Header Ads
Showing 135001 words to 138000 words out of 163596 words

Chapter 46 - YANCNKI Book Complete by Aisha Bagudu.txt

Ads the beginning of article before Image

02 Jun 2024

1319

Ads at the middle of Article

,Dan har suna iya jiyo numfashin junansu, da yadda zuciyoyinsu ke bugawa da matsanancin karfin gaske .


hannunsa daya ya kai kan nata hannun yana k'ok'arin zare hannunsa dake cikin nata , domin isa ga bakin kofar da har lokacin ake kan bugawa da karfin gaske ana kiran sunanta.
muryarta cike da rud'ani da matsanancin kuka tace "Dan...dan girman Allah abban nasreen karka min haka ,kar ka bud'e kofar nan if possible ma ka bari ni na bud'e ,kai kuma ka samu guri ka 'buya Dan kwata kwata banason dady ya ganmu tare .... ta k'arasa mgnr wasu zafafan hawaye na gangarowa saman kuncinta...


Wani irin duba yayi mata mai d'auke da tambayoyi iri iri sannan yace "No no me'ad!! It can be possible na boye ,at where ?
"No bazan iya ba wallahi ,"ba zan iya wannan lusarancin ba , kamar wani kwarto ko mara gasky zan hiding din kaina "a ina kike tunanin zan buyavacikin dakin nan ?


"ai ni nama fi son muyi harba dashi ,muyi ido da ido da dady ,so that zai sake fahimtar raba tsakanin me'ad da fu'ad ba Abu ne mai sauki ba .....
Kuka take sosai har da shesheka jikinta na wani irin rawa ,gabadaya tausayinta ya rufesa , Dan hk Hanky ya ciro daga cikin aljihun wandosa yashiga goge mata fuskarta dake kwararar da hawayen daya rasa dalilin zubarsu sannan ya kawar da fuskarsa yana kallon kofar zuciyarsa na wani irin tafarfasa "shi bai ga wani abun damuwa da tashin hankali akan Dan mahaifinta ya gansu tare ba .


"Abban nasreen ....... ta sake kiran sunansa muryarta a matukar raunane, ya d'ago idanuwansa ya kalleta da matukar 'bacin rai Wanda yasa jikinta ya sake d'aukar rawa gbdy ta rud'e ta kasa furta komai illa jikinta daya cigaba da kyarma.
ganin yasoma d'aga kafafunsa tayi saurin kamosa ta rungume shi ajikinta tana wani irin kukan mai ta'ba zuciya "kayi hakuri abban nasreen kar bud'e wallahi tsoron dad'y nake yi banason abinda zai sake shiga tsakanina dashi..
ya fizge jikinsa yayo baya kad'an yana fuskantarta "hakuri me kike bani ?
"Hakurin kar na bud'e kofar nacigaba da cutar kaina ?
"Ko kuma hakurin na boye kaina alhalin akan right dina nake.
"ke bakisan right dina ake kokarin tauye min ba ?
Hawaye suka sake gangaro mata ta sake riko tafin hannunsa cikin nata "ina baka hakuri ne saboda dalilai na Dan Allah kayi hakuri kayi yadda nace tsaki yaja tare da fixge hannunsa da karfi yasoma tafiya kafin tayi wani hanzari tuni har ya isa kofar ya bud'e ,gama Bud'e kofar ke da wuya idanunsa ya sauka akan mumy da dady tsaye suna dubansa.


kallon kallo suka shiga yiwa juna daga dady har fu'ad dake tsaye daga shi sai dogon wando da farar singlet .....
Da sauri me'ad ta dafe kirjinta dake bugawa da karfin gaske ,saboda gabanta dake wani irin bugu ,take gefen kanta yasoma Sarawa tasoma ganin juya, d'akin ya dinga jujjuya mata.
dishi dishi take ganinsu acikin idanunta, tsawon minti goma fu'ad na tsaye rike da kofar yana duban dady dake watsa masa wani irin kallo mai gauraye da harara .
banda zallar 'bacin rai da firgici babu abinda fu'ad ke hangowa atattre da dady .
Cike da matsanancin tashin hankali dady yace "daman abinda kuke yi kenan da yasa kuka ki bud'e mana kofa tun dazu ?
Fu'ad ya yayi saurin sauke ajiyar zuciya da amsar "Eh acikin ransa .


Ahankali dady ya kallo me'ad dake rike da goshinta tana k'ok'arin kaiwa kasa tana nishi da kyar kmr mai cutar asthma yace "Amman me'ad kinji kunya a gidan uban.......
ai tun kafin ya kai ga k'arasawa ta lumshe idanunta ruf...
numfashin gabadaya ya tsaya cak tasoma k'ok'arin zube kasa cike da matsanancin tsoro da firgici fu'ad ya tarota ta fad'a jikinsa ya rungumeta tsam tsam yana kiran sunanta "me'ad!!!
amman numfashinta tuni ya tsaya
Mumy naganin haka ta bangaje dady dake tsaye a gefenta tayo cikin d'akin tana kiran sunanta"me'ad !!! ......
ai ganin kwata kwata bata numfashi yasa ta fashe da wani irin kuka "shekenan ta mutu fargaba da tsoronka ya bugar mata da zuciya ta mutu ... "
ba fu'ad dake tsugune rungume daita ajikinsa ba hatta dady yayi matukar tsorata ,mutuwar tsaye dady yayi agurin sakamako abinda yaji mumy ta fad'a ..


fu'ad ya dinga jijigata tare cewa " ruwa mumy "
ai da wani irin sauri momy ta nufi fridge din dake cikin d'akin ta d'auko ruwa ta dawo da sauri ta mikawa fu'ad tana furta kalmar inna lillahi wa inna ilaihi rajiun
shi kawai take maimatawa.


fu'ad ya yayyafa mata ruwa yafi sau Goma amman me'ad taki motsowa, nan fa hankalin kowa yayi mugu mugun tashi, mumy ta kwasa da gudu ta bar d'akin ta nufi d'akinta domin kiran doctor, yayinda fu'ad yayi saurin d'aura bakinsa kan lip's dinta ya had'e bakinsu guri daya yashiga tsotsa da zumar bata taimakon gaugauwa.
gaban dad'y ne yayi wani irin mahaukacin bugu da karfi gaske yayi baya luuuuu jiri na neman zubar dashi kasa Allah ya taimaka ya tsaya bisa kafafunsa yana cigaba da duban fu'ad dake tsotsan bakin me'ad..
mumy ta dawo d'aki tana salati ai da sauri ta juya ta koma saboda abinda idanunta yaci karo dashi..

kusan minti shabiyar dad'y na tsaye yana duban fu'ad da har wannan lokacin bai zare bakinsa daga cikin na me'ad ba ,har sai daya ga numfashinta yasoma dawowa jikinta sannan ya zare bakinsa ya cici'beta zuwa saman gado ya kwanatar daita batare da ya kalli inda dad'y yake tsaye ba .


cikin haka doctor yashigo d'akin da sauri tare da ajiye kayan aikinsa akan bedside yasoma k'ok'arin kai hannusa jikinta, zaraf fu'ad ya riko tafin hannun likita "karka soma kai hannunka jikin matata haka kai tsaye "
sororo likita yayi yana dubansa cike da matsanancin mamaki sannan yace "ba kaga halin da take ciki bane?
"kabari na dubata musan abinda ke damunta mana"
"nafika son sanin abinda ke damunta da bukatar lafiyarta gbdy ,"amman ba zan ta'ba lamunta ka ta'ba min jikin mata ba,"
idan kuna da likita mace kana iya kiranta tazo yanzu, idan kuma babu ni zan nema da kaina period .....yana gama fad'ar hk ya mike tsaye ya janyo rigarsa ya zira ya zagayo ya sanya mata hijabinta yana jan tsaki ya kamo hannunnta tare da riko kungunta ya mikar daita tsaye, yasoma tafiya daita.
yayi taku daya biyu dady ya tsaida shi ta hanyar cewa "ajiye min yarinyata likita ya duba min ita tukun, musan abinda ke damunta ,idan kai baka damu da lafiyarta a halin yanzu ba ,mu mun damu da lafiyarta ya fad'a takaice ..
yana nuna masa saman gadon ,har ya bud'e baki zai yi magana me'ad ta matse hannunsa dake cikin nata ala'mun kar yace komai, jiki a sanyaye ya meidaita ya kwantar ya tsaya akanta yana kallonta kafin daga bisani likita yasoma dubata..


bayan likita yagama gwaje gwanjensa ya bukaci fitsarinta domin ya gama dubata tsab bai gai ala'mun wata cuta ajikinta ba, cikin minti biyar fu'ad ya mikawa likita karamar robar daya bashi .
Likita ya amsa ya tashi cikin sauri ya fice ,kai tsaye hospital ya nuna gwajin farko likita ya tabbatar da ciki gareta har na tsawon wata uku...
Lokacin daya dawo yake sanarmusu da abinda gwajin ya bayar..


"what?


"when?


"and how this happened ? dady ya fad'a a matukar razane, kallon doctor yayi yace "kaje ka sake dubawa sosai "wallahi ranka ya dad'e ciki gareta kmr yadda kaji na fad'a .
take gefen kan dad'y yasoma sarawa jikinsa ya d'auki zafi kamar garwashin wuta ,tsinuwa kuwa ya tsinewa fu'ad yafi sau d'ari da cikin jikinta domin ya rusa masa duka budget dinsa ..


dad'y ya tsurawa me'ad dake kwance ido yana dubanta, kasa kallonsa tayi, ta sunkuyar da kanta tana wasa da yatsun hannuna, tunda take bata ta'ba jin kunya da firgici irin na wannan lokacin ba, gbdy taji kanta yayi mata nauyi, jiki a sanyaye likita ya mike ya had'a kayan aikinsa yakama gabansa, ya bar dad'y jingine da bangon d'akin yana kallon fu'ad da me'ad ,kwakwaluwarsa na karanto masa abinda ya kamata yayi da matakin da zai d'auka akansu.


kusan minti goma yana dubansu sannan yasoma mgn cikin kausashiyar murya "komai zakayi, sai dai kayi amman diyata me'ad bazata cigaba da aurenka ba...


"har da cikin jikinta ma yunkurin raba aurenmu kakeyi dady ?
" wai dad'y me nayi maka ne arayuwa daka tsane haka ?
" a tunanina ka tsaneni saboda ni talaka ne jikan talakawa..
"but ka duba qualities dina yanxu ba fariya ba a halin yanzu yarinya ko diyar waye a garin zan iya mallakata saboda matsayina a yanzu ya zarta yadda kake tsammani....
"Duk da cikin jikinta kuwa bazaka cigaba da rayuwa da diyata ba, kai nifa ba arzikinka nake bukata ba," komai zaka zama a duniya fu'ad bazaka taba burgeni ba saboda bana sonka, kai kanka ne banason ba wai talaucinka ba..
Dan haka maza ka bar min gidana kuma daga yau daga rana mai kamar ta yau kar ka sake kuskuren takowa cikin gidana.. ..


"kai kanka ne banaso ba wai talaucinka ba fu'ad ya sake maimaitawa yana duban dad'y kmr zai zubar da hawaye..
me'ad dake kwance banda ruwan hawaye babu abinda take zubarwa" duk itace silar faruwar komai..
"itace silar jefa rayuwarsu cikin tsaka mai wuya da shiga halin ha'ulai ...
"gabad'aya itace silar kiyayyar da dad'y kewa fu'ad..
to ya zatayi da rayuwarta kaddararta ce auren fu'ad bata yadda zatayi ,kuka take sosai..


a matukar tsawace dady ya sake bawa fu'ad umarnin bar masa gida "ka bar min gidana idan ma Ka tashi wucewa ka wuce da wacan yarinyar taka wace ganinta kullun ke k'ara min damuwa ..


"idan na bar gidanka, ko na daina zuwa gidanka matata da d'ana ko 'yata dake zaune a cikin gidanka fa ?
"dady .......fu'ad ya kirasa muryarsa a kasalance "banason kana fad'a ina fad'a saboda daraja da kimarka acikin idanuna, banason yi Abinda daga baya za'a yi Allah wadai dani amatsayinka gareni,..
"ni yanzu duk abar wani zance zuwa gida da sauransu ka bani matata muje mucigaba da rayuwarmu saboda abinda kake son faruwarsa bazai ta'ba faruwa ba tsakanina da me'ad.
"saki ne dai wallahi duk duniya idan za'a taru bazan saki matata ba zuwa gidanka kuwa kamar nazo nagama matukar matata da cikina na gidanka dole na shigo har ma nayi abinda naga dama ,abu na karshe a bari wani abu yasamu cikin jikin me'ad, anan za'a san waye asalin fu'ad yana gama fad'ar haka ya juya fuuuuuuu ya fita daga d'akin a parlour ya iske mumy zaune gefenta suhailat ce rungume da nasreen ,keyarsa ya shafa yana jin kunyar abinda zai fad'awa mumy ,domin yana matukar jin kunyarta yana ganin kimarta fiyye da komai ,Amman babu yadda zai yi Dole ya furta abinda ke ransa ahankali cikin sanyi murya yace" momy a hado min kayan nasreen daita zan wuce "
Jikin mummy a sanyaye ta mike tashiga d'akinta Dan Sam bazata iya mutsu da sirikin nata ba ,tunda duk abinda ya faru ,ya faru ne acikin kunnuwansu ..
Zuciyarta ke bugu da karfin gaske kasa had'a kayan tayi ta tsaya tunanin yadda zata shawo kansa ya tafi batare da nasreen ba ..


Manage ......


Mmn sudais ce
[11/3, 8:31 AM] El~hajj: 💗💗💗💗💗💗
'YAN CINKI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗


~NA~


*AYSHA A BAGUDO*


~DEDICATED TO~
*MARYAM ALHASSAN D'AN'IYA (MAR'OB)*


page 88


...tunda fu'ad ya fice daga d'akin ,dad'y ya tsura mata idanunsa yana kallonta ,har lokacin mamakin abinda ya faru yake, ayi ciki har na tsawon wata uku acikin gidansa batare da saninsa ba ..
"hakika ya cika babban sakarai da yayi tunanin hargaginsa na wancan ranar zai yi tasiri a zuciyar fu'ad, a she ihu kawai yake baya ga hari, yana lalla'bowa ya more diyar da yake da burin rabata da rayuwarsa.


naunayen ajiyar zuciya ya sauke da karfin gaske, lokacin guda kwalkwaluwarsa tashiga caji domin neman mafuta, dan dole yasan abunyi kafin ruwa ya karewa d'an kada, kar abubuwa suzo suyi masa tsamari.
" da ala'mun yaron na son ganin bayansa ne a dalili shishigi dayake masa cikin lamarinsa.
"Shi duk cikin lamarin ma shi yafi ganin laifi me'ad domin sai bango ya tsage kadangare ke samun guri 'buya ,duk laifinta ne anan Sam yaron bashi da laifi .


runtse idanunsa yayi sosai yace "ina alkwarin da kike min me'ad na zaki cire fu'ad acikin rayuwarki?
"ni shikenan kullun ni ke da fad'uwa, shi yake da galaba akanki ?
"da fari yayi nasarar akanki yanzu ma kina k'ok'arin sake bashi wata damar, koma nace kin rigada kin bashi..
"Yanxu kin kyauta min kenan?
" gabadaya kin rusa min shirina akanki kinsa karfin gwiwata ta raunana .
"me yasa tun farko kika nuna min zaki rabu dashi?
"Me yasa kinsa bazaki iya rabuwa dashi ba kika zabeni akansa?


"zaki sake tozartani a karo na biyu a idanun safwan ?"me kike son na cewa safwan?
" fad'a min, fad'a min abinda kike son na fad'a masa akan tsinancin da kika yi ?
ya bud'e idanunsa da suka canza kala tmkr garwashin wuta tsinuwa kuwa har lokacin bai dana yiwa fu'ad ba.
kuka take sosai har sanda momy tashigo d'akin a fusace tace "enough is enough idris yaya da wahala haka?
" ina fa guje maka karshen inda taurin kanka zai kai rayuwarka, da iliminka da komai kake jayayya da ikon Allah,ka hakura ka daina nuna karfin ikonka dayawa akan lamarin nan ,saboda kai ba kowa bane ,yanzu idan Allah ya gamada zai iya d'aukeka a doron duniyar gabadaya muga karshen taurinka .
" haba wasu abubuwan fa boyesu ake a danne zuciya domin rayuwar ta tafi yadda ake so ..
A matukar tsawace ya dakatar da ita ,ta hanyar d'aga mata hannunsa "ya isheki haka , karkiyi tunanin zan yi gun da bakina na boye abinda ke raina, dole na fito na fad'a saboda bana sonsa...
Kirjin me'ad ya buga da wani irin matsanancin karfi tayi saurin runtse idanuwanta saboda d'acin kalmar da mahaifinta ya fad'a ,
"tun ranar farko dana d'aura idanuna akansa naji muguwar tsanarsa ta dira a kahon zuciyata ,Wanda har yau ban daina jin hkn ba .
bana son sa kuma banga mahalukin da zai sani dole nasoshi ba ,Dan haka karki sake saka bakinki acikin maganata da ya'yana....


"Magana kmr nayi nagama tunda ba kai kad'ai ka haifesu ba ,
" kuma ina son in sanar da kai wani abu ,zaka so fu'ad a lokacin da shi son bazai maka amfani ba, domin zakayi nadamar abinda kayi ,yayinda ni nadamarce bana son kayi shiyasa kake ganin kullun nake nusar da kai.


"ni na d'auki cikin me'ad na tsawon wata tara da kwanaki tara, nice wace idan na tsine mata take tsinewata zatayi tasiri akanta sabanin kai , Sam Sam Sam me'ad bata aikata tsinanci ba illa ibada ga ubangijinta wanda kai kaima kasan da wannan,
daga yanzu ina adduar ta haife wannan cikin lafiya, fu'ad ya sake yi mata wani, idan ka hanata rayuwar aure a gidanta ,tayi rayuwar aure anaka gidan,tana gama fad'ar hk ta juya ta dubi me'ad dake kuka tmkr ranta zai fita "kingani ba, kinga abinda d'an burouban abinda taurin kanki da kika gada na wahala ya janyo miki ko, "kullun nake gaya miki illar abubuwan dakike yi Amman baki ji saboda mugun halinsa da kika d'auko.
" ina jin kmr na cire hannuna acikin lamarinki na barki da damuwarki ki karata saboda duk rashin jin maganarki ne ya janyo faruwar komai..
Da sauri me'ad ta duro ta durkusa gaban mumy tana kuka "Dan girman Allah mumy karki cire hannunki cikin lamarina, idan kika cire hannunki rayuwata zata sake taggaya. .
"Dady kayi hakuri ka yafe min a karo na biyu ba Dan na sa'bawa umarninka ,dady kayi hakuri ka sausautawa fu'ad wannan kiyayyar ,wallahi fu'ad mutun ne gari abun alfahari ,dady kayi hakuri ka yafe min kabarni na koma gidana nacigaba rayuwa da mijina saboda har yanzu ina son shi takarasa mgnr wasu zafafan hawaye suka shiga zubo mata.


"Abinda yakamata tun farko kenan kiyi kowane acikinsu suna da matukar tasiri acikin rayuwarki, Baki za'bi daya ki bar d'aya ba momy
na gama fad'ar hk ta juya ta bar d'akin ta sake koma d'akinta.
shima dady jikinsa a matukar sanyaye ya fita zuwa nasa d'akin yashiga zariya ad'akin tunani kawai yake yana jin kmr yakira safwan yasanar masa abinda ke faruwa Amman yana fargaban abinda zai faru , domin yasan yana jin zance me'ad na d'auke da ciki zuciyarsa bugawa zatayi......


tsawon minti 20 fu'ad na tsaye jiran fitowar mumy ,amman babu ita babu al'amunta, wanda zuwa lokacin shi ya rigada yasan dalilin rashin fitowarta daga d'akin, saboda batason ya wuce da NASREEN ne .
Yayinda shi yake jin ruwa da iska babu abinda ya isa ya hana hakan faruwa ,
sai ya d'auki diyarsa daga wannan bakin gidan da bai san lokacin da zai zama tubalin farinciki garesa ba..
duba soyayya da abubuwan da suka faru abaya ,yasa yake da muradin cigaba da rayuwa da me'ad ,uwa uba tsagwaron soyayyarta bazai barshi ya iya hakura daita ba, amman wallahi daya bawa dady mamakin da har ya koma ga mahalicinsa bazai ta'ba mantawa dashi ba.
ganin cigaba da tsayuwar agurin bazata amfanar dashi da komai ba, yasashi d'ago idanunsa ya d'aura akan suhailat dake rungume da NASREEN tana kuka itama yarinyar na kuka wanda yasa kirjinsa tsananta bugawa har lokacin zuciyarsa bai

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads