Header Ads
Showing 144001 words to 147000 words out of 171869 words

Chapter 49 - BIBIYATA YAKE YI COMPLT Document by Zainab Bawa.txt

Ads the beginning of article before Image

05 Jun 2024

1096

Ads at the middle of Article

suke cikin mutane kawai yasa ban mata rashin mutumci ba dama inaji da haushin ɗatsu. Kallona yayi naci magani yasan za'a.


"Menene?" yayi magana a yanayin son shagwaɓa mutum. Idea ce mai mugun zafi ta faɗomin dan haka na kalli ƙafata shima kallon ƙfar yayi sannan ya dago gareni.


"Ya kama miki ƙafa? Dasauri na ɗaga kai,"Kina buƙatar na sassauta miki?" nanma kai na gyaɗa masa. Ya zare hannunsa cikin nata a wajan ya durƙusa Akan gauiwarsa guda ɗaya a gabana batareda damuwa da matsayi ko cincirindon mutane da suke wajanba. Hannuna yasa yafara gyaramun igiyar takamin. Wani irin rikitaccen ihune kawai yake tashi a wajan fans ɗinsa mata kuwa ji suke inama ace sune masu wannan sa'ar. Bayan yagama ta ɗaya ƙafar na miƙa masa ɗayarma ya gyara. A zahirin gaskiya fa babu wani kamani da takalmin yayi kawai dai inaso na nuna matsayina a wajansa ne. Ya miƙe haɗeda sakarmin murmushi nima murmushin nayi masa.


"Yayi miki? Na gyaɗa kai alamun yayi kuma fa ya ɗan yimin ruwa amma tunda buƙata tabiya komai yayi dai-dai. Shida kansa ya buɗemin ƙofar mota na zauna ya rufe kafin ya isa an buɗe masa yashugo muka tafi.

Wani tangamemen hotel ne wanda aka sauƙi palyers na team ɗinsu kusan gaba ɗayansu sun iso Hammood na ɗaya daga cikin wanda sukazo late. Kowane player apartment yake dashi shida family ɗinsa sannan duk wani expenses both nasa dana family ɗinsa an ɗauke. Su kansu naga alamun wajan ya burgesu bare ni wacce inbanda Abu dhabi danaje shima hakan ina ƙwance zazzaɓi banga ko'ina ba sai wannan ƙasar. Apartment ɗinmu yana ɗaya daga cikin apartment na musamman a gajiya muka ƙarasa ciki ni dashi Dama ɗaki ɗaya muka zauna Nwarh da Lina kowacce takama ɗakinta.


Ana gobe za'a fara buga worldcup washe garin ranarda mukaje kenan saiga Yaya Ahmad da Yaya habibu harda matan Ya Ahamd wacce cikinta ya fito sosai Bansan da zuwansu ba sai ganinsu kawai nayi babu wanda ya sanar dani ko Hammood bai faɗamin ba ashe shiya shirya tafiyar. Baisan Matar Ya Ahmad nada juna biyu ba ya haɗa harda ita da Mummy tace tazauna Baba yace tataho kawai duk wnai kula zata sameshi acan kusa da mijinta. Mum ma aranar ta iso ni ina wajansu Yaya Ahmad banmasan ta iso ba a wajansu na raba dare saboda Hammood bai dawoba kuma ya shaidamin ba lallai ya dawo ba zai iya kaiwa safiya."


Nagama exam Please kuyimin addu'ar fitowa da kyakkyawan sakamako."


PAID BOOK


Littafin BIBIYATA YAKEYI (WAYE SHI) na kudine ki biya Naira Dari uku 300 Domin kisha karatunki hankaki kwance,
account 0003075326
Zainab m Bawa JAIZ BANK Ko katin MTN ta wannna lambar 08161146563 shaidar biya Ta 08161146563 da zarar kin biya Hankli kwance zaki samu damar karanta wannan labarin ku shigo daga ciki kar ayi babu ku domin wannan
tafiyace wanda salonta da tsarinta ya bambamta da ko wace irin tafiya karki bari ayi babu ke."
Idan Kuma kina bukatar Aringa tura miki pc kullum Dari hudu 400 kacal zaki biya batareda an Sanyaki cikin group ba zaizo ya sameki har yanda kike."




ZAYNAB ALABURA
Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun banking Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya.






Ranarda za'a fara buga worldcup bansaka Hammood a idona ba motocine sukazo har yanda muke ɗaukanmu Sai alokacin naga Mum na gaisheta ko kallon yanda nake batayiba Gabaki ɗaya muka shiga mota Ya Habibu ba mota ɗaya mukaje dashiba bansan yaya akayi ba nidai naga bayan mun isa suna magana da Nawarh bansan ko ɗan zamansu da baifi 30minute a mota bane har suka saba. Bata yanda kowa yakebi ba mukabi ta wani waje daban muka shiga ciki.




Fili yacika da ƴan kallo tamƙam da ƴan kallo amma sai da mu ba cikin wannan wajan muke ba wani wajene da ake kira da VIP suit daga cikin wajan kallon duk wani abunda yake gudana a cikin filin da glass aka rufe wajan sannan akwai set na Sopa a ciki da table na drink da komai a takaice dai wani ƙayataccen living room akayi a wajan. Nida Nawrah da Lina sa Ya Ahmad ta matarsa da Mum Da Yaya habibu. Wajan ya tsaru sosai banajin wannan wajan Hukumar worldcup ne suka ɗauki nauyin biyansa tunanina yafi karkata akan Hammood ne ya kama mana dakansa wanda suke cikin fili suna iya ganinsu da duk abunda mukeyi. Muna kallo ƴan wasa suka fara shigowa har suka gama idona yanakan Hammood yayi kyau sosai cikin kayan ball ɗin bayan angama duk wasu ɗabi'a da ake gudanarwa kafin fara ball Juyowa Hammood yayi ya kalli wajan da muke murmushi na sakar mas adake da wajanda muke babi wani nisa sosai shima ya maidomin.
Ana shirin fara wasa yaya habibu yamin magana cikin harshen hausa.


"Marmeeyy bani wayarki nakira Maryam tace nakirata video call da zarar anfara" miƙa masa wayar nayi ya ya amsa ya kirata mamaki da al'ajabi yagaza ɓoyuwa a fuskar Nawrah bata taɓa tunanin Yaya Habibu ɗan uwana bane sai a yanzu dataga munyi magana da yare ɗaya sannan ta ƙare mana kallo. Har ɗan kama mukeyi. Aranta tana faɗin aida nayi kama da Yaya habibu toda komai zaizo da sauƙi ko Mum ɗinsu zata ɗauki abun dasauki akan yanda ta ɗauka yanzu. Duk da Yaya habibu Bai kaisu haske ma amma tsakanin haskensa da nawa akwai bambamci sosai kuma suma a cikinsu ana iya samun masu madaidaicin haske kamar nasa Kuma gashi kyakyawa ni mace dayakamata ace nice nayi kyau sai shi namiji yayi kalar kyau sosai. Saida na ɗago na kamata tana kallonmu sannan ta kauda kanta mamaki yaƙi barin ranta Ba ita kaɗai ba ashe har Mum da Lina sunyi mamaki amma babu wanda yafito ya nuna mamakinsa a fili.


Kiran maryam Yayi suka fara waya tana kallon abunda yake faruwa. Cikin ƙwraancewa da salo haɗeda son burgeni Hammood yake buga wasa. Wannan wasan da zaiyi yasan zai sake taka muhimmiyar rawa a jawo hankalina gareshi. Duk wani salonda yasan idan yayi a wasan zai burgeni shi yakeyi. Shi awajansa hakanma rahama ne tunda Allah ya bashi baiwa sannan yasaka baiwar tazama abunda matarsa takeso da muradin gani a rayuwarta a ganinsa wannan wata dama ce da ubangiji yabashi tun kafin atafi Fisrt half Hammood yaci ball ɗaya celebaration muka fara anata murna da ihu. A idona Nawrah Da yaya habibu suka rungume juna da alamu basusan sunyi hakan bama saida suka ankara da abunda suka aiakata sannan ya saketa su duka sauka shiga taytayinsu. Ni kaɗai na lura da abunda yafaru Maryam kuwa baiwar Allah anjuya camerarta zuwa fili can kawai take kallo batasan wata na shirin iskantar mata da masoyi ba. Sa'i-Sa'i suke kallon juna sai suyi murmushi duk ina ankare dasu. Ana dawowa daga first half suka rama cin da Hammood yayi musu baƙin ciki raina kamar nayi kuka har wani ɗaci nakeji. Ana cikin wasa team ɗin su Hammood suka ƙara ɗaya. Angama wasa Su Hammood sunada 2 sukuma 1 aka tashi wasa akayi declaring su Hammood winners. munkoma gida batare dasu ba sai wajan 12yashugo idona biyu dan dawowata daga wajansu Ya Ahmad kenan.


Inajin buɗe ƙofarsa da gudu na tashi na nufi ƙofa yana kallona ya buɗemin hannu na ƙarasa na ɗaleshi gabaki ɗaya da.


"I made it Rouhi"
"Nasani I know You'll"
مبروك إليك أحسنت عملاً
(Natayaka murna Job weeldone)"


"Dagaske nayi?"


"Yes ka iya buga wasa sosai bantaɓa kallon ɗan wasan ƙallo kamarka a tarihin wasa gabaki ɗaya ba" murmushi yayi yaji daɗin maganata sosai. Sauƙa nayi daga jikinasa naja hannunsa har zuwa ciki. Saida yazauna sannan na kaleshi fuska cikeda murmushi da kuma zullimun abunda nakeson aikatawa nace.


"اسمح لي أن أهنيك"
(Let me offer you my congratulations). Yatsaya yana kallon abunda zan bashi. Murmushi nayi na sunkuyar dakai sai inajin bazan iya ba. Ya miƙe haɗeda riƙe hannuna yana kallon fuskata.


"Ina sauraronki Rouhi I'm eager naji abunda zai fito daga bakinki please say it" shi duk tunaninsa zan faɗa masa irin soyayyar da nake masa ne. Saida na runtse idanuwa na sannan na buɗesu akansa ƙara tsayina nayi yanda bakina zai iya sauƙa a dai-dai nasa saida na rufe ido sannan na sada Lips ɗina da nasa na kama lip ɗinsa na ƙasa nashiga tsosa rikicewa yayi dasauri ya mannani da jikinsa baiyi zaton abunda zanyi ba kenan. riƙe waist ɗina yayi ya ƙarfafamun tsayuwata yayinda ƙarfina yazama duk ajikinsa saboda akan yatsuna na tsaya yasan zan gaji. Sosai yake tayani muna kissing juna munji daɗinsa fiyeda wancan karo na baya dan wannna karo ana yinsa ne cikin shauki saboda duk rai sunason abunda suke aikatawa tsawon lokaci muka ɗauka a haka banja jiki ba har saida naji ni kaina ya isheni. Shikuwa maimaikon yaji yagaji saima wani kaimi dayake ƙara samu dukda nagaji amma ban daina bashi ƙwarin guiwa ba har yazare lips ɗins dakansa. yayi taking deep breath sannan ya sake manneni yana neman bakina zai sake mayarwa yatsuna nasaka akan lips ɗinsa ya tsaya yana kallona da kyawawan idanuwansa wanda suka fara canjawa. Saida na tsotse damshin dayake kan lips ɗina sannan nafara magana


"Is okay ya isa haka thats your reward dakayi wanning wannan match ɗin. You only scored 1."
Yana rumgume dani batareda ya sakeni ba yace.


"Thank you thats a huge gift da na taɓa receiving alokacin danaci ball"




"أنت تستحق ذلك"
(You deserve it) nafaɗa ina sunna kaina.


"Nayi scroring 1 You kissed me sau 1 What if I scored 2 next time?" Da yatsuna nayi alamun 2 sannan nace.


"Then You'll have 2"


"dagaske" batareda na kalleshi ba na ɗaga kai.
"Zan bakai mamaki next match"


"I'll be waiting" nafaɗa ina ɓoye kaina cikin jikinsa.


"kedai kawai Keep your Words kinyimin alƙawari dayawa remember?" na gyaɗa kai.


"Yeah ban mantaba"


"Muyi bacci koh? I'm tied amma kafin mu ƙwanta kinci abinci" kai na gyaɗa masa.


"Naci kaifa?"


"Ina jin yunwa amma ba abinci nakeson ci ba" shieu nayi kamar bansan abunda yace ba na raba jikina da nasa.


Kwanciya mukayi saboda shi kansa yace gajiye yake."






A match na biyu Hammood saida yayi scoring 3 each one yaci saiya ɗago hannunsa yayi kiss ajiki ya nunamin nafarko yatsa 1 yaɗaga na biyu ma haka. Haka na 3 mutane sai kallon al'ajabi suke dake akwai camera tako'ina kuma ansan matarsa ke wajan sai akayi tunanin kawai yana nunamin abunda yayi scoring ne ni dashi kawai muka san ma'anar kayanmu, wannan karonma haka aka gama cikeda nasara har yafi karon baya ma.


Yana wajan ɗan ƙaramin celebration da suka haɗa na winning match ɗinda sukayi amma gabaki ɗaya hankalinsa yana wajena Allah-Allah yakeyi ya dawo yasamu kyautar danayi alƙawarin bashi.


Muna zaune Da matar Ya Ahmad shikuma da yaya habibu sun fita ta dubeni.


"Marmeeyy kekam Allah yabaki wallh kinyi sa'ar miji mijinda kowace mace take fatan samu abun kamar wani mafarki Allah yabarku tare mijinki yana sonki sosai" na amsa da.


"Amin" sannan na ɗaura da faɗin.


"Kema ai kinyi sa'a Ya Ahmad mutumin kirki ne" tayi murmushi.


"Sosai ma yayanki yanada kirki sosai. Yawwa kinga wannan Lina take koh Wallh kiyi hankali da ita hatsabibiya ce duk wata hanya da zataja hankalinsa na lura abunda takeyi kenan. Ranar mun fita da yayanki inaso naɗan taka ƙafata dake kinaan ai duk dare muna zaga waja koh? Tana tsaye ta sanya wasu mugayem kaya tana jiransa ya dawo mu munganta zaune ashe shugowarsa take jira. Yana zuwa ta miƙe da gudu ta rumgumeshi ƙoƙarinta ta haɗa bakinta da nasa wai adole tana masa murna. Dake shiɗin tsayayye ne kuma yana sonki yaraba jikinta da nasa bai bari tasanu nasarar abunda takeson yiba ya ɓata rai sosai yanayi mata magana akan bayson haka karta sake ƙoƙarin yimasa haka yanada mata kuma yanason matarsa baice mata yana neman komai a wajanta ba, ke dagani har Yayanki tsayawa mukayi muna kallon ikon Allah. Ba ita kaɗaiba kafin ya isa zuwa wajanmu mata nawa sun tsareshi? Kedai ki riƙe abunki Ki kalallameshi kinayin sake zakiji wuff irin wannan mazan ba ƙaramin riƙo akeyi musu ba Kiyi masa biyayya sosai yanda zaiji babu wata sai ke idan kikayi masa riƙon gaske shima zaiyi miki na gaske kinsan larabawa akwaisu akwai riƙon mata" murmushi kawai nakeyi amma araina inajin zafin cewa wai Lina na jiramsa yadawo. Banajin bacci amma nayi mata sallama na fita dan inaso naga marassa kunyan da suke taremin miji."




______________


Da sallama yashugo ɗakin ta amsa daga ƙwance yanda take. Ya zauna bakin gado.


"Sannu ko zamuje asibiti? Zazzaɓi tun jiya amma yaƙi sauƙa kekuma kinki muje asibitin banga mai son zama da ciwo ba sai ke" Turo baki tayi zatayi magana tunoda wanenne Hamma ya sanya tayi saurin maida bakinta.


"Hamma Nifa banason asibitin nan wallh koda yaushe cikin zuwansa muke daga wannan sai wannan gara kawai na ƙwanta har naji sauƙi" ɗan siririn tsaki yaja saboda wani lokaci taurin kan Aysha na damunsa"


"Bari naje nazo ki shirya Nima zanje na shirya idan kuma kin warke idan nazo saiki sanar dani zaki kama duk wata hidimar da take kanki saboda na ɗaga miki ƙafa ƙwana biyu bakida lafiya amma tunda kin gwadamin bazakije asibiti ba kin warke shikenan saiki cigaba da duk wani abunda yake kanki" Sarai Aysha tasan abunda yake nufi tayi ƙoƙari tamiƙe duk da zazaaɓin dayake jikinta.


"A'a Hamma bari na shirya kawai kaje ka shirya mutafi" saida yayi dariya ganin yanda tayi reacting lokaci guda.


"Okay Toh kona taimaka miki? Naga jikin babu ƙarfi"


"No kaje ka shirya kawai zn iya" miƙewa yayi yafice 10minute gabaki ɗaya sub shirya kashe abubuwan wutan gidan kawai yayi ya ɗauki wayoyinsu suka wuce asibiti. Bayan wasu ƴan gwaje-gwaje ya nuna tana ɗauke da ciki na sati 7. Dagashi har ita sunyu murna likitar tayita jan hankalinsu da bayani akan yanda zasu tafiyarda lafiyar ta sannan tace idanda hali ya ɗaga mata ƙafa har na wani lokaci zuwa cikin yayi ƙwari. Bayan ya biya kuɗin ganin likita dana test dana magani suka tafi gida. Yana zuwa ya kira Ummi akan Taturo masa maryam tazo Aysha babu lafiya Ummi ashe Likitar takira ta gaya mata tun bayan fitarsa toh kawai ta amsa masa sukayi sallama.


Bayan wajan 2hours dayin wayarsu sukaji sallamar Maryam hamma yatashi yaje ya buɗe ƙofa a tsaye yaga Ummi da Maryam Suna jiran abuɗe.


"Bismillahi Ummi kushigo ai bansan har dake za'azo ba Mun ɗagoku" ummi bata kulaba suja shuga palourn dake Aysha na palour basukai ga shiga ciki ba ta miƙe zata taryi Ummi.


"Aah aida kinyi zamanki jiki babu ƙwari zauna abinki zan ƙaraso har wajan" kanta yana ƙasa takoma ta zauna bayan sun gaisa Ummii ta tambayi ya jiki tana ƙare mata kallo duk da rame ta ƙara wani haske tayi fatt bayan jinya harda jarabar Hamma. Cikin tausayawa Ummij ta dubi Hamma.


"Haɗo mana kayanta tare zamu tafi idan cikin yayi ƙwari lokacin ta daina laulayi saita dawo"


"Ummii tafiya da ita kuma? Dan Allah da kin barta anan sai Maryam tazauna Ta kuka da ita"


"Maryam ai yarinyace bazata iya kula da mai laulayi ba haɗo kayanta ƙwana biyu kawai zatayi nadawo da ita" Hamma badon ransa yasoba yashiga ciki ya haɗo mata kaya itakuwa Aysha kamar ta goya Ummi dan daɗi zata samu sauƙi kenan farin ciki har a fuskarta saida ya nuna. Ummi dama duk halin da suke ciki yarinyar brother ɗinta tana sanar da ita dan itake duba Aysha tun kwanaki da tayi ɓari sau biyu tabada shawarar ta ɗauketa dama tana jira saita sake samun ciki saboda ta ɗauketa da Hujja."




PAID BOOK


Littafin BIBIYATA YAKEYI (WAYE SHI) na kudine ki biya Naira Dari uku 300 Domin kisha karatunki hankaki kwance,
account 0003075326
Zainab m Bawa JAIZ BANK Ko katin MTN ta wannna lambar 08161146563 shaidar biya Ta 08161146563 da zarar kin biya Hankli kwance zaki samu damar karanta wannan labarin ku shigo daga ciki kar ayi babu ku domin wannan
tafiyace wanda salonta da tsarinta ya bambamta da ko wace irin tafiya karki bari ayi babu ke."
Idan Kuma kina bukatar Aringa tura miki pc kullum Dari hudu 400 kacal zaki biya batareda an Sanyaki cikin group ba zaizo ya sameki har yanda kike."




ZAYNAB ALABURA


Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun banking Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya.








Bayan ya haɗa kayayyakin ya fito dasu palour Ummi ta dubeshi.


"ƙarasa dasu waje ina zuwa"


"Ummmi kuɗan huta mana yanzu kukazo fa Saina maidaku."


"Bada driver nafito ba Nida kaina na ɗauko mota yanzu zamu tafi karka wahalar da kanka ka huta" suna magana ne cikin harshen Fulatanci. Yayi waje da kayan Ummi tadubi Aysha.


"Zan tafi dake saboda laulayi idan kika warwaee saiki dawo na yanke shawara batareda izininku ba amma idan kinji zaki zauna gidanki saina bar muku maryam tazauna daku" dasauri ta girgiza kai.


"Zan biki mutafi Ummi nima zanfi jin daɗin zaman can"


"Toh saka mayafinki Maryam taimaka mata naga jikkn babu ƙarfi inaga idan munkoma gida ma sai an ɗaura mata ruwa" Maryam ta taimaka mata suka fito Hamma na tsaye jikin motar data ƙaraso ta buɗe suka sshige Shidai Hamma kawai faɗan dayafi ƙarfinsa ne babu yanda zaiyi amma baiso tafiya da ita da Ummi tayi ba har wane laulayi takeyi da za'ace bazata zauna a ɗakinta ba?"


Asama su Mama sukaji zancen komawar Aysha gidan Ummi harga Allah hakan yayi musu sosai Kuma Ummi tayi dattako.




________


A kan wasu kujeru na zauna wanda suke kallon ƙofar shigowa harabar wajanda nake ina zauna Lina da Nawrah suka fito da alamu akwai yanda Nawrah zatace ko ima zata a wannan daren? Koda yake nagasu Awajansu babu wani dare da rana aduk lokacin da mutum yakeso zaije yanda yakeso tunda na kallesu sau ɗaya na ɗauke kaina Lina har tayi nisa ta juya ta dubeni tanamun wani kallon ƙasƙanci wanda bata taɓa samun damar kwatantamin hakanba sai yau data ganni mi kaɗai.


Harararta nayi na jaa tsaki haɗeda kauda kana gefe wani irin haushin ya ziyarci zuciya ta dama inaji da Haushinta. Tana ganin kallon da nayi mata yafi nata zafi sai tayi saurin kauda

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads