba, aunty ameena ,itama ta fuskancin wannan matsalar akan masu aiki,kina kallon yadda me aiki ta d'auki hannun yarinyata karama ta tsunduma cikin tafashashen ruwan zafi dan tsabar mugunta "yet now expect me to employ house maid and put my self into trouble ina bazan iya ba wlh , ke bamazan sake kallon kowace irin me aika bace.


"aunty me'ad.. ki ajiye zance wata aunty ameena a gefe, saboda itama sakarcinta ne, da nacin son aikinta ya jawo mata wannan matsalar, yanzu dai yaza'ayi da wanda zai zauna tare da NASREEN?


"uhmmm ta sauke ajiyar zuciya tare da cewa "suhailat wallahi ni kaina bansa abinda yakamata nayi ba, "
ni dai idan zaki taimaka min zanji dadi sosai saboda aikina na da matuka mahimmanci.. .


a matukar harzuke suhailat tace "a gskt aunty bazan iya ba , domin kuwa akan wannan matsalar bani da abinda zan iya miki, dan bazan iya ajiye karatuna ba kmr yadda bazaki iya ajiye aikinki ba, dan kula da yarinyarki ba ,dan haka sai ki san abun yi takarasa mgnr tana
me Mikewa tsaye tare da rataye karamar jakarta " aunty me'ad ki zauna gida ki kula da yarinyarki, domin idan wani abu ya sameta kece da hasara ba uncle fu'ad ba, "aikin banza aikin wofi ,yanzu har aiki ya kai rayuwar tilon yarinyarki, sannan ki bari mugun halinki yasa abban NASREEN ya sakeki ,idan dai baki manta ba kisan abinda dady yace miki kafin kuyi aure dashi "karki kuskura ki zo masa da wata matsalar komai akan aurenki dashi, domin kece kikaji kika gani akan soyayyarsa ....
tana gama fad'ar hk tasoma kokarin karasowa bakin kofar domin barin gidan.


tana d'aura hannuta kan handle taji an murd'a ala'mun bud'ewa ,da k'awar me'ad sajida suka had'u " gaisawa kawai suka yi a takaice suhailat ta ra'ba ta gefenta ta wuce ranta a bace ,bayanta sajida tabi da kallo tana mamakin ganin yanayinta sannan ta meida kofar ta rufe tana k'ak'alo dariyar dole ta isa inda me'ad ke zaune dafe da kuncinta tana tunani.


guri tasamu kusa daita ta zauna "meke faruwa ne me'ad, ga suhaita ta fita da bacin rai, ke kuma gaki zaune cikin damuwa ?


"ke dai bari kawata matsalar NASREEN ce dana kiraki akanta, shine ta d'auki zafi akan rashin zamana a gida na kula daita.


"hakika gsky yar'uwarta ta gaya mata but ,idan ta fito ta gaya mata gsky zatayi fushi tunda tasan halinta ba tun yau ba.
yanxu tana mata magana zatace "salary dinsa ba wata uwar yake tsinana musu ba gara shi ya zauna ita ta fita..


"karki damu kawata da zance suhaila, ai ku duka biyun ,kuka haife NASREEN ,idan ma haka ne ai dukanku yakamata ku zauna ku kula daita acikin wannan yanayin ba wai ke kad'ai ba ..


"ki duba min lamarin nan fa kawata, amman ya tsaya tsayin daka lallai sai nice zan zauna tare daita ..


" rabu dashi kawata wallahi shi yafi dacewa ya zauna a gida bake ba,me yasa zai ce lallai sai ke?


"Allah yayi miki albarka kawata ,kinga yadda kika ganni yanzu ,wallahi bazan bari damuwar kowani nmj yayi silar kamuwata da hawan jini ba.


"it's impossible inji cewar sajida .


me'ad ta numfasa kana tace "the right that fu'ad has as a father in this house on NASREEN haka nima nake da right akan NASREEN coz we have equal right akanta ..


"yes zanceki zahiri ,dan hk wallahi karki sake ki yarda da wani tsarinsa ,duk abinda zaiyi sai dai yayi amman shine yafi dace daya zauna a gida.


" uhm wace miki yarda zanyi?
kema kmr bakisan halina ba, ai ina tabbatar miki ina nan akan bakana, dole nasan shine zai hakura ya zauna ,ba dai ni ba .


"kina jina kawata komai da kike gani understanding ne, ni dai abinda zance miki ko zaki je ki samu amininsa uncle sudais , kiyi masa bayanin duk abinda ke faruwa , im very sure zai taimaka miki saboda nasan yadda yake kaunar aurenku da fu'ad a tun farko .


"kuma kin kawo shawara me kyau fa uncle sudais na da matukar saukin kai da kirki, in fact uncle sudais yasan yadda ake tattalin mace tare da bin duk wani dokokinta, idan kika ga yadda yake ririta matarsa da gudun 'bacin ranta sai kinyi mamaki, gashi baya tsakallake dokarta, duk abinda tace ko ba daidai bane,shi daidai ne agurinsa, in takaice miki zuwan da fu'ad yayi gidansu last, daya dawo yake gaya min yana mamaki "wai uncle sudais yana wa matarsa guga bayan ya wanke mata kaya, daya tmbyesa meyasa yake mata wanki da guga, "wai batason na masu aiki tafi son nasa, abinda nawa mijin bazai ta'ba min ba kenan..


"can you imagine.


"tmbayeni ko wani suna uncle sudais yake kiran matarsa dashi .


"wani suna yake kiranta dashi?


"mommy......


"what? sajida ta furta tana jin k'azarta abun acikin ranta.


"am taling you sajida wallahi sunan dayake kiranta dashi kenan .


ai kuwa sajida tace me zatayi idan ba dariya ba, aiko ta dinga k'yalk'yale dariya har da rike ciki "gasky nashi hauka yayi yawa me'ad momy fa kmr wata uwarsa.....


"kinji ke kuma da wani zance ai duk cikin salon so ne..


"wallahi babu wani so anan ,abu babu ko dadin ji, ni kin ganin nan banason na aure mijin da zan dinga juyawa , nafison kmr mijinki me shegen tsurin kan tsiyan nan ,dan allah kimin addua samu miji kamar mijinki..


"dakata dakata ba ameen ba, "dan Allah mubar maganar nan haka ta isa, saboda naga kmr maganar na neman canza salo, idan kuma son mijina kike ,ai sai ki fito ki gaya min baki tsaya kwana kwana ba takarasa mgnr tana jan tsaki.


" haba haba kwantar da hankalinki kawata, bance mijinki ba, irinsa nake maseefar so ...amman dai kiyi hkr ..


"ba damuwa zo ki wuce gida ,nagode da shawarar da kike zo min dashi ,i know my problems is solve uncle sudais zan kai wa damuwata ..


"very nice man sai dai....


"sai dai me?


"ni dai tashi tashi ki wuce ,kin fara bani tsoro wlh ,sannan na rokeki karki sake cewa kina son irin mijina i dont like it, "kije kisamu daidai dake ba irin nawa ba ki aura .


"sajida ta mike tsaye tana murmushi korata fa kike yi me'ad acikin gidana ?


"ban gane gidanki ba?


"no no ba abinda kike tunani bane ,ai gidanki tamkar gidana ne, haka zalika gidana tamkar gidanki ne ko ba hk ba?


" ba haka bane gidanki daban, haka nawa, sajida ta Bude baki zatayi magana, me'ad tayi saurin cewa "ke dai jeki kawai ba sai kin sake cewa komai ba, Allah ya tsare idan kuma baki da kudin fuel ne na baki..


"no motata a cike take taf, sai anjima Allah yasa idan kin gayawa uncle sudais matsalarki tazo karshe.


"ameen ameen thank you so much dear.


sajida tasoma tafiya ahankali tana girgiza jiki wanda ya zamemata jiki, me'ad nabiye daita, a baya har harabar gidan, sai da taga tashin motar sajida sannan ta juya zuwa cikin gidan kirjinta na bugawa wanda tarasa dalilin jin hk a tun sanda sajida tasoma sanyo zance, tana son irin mijinta .


direving sajida take but zuciyarta da k'walk'waluwarta na can gurin kisma mata yadda zata kwacewa me'ad, fu'ad a hanunta yazamo mallakinta, domin ta dad'e da kamuwa da matsanancin sonshi ,km tana jin ko ta wani hali ne sai ta mallakeshi arayuwarta.
take zuciyata tasoma nusar daita," sajida gara kiyi addua idan da alkari son da kike masa km rabonki ne sai kiga kin sameshi cikin sauki tunda gashi bai yi sa'ar matar ba.


sajida aminiyar me'ad ce kut da kut, tare sukayi karatu, tun daga primary up to university, sannan iyayensu aminan junane,aikinsu ne kawai ya bambanta, mahaifin me'ad custom ne ,yayinda mahaifin sajida ya kasaance police.
sajida ita daya ce ga iyayenta, ta ta'ba aure sai dai auren nata bai je koina ba ya mutu sakamakon wasu dalilai.


*****


zaune yake agaban me gidansa ya rafka uban tagumi yana dubansa, a zahirin gasky zaka d'auka hankalinsa da natsuwarsa na gurinsa ne, wanda sam abun ba haka yake ba,tunaninsa da hankalinsa nacan gurin yarinyarsa daya baro ,sannan yana tunanin yadda monday gobe zata kasance garesu.


ganin shirun yayi yawa yasa me gidansa ya kai hannunsa ya dafa kafad'arsa "mr fu'ad lafiyarka kuwa tun d'azu kabar inata magana ni kad'ai?


firgigib fu'ad yayi ya dawo haicinyasa yana rike goshinsa saboda sarawar da yayi masa sannan ya sauke naunauyen ajiyar zuciya, sai dai yayi shiru ya k'asa furtawa me gidansa daidai da kalma daya, har zuwa sanda ya sake maimata abinda yace "idan kana da damuwa fu'ad ka fito kasanar min, ni din tamkar mahaifi ne agareka domin kmr d'an cikina na rikeka, dan haka maza ina sauraronka kasanar min damuwarka.


ahankali fu'ad ya cire hannunsa dake dafe da goshinsa ya tsura me gidansa ido kawai yana kallonsa ," hakika ya yarda dashi ,arayuwa zai iya boyewa kowa matsalar gidansa amman banda mutumin dake zaune gabansa domin yayi masa komai arayuwa, yayi masa abinda mutane dayawa suka kasa masa, ciki kuwa har da surikinsa uban matarsa .


tsawon minti goma fu'ad ya d'auka yana dubansa kafin daga baya ya bud'e bakinsa da kyar, yasoma korowa me gidansa bayanin abinda ke faruwa atsakaninsa da me'ad.


"no no what sort of nonsense is that?


"wace irin magana banza, maganar iska ce take gaya maka ,tana hauka ne?


"ko kuma a wani garin mahaukanta ta ta'ba ganin anyi irin haka?


fu'ad ya numfasha tare da ajiyar zuciya atare tace "dole kace hk sir abun nan ya dameni ya caza min k'walk'waluwa,gbdy narasa dawa zanyi maganar, gabadaya duk kwanakin nan dauriya kawai nake yi akan lamarin nan, matsalolinta sun fara damuna ina jin kmr na sauwake mata na hutawa rayuwata ne, domin zama da me'ad babu komai ciki facce tsagwaron bacin rai, nayi rarrashin nayi bala'in amman duk a banza ..


" ta yaya ma zatace kana nmj ka ajiye aikinka , dan kawai ka zauna gida tare da yarinyarta ,ni ai mace nasani da zaman gida ,har ma ta kula da gida da yaranta, ba wai nmj ba saboda ita ta haifi yarinyarta .


"sam wannan aikin mace ne kar ka sake kayi kuskuren amince mata, dan ubanta na da kudi, sai akace ta dinga nuna maka isa da iko, duk tsiyarka dai haka ta ganka ta nace lallai sai kai, dan haka karka kuskura ka amince da wannan tsarin , domin so take ta dinga juyaka yadda ranta ke so daga karshe ta meidaka mijin tace .


"ko tana tunani wawa ne kai, da take fadar irin wannan banzar maganar?


"zance da nake maka sir duk ta kaiwa kawayenta karata, akan wannan matsalar "every body knows about this matter ,she has tired several means that she knows ,but i have made her realzed that it's over my dead body .


gaskiyarka "we can't afford to throw a way our culture simple because of civilization ,inji cewar me gidansa. sai

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads