Showing 48001 words to 51000 words out of 163596 words
Chapter 17 - YANCNKI Book Complete by Aisha Bagudu.txt
mai gidanta, in sha jinita sannan nayi maganin abinda ke damun kwalkwaluwarta. Take yaron ya isa inda sajida take ya kama hannunta da karfi ya fixgota xuwa jikinsa, tayi waya siririyar kara tare da kiran sunan emran da mahaifinta cikin tsananin tsoro da razana.
Emran yayi saurin d'agowa ya dubi ogan zuciyarsa na beating yace "Dan Allah oga kayi hakuri wallahi duk abinda kake so zan baku in dai zaku kyalemin mata amarya ce ka duba girman aure.
Ogan yayi dryr mugunta yace "kada ka damu abokina zan koyar daita komai sannan zai koya mata hankali da ilimin rayuwar duniya ba cutar daita zaiyi ba, idan kuma ka sake mgn abakin ranka ya afka d'akin daaka shigar daita,shi kuwa emran bai sake cewa komai ba yana jiyo ihun sajida tana kwalla ihu da gudu ya tashi ya nufi hanyar d'akin yana kiran sunanta Amman Kan ya karasa wani ya daki kansa da tsinin bunduga anan ya zube kasa a sume bai sake jin komai ba, sai farkawa yayi ya gansa kwance a d'akin ummansa su km kannensa sun zagayeshi ya dubi umma yaga fuskarta tana cikin damuwa ya sauke ganinsa Kan wasila kanwarsa yace "wasila sun kashe min sajidata ko?
Sun kashe min yar amana," amanarta mahaifinta yabani, sun kashe min ita ko?
Wasila ta girgiza kai tace "kayi hkr yaya basu kashe kowa ba sai dai sunyiwa sajida fyade , wata irin zabura yayi ya mike tsaye cikin takaici, tabbas sajida ta cucesa wata daya da yin aure Amman bata ta'ba zuwa dakinsa ba kullun akwai wulakanci datake masa daban daban akan hakinsa tace"bai isa ya kusanceta, yau gashi wani katon banza wanda bashi da imani yazo har gida kuma har cikin dakin aurenta ya keta mata alfarmar aure, tabbas hakkinsane ya kamata tun baaje koina ba.
Ya dawo da kallonsa wajen ummansa yace "umman yanzu tana ina?
Umma ta d'auke kanta daga kallonsa tace"ina zata? "Tana dakinta mana ,wannan mugun halin nata da kunya bazai barta ta zauna cikin mutane ba .
Emran bai ce komai ba ya mike cikin sanyin jiki tana can kuryar gado ta had'a kai da gwiwa tana kukan nadama da cutar kanta datayi bisa rashin kunya wanda ba halinta bane a da.
Ya tsaya abakin gadon ya tura hannuwansa duka biyu cikin aljihun wandosa "ina ganin bamu ya kamata ki zauna kinawa kuka ba, kamata yayi ki bisu kiyi musu kuka ina tunani hk ne zaifi ,tunda su suka miki laifi ba mu ba, in km baxaki gane inda suke ba ya zame miki tilas kiyi hakuri Dan ba zai yiwu ki cika mana kunne ba.
Sajida tayi saurin kallo emran cikin mamaki ,cikin sanyayyiyar murya daya santa dashi tun farko haduwarsu tace "amman emran ai ya kamata..
"Yi min shiru muguwa in mugunta ce ai kanki kikayiwa bamu ba, Dan hk tun kan dare yayi miki ki nemi wanda yayi miki fyade kiyi masa wannan banzar kukan naki bani ba ,yakarasa mgnr yana saukar da numfashi zai yi mgn sai km ya fasa ya juya ya fita cikin bakincikinta.
Sajida ta km fashewa da wani kuka yanzu ya zatayi kenan ? Tarasa fu'ad tarasa emran tarasa budurcinta tyi biyu babu.....
**********
Kwana goma kenan sajida bata saka emran acikin idanunta ba ,kai ita kan tana cikin taskon rayuwa duk batagane abinda yake nufi da hkn da yayi mata ba ,ta mike jiki a sanyaye ta nufo hanyar parlour'n inda tasame shi zaune yayi tagumi itama ta nemi kujera kusa dashi ta zauna tana kallonsa kafin daga baya tayi ajiyar zuciya da numfashi atare sannan tace" emran ina son kasakeni....gabansa yayi wani irin bugawa saboda har ga Allah yana sonta ransa a matukar bace yake daita shiyasa ya shareta, amman ji mgnr banzar datake gaya masa,wani kallon wulakanci yayi mata sannan a matukar hassale yace"ai kin san yadda ake yin sake, ki dauko takarda da biyo kiga yadda bazan sakeba, aikin banza kawai yakarasa mgnr yana furzar da iska ta bakinsa.
tsam ta mike ta shiga dakinta ta fito hannunta rike da fallen takarda da biro tazo ta mika masa gashi" ka sauwake min yanzu na bar maka gidanka dan konace zan cigaba da zama da kai ba daraja zanyi ba ,batare da bata lokaci ba ya amsa yasoma rubuta mata yana cewa "idan akwai gaba da gidana kije me ya dameni..
Cikin minti biyu yace "gashi ya miko mata takardarta "na sakeke saki biyu yana gama fadar hk ya mike ya bar parlour'n yana goge zafafan hawayen da suka zowa kuncinsa ,wannan shine karo na uku daya zubar da hawaye akanta Dan tunda yake baitaba jin bacin rai kmr na yau ba yadda ta nuna kiri Kiri bata son zama dashi ,alhalin shiya kamata ya gujeta gashi har yanxu zuciyarsa na tsananin sonta yana fita harabar gidan yakira mahaifinta ya sheida masa daga ya kashe wayarsa da zumar barin kasar a gobe goben nan.
"dady yasoma tsarguwa aKan rashin zuwa safwan gidansa, alhalin yana kasar , amman kiran Gaugauwan da mahaifin sajida yayi masa ya hanashi nemansa a wannan lokacin, yana fitowa mead na fitowa agigice saboda labarin mutuwar auren sajida yasameta atare sukaje, koda ya isa tarin bakinciki ya iske,domin yana xuwa acp ya mika masa farar takarda da sajida ta bashi, yana masa karin bayani "bansan abinda yarinyar take nufi dani ba?
"ta kashe aurenta batare da wani mahimmin dalili ba ," yanzu emran din ya kirani yake gaya min abinda ya faru sam banga laifinsa ba sai na wannan yar iskar yarinyar, ya dubi gefen inda take rukube yace "ba dai zaman gidan kike bukata ba gaki ga gidan ina tabbatar miki har ki kare rayuwaeki bazaki taba samun miji irin emran ba, tunda dady ya rike takadar yake zabga kalmar inna lillahi wa inna ilaihi rajiun "amman sajida baki kyautawa rayuwarki ba ke yanzu a tunaninki zaki samu kmr emran? ita dai kuka kawai take har da shesheka "dady ka rokon mun babana ya yafe min dan Allah nasan fushinsa atare dani babbar matsala ce "kinsa da hk kika ki zama a gidanki byn duk abubuwan da suka faru dake ,a wannan zamani wani nmj zai iya hkn?
fad'a sosai dady yayi mata sannan ya bawa acp hakuri da nasiha "akan hk Allah ya kaddaro babu yadda zasuyi sai adduar, sannan yace tazo ta roki mahaifinta yafiya.
akan hanyar komawarsu gida "yar baba dady yakirata "na'am babana "kwana biyu sai nake ganin wasu canje canje agame dake sannan safwan baya zuwa gurinki ,fatan dai lfy? Dan bana son asamu matsala irin na sajida dake.
tayi shiru tana souronsa batare datace komai ba har ya dasa ayar mgnrsa, a zahirin gasky taso gaya masa gdkyr lamari amman ganin zuciyarsa a hannu take akan lamarin Sajida ,tayi tunanin tabari har su isa Gida.
suna isa gida direba yayi parking atare suka fito tare da dady.
"barka da cikar k'arin shrkara ....me'ad ,saitin data jiyo kenan ,wanda yasa ta waigo daidai inda tafi zaton daga nan sautin ya fito safwan tagani tsaye ajikin motarsa yana mata murmushin mai cike da farincikinki ganinta, da wasu kayayyakin kyauta gareta ,har da cak ,yakarso gurinsu yana murmushi ya mika mata wannan naki mead yayi mgn yana gaisar da dady cike da girmama"aiko dai na gode sosai tare da fadada murmushin fuskarta. dady yace "dan albarka mgnrka nake acikin raina ,suka karasa cikin gidan inda sukayi masauki a babban parlour'n gidan dady ya dubeshi "ya baban naka yake yana dai lfy ko? "yana lfy ,tare da kai cup din coffe bakinsa ita km me'ad tana daga gefen hannun kujerar dady"yana Dai kula da sukari ko? "narasa dalilin dayasa ya kasa barin shan sukari gashi yana tattare da ciwo , ga itama wannan hk take kmr sha xumamu take .
"kai dady yaushe kake barina nasha ,duk wasu abu da suka danganci sukari in dai ba wai baka kasar nan ba mutun yasamu yasha gidanmu ya dawo tmkr sanssani sojoji takarasa mgnr tana me mikowa safwan tiren hannunta "a'a ki ci kawai na gode yayi mgnr idanunsa na kanta "dady bari na baku guri ina zuwa ta mike tashige ciki ,inda hira ta barke atsakaninsu har inda safwan ya zayyanewa dady komai dake faruwa fada dady ya rufe shi dashi "dan me zaka min hk?" idan ka daina sonta sai akace kabata damar cigabada soyaya dan talaka dan matsiyata "dady safwan yakirasa "karka damu wallahi ina son me'ad har yanzu, na dai barta ne saboda akwai taku dana shiryawa lamarin kasan yaran yanzu sai da rarashi da dabaru ta hkn ne kadai zamu samu abinda muke so, yanxu ma hk nazo ne mu fita domin tayata murna karin shekarrata, numfasawa dady yayi duk da yaji dadin rashin janyewarsa amman hankalinsa a matukar tashe yake banda gumi babu abinda ke fitowa daga cikin jikinsa.
Safwan ya mike dady sai kajini zamu fita daita yanzu, km Dan Allah karkayi mata zance "dady bai yunkurin cewa komai ba ya fice yacigaba da zaman tunani da mamakin abinda ya faru agurin ina ai baya jin zai iya hakura da wannan tashin hankali yana zaune yaji tashin motarsu sannan yasamu ya yunkura da kyar gefen kansa na wani irin sara kmr zai rabe gida Biyu..
Washegari
Da misalin Karfe tara na dare ranar ta yiwa fu'ad rakiya ya tafi tana dawowa ta cimma dady, zaune a parlour'n ya zabga uban tagumi yana huci takarasa ta sauke masa tagumi tace "dady'nmu lafiya ka zuba wannan uban tagumin hk? "Har nashigo bakasan nashigo ba.
Ya dubeta sosai da idanunsa da babu sauki a cikinsu yace "mead.
Bata amsa ba illa zuba masa idanu datayi saboda yadda yakira sunan nata cikin kakkausar murya.
"Waye wancan yaron da kika raka yanzu?
Ta sauke naunayen ajiyar zuciya sannan ta sunkuyar da kanta kasa batayi mgn ba saboda batasan abinda mgnr nata zai haifar ba, har da dady ya buga mata tsawa yace "Dan ubanki ba mgn nake miki ba?
cikin sarkewar murya tace "dady kayi hakuri da...daman dady ina son sanar maka ko waye shi, sunansa fu'ad kuma muna son juna dashi dan har mun yanke shawarar yin au....ji kake dau..daun..dady ya dauketa da wani gigitaccen marin har guda uku dayasa ta hantsila tayi bayan kujera tare da ganin wasu taurari sun gilma ta cikin idanunta, take ta nemi ji da ganinta tarasa, dady yana huci yacigaba "yanzu abinda zaki mana kenan? "Tozarcin dazaki mana kenan?
"Karamar yarinyar dake kinsa kan mugunta, kina kokarin yiwa iyayenki bakinciki saboda yanzu kina daukar salary mai tsoka "kina nufin bazaki auri safwan ba mai kaunarki da son farincikinki "me wannan tantirin yake dashi wanda yafi safwan?
"Ke yanzu ko kunya bakiji ba ki rasa Wanda zaki so sai wannan mai wuyan kmr marakin leman dan talakawa Dan matsiyata?
Me yake dashi ? "Me zai baki? Bashi da abinda zai baki tunda shima bai ci ya koshi ba ,wannan rayuwar kike ganin yayi miki daidai?
ga mamakin dady sai jiyo sautinta yayi" ni babu ruwana dady da wani babunsa ,matsayi ko mukami ni shi din kawai nake so, km ni bakin safwan nake ba, kawai dai bazan iya aurensa bane nabar fuad ,ni dai dady kayi hakuri ka amince na auresa shi zuciyata take so muddin ban auresa mutuwa zanyi fu'ad nake so km shine zabin zuciyata"inna lillahi wa inna ilaihi rajiun yashiga furtawa yana maimaitawa tare da maida idanunsa kan momy da hayaniyarsu tashigo daita da suhailat momy kuka ta fashe dashi ita da suhailat ganin dady na fada tana fada akan nmj da bashi da tabbas .
dady yace yanzu nufinki bazaki auri safwan ba ko me ? Ni dai kuyi hakuri wallahi banason aurensa "ashe kuwa zaki mutu ashe kuwa lokacin mutuwarki tayi kusa matukar baki auri safwan ba sai dai ki canza uba " mayaudariya maci amanar kauna, kin ci amanar safwan ,yaron na yana sonki ba tun yau ba, muryarta cike da shesheka tace "nifa ban ci amanarsa ba amman idan kuna bukatar lallai sai ya auri yar gidan ga suhailat nan kubashi ya aura ,wani marin ya sake d'auketa dashi "kinfi shi ido ne bai ganta ba yace ke yake so shashar banza da wofi maza tashi kibani guri kafin na tsine miki albarka keda zabin naki ...
kafin ta yunkura yayi wani kwallo daita sai ga ta zube ajikin safwan da shigowarsa gidan kenan, tsam ya rungumeta jikinsa batare daya fuskanci iyayenta ba, hankalinsa yayi kololuwar tashi ganin yadda kamaninta ya sauya hawaye ne suka zubo masa lokacin dayaga nata hawayen na tsiyaya daga cikin kumburarun idanun "haba dady zaka kasheta dan tace bata sona?
"Shi fa soyayyar d nan baa ayinsa dole dan Allah dady karka sake dukanta akaina nifa tuni na hakura ya fadi hk tare da mikar da tsaye bisa kafafunta "sorry kanwata kukan ya isa hk babu me miki auren dole"Ba dai fu'ad kike so ba?
Ta daga masa da kyar "to kice ya turo iyayensa "no no karka min hk safwan ba dai iyayensa ba sai dai shi kadan sa tukun , yakarasa mgnr yana juyawa tare da goge hawaye .
suhailat kuka momy kuka hatta safwan kasa rike kukansa yayi ita kuwa uwar gayya ji take idan duk duniya nan zasu taru akanta bazata auri wanda zuciyarta bata so ba fu'ad take so kuma shi zata aura.
********
Bangaren sajida kuwa babu laifi, ta saki ranta kad'an banda murnar rabuwa da emran babu abinda take, sai dai idan ta tuna tarasa budurcinta ,ranta idan yayi dubu yakan baci, acp na zaune a d'akin baccinsa yana sauraron BBC sajida tashigo jikinta a matukar sanyaye tasamu waje ta zauna kusa dashi jigun ranta a dan jagule saboda ganin halin damuwar dayake ciki a dalilinta, kallo daya yayi mata ya dauke idanunsa akanta, sannan cigaban da sauraron BBC, ahankali tasoma magana cikin sanyayyiyar murya" baba kasaki ranka Dan Allah akan yarka, kasamu yakini akaina na maka alkwarin cewar bazan baka kunya baba , ina tabbatar maka babu wani haufi akaina ni kaina nasoma nadamar abunda na aikata ...
"me kike bukatar daga gareni sajida?
"Amatsayina na ubanki nafi kaunar ganinki karkashin inuwar aure amman kika watsa min kasa a ido "Mai kike tunani duniya zatace akaina dake karon kanki?
"Ina dai rokonka baba kayi hakuri ka kasamu yakini acikin zuciyarka akaina ni bazan sake baka kunya ba....ko fushin karya ma bana iyawa dake driya tayi sosai sannan ta mike ta bar d'akin cike da matsanancin farinciki mara misaltuwa .
Mmn sudais ce
[11/3, 8:27 AM] El~hajj: 💗💗💗💗💗💗
'YAN CINKI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~NA~
*AYSHA A BAGUDO*
~DEDICATED TO~
MRS ADAM
( YAR MUTAN KAGARA)
Page 59 to 60
Not edit
........Sajida ta nufi d'akinta ta fad'a kan gadonta cike da matsanancin farinciki ji take tmkr tasamu fu'ad tagama , tunani ne ya fad'o mata a rai ta mike zumbur tayi bathroom tayi wanka, ta canja kaya zuwa wasu hadaddun kananan kaya, riga da siket blue da dan ratsin yellow,tasanya abaya ta yafa mayafi ta fito ,she look very attractive parlour'n kasa ta sauko adaidai lokacin da motocin mahaifinta suka bar gidan,sai aunty nadiya mai aikin da'aka samo musu ce a tun sanda aurenta ya mutu a zaune ,sajida batayi mata magana ba sai ita aunty nadiyar ce tace, dining fa ya kammala .
"No karki damu aunty,zan fita ne but yanzu zan dawo takarasa mgnr idanunta na ga duban agogon bango parloun dake walwalin haske kwan fitila ya sake kara haskawa, karfe 12 na safe yanzu ta wuce, aunty nadiya tace sai kin dawo. .
kai tsaye motarta tashiga ta nufi gidansu misna, kmr koda yaushe momyn misna tana kitchen tana aiki domin akwaita da kaunar girki, wanda hkn ke sata tuno da amminta sam itama hk take da son girkin tsiya dan wani lokacin babanta kance "Kyan 'ya tagaji uwarta amman ke sam baki d'aukota a komai ba...
Ita kuma sai tace masa" ai shi ta gado tunda ba asan nmj da shiga kitchen. ba...
ta gaidasheta kana ta nufi dakin misna straight ,akwance ta tarar daita tana kallo a zeey world misna naganinta ta mike zaune da murnarta ta rungume sajida ajikinta tana jin dadin ganinta cikin koshin lfy bakamar kwanakin baya ba, itama sajida ta rungumeta tana jin dadi aranta, tana matukar jin dadin yadda misna ke nuna mata kauna sajida tace "wani guri mai mahimmanci nazo ki rakani "a tunanin misna ko gurin shakatawa zasu kasancewar tasanta da son zuwa irin wuraren.
da azama misna ta diro daga kan gadonta tare da daura after dress akan riga da wando datake sanye dashi domin fitowarta wanka kenan , tare suka fito misna na rolling mayafin after dress akanta umman misna tace "sai ina adaidai wannan lokacin?
Sajida tace "umma fita zamuyi amman yanzu zamu dawo, umma tace " karfe 1 ta kusa kuje kuyi sallah sai ku zo kuyi lunch sannan rana ta fara yin sanyi sai ku fita, babu musu suka bi umarninta suka koma d'akin sukayi sallah sannan suka ci abinci Wanda sama sama sajida taci dan ta matsu bata isa inda zuciyarta ke bukatar zuwa ba,
sun fito suna yiwa umma sallama tace "karsu dade .
tafiya suke ahankali sajida ke jan motar muryarta a raunane sajida tace "kawata baki tmbayeni inda zamu ba ?
"tambayar mai zan miki byn nasan wata killa wajen shakatawa zaki.
"No kin sa'ba tsaitin tunaninki ,domin kuwa ba nan zamu ba ,kina jina ko a watanin baya da suka gabata kin sha ganina cikin tashin hankali da damuwa wanda kowa ke bukatar son sanin abinda ke damuna alokacin, amman naki bada wannan kofar ,sai dai a yau zuciyata ta aminta da nasar miki da damuwata ,bisa aminta da zuciyata tayi dake, me'ad itace wacce tafi cancata tasan matsala fiyye da kowa a duniya,