Showing 42001 words to 45000 words out of 163596 words
Chapter 15 - YANCNKI Book Complete by Aisha Bagudu.txt
bana jin kiyayyarki cikin raina sakamakon kyawawan halaiyenki ki cigaba abu ne mai kyau taimako da kyatatawa kmr hk.....
yana gama fadar hk ya juya zai wuce tayi saurin riko lauluasar tafin hannunsa cikin nata tana murzawa,ahankali"ina zaka fu'ad kabarni ?
"Dan Allah kagaya min kana sona ko akasin hk saboda ina son na karshen komai a tsakaninmu takarasa mgnr tana cigaba da Murza laulausan tafin hannunsa ."a zahirin GSKY bazan sani ba, ko zuciyata na sonki ko akasin hk amman zaki iya tmbyr ita zuciyarta duk amsar databaki zaki iya d'aukarta amatsayin kaddararki.
Ta narke masa fuska tmkr zatayi kuka alamun shagwaba "ni dai kace kana sona plx tafiya zanyi gobe zuwa Abuja takarasa fad'ar hk tana kai hannuta daidai saitin zuciyarsa dake wani irin harbawa "plz now say something to me "kace kana sona Dan Allah.
"Baza'a ce ba , yasanya d'ayan hannunsa ya zare hannunsa dake rike cikin nata, yakara gaba ya barta tsaye agurin , ita km tsurawa bayansa idanunta tana kallonsa har sanda ta daina ganinsa sannan ta juya ahankali zuwa inda tayi parking din motarta.
tana isa tun daga nesa ta hango safwan zaune akan motarta yana dubanta tare da yi mata kallon kasa da sama sannan yace "sweetie daga ina kike haka? Tayi masa banza ta isa jikin kofar tana kok'arin bud'ewa ya duro daga saman motar tare da riko hannunta ,a matukar fusace ta d'ago kyawawan idanunta ta. Zuba masa tana yi masa kallon kaskanci "cool down sweetie abinda nake son sanar dake akwai kuskure acikin abinda kika aikata a mintunonin da suka gabata, barin mota a irin wuraren nan Sam bai kamata akwai hatsari aciki,gashi kin bar motar dake tattare da sirrikan rayuwarki abud'e "saurin me kikeyi da har kika bar kofar motarki a bude?
Tayi kokari fixge hannunta cikin nasa Amman ta kasa saboda irin rikon da yayi mata bazata iya kwatar hannunta ba ,"karki wahalar min da kanki dan bazaki iya ba ,shiga mota kawai muje gida akwai mahiman bayanan, ko nace magana ta karshe dazamuyi dake ..
Qakarasa maganar yayi tare da bud'e mata kofar motar tashiga ya mayar ya rufe mata, shima ya zagaya ya shiga suka bar gurin, ascot da direbobinsa suka biyosu abaya .
Kai tsaye babban parlour'n gidan suka shiga, tayi tsaye nesa kad'an dashi ta rike kugunta tana cika tana batsewa, ta matsu bai fara maganarsa domin kawowa karshen zancesu ,saboda ita Sam bazata iya aurensa ba , sannan duk duniya a halin yanzu babu wanda zai takurata akan zancen aurenta dashi "kayi sauri kayi maganar sannan idan zakayita ka takaita saboda ina da abun yi ta qarasa mgnr tana furzar da iska ta bakinta "ki duba yanayina ,da yanayin shekaruna Wanda yaci ace zuwa wannan lokacin nasamu natsuwar ajiye iyali atare dani ,mead ina sonki son mai yawa, son da bansa lokacin daya shigeni ba ,amman dai yanzu ajiye wannan a gefe, a ina maganarmu ta kwana dake?
"ta kwana ne, a in da nace maka bana sonka,bazan iya aurenka ba ,ka nemi wata matar ka aura period ta fadi HK tare da runtse idanunta..
Shima runtse idanunsa yayi tare da cewa "Amman ke kad'ai ce a zuciyata ,shekara biyar kenan ina dakon sonki me'ad kuma har yau bansamu wata wacce naji ina sonta kwatankwacin naki ba, sai ke mead.
duk maganar dayake mata ahankali take fita kamar yana mata rad'a ita kuwa har lokacin , kasa bud'e idanunta tayi balle ta sake furta komai ko ta kalli kwayar idanun safwan wanda ke fitar da wani irin abu acikinsa mai kama da kibiyar so ......
jin ya qara yin kusa daita tare da riko laulausar tafin hannuwanta ahankali, shi yasa tayi saurin ja da baya daga tsayen datake.
"safwan idan saboda kyawuna ne I thought kaima kana da naka kyawun daidai gwargwado, sannan akwai yammata masu kyau wad'an da suka fini suke da duk abinda kake gani ajikina dakaji kake sona ka zabi daya daga cikinsu ka aura mana zakaji dadin rayuwarka dasu , zaka samu tattali fiyye da yadda kake tunanin samu a wajena, safwan ina son fu'ad fiyye da son kowa a duniya idan har ka fitar da iyayena "har ni me'ad kin fi son shi akaina yayi mgnr muryarsa na kmr zaiyi kuka?
"daman kai ni ban ta'ba kawowa zuciyata kai a matsayin mi....
yayi saurin janyota jikinsa ta fad'a cikin fad'ad'd'en k'irjinsa inda bai tsaya wata wata ba ya rungume tsam sbd yarigada ya fara rud'ewa daita, "karya kike me'ad bakya son shi ni kike so, shekara biyar din da muka d'auka tare, ban ta'ba jin kin ambaci sunan wani d'a nmj ba ,asalima sunana ne acikin bakinki meyasa kike son ki gujeni yanzu alhalin ina mutuwar sonki ......... ?"ki aureni zan mallaka miki komai nawa dana mallaka ke ko rayuwata kike so zan baki amman karki barni...
Tayi saurin janye jikinta tare da sake ja baya sosai tana fitar da numfashi sama sama sai alokacin ta lura babu mayafi ajikinta balle abinda takama gashinta dashi, ta bata fuska sosai tmkr zatayi kuka "me yasa ka cire min mayafi?ko kayi zaton nima kmr irin mutanenka ce ,to bari kaji na gaya maka nifa ba yar is...
"Me ya kawo wannan batu mead?su waye km mutanen nawa? Yayi tsoki yana dafe gefen kansa daya ji yana sara masa kad'an kad'an sannan yace "ki samu guri ki zauna muyi mgn, naji na janye zance aurenmu hk yayi miki?"kije ki gayawa shi wanda kike son din ya turo iyayensa kawai musha biki .
"da gaske!!! kake safwan ka janye batun aurena ?"sosai kuwa ai nafi bukatar farincikinki akan nawa.."sai me ?" Sai ga me'ad ta dawo kusa dashi ta zauna rike da hannuwansa "nagode nagode safwan Allah yabaka wace tafini "ai kibar wannan adduar me'ad saboda bazan ta'ba samun kmrki ba ,dubi surar jikinki fa meye baki dashi me'ad?
Take ta had'e rai "Ka d'auke idanunka ajikina ,ni dai na.......gode sosai, sannnan ina neman alfarma agurinka "uhmmmmm ina jinki ki roki komai kike so?
"ina son ka gayawa dady ka janye batun aurenmu sannan kayi masa zance fu'ad dan Allah idan kamin hk ka gamamin komai a duniya, kuma zan tabbatarwa kaina lallai kai mai sona ne da son farincikina.
"karki damu swe ...am kanwata an gama, ba sai hira ta barke tsakaninsu ba har inda take gaya masa zatayi tafiya zuwa abuja gobe, amman kwana biyu zatayi ta dawo Dan Allah tana son kafin ta dawo yayi mata kok'ari, har kusan la'asar suna tare makale da juna kmr tun farkon shakuwarsu, kafin shakuwar ta juye zuwa soyayyar da iyayensu suka karfafata, har farfajiyar gidan ta rakashi suna cigaba da tautaunawa da kanta ta isa ta bud'e masa mota yashiga ya zauna yana d'aga mata hannu tana daga masa har motacinsa suka fita daga harabar gidan , safwan ya bar gidan zuciyarsa na wani irin tsalle da zafi tmkr ana zuba masa ruwan dalma acikinta.
**********
ta bangaren sajida kuwa, tana cikin tashin hankali mara misaltuwa ,ganin yadda kullun kwanakin aurenta ke sake. matsowa ,gbdy ta rame tayi baki ta fita haiyacinta ,bata samun ishashen bacci akan mutumin da bai san da zamanta ba ,lamarin aikinta ma tattara shi ta ajiye agefe ,sai zaman d'aki da kuka, har ta kai ga kiran emran dake k'asar London yana aiki da BBC, tana kuka take gaya masa ita tafasa aurensa ba ,shima kukan ya fashe mata dashi yana tmbyrta dalili had'e da rarrashita tare da bata hakuri " idan narasaki sajida Zan iya rasa raina nima ,byn sun gama waya daita,ya kira acp yake gaya masa abinda ake ciki, acp yace" ya kwantar da hankalinsa tare da bashi tabbacin mutuwa ce kawai zata hana yiwuwar aurensu , tunda gashi ma lokaci ya kusa ,a daren acp bai runtsa ba sai daya dangana da d'akinta in da ya sketa kwance tana kuka "yayi mata kaca kaca sannan ya k'ara"matsawar kika butulcewa auren emran bani babu ke ,sai dai ki nemi wani uban Amman bani ba... wannan tashin hankali ke hanata sukuni da walwala tasha gwada kiran fu'ad, amman ko ya d'auka bata mgn ,sai dai ta saurari sautin muryarsa ta kashe, a ranta take aiyana ko ta auri emran zata kashe auren domin cikar burinta.
**********
Dare yayi nisa amman fu'ad ya kasa runtsawa ,shi yasan ya dad'e da tsintar kansa cikin shaukin soyayyarta, sai dai yasan rijiya ba gurin wasan yara bane, dan haka yasoma yaki da zuciyarsa, ta hanyar yakar sabbin kibiyoyin dake hud'a kowanne sako na cikinta. Sai dai duk iya kokarinsa a wannan daren baccin dayake bukatar samu ya gaza samunsa ,surar me'ad kawai yake gani cikin kyakkwan murmushinta ,Dan hk da yayi sallar asubahi ma ya dad'e zaune yana rokon Allah saukin al'amarin amman ina mead ediress takai ta kankane koina na zuciya da kwalkwaluwarsa ta karasa gangar jikinsa bata barshi da ko saqo daya da zai sanya tunanin kansa..
*********
Kmr yadda fuad bai samu runtsawa ba hk rayuka uku nan ,basu runtsa ba mead sajida safwan, safwan na kokarin ganin ya cire me'ad da lamarinta acikin rayuwarsa, ita km sajida tashin hankalinta yadda kullun me'ad take nacin son mallakarsa wannan takaicin ke hanata runtsawa . Yayinda me'ad abubuwa guda biyu ne suka hanata runtsawa da fari farincikin janyewar safwan da kuma tunanin yadda fu'ad zai fuskanci lamarinta, wanda kusan nashi tunanin ne ya hanata runtsawa, abinda tabasayi, shi mike domin yi wato sallar dare, allah yayita da dabi'u mabanbata Amman sai ya tsaida ita,da yawon son ibada acikin zuciyarta, duk iskancinta bata bari alokacin sallah ya wuceta ,wannan kuma Allah shi ya barwa kansa sani akan manufarsa gareta , alwala tayi domin gabatar da nafilfilinta data saba, tana nan zaune har sanda aka kira sallah sannan ta tashi ta gabatar, bata yi yunkuri komawa bacci ba tasoma shirinta, Dan hk washegari byn tayi sallama da iyayenta itace mutun ta farko data yiwa inna sallama a bakin kofarta , tazo ta bud'e ita kuma ta umarci direbanta daya kwaso kayan dake bayan boot din yashigo dashi sannan tasanya kanta cikin d'akin bakinta d'auke da sallama, Zuwansa gidan inna kenan yana kalaci.
Fu'ad ya d'ago kyawawan idanunsa yana kallonta kirjinsa na wani irin mahaukacin buga domin sam baiyi tunanin zai ganta adaidai wannan lokacin ba ,itama kallonsa cikin kwayar idanunsa take wad'anda atake ta gane kankancewar da sukayi gashi sunyi ja alamun rashin wadataccen bacci kmr nata, kada tayi haufi inji zuciyarta shima ya kwana cikin kwatankwacin irin situation din data kwana.
Inna ta shimfid'a mata sallaya, tace "bismillah ki zauna ki kasance tare damu tasoma kok'arin zama idanunta na cikin mayatattun sexy eyes dinsa "tace anya kuwa inna ayi hk?"akan hanyar aiport nake .
"Duk da hk dai yar nan wannan sammakon da kikayi bai isa ace kin sanyawa cikinki abinci ba sai dai idan kalar namu abinci ne bai miki ba...
Tace"wallahi ba hk bane inna ,babu yadda mom dina batayi ba ,Dan na tsaya naci amman idan wannan jikan naki yayi min izini sai in ci ko acikin nasa ne.
Fu'ad ya ajiye kofin shayinsa dayake kur'ba ahankali ahankali ,idanunsa acikin nata yace "idan ni ne sai dai ince kada Allah yasa kici, me'ad da inna suka tsurawa bakinsa ido "kina kallona inna wace bataji mgnr mahaifiyarta ba, Dan me zataji tawa?
Tayi ajiyar zuciya tana mai nunasa da d'anyatsa hannunta" kai ko sannan tayi kasa da murya wanda shi kad'ai zai iya fahimtar abinda zatace "hidimomin tunaninka ne fa ya hana tsayawa na karya .
ya murmusa gently abinda bata ta'ba gani ba kenan a fuskarsa, shiru tayi tacigaba da kallonsa.
inna tace "manta dashi ki zauna kuci tare bari na qaro muku "a,a inna kibarshi kawai Dan banajin yunwa , ga sako can an shigo dashi karki ce bazaki amsa ba dan Allah inna ni dai fatana kin sanya min albarka "fu'ad ya runtse idanunsa Dan dadi yaji dadin abinda tayi amman bazai bari wannan kyautar shiga tsakaninsu ba ,ahankali ya bud'e idanunsa yasanya cikin kwayar idanunta sannan yakira sunanta"me'ad ..
wannan shine karo na farko da hkn yafaru taji sautin sunanta abakinsa wani irin abu taji yana yawo acikin jikinta. Dama kwalkwaluwarta gbdy ta amsa da "na'am fu'ad "ki koma da abinda kikazo dashi mun gode kwarai da kulawa....
tayi kicin kicin da ranta sannan tace "ina ruwanka da abinda na kawo?"inna na kawowa ba kai ba balle kace hk ta waiga gurin inna "inna ni zanyi tafiya zuwa abuja ki min addua sannan ki sanya min albarka, kai kuma sai kaji wayata ta mike tsaye inna na kwararo mata addua sukayi sallama.
Can dare har ya kwanta wayarsa ta d'auki kara yasan babu wanda zai kirashi a daidai wannan lokacin sai ita, ya mika hannu ya d'auka zuciyarsa na beating ya manna a kunnensa a kasalance yace baki kwanta ba ?
Tace "na kasa bacci ne ,na sauka lfy Amman tunani na neman mayar dani mara lafiyar karfi dayaji.
Ya rage muryarsa saboda kada ya tashi su kabeer yace " ke kuwa tunanin me kike hk me'ad?
"Kai tsaye tace "tunaninka?
Yayi ajiyar zuciya mai sanyi cikin ransa yace "nima hk tunaninki ya hanani walwala da runtsawa ,bai san cewa a fili ya fad'a ba ita kuwa kunnuwanta sun rigada sun zuko mata sautinsa, tayi murmushin jin dadi wanda ya fidda sauti, cikin ranta km godiya tayiwa Allah daya takaita mata wahala da rashin tabbas din datake hangowa alamarinsa.
Daga nan sai me? Sai hira ta 'barke tsakaninsu kmr ba fu'ad ba shi kansa har mamakin kansa ya shigayi ta yadda cikin kankanin lokacin me'ad ta tankwasa zuciyarsa ta sauya mata akidar tunaninsa, na bazai saurari kowace mace ba har sai byn ya samu aiki, tare da daidaita a rayuwarsa sannan zai bud'e shafin soyayya.
Amman gashi a wannan daren ya kulla soyayya mai karfi mai ban mamaki da me'ad takai wanda bai ta'ba tsintar kansa ciki ba.
Tun daga ranar kullun sai sun raba dare suna wayar soyayya, har tabaro abuja, yanzu ne me'ad tasan tana cikin shaukin soyayya, ba soyayyar kuruciya ba da'ake son tursasa zuciyarta ciki . wasu emotion ke tangaliliya da rayuwarta da zuciyarta akan fu'ad dake aiki cikin zuciya da kwalkwaluwarta. bata 'bata lokaci ba gurin sanarwa da aminiyarta sajida ba ,wanda wannan sakon yayi gigita ya haukatata har yayi nasarar kwantar daita a gadon asibitin ..
Mmn sudais ce
[11/3, 8:27 AM] El~hajj: ππππππ
'YAN CINKI
ππππ
ππππππ
~NA~
*AYSHA A BAGUDO*
~DEDICATED TO~
MRS ADAM
( YAR MUTAN KAGARA)
Page 55 to 56
.......bata san inda hankalinta yake ba, sai farkawa tayi ta ganta a gadon asibiti ,ta fahimci hakan ne ta hanyar ganin wata nurse a tsaye akanta, dan tana bud'e ido daita tasoma cin karo tana kokarin sanya mata k'arin ruwa.
tayi saurin mikewa zaune tana raba idanu tare da tuna abinda me'ad takirata a waya ta sanar mata wanda shine abinda ya haddasa mata zuwa asibiti , me'ad wace dawowarta kenan daga tafiyar datayi zaune take abayanta tana mata sannu , jikinta a matukar sanyaye, sai dai kallo daya sajida tayi mata abinda ta gaya mata ya sake dawowa cikin 'kwa'kwalwarta da gangar jikinta, idanunta gbdy sun rikid'e sun dawo kamar gauta al'amar taci kuka tagaji dan har lokacin hawaye ke bin kuncinta,tana jin tmkr ranta ake zara gbdy takaicin me'ad take ,a halin yanzu bata jin akwai halitar data tsana sama da emran daya nacewa aurenta sai km me'ad datayi wa rayuwarta karan tsaye ,tana matukar son fu'ad kmr tayi hauka aganinta ita tafi cancanta yaso ba me'ad,saboda tafi tsananin son shi da buk'atarsa .
"Me yasa so yayi mata yanka kauna irin hk?"me yasa idanunta suka had'u dashi? "Ina ma batayi mata rakiya ba a wannan ranar, ranar datayi silar dagulewar duk wani lisafin rayuwarta.....takarasa zance zuci tana sake fasa wani irin gigitaccen kuka tare da fizge hannunta daga rikon da nurse tayi mata,sannan ta bar jikin me'ad ta kakkame misna tana wani irin kuka "shikenan narasa shi ko misna ?
Ta furta hkn a bayyane ta sake tafiya luuuuuuu sai gashi ta kifa k'asa daga misna da me'ad har nurse din sun gigice har aka rasa wanda zai yi wani abu akai.
me'ad ta durkushe bisa gwiwowinta tana jijigata cike da matsanancin tashin hankalin ,da kiran sunanta cikin k'araji, yayinda kukan datake ta rikewa tun d'azu ya kwace mata, ita kuwa nurse da gudu ta fice daga d'akin dan kiran likita atare suka dawo wannan karon har da dady da acp da hjy Khadija mahaifiyar me'ad suka biyo bayansa.
likita ya d'agata da taimakon su dady suka maidata kan gadon yayyafa mata ruwa sukayi, sai kuwa ta bud'e idanunta tare da sakin wata ajiyar zuciya da karfi ,idanuta ya d'auro akan mahaifinta da iyayen me'ad "Allah sarki uwa mai dadi,ina ma tata uwar na raye da wata killa tazamo sanyi idaniyya mai share mata hawaye, acikin wannan halin datake ciki.
kallon mahaifinta take tana kuka sosai a zuciyarta ta sake furta "shikenan narasa shi ko?
gbdy suka k'araso gareta cikin tashin hankali saboda jin furucinta a she a filli tayi mgnr batasani ba "waye shi din wanda kika rashi?
me'ad da momy suka rungumeta suna gunji kuka cikin kuka momy tace "sajida waye shi ki gaya mana ko waye shi da kike ikirarin kin rasashi, "a tunaninmu emran kike so kuma yana raye bai mutu ba, asalima yanzu muka gama waya dashi.
Girgiza kai tasoma yi tana fidda numfashi sama sama "bashi ba..bashi nake nufi ba ni kad'ai nasan kowaye ,wanda nake nufi yana raye sai dai narasashi.....
".ki gaya mana kowaye shi zamu