Header Ads
Showing 27001 words to 30000 words out of 171869 words

Chapter 10 - BIBIYATA YAKE YI COMPLT Document by Zainab Bawa.txt

Ads the beginning of article before Image

05 Jun 2024

1064

Ads at the middle of Article

ya yanke idan zata koma zai bita sutafi tare dan yaje ya gana da iyayen yaron.


Takirashi ta shaida masa abun yazo masa a bazata dan haka yashiga matuƙar tashin hankali tayaya zai iya tunkarar mutumin daya zama musu uba alokacinda suke tsakanin buƙatar uba kuma yayi musu alƙawarin aurar masa da ƴarsa da zancen auren wata daban? Yasan ko mahaifiyarsa bazatayi na'am da zancen ba."




ZAYNAB ALABURA


*BIBIYATA YAKEYI*
*(WAYE SHI?)*






Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya.






PAGE 14


Ganin baida wata mafita yasa yaje ya samu mahaufiyarsa da maganar yasha faɗa sosai, ita cewama tayi yayi ƙarami a auren gabaki ɗayansa nawa yake da zaice zaiyi aure ko mahaifinsa baiyi aure dawuri hakaba sannan gashi abokin mahaifinsu ya rigada ya bashi ɗiyarsa itakam bada ita za'a watsa masa ƙasa a ido ba, shidai dayake baida kunya ya taro auren toh yaje da kansa ya samu abokin mahaifin nasa yayi masa bayani."


Rashin mafita da rashin samun goyon bayan mahaifiyarsa ba ƙaramin ɗaga masa hankali yayi ba yarasa ta ina zai kamo bakin zaren komai ya cukurkuɗe masa shi bai taɓa tunanin iyayenta zasu amince mata da aurensu ba shiyasa yabata dama kai tsaye akan taje ta samesu. Gannin baida wata mafita yasa yarufe idanuwansa ya tunkari abokin mahaifin nasa ga mamakinsa bai nuna wata damuwa ba ya gwada zai tsaya masa har ayi auren kuma bai janye ƙudirinsa na bashi auren ɗiyarsa ba yace masa bazaiyi alƙawari ya karya ba dan haka zancen bashi aurenta yananan daram. Sannan yace zai kira mahaifiyarsa ya shawo kanta. cikeda kunyarsa yayi masa godiya yatafi.


Yatafi yabarshi da al'ajabi iyayen mace zasuzo ganin iyayen namiji baisan yanda lamarin nasu yake acan ba amma sukama nan bahaka sukeyi ba."




Gabaki ɗaya mahaifanta suka taho tareda ita suka sauƙa a gidan daya saya mata.


Bayan sun iso ta kirashi ta sanar dashi shi washe gari abokin mahaifinsa yatada wasu daga cikin ƴan uwan babansu Muhammad sukaje can gidan dan nema masa aure. Sun tafi da goron tambayarsu da sadakinsu. Sunsha mamaki matuƙa ganin gidanda yaje yataro aure. amma ga mamakinsu an karɓesu Hannu bibbiyu akayi magana ta manya. Mahaifinta ya sanar dasu cewa zai yanke lokacin aure idanya yanke zai sanar dasu."




Muhammad yana gida sai taraddadin irin karɓanda za'ayiwa mahaifansa yakeyi amma bayan dawowarsu dayaji komai yatafi dai-dai sai hankalinsa ya kwanta.




Yana zaune wayar tafara ruri saida yasamu kansa da murmushi ya ɗaga wayar tace.


"kaga nacika zancena koh? Yanzu maganar aure ba fashi dole sai anyi" ya taɓe baki jin yanda take maganar aure ba shauƙi babu alamunsa yace.


"Eh boss lady nagani kincika maganarki"


"Toh yanzu yaushe zan ganka Dady ma nason ganinka kafin yatafi kuma zuwa gobe zai koma" Saida yaja numfashi sannan yace.


"In sha Allah zanzo bayan magrib dan kema inaso muyi magana dake"


"Okay I'll be waiting for you sai kazo". Sukayi sallama. Bayan magrib ya shirya domin samu mahaifinta. dake dama mahaifin yasanda zuwansa yasa akayi masa tarɓa ta musamman, da mahaifinta yafara ganawa ya sameshi sukayi magana sosai ta fahimta sannan mahaifinta ya gamsu zai bashi aurenta ɗari bisa ɗari. Tun farko daya ganshi ya tabbata dole ƴarsa da kamu da soyayyarsa saboda kyawun da Allah yayi masa sai bayan ya zauna sunyi magana yagane nutsuwarsa da kyawawan kalamansa. Kowane laffuza zai furta yana tacesu ya tauna ya aunasu a mizani sannan yake furtasu mahaifiya ya yaba sosai da irin mjinda ƴarsa tasamo"




Bayan sungama da mahaifin yafita yabasu waje sannan ita tashigo. Kamar yanda suka saba mu'amalarsu haka sukayi babu wani canji dukda maganar aure tashiga tsakani haka take yimasa magana cikeda umarni da gadara shi atunaninsa zata canja idan bata canjaba yanzu yasan dole zata canja da zarar anyi auren daya tuna hakan saiya samu sanyi acikin zuciyarsa. ta kalleshi tace.


"yanzu me dame kake gani zaamu shirya a bikin?" maganarta ta dawo dashi daga duniyar tunaninsa ya nisa sannan yace.


"Bikinda ba yanzu za'ayishi ba mubari sai lokacin yayi sai mushirya abunda za'ayi"


"Nasan Dady bazai saka lokaci kai tsawo ba danmu familyn mu ba'a saka lokaci mai tsawo abiki"


"Eh toh mu namu famlyn ya bambamta gaskiya danmu ana sakawa da tsayi dan agama haɗa komai na al'ada, kuma kinga ƙarfinmu da naku ba ɗaya ba so mu dole mubi komai a hankali, yatsine baki tayi tace.


"Au nina ɗauka anwuce wannan ai kana dani menene wata damuwarka da abunda za'a kashe hidimar biki? Zanji da komai" girgiza kai yayi yace.


"Nidai nafiso abi komai a hankali banaso kiyi hidimar abunda ya shefeni zanyi da kaina kuma tunda kinga abokin mahaifina zan auri ƴarsa nan gaba shima bazan ɗaura masa nauyi ba zanfiso nayi komai da kaina" canja fuska tayi ta ɗaureta tamau tace.


"Banganeba? Har yanzu batun aurenka da yarinyarnan yana nan? Naɗauka anwuce wajan tunda yanzu zakayi aure" girgiza kai yayi yace.


"Bamu wuceba nafaɗa miki nayi alƙawarin aurenta kamar yanda mahaifinta yayi alƙawarin auramin ita banaji akwai wani abunda zai kunce wannan alƙawari kisakawa ranki ko ba daɗe ko bajima zan aureta wannan arubuce yake" Hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba tace.


"nikuwa har yanzu ba'a haifi macenda zan haɗa miji da itaba dole ka zaɓa koni ko ita" yayi murmushi sannan yace.


"Dole ai Sallah ce kedai kije kiyi tunani kiji ko akwai macenda zaki iya haɗa miji da ita idan kin yanke shawara saiki sanar dani" fuuuu tabar wajan bata sake juyowa ba haka yajuya yatafi yanajin ransa babu daɗi shidai bazai ce yafasa aurenta ba kuma bazai fas alƙawarinsa ba idan taji zata iya ahaka ashirye yake daya aureta. Tana shiga cikeda takaici take sanarwa mahaifiyarta abunda yafaru. Mahaifyar tace.


"Toh ki haƙura da aurensa mana tunda bashine kaɗai namiji ba zaki samu wanda yafishi"


"Bazan iyaba tabata amsa kai tsaye" tace.


"toh ki yarda ki aureshi ahaka daga baya zamusan yanda zamuyi bazai tada zancen aurenba zamu sake masa kuɗi arufe bakinsa yanda zamu juyashi son ranmu" wannan shawara tayi haka suka yanke sannan tace kada su sanarda mahaifinta dan bazai yardaba."




Saida yayi ƙwana biyu bai nemetaba itama bata nemeshiba saida tagaji dan kanta taga baida niyyar kira ita takira. Yana picking tace.




"Kwana biyu meyasa baka nemeni ba?" baka janye akan maganarka bane?" Murmushi yayi sannan yace.


"Naɗauka zaki nemeni kamar yanda muka tsaya idan kin yanke shawara"


"Yanzu baka yanke ba kenan?" ta jefo masa tambaya.


"Uhum" kawai yace mata tace.


"toh shikenan naji na yarda ka aureta ɗin" tayi magana kamar wanda idan baya yardaba ba auren zaiyi ba."




Bayan sati biyu mahaifinta ya saka lokacin biki wata mai zuwa aka fara shirye shiryen biki yanda suke kashe kuɗi kamar wanda basusan darajarsa ba ansaka lokacin bikin yayi kusa yanda shi da danginsa babu wani abunda suka tanada Kuma basusan yanda zasuyi ba shidai abokin mahaifinsa yayi nasa tunda ya biya masa sadaki yanzu sai dai ya taimakesu da abubuwanda baza'a rasaba. Sanin cewa baidashi ya sanya zainab ta sake masa kuɗi kamar bata sonsu sanin bashida yanda zaiyi ya sanya ya amshi kuɗin yana amfani dasu amma zuciyarsa a kullum tana jiye masa tsoron abunda zaije yazo dan yanaji wata rana dole akwai abunda zai biyo bayan wannan kashe masa kuɗinda takeyi. Dama duk namijinda zai sake jiki yaci kuɗin mace toh ya jirayi sakamako."


Lokacin biki yayi anyi hidima bana wasa ba mahaifinta ya nuna bajintarsa a auren ɗiyarsa tilo wani gida daban yasiya yabasu wanda zasu zauna aciki. Duk wata hidima a wajan bikin shi ya ɗauki nauyinta anyi biki komai angama lpy."




******
Mahaifinta ya biyawa Amarya da ango suka tafi honeymoon daganan sukace saudi suka dawo.
suna zaune agidansu lpy amma daga baya halayanta suka fara damunsa tunda sukayi aure koda sau ɗaya bata taɓa gaisheshi a matsayinsa na mijinta ba, gadara da iko kuwa yanzu ƙaruwa sukayi komai umarni take bashi gani takeyi kamar itace mai juya gidan dole kuma abita tunda gidan ma mahaifintane kuma dukiyar mahaifinta sukeci.


Suna zamane babu wata soyayya ko kyautatawa babu mu'amala kai kyau atsakani, batasan yanda ake kulada miji shi kansaba bare aje kulada gida sau ɗaya yayi mata complain dake shi dama bamai ƙorafi bane sai kawai gani anƙaro ƴan aiki. Mamakine ya kamashi sosai shin ƴan aiki zasu kula dashi kenan?"


Gashi ko fita zatayi ita bazata taɓa tambayarsa ba sai dai yadawo yaga batanan, sannan yanzu yagama school amma har yanzu bai samu aikiba itakuma ta wajanta babu alamin za'a sama masa aikin.


Da saninta ta hana mahaifi ta sama masa aiki saboda tana gani da zarar ya kafu da ƙafafunsa toh tabbas wata rana zaiyi maganar aure gara ta su zamana dimun da'iman duk wani abinda sukeso ana tanada musu shima kansa ta hutar dashi basai yasha wahalar aikiba sannan bazaisa wahalar nema wajan sana'a ba yana kwance ake tanada masa komai.


Daya gaji da irin wannan zamanda yakeyi sai kawai ya yanke shawarar nemawa kansa aiki haka yayitabi bai sami aikiba sai wata rana kawai school ɗinda yagama suka bashi appointment na lacturing a wajan yadawo gida da murnarsa ya shaida mata sam batayi murna da aikin daya samu ba. Kwanaki kaɗan da faruwar hakan akayi terminating appointment ɗinsa. Baisan daliliba haka ya haƙura daga baya yazo yagane cewa matarsa ce sila sai yabar zancen aiki yashiga neman sana'a ranarda tasan yana sana'a kuka ta sanyashi gaba tanayi tana faɗin dame ta rageshi bayan babu wani abunda ya nema yarasa yau abun kunyane ace anga mijinta wajan sana'a sirikin senate president, har mahaifinta saida yashiga maganar akan shima bai yardaba zai zubar masa da kima duk abunda yakeso ya sanar dashi zai bashi.


Wannan dalilin yasa ya zauna gabaki ɗaya ya daina taɓuka komai sai dai kawai akawo yakashe."


ana cikin haka kwatsam saiga ciki nan rikici yatashi tace itakam bata shirya haihuwa yanzu ba sai dai azubar da cikin. Rikici har gaban iyayenta wannan karon kam basu bata gaskiya ba dan haka dole tabar cikin amma anyi differing karatunta saboda tana laulayi sosai."






ZAYAB ALABURA
*BIBIYATA YAKEYI*
*(WAYE SHI?)*






Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya.


PAGE 15




Haka da sukaci gaba da zama amma gabaki ɗaya yanda al'amura suke tafiya a rayuwarsu. Ina nufin mu'amalar rayuwa banda abubuwan more rayuwa.


Ko faɗa sukayi idan zasuyi sati guda bai bata hakuri ba bazata taɓa kulashi ba bazata sauƙo ba tunda sukayi aure bata taɓa fara sauƙowa alokacinda suka samu saɓani ba.


Hajiya Zaynab tacigaba da samun kula wajan mijinta da mahaifinta har Allah yasa tasauƙa aka samu mace. Mahaifanta da muhammad sunyi matuƙar murna aransa yaso saka sunan mahaifiyarsa amma yanda ta nuna tanason yasakamata sunan mahaifiyarta ya sanya bai fito danasa burin fili ba ya cika mata nata burin.




Dukda taimakon da masu aiki suke yimata wajan raino amma hakan tana complain akan shan wahala kuma yarinyar babu abunda yake kawota wajanta sai idan zata shayarda ita. Hakan yasa batayi gigin komawa makaranta ba wata shekara data zagayo sai aka sakeyin differing. Shekara ɗaya da haihuwarta tasake samun wani cikin batareda ta saniba babu wani laulayi sai dai ƴar ƙiba datayi alokacinda tagane cewa tanada ciki sai rikici yatashi wannan karon iyayenta sun goyi bayan azubar da cikin haka babu yanda ya iya dole ya amince ana zuwa asibiti aka gwada cikin yana 15weeks har yashiga 4month likita ya nuna musu hatsarin dake tattara da zubarda cikin daya shiga Second trimester jin haka yasa mahaifinta ya haƙura itama yashiga lallaminta akan idan ta haihu sai ɗauki mataki dawuri.




Awannan lokaci aka ɗaga bikin ƙanwarsa wacce kebi masa Halima abokin mahaifinsa Alhaji habibu shine yayi komai a wannan lokaci dan awajansa take. Itakam zaynab dake tana famada cikinta bata halarci bikinba sai dai tayi musu kyauta ta bajinta."


Cikin yana 7month taje asibiti aka cire mata shi dan acewarta tagaji. Wannan karonma sunan mahaifinta aka saka masa yaro yaga bajinta sosai wajan iyayenta. Tun batayi arba'in ba tabi majors na kariya daga sake samun wani cikin.


Shikuwa muhammad ganin irin rayuwarda matarsa da mahaifanta sukeson yayi na zama zauna gari banza ba aiki ba sana'a yasa yafara tanada kuɗin dayake samu daga wajanta dana mahaifanta. Ya buɗe shaguna da kuɗin nan da nan Kasuwancins aya haɓaka Allah yasaka masa albarka aciki duk wannan abin batasan yaan faruwa ba data daƙile tunda wuri.
saida ta shekara biyar cis bata sake haihuwa haihuwa ba awannan shekara biyar ɗin Allah yasaka masa albarka a kasuwancinsa na bam mamaki komai haɓaka kawai yakeyi.



Ahaka yatara kuɗi mai yawa yasaya fili mai masifar girma sai bayan yasaya yake sanarda ita data tambaya yanda yasamu kuɗi yace mata kuɗinda mahaifinta yake bashi yatara tunda yana samun na amfani a wajanta tayi murna sosai nan ta nemi kuɗi a wajan mahaifinta masu yawa domin fara gina filin mahaifinta batareda ya tambayeta abinda zatayi dashi ba ya bata fiyeda yanda ta buƙata. Nan da nan aka fara ginawa amma a hankali tsararren gini nagaske shima yana saka kuɗinsa acikin ginin amma nata yafi yawa ahaka aka gama tsara gida mai kyau alokacin gidajen da suke sakyawun wannan gida a garin gabaki ɗayansu basufi a irga suba yanda aka tsara gidan ko nan zuwa shekara ashirin gaba design ɗinsa bazai taɓa fita ayayi ba Shashinsa da nata a haɗe suke a waje ɗaya babban palour da 4bed rooms funitures ɗin da tsarin ginin yazo sai extra 2room and living room (palour) da bathrom guda uku, da zallan bedroom guda biyu sai ɗakunan ƴan aiki dana sauƙar baki akwai babban fili a gaban gidan yanda aka cikashi da flowers da ɓarin mai gadi sai wajan kiwon dabbobi acan gefe da wajan shaƙatawa da aka buga masa canopy mai rufin china ana gama tsara ginin suka koma gidansu da yaransu guda biyu."


Mahaifiyarce tafara yimasa zancen Auren ɗiyar abokin babansa da yayi alƙawari dama abun yana ransa ganin bata daɗe dafara karatu ba yasa bai tada zancen ba amma dayake tayi zancen akan gaɓa kawai saiya tashi yasamu mahaifinta Yabada sadaki mahaifinta yace bayan sadaki baya buƙatar komai dan haka aduk lokacinda ya shirya aure yasameshi kai tsaye zaisaka rana ayi biki.


A shekara na shida tasamu ciki ta haifo ɗiyarta mace aka sanya mata fadeelah mahaifiyarsa ne yasa aka saka mata.


A shekarar zancen aurensa tatashi dake maganar duniya bata ɓuya ya sanya kai tsaye abun yake kunneta ta birkita sosai jiransa kawai takeyi ya iso taji daga bakinsa. Yana shigowa daya ganta yasha jinin jikinsa yaranta suna zaune a falo ko takansu bata biba bare tace sutashi su basu waje tafara bala'i tana faɗin.




"Yau ni zakaci amana duk wani abunda nake maka a duniya da kyautatawarda nake maka nasake maka kuɗi duk abinda kake buƙata shi nake Maka amma da abinda zaka sakamin kenan? Sakamakon kyautatawar da nake maka kenan?" jin tana masifa yasa second born ɗinta Ahmad yace.


"Mummy mai dady yayi kike masa masifa?" dady kabata haƙuri kaga ran mumy ya ɓaci" dake dama sun saba duk lokacin wani saɓani yashiga tsakaninsu shike bata haƙuri ko agaban yaran yasanya suka ɗauka Dadynsu yana tsoron Mummynsu ne kaman yazama dole komai yafaru yabata haƙuri. isawa yayi sannan yace.




"Wani irin sakamako nayi miki tun kafin na aureki na sanar dake auren yarinyar kuma ke kika amince zaki aureni ahaka ni ayanzu banida wani abunda zan iya cewa sai dai kiyi haƙuri dannasan dole zakiji zafi"
jin yabata haƙuri yasanya tafara sauƙa tace.




"Shikenan naji zan haƙura amma yanzu yazama dole ka janye zancen aurennan kamar na faɗa maka har yanzu ba'a haifi macenda zan iya haɗa miji da itaba" girgiza kai yayi yace.


"Bazai yiwba zancen aurena babu fashi tunda kinada masaniya akansa bare kice na ha'inceki bazan iya karya wannan alƙawarinba" Yafaɗi hakan har cikin ransa saboda koda abaya baida niyyar auren nan kusa yanzu dole tasa zaiyi. Yanasp shima yafito a


Kuka sosai tasaka tayi ciki takira mahaifinta ta shaida masa yace ta tattara tataho haka ta kwashe yaranta tatafi can bayan yatafi da sati suka nemeshi yaje yayiwa mahaifinta bayanin komai tun kafin zancen aure yashiga tsakaninsu har lokacin data amince zata aureshi bayan aurensu kuma zai ƙara aure. Mahaifinta yanajin haka yace tunda da amincewarta dole ta haƙura yayi aurensa yayita lallashinta sannan yace tabi mijinta su koma.


Yasakata agaba da yaransa suka koma dukda hakan bawani ƙwanciyar hankali rikici na yau daban na gobe daban duk wata hanya da tasan zatabi yafasa auren tabi amma hakan baiyiwuba."




----
Dake mahaifinta yace kada yayi komain na auren hakan yasa shima yace zaiyi funitures acikin 2bedroom da lving rooms ya zaɓa mata guda ɗaya wanda yake nasa da nasu shida Hajjaju."




Haka ta tada rikici bazai saka amaryar agidanba sai dai ya nemi wani wajan ya sakata daƙyar ta haƙura yashawo kanta tabari ta zauna agidan."




Akayi aure yasamu amarya beyond expectation nasa saboda biyayya take masa da girmamwa duk wata kyautatawa tanayi masa alokacinnne yasamu damar da zaice ayi sannan ayi kuma yace abari, abari.


Amarya na cikin wahala wulaƙanci na duniya babu irin wanda ba'a mata ga gori kullum acikinsa take ko sau ɗaya bata taɓa tankawa ba kuma bata taɓaji ta tankaba saboda mijinta ya hanata kuma tasan ko tankawar tayi batada riba tunda taga mijinda take aure wanda yake

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads