Header Ads
Showing 93001 words to 96000 words out of 163596 words

Chapter 32 - YANCNKI Book Complete by Aisha Bagudu.txt

Ads the beginning of article before Image

02 Jun 2024

1315

Ads at the middle of Article

good news, ki godewa Allah watakila najma kawai zan aura saboda mahaifin sajida yaki amincewa da batun auren ..tunda yasoma mgnr take kuka har yayi shiru,tana zaune ta dawo tmkr mutun mutumi ,jinta na neman d'aukewa ,Allah sarki a she hk rayuwa zata zo mata?
Ganin hankalinta na neman gushewa yasa ya matsota ya kamo hannuwanta duka cikin nasa yasoma massaging dinsu yana kallon cikin kwayar idanunta dake tsiyayar hawaye, Yasan tana mugu mugun son shi ,sannan yana da tabbacin duk duniya babu macen dazata so shi fiyye daita ..ahankali ya janyota jikinsa yana k'ok'arin rungumeta ,ta kasa saida shi saboda zuwa lokacin gbdy jikinta bai da laka kallonsa kawai kmr wata ta'ba'bbiya ,tsawon lokaci suna manne da juna batare da suncewa juna k'ala ba ,kusan a mota suka kwana makale da juna, sai dai mead bata runtsa ba kwance kawai take ajikinsa numfashi kawai take iya fitarwa shima Dan tasan dole ya fito tunda akwai rai ajikinta.


******
Washegari babu laifi nasreen tasamu natsuwar zuciya, daman firgici da tsoro ne ya haifar mata da suman datayi , sai dai fad'uwar datayi kasa yasa hannunta na hagu ya D'an bugu, har gurin ya kunbura abinka da sickle cell k'ashinsu bashi da kwari, koman yaya suka ji ciwo yanzu gurin zai kunbura. suna zaune tare daita kowanensu na rike da hannunta daya ,suna k'ok'arin bata kulawa doctor yashigo dubata yanayin jikinta, sosai ya ji dadin yadda ya isketa atsakiyarsu me'ad na bata apple abaki sannan tayi mata hira, irin sanya farinciki.
Tashi sukayi atare suka tsaya ajikin bango, batare da sun kalli junansu ba,doctor yashiga aikin duba jikin nasreen yana mata wasa.


Kwana nasreen biyu a hospital doctor yabasu sallama, lokacin fu'ad bai nan yana can tare da me gidansa, kai tsaye me'ad hanyar gidansu ta dauka da nasreen, Dan bata jin zata koma gidansu da sunan cigaba da rayuwa fu'ad, zuciyarta cike da bakinciki, wai shin me zatawa sajida da najma arayuwa ta huce?
Kodayake bata jin najma, tafi jin sajida Dan a yanzu ta sauya shawarar akanta ,Dan har in takashe sajida, bata more rayuwa ba ,tunda bata zauna a duniyar ba balle taga bakinciki, yanzu tafi yarda da shawarar zuciyarta wanda babu tantama abinda zata mata har ta mutu sajida bazata ta'ba mantawa daita ba,gaba idan ance ta kalli mijin wata tace tana so ,ko taci amanar wanda ya Aminta daita bazatayi ba ,murmushin mugunta tayi adaidai lokacin da ta iso bakin get din gidansu inda tashiga matsa hon, madu gadi na ganin motarta ce suka hau k'ok'arin bud'ewa cikin rawar jiki, tasanya hancin motarta tana hura hanci, tayi parking a inda aka tanada domin ajiye motoci sannan ta fito har lokacin fuskarta a murtuke take, ta dubi nasreen dake zaune tana kallonta, dan ita a tunanita gidansu suka nufa sai kuma taga momy'nta tayo gidan kakaninta dasu, me'ad ta Dan saki fuskarta kana tace "bby fito muje ...


*"Uhmmm to ga dai me'ad an kwaso jiki an dawo gida uba...ko yaya zatak'aya da mahaifinta ?" ko kuwa ta manta furucinsa akanta ne?*


Mmn sudais ce
[11/3, 8:29 AM] El~hajj: 💗💗💗💗💗💗
'YAN CINKI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗


~NA~


*AYSHA A BAGUDO*


~DEDICATED TO~
FAIZA HAMMADU BARAU
(YAR NUMAN)


Page 77


......nasreen taji abinda momy'ta ta fad'a sarai amman taki motsawa daga inda take zaune, illa idanun data tsurawa momy'nta tana kallonta cike da tambayoyi.
ahankali Me'ad ta zagayo inda take zaune tana kallonta "bby let's go now tana me kamo tafin hannunta ta fito daita daga cikin motar, sa'an nan ta meida murfin motar ta rufe, tasoma tafiya rike da hannun ta.
yayinda ma'aikatan gidan suka shiga gaisheta cike da girmamawa, hannunta kawai ta iya d'aga musu tacigaba da tafiyarta batare da juyowa ba,
Momy tana zaune a parlour'n tana waya Me'ad tasanyo kai cikin parlour'n a matukar birkice bakinta d'auke da sallama, momy na ganinta tayi saurin katse kiran saboda yanayin data ganta ,wujiga wujiga tamkar wace tayi shekara tana jinya.
"me'ad lafiya kuwa naganki haka kmr wacce ta tashi a jinya?
"ko kuma kunyi Abind kuka saba ne da mijinki kika kwaso jiki zuwa gida?
momy tajirowa me'ad wannan tambyar Tana dubanta a matukar tsorace me'ad tasamu guri ta zauna a gefen kujerar da momy ke zaune batare da tace mata komai ba, illa wani tashin hankali data tsinci kanta ciki.
NASREEN ta isa gurin momy tashige jikinta tana gaisheta ,momy ta rungumeta ajikinta tsam kana tace "ykk nasreen?
"yana ji jikin naki da zafi ko bakida lfy ne?
Naunayen ajiyar zuciya me'ad ta sauke kana tace "fitowarmu kenan daga hospital yau kwananmu uku NASREEN babu lafiya Tak'arasa mgnr muryarta na rawa kmr zatayi kuka.
momy tayi Shiru tana kare mata kallo had'e da nazarin yarinyarta, a kallon da take mata ta fuskaci tana cikin matsananci damuwa da tashin hankali, yayinda ita kuma me'ad din tashiga share hawaye wasu na gangaro mata...


"To meye kuma abun kuka ?
" ko ciwon ne yayi tsanani?
Me'ad ta girgiza mata kanta wasu sabbin hawaye na sake gangarowa bisa kuncinta.
" meke damunki me'ad dan banji dadin ganin yanayinki ba ? " sannan meye damuwarki ahalin yanzu da kike zubda hawaye ko duk akan matsalar ciwon NASREEN ne?
ta sake girgiza kai kawai tana share hawaye, momy ta fuskanceta sosai hankalinta a matukar tashe "ke me'ad ki bud'e idanunki ,ki saka cikin nawa ni mahaifiyarki ce da duk duniya baki da kmr ni kuma nice nazama dole nasan damuwarki da abinda ya kawoki gida adaidai wannan lokacin daya kamata ace kina gurin aiki ne ko gidan aurenki "ki sanar dani damuwarki da abinda ke damunki domin Nasan mataki d'auka..


me'ad ta kalli momy fuskarta cike da tsantsar damuwa da tashin hankali still hawaye na tsiyaya daga cikin idanunta tace "momy ina cikin babbar matsala ,ina cikin damuwa da tashin hankali, momy na cuci kaina da kaina na yaudari kaina,na zalinci kaina, na jawo kaina maseefar datafi karfina.... Momy nayi aure batare da farincikinku ba ,most especial dady, banyi muku biyayya akan aurena da fu'ad ba , gashi ayau an wayo gari komai na neman ta'bar'bare min, narasa gane komai nawa ,rayuwa na neman juya min baya ,
"ahalin yanzu na dawo gida ne saboda bana jin zan iya cigaba da rayuwar aure da fu'ad .......
jin wannan maganar yasa jikin momy yayi sanyi ta gyara zamanta tana duban me'ad cike da matsanancin tashin hankali, sannan tace "amman meye dalilinki na fad'ar duk wad'an nan maganganun hk ?
"abinda akayi shi tsawon shekarun goma sha meye na dawo shi ahalin yanzu?
"sannan meye dalilinki na cewar bazaki sake rayuwar aure da fu'ad ba wani mummunar abun yayi miki ? Momy ta tambayeta jikinta na wani irin rawa haka zalika gabanta na fad'uwa ..


me'ad ta kalli momy ganin damuwa kwance akan fuskarta ,yasa wani irin tausayin mahaifiyarta ya saukar mata, ta sauke naunauyen ajiyar zuciya sannan ta kwashe duk abinda ya faru ta gayawa momy.


momy tayi wata irin zabura daga zaunen datake rungume da nasreen ta mike tsaye kana ta zaunar da nasreen jikinta na d'aukar kyarma , dan maganar ta bugi zuciyarta matukar , ahankali tasoma kai kawo acikin parlour'n, lokaci guda kuma ta koma ta zauna ta kalli me'ad tace" yanzu ina najma take sannan a wani hali Sajid take ciki?
"momy nagaya miki na barsu agidan ,dan tunda abun nan ya faru ban sake taka kafata cikin gidan ba ,kinga sai suji dadin yin aurensu da tushe .
"shikena me'ad to yanzu meye abun yi?
me'ad tayi murmushi me tattare da takaici abinda sajida tayi mata ,sannan tace "momy kada ki damu ni nasan yadda zanyi da Sajida ,wallahi Momy sai tayi datasani tunanin auren fu'ad arayu....


"datasani uwar me zatayi tunda ke bakiyi dakinsani ba a aurensa da kikayi ? Wannan Sautin muryar ta katse mata hanzari ,ko ba'a gaya mata ba tasan sautin muryar mahaifinta ne yashigo parlour'n ,atare suka jiyo daga ita har momy suna mamaki jin Furucinsa.
Ahankali ya tako har zuwa inda suke yana tafi da hannunwansa Duka cike da tsansar jin dadin ganinta cikin damuwa da tashin hankali"ku daina mamakin jin abinda na fad'a "arayuwa kowa abinda yake so yake da burin mallaka, "kmr yadda kikayi tsayin daka kikace duk duniya babu wanda yayi miki sai d'an talaka dagin matsiyata, itama hkn ce zata kasance daita Dan hk banga abun tada jijiyoyin wuya ba .....


"Me'ad.... !!! dady Ya kira sunanta har sau uku in a serious thought wanda yasa kirjinta bugawa da sauri batare da tasan da hakan ba, "na'am dady ta amsa masa wasu hawayen na ciccikowa a idanunta sannan tasanya kwayar idanunta cikin nasa zuciyarta na sake lugud'en bugu da karfi saboda fargaban jin abinda zai sake fad'a.
" yanzu dai me kika zo yi gidana ?
"hope ba kashe aurenki kikayi ba akan mijinki zai aure aminyarki da yar aikinki?


"idan kashe aurenki kikayi ko yaji maza maza ki tashi ki bar min gidana, dan babu masaukinki acikinsa.
" idan kina tunanin zaki kashe aurenki ne ki dawo gidana ki zauna kiyi saurin canza tunani ,dan idan kin kashe aurenki har abada bazaki zauna tare dani ba. "idan kin manta sharrud'ana akanki bari in tuna miki .
" yaji ,mutuwar aure alkahari kowani iri ne damuwar rayuwa ,yasameki bazaki tunkaro hanyar gidana ba," kikace kinji kin gani kin yarda kin amince , kika zabi auren d'an matsayata akan mu iyayenki da mukayi silar zuwanki duniya.
"daman kuma wannan ranar nake zaman jira zuwanta wanda nasan komai daren dadewa zata zo gashi tazo kuma na godewa Allah datazo ina raye cikin koshin ..
" dan haka tun wuri ina shawartarki ki tashi ki koma gidanki, idan ba sakinki yayi ba, idan kuma ya sakeki ne sai kin nemi gurin zama amman ba'a gidana ba.


"haba dady wace irin mgn ce haka ? "da me kake son taji?
"Ina ruwana da abinda zataji, nace ina ruwana lokacin danake rokonta ta auri safwan me tayi min?"in ce komai ya faru ne akan idanunki ?
"kamata yayi ka duba lamarin da rabon dake tsakaninsu , idan basu auri junansu ba ,ta yaya kake tunanin za'a samun rabon NASREEN ?


"NASREEN din banza ina ruwana da wata nasreen?
"kuma wallahi bari kiji ingaya miki ni nan me d'aurawa mijinki aure ne da sajida matsawa tana son shi da gaske shima kuma yana sonta , ke koni sajida tace tana so zan aurenta balle wani mijinki din banza da wofi ,oya zo ki bar min gidana kije ki rungumi matsalarki ,ki bar rayuwarmu, dan tuni na manta da na haifeki arayuwata ,a halin yanzu diya daya gareni itace suhailat yar albarka yarinyar kirki kuma InshaAllahu zatayi albarka saboda tana min abinda nake .....
cikin kidima da tashin hankali me'ad ta durkushewa agaban mahaifinta tana wani irin kuka "dan girman allah dady kayi hakuri ka yafemin , na yarda nayi kuskure arayuwata,Amman na tuba dady karka min haka ,karka juya min baya, banida wad'anda suka fiku ,ka yafemin nasan hakinka ne ke bibiyata ya fixge karfarsa daga rikon datayi masa.


"baki ga komai ba tukun me'ad sai ranar da kikaji na d'aura auren sajida da mijinki ,kijira abinda zai biyo baya sai fu'ad ya zame miki annoba arayuwarki sai ya tarwatsa rayuwarki da farincikinki ,ke hatta wannan aikin da ni nasan wahalar dana sha kafin ki sameshi da har kike tinkaho da dashi, wallahil azim matsawr ina da haki akanki shima sai yabar hannunki kmr yadda Fu'ad ke shirin barin hannunki ......
"ki tashi ki bar min gidana ya k'arasa mgnr cike da hargagin 'bacin rai ...
Kuka me'ad take sosai tana Jan gwiwowinta tana bashi hakuri ,momy ma ta durkusa agabansa tashiga bashi hkr. "kayi hakuri Dan girman Allah kabarta ta zauna tare damu ,yanzu ina kake tunani zata ga yarinyar mara lfy atare daita ?
"khadaji ....dady yakira sunanta a zafafe "na'am dady. Ta amsa masa jikinta na rawa.
"a iya tsawon arayuwamu, mun ta'ba samun wata matsala dake ?
momy tayi saurin girgiza kanta tana jujuya hannuwanta alamun dai yayi hakuri .
"to karki bari musamu matsala akan wannan yar isakar yarinyar mara jin magana .
"gidan nan ma tukun naki ne ko nawa ?
Momy tayi saurin girgiza masa kai tare da cewar "naka ne.
"to nagodewa Allah daya kasance nawa ne ba naki ba, kuma lokacin dana tashi gidansa baki sanya sisin kwabonki ciki ba ,Dan haka bana bukatar ganin me'ad cikinsa taje can gurin wad'anda take tunani sun fini daraja agurinta, sannan ya fuskanci me'ad sosai yana huci "minti biyu kacal nabaki ,ki d'auki yarinyarki kibar min gidana bana bukatarku cikinsa, hakuri tashiga bashi amman sam yace bai san da zance wani hakuri ba sai ta bar masa gidansa .


Ta mike ta tashi tsaye jikinta na rawa ta janyo hannun NASREEN ta rike cikin nata gam kmr wace za'a kwacewa ita, tasoma tafiya tana kuka ,momy na kuka , hatta NASREEN kuka take sosai tana tausayawa momy'nta "yanzu saboda ta auri dady'nta yasa babanta yayi mata wannan wulakanci, daman grandpa dinta bayason auren iyayenta ?
Hakuri take son bashi Amman tashin hankali datake hangowa tattare da momy'nta da ita kanta yasanya ta kasa magana sai kukan datake har da shesheka.


Jikin momy na 'bari tabiyo bayan me'ad tana kuka tana kiran sunanta....shi kuwa dady ko ajikinsa, Sam bai ji wani abuba dangane da halin da ta tsinci kanta ba.
me'ad ta tsaya tare da cewa " momy ki daina kuka ki koma kawai duk abinda ya faru dani ,ni na jawowa kaina na zabi d'a namiji akan mahaifina ,na fifita soyayyar fu'ad akan ta mahaifina, yau wa gari ya waya?
""yanzu ina zaki?
"duk inda Allah yayi momy zan tafi na bar rayuwar kowa, zanje nayi sabuwar rayuwa tare da diyata, zan rungumi kaddarata....
"amman ki rokon min dady yayi hakuri ya yafe min abinda nayi masa wallahi nayi danasani arayuwata, ki min addua momy ko zan daina jin rad'ad'in da zuciyata ke min ... ta juya tacigaba da tafiya har ta isa jikin motarta tashiga ta tayar , ta fito daga cikin gidansu tana wani irin kuka.


Gudu kawai take shararawa akan titi, duk hanyar data gani ,bi take saboda bata San inda zata ba ,banda bugawa bubu abinda zuciyarta keyi, kuka take sosai tana dukan sitiyari motar "me yasa nayiwa mahaifina abinda nayi masa akan soyayyar fu'ad ta furta a fili?
" me yasa ban bi zabinsa ba nace lallai sai fu'ad zan aura gashi komai na neman birkice min ?
Ta sake fashewa da wani sabon kukan ,hakika na cuci kaina, iyaye duk lallacewarsu sun wuce wulakanci ,ballanatana irin nawa iyayen da samun irinsu ke da wuya, dady uba ne har da rabi ,wanda ke maye gurbin uwa idan tana raye ko amace .
"sun haifi ne sun min gata ,mahaifina ya inganta rayuwata sosai yabani abinda duk wani d'an Adam zaiyi tinkaho dashi arayuwar duniya ,bai rageni da komai ba a tun tasowata ,komai nace shi za'ayi .
",me yasa nayi masa abinda nayi masa?
" me yasa banyi masa biyayya ba alokacin dayace na auri safwan? " why why why !!! Me'ad meyasa nayi abinda nayi ?
"Wayyohlly Allah na cutar da kaina, Kuka take sosai Sam ta manta da nasreen dake zaune agefenta sai da taji yarinyar ta riko hannunta a matukar afirgice tare da sakin razananniyar k'ara sannan taja birki da karfi ta tsaya cak tana Jan ajiye zuciya, hawaye sha'be sha'be kwance Akan fuskarta, itama nasreen din kukan take sosai har lokacin da shesheka ,tana jin tausayin dady'ntan sosai fiyye da mahaifiyarta , Amman ayau tausayin momy'nta ne ya rinjayi nashi har batasan a mizanin dazata ajiye hkn ba, rungumeta me'ad tayi ajikinta tana kuka "am sorry bby gudun danake ya tsorotaki ko.. ?
Nasreen ta d'aga mata kanta al'amun Eh tana kuka.
"am sorry na daina bazan sake ba kinji bbynah, ta d'aura idanunta akan agogon fatan dake d'aure da tsinyayar hannunta , lokacin shan maganin nasreen din yayi ,Dan HK ta kai hannuta sit din baya ta d'auko ledar maganinta da ruwa ta balla ta bata ta sha sannan ta mai daita ta kwanta akan kujera, itama ta meida bayanta akan kujerar datake zaune akai, byn tayi baya kad'an daita, ta runtse idanunta still hawayen idanunta suki tsayuwa har lokacin nadama ce fal cike da zuciyarta.


Kusan minti talatin tana gurin tana zance zuci wayarta ta d'auki k'ara sauti me dadi da ta'ba zuciyar Wanda ya saurara,ko bata duba wayar ba, tasan ko waye me kiranta, sakamakon sautin dataji "fu'ad dinta ne ,dan shi kad'ai tasanya wannan sautin saboda matsayinsa gareta ," mutumin data sadaukar da rayuwarta da komai nata akansa, mutumin da shine silar 'batawarta da mahaifinta,a yau tayi datasanin a had'uwarta dashi a wancen lokacin" duk duniya tasani kowa yasani babu halittar da mahaifinta ke so sama daita Amman an wayi gari sanadin had'uwarta da fu'ad komai ya canza, soyayyarta ta juye zuwa kiyayyar da batasan ranar gushewarta ba..
Wani kukan ne ya kufce mata tasanya duk hannuwanta ta toshe bakinta ,"tarasa fu'ad rashi na har abada, sannan tarasa soyayyar mahaifinta, ga aikinta datake ganin shine gatanta da rufin asirinta shima tana nema rasashi adalilin takasa samun natsuwar zuciyar gabatarwa.
akalla bazata tuna karshen shigarta office dinta da sunan yin aiki ba, gashi tun rashin lfyr nasreen bata taka kafafunta zuwa cikin ma'aikatar ba, ko kiran chairman bata samu damar yi ba ,batasan me zai biyo

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads