Showing 3001 words to 6000 words out of 171869 words
Chapter 2 - BIBIYATA YAKE YI COMPLT Document by Zainab Bawa.txt
son tashin hankali, ku girmama su gabaki ɗayan su mahaifanku ne." Suka amsa da.
"Toh." Sannan suka fice. Yaya Ahmad wanda yake zaune a wajan tunda aka fara bai yi magana ba sai bayan sun fita ya yi masa sallam ya fita."
——————
Ina zaune a aji amma gabaki daya na kosa lokacin tashi yayi na dawo gida dan son sanin halin da Hussaini yake ciki ga kuma tambayoyin da suke raina fall inaji yau gabaki daya sai na sauke su akan Aunty, kuma ina addu'ar kowacce tambaya idan nayi tabani amsar ta.
Ana tashi kuwa jikina har bari yake na dauki Qur'ani na nafice na tattara kan kannena sannan muka yi gida. Ina shiga na riski wani labarin daban da murnata na fito daga dakin Mama zuwa dakin da aka sauke su, sun amasani babu yabo babu fallasa amma ko ajikina danni dama zaman kadaici ni kadai agidan ya isheni. Hira nake yi musu suna amsawa sai da aka kira sallar asubahi sannan na fice dan yin Sallah. Dake dakin da aka sauke su ciki ne da falo harda bandaki ya sanya tunda suka shiga basu fito ba sai da Mama ta aikani na kirawo su muci abinci. Naje na sanar dasu suka shaida min na kawo musu shi nan kamar yanda aka yi musu jiya. Mama tace lallai su fito aci dasu naje sanar musu. Sai da suka dauki lokaci kafin suka fito basu wani tsaya sunci abincin ba suka koma ciki yanzu nikam jikina ya fara sanyi yanda suke mu'amalantarmu kamar ba yan uwansu ba. Hakan yasa nima banbi takansu ba dare nayi na shige dakin Aunty.
"Anty waini menene yasa Yaya yake miki haka?" Na jefa mata tambaya,
"Ba Yaya kadai ba dukkan su haka suke min." Ta bani amsa.
"Amma Anty na Yayan yafi yawa shifa ko yaranki baya kulawa."
"Hmm Mamee kenan sarkin tambaya, kwanaki da kika tambayeni bana fada miki dalilin ba?"
"Eh kin fada amma Anty jikina yana bani kamar ba wannan dalilin bane kadai yasa yake miki haka ta iya yiwuwa akwai wani dalilin daban tunda kinga mu yana mana magana amma baya yiwa su Meema."
Sai da ta zuba min idanuwa kamar zatace wani abun saita fasa, afili tace.
"Mamee kenan sarkin wayo, kema bakya jin dadi yanda yake nuna musu koh?" Gyada kai nayi tayi murmushi tace.
"Shikenan tunda shi baya son su ke ai kina sonsu kiyi karatu sosai ki zama gatansu gabaki ɗaya."
Murmushi kawai nayi amma tabbas nasan akwai abunda Anty ke boyewa saboda ga dukkan alamu Yaya ba haushi daya yake nunawa akanta ba. Har zuciyarsa yake jin haushinta da abunda ta haifa.
Sallama nayi mata na shige dakin Mama na samu ta kwanta amma ba bacci na keyi ba. Nabi gadon nima na kwanta.
"Mama!" Na kira sunanta.
"Uhm" Ta amsa.
"Mama wai menene a tsakanin Yaya da Anty yasa yake jin haushinta?" Kamar bazata amsa niba sai can naji tace,
"Ke ina ruwanki da kike son sani?"
"Mama ni bana jin dadin yanda al'amura suke gudana a gidan nan, idan inada hali dana gyara."
"Allah yabaki halin wata rana ki gyara. Amma kidaina bibiyar abunda ya hada Antynku da yayyunku banaso." Amin nace sannan nadaura da faɗin.
"Kwanaki Anty ta taba fadamin dalilin, Amma ni gani nakeyi kamar wannan dalilin yayi kadan a tsanar da Yaya ya ke yi mata inaji kamar akwai wani abun." Mama tace.
"Menene tace miki dalilin?."
PAID BOOK
Littafin BIBIYATA YAKEYI (WAYE SHI) na kudine ki biya Naira Dari uku 300 Domin kisha karatunki hankaki kwance,
account 0003075326
Zainab m Bawa JAIZ BANK shaidar biya Ta 08161146563 da zarar kin biya Hankli kwance zaki samu damar karanta wannan labarin ku shigo daga ciki kar ayi babu ku domin wannan
tafiyace wanda salonta da tsarinta ya bambamta da ko wace irin tafiya karki bari ayi babu ke."
Idan Kuma kina bukatar Aringa tura miki pc kullum Dari hudu 400 kacal zaki biya batareda an Sanyaki cikin group ba zaizo ya sameki har yanda kike." A
✔️ote
Follow
Comment
Share please
To be continued
Zaynab Alabura 💕
*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡
*BIBIYATA YAKEYI *
_(WAYE SHI?)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
BY
ZAYNAB BAWA
Marubuciyar
*BIBIYATA AKEYI*
*Y'AR FARI*
*YARIMA FAYAD* paid book 200
*ƘADDARAR RAYUWA*
Assalamu alaikum
Ina kuke manyan mata?
Matanda suka san kansu, Suka amsa sunansu Mata, Amarya, Uwar gida shin kin taba using kayan *ROYAL EXQUISITE* kuwa??? Idan kin taba to barkanki danna tabbata kin fita daban da sauran mata, idan Baki taba ba kuwa lallai an barki a baya kuma kin dade kina cutar kanki da mijinki, Domin samun kayanmu masu kyau da inganci zaku iya tuntubarmu domin munada Kayan mata masu kyau da inganchi Kamar su
Virgin again
Tightening pills
Turaren ban mamaki
Sweetness agents
Wetness agents
Infection set da sauransu
Domin ƙarin bayani ku tuntubemu ta wannan numbern
08030644073
*Assalamu alaikum barkanmu da warhaka*
INA MASOYANA WANDA SUKA KARANTA LITTAFIN BIBIYATA AKEYI 🤝 WANNAN SALON SHEKARAR 2017 NE, YA KUKAJIN LABARIN? NASAN DA YAWANKU BAKU MANTASHI BA!
TO MASOYA GANI NAN NA KAWO MUKU WANI ZAZZAFAN LABARI MAI CIKE DA SALO KALA KALA!!! WANNAN SABON LABARI SHINE BIBIYATA YAKEYI(WAYESHI).
WANNAN SALON 2023 NE! SABON LABARI SABON SALON LITTAFI DABAN YAKE DANA BAYA BIBIYATA AKEYI!
BIBIYATA YAKEYI(WAYESHI) PAID BOOK NE BA FREE BA.🤝
PAGE 3
Kallon Mama nayi naga tayi shiru tana saurarena ni take jira na bata amsa batareda bata lokaci na nace.
" Tace saboda mahaifiyarsu tabar gidan ta dalilinta." shiru Mama tayi sai can tace.
"Allah ya rufa asiri." Na amsa da
"Amin."
"Gobe idan Allah ya kai mu zaki koma dakin yayyunki da kwana, Saboda bai kyautu ace mu muna kwana da yaran mu daki daya su kuma suna can su kadai ba." Toh kawai na amsa dan nasan dole hakan zata faru. Mama nasake kiranta. Cikin kaguwa da tambayoyina tace.
"Mamee ki kwanta kiyi bacci yanzu dan bazaki fahimci lamuranda suke faruwa agidannan ba amma idan lokaci yayi zaki fahimta"
"Zan kwanta Amma Mama yakamata izuwa yanzu ace kowa yayi hakuri tunda abun yadauki shekaru" kallona sosai tayi sai can tace.
"Mahaifinku yana bukatar ganin iyalansa a hade waje daya baida burin daya wuce wannan, ki kasance mai son yan uwanki kada kitaba kullatar yan uwanki a wani dalili komai girmansa" Kai kawai na gyada tace.
Dare yayi ki kwanta na amsa na lumshe idanuwana ina karanto addu'oi ahaka har bacci ya daukeni."
Washe gari na koma dakinsu da kwana, naji dadin zamana a dakin Saboda suna da wayar Android hakan ya sanya idanna bace cikin dakin ko motsina ba'a jiyowa barin ma idan na samu wayar da data na ringa bin labaran yan wasanni kwallon kafa kenan. Nafi amfani da wayar Fadeela dan tafi saukin kai saboda kwanaki kadan da muka yi da ita har mun saba da ita, kuma itace Babba dama. Zaman mu da ita yasa ta fahimci yanda nake masifar son wasan kwallo hakan yasa take download na wasannin koda na tafi hadda ta ajiye min. Aysha kam yawanci gaisuwa kawai ke shiga tsakanina da ita dan ita sam bama tada sakin fuska ba kamar fadeela ba."
———
Dawowar mu daga sallahr la'asar kenan babu wani malamin daya shiga mana, hakan yasa muka zauna muna ta hira nida kawayena muna dan hirar mu, Maryam ta dubeni tace,
"Mamee an duba miki results kuwa?" Da mamaki na dubeta nace.
"Result ya fito ne? Kai Wallahi ban sani ba."
"Toh Yaya zakiyi ki sani tunda ke ba waya ce dake ba? nidai an duba min nawa kuma na haye, gabaki daya fa mu hamsin ne muka haye cikin mutane dari biyar."
Gabana sai da ya buga darram dan ni kaina nasan bani da kokarin da zan haye mutane dari biyar. Kuma Maryam ma ai bawani kokari take da shi ba tunanin ya fado min cewa ai baban Maryam yana da kudi sosai ko nawa ne zai iya biya dan Maryam ta haye jarabawarta. Maryam ta tabani tace.
"Wai ya haka ne daga cewa result ya fito sai jikinki yayi wani sanyi?"
"Uhm ai naji kince mutum dari biyar ne Maryam ina naga kwakwalwar haye mutane har haka? Kedai na miki murna Allah ya sanya alkhairi amma nikam nasan bazan wuce ba." Dariya tayi tace.
"Haba karki bani kunya mana har nawa mutane dari biyar suke?"
"Uhmm keni kibarni tukunna ban san me zan cewa Baba ba har indai banci jarabawar nan ba."
"Babu komai in sha Allahu duk yanda nasa kafata kema zaki saka taki da izinin Allah"
Karfafa min guiwar da Maryam tayi ta yi ne ya sanya na dan ji sanyi amma jikina ya gama bani bazanci wannan jarabawa ba.
Ganin yanda na dawo ya sanya Maryam yin dariya sosai ta dauko wayarta kirar iphone 7 ina kallon wayar nasan abunda zata yi hakan yasa nayi saurin sauke nikab dina a hakan Maryam ta dauki photon, nayi saurin fauce wayar na maida jakar ina fadin.
"Ke baki da hankali koh? Idan aka sake kama wayar nan kinsan bazata fitoba, kuma wallahi ni dake duka sai munsha duka."
"Toh wazai kama? Bayan duka malaman suna meeting.?" Mtsww naja tsaki nace.
"Wancan karon ma waya san za'a kama?"
"Oho dai nidai bani wayata"
"Bazan bayar ba." Na fada ina sake ɓoye Jakarta. Bangama rufe baki ba malami ya shigo na dubeta nace.
"Kinganni koh?" Shiru tayi bata kulani ba.
Malamin bai dade aciki ba ya sallama mu saboda lokacin tashi yayi. Sai da aka tashi kafin nabata wayar tata. Kamar munafuka haka na shiga gida dan nasan har indai Baba yaji labarin fitowar result to ya saka an dubo masa. Amma sai naji shiru hakan ya tabbatarmin da Labarin bai iso Baba ba.
Washe gari sassafe na tattara kannena muka wuce Hadda dan banaso labarin fitowar result ya isko baba ina gidan.
Picture dinda Maryam ta daukeni a wayarta nake dubawa bada son raina akayi pic dinba amma ba karamin kyau nayi ba dukda kasancewar da nikab a fuskar sai yaba pic din nakeyi Maryam ta harareni tace.
"Da jiya ba kin tsayawa nadauki pic din kikayi ba? Gashi yanzu sai kallo kikeyi inada tabbacin baki taba daukan pics mai kyawunsa ba" tsaki naja na mika mata wayar hadeda fadin "yar rainin hankali Allah yasa akarbe wayar"
"Ba amin ba muguwa" ko kulata banyiba na tashi nabar wajan, mikewa itama tayi ta biyo bayana muka koma aji.
Yau ba kamar kullum danake jiran lokacin tashi yayi kawai natafi gida ba. Yau lokacin nema banaso yayi. Saboda nasan komai ake ciki yanzu Baba yasan da zancen fitowar result kuma yasaka anduba masa. Hakan yasa nake ganin kamar lokacin yana tafiya dasauri.
Ganin gabaki daya Hankalina baya jikina yasanya maryam tace.
"Wai har yanzu zancen result dinne? Meyasa jiya baki sanarwa Baba ba? Nasan daya dade da sakawa an duba miki"
"Hmm ke kibari wallh tsoro nakeji shiyasa dan aure zaiyimin idan banci ba"
"Aure!" Maryam tayi exclaiming hadeda zaro ido. Toh har nawa kike ma?" Sai kuma ta tuntsure da dariya tana tsoanata amarya takaici ya sanya nakasa amsa mata.
Har lokacin tashi yayi ban kulata ba da aka sallememu saida gabana yafadi saboda bansan abunda zan taras ba agida ba. Banbi ko takan maryam ba jikina babu kwari natashi naje na hado kan kannena mukayi gida, Haka nashiga gidan kamar wata munafuka sai rabe-rabe nakeyi dan banaso na haduda Baba.
Ina shiga nasanu Mama zaune a falonta nayi mata sannu zan shige ciki tace min.
"idan kin canja kayanki kije babanku yana kiranki." Tun datsu ya aiko yace idan kika dawo yana nemanki Sai da naji faduwar gaba. Na amsa na shige ciki na canja kayan Uniform zuwa kayana na gida. Haka dai na nufi wajan Baba jiki a sanyaye."
PAID BOOK
Littafin BIBIYATA YAKEYI (WAYE SHI) na kudine ki biya Naira Dari uku 300 Domin kisha karatunki hankaki kwance,
account 0003075326
Zainab m Bawa JAIZ BANK shaidar biya Ta 08161146563 da zarar kin biya Hankli kwance zaki samu damar karanta wannan labarin ku shigo daga ciki kar ayi babu ku domin wannan
tafiyace wanda salonta da tsarinta ya bambamta da ko wace irin tafiya karki bari ayi babu ke."
Idan Kuma kina bukatar Aringa tura miki pc kullum Dari hudu 400 kacal zaki biya batareda an Sanyaki cikin group ba zaizo ya sameki har yanda kike."
✔️ote
Follow
Comment
Share please
To be continued
Zaynab Alabura 💕
*BIBIYATA YAKEYI *
_(WAYE SHI?)_
2023
*بسم الله الرحمن الرحيم*
BY
ZAYNAB BAWA
PAGE 4
Marubuciyar
*BIBIYATA AKEYI*
*Y'AR FARI*
*YARIMA FAYAD* paid 200
*ƘADDARAR RAYUWA*
Assalamu alaikum
Ina kuke manyan mata?
Matanda suka san kansu, Suka amsa sunansu Mata, Amarya, Uwar gida shin kin taba using kayan *ROYAL EXQUISITE* kuwa??? Idan kin taba to barkanki danna tabbata kin fita daban da sauran mata, idan Baki taba ba kuwa lallai an barki a baya kuma kin dade kina cutar kanki da mijinki, Domin samun kayanmu masu kyau da inganci zaku iya tuntubarmu domin munada Kayan mata masu kyau da inganchi Kamar su
Virgin again
Tightening pills
Turaren ban mamaki
Sweetness agents
Wetness agents
Infection set da sauransu
Domin ƙarin bayani ku tuntubemu ta wannan numbern
08030644073
Sallama nayi a bakin dakin mahaifinmu ya amsamin Sallamata yana daga zaune a kan kujera jikina yafara rawa dakyar na sanya kafata nashiga palourn, idona yakai kan takardar dake gefensa tana ajiye, na dago kaina na kalli fuskarsa dan ganin yanayin da yake ciki murmushi ya sakarmin Hadeda fadin matso nan zo kusa ki zauna da sauri na karasa nazauna a kasa gefen kujerarda yake a zaune, nima nasaki murmushin dan yanayin fuskarsa ya tabbatarmin babu wata matsala amma ina tunani toh baisan da cewa result yafito ba,
"Mamee andawo daga makarantar?" Muryarsa ta katsemin tunanina "Eh Baba mundawo shine mama tace kana nemana sannu da hutawa"
Murmshi yayi mai sautin Dariya yaɗauko takardar yace.
"Mamee kinyi abun kai yanzu na aika yayanki yaje ya karbo result dinku gashinan acikin mutane dari biyar kece ta goma sha uku"
bansan lokacinda nadaka tsalle ina ihu ba Baba dariya kawai yakeyi na suri takardar nayi waje girgiza kai kawai yayi a gaskiya yayi murna sosai dacin wannan jarabawa da nayi dan tabbas yanaso tayi karatu dan tayi karama idan aure yace zaiyi mata,
Mama tana zaune a yanda nabarta na shiga ciki da gudu ina fadin na "haye mama na haye"
"Me kika haye?" Ban kulataba naci gaba da tsalle ina murna Mama tace.
"Ke banason Hauka ki tsaya ki fadamin me kika haya?"
"Jarabawar Weeding mana Mama ta nursing Baba yasa aka karbomin na haye, murna sosai Mama tayi tana fadin "kai Alhamdulillah amma naji dadi Allah yacigaba da baki nasara Arayuwarki" na amsa da,
"Amin" sannan nawuce izuwa dakin anty na nuna mata na juyo zuwa dakin Baba dan kai masa takardun dan duk wasu takardunmu shike ajiyewa,
A yanda nabarshi anan na sameshi ya kunna Babban TV dake babban palourn nasa wanda yake ajiye akan TV stand na makalawa a bango ne amma dake yayi girma sai kawai aka ajiyeshi,
Mika masa takardun nayi na zauna dake kwallo yake kallo nima nafara kallo, dama tun asali wajan mahaifina na koyi kallon kwallo domin bayida wata tasha dayake kallo irin sunna Tv daganan kuma sai tashar kwallo duk kwallonda za'ayi baya missing shiyasa gabaki daya gidanmu akayi mana searching tashar da take kama wasan ball kai tsaye, muna kallo muna yar Hirarmu dake kaff cikin yan wasan kwallo babu wanda bansansu ba, muna cikin kallo akaci team din da muke supporting cikeda bacin rai da takaici na bugi kujerarda take gefena, Baba yajiyo ya dubeni shima yaji babu dadi yace.
"Sorry kiyi hakuri zamu rama yanzu tunda Akwai Hammud Acikin yan wasan kwallon nan, Shekara nawa yanzu yakafa tarihin da ba'a taba kafawa ba a kwallon kafa izuwa yanzu duniya ta yarda cewa kaff yan wasan kwallon duniya Babu kamarsa" Baba yanamin hirar kamar wanda yakeyi da abokinsa shi kansa yaji dadin zama tayashi kallon wasan ball din danayi dan yanason yin kallo da wani gefensa koda kuwa ace bamai kallon kwallon bane bare ni da dama nice wacce na gado kallonsa ko mazan gidanmu Babu mai son wasan kwallon kafa kamar yanda nakeso. Baba baiyi shaidar Hammod a banza ba dan kuwa ya Rama cin kwallon da akayi musu, Baba yace.
"Kingani koh kingai koh" Mama ce tashigo dakin da Sallama mu duka muka amsata amma ni ban juyo na kalleta ba gabaki daya hankalina nakan ball din, mama tace "mamee tashi kije ana shirin kiran Sallah shima baban naku yanzu zai tafi masallaci"
Mikewa nayi zan fice sai da nakai bakin kofa Baba ya kirani "Mamee" na juyo nace "Na'am" ki dafamin Baƙin shayi idanna dawo a masallaci saiki kawomin toh na amsa sannan na fice . Ina fita mama tadubi Baba tace"
"Yarinyar nan yanzu tanaso tafika kallon ball abun har damuna yakeyi idan tafara kallo" murmushi Baba yayi yace .
"Ke baki fahimceta ba amma ni na fahimceta. tafara kallon ball ne kawai danta farantamin tun shekarun baya idan tazo taganni cikin damuwa saita canja tasha zuwa ta kwallo tunda tasan inaso dan kawai ta cireni a damuwa. Yarinyace karama amma tanada matukar wayo, duk wani abunda zai kawo farin ciki a cikin gidannan shi takeyi yanzu ki kalla taci jarabawarta dan kawai ta faranta mana inaji ajikina ta dalilinta kan gidannan zai dawo ya hade kamar yanda yake a shekarun baya. Kinga ta dalilinta yan uwanta guda biyu sun dawo gareni inaji wata rana zatayi abunda zaisa gabaki dayansu su dawo" mama ta kalleshi da rashin fahimta, Baba ya nisa sannan yace.
"Aysha da Fadeela sun dawo nanne saboda mahaifiyarsu tasamu labarin na sanya Mamee a makaranta shiyasa taturomin yaran acewarta suma na biya musu ita gani takeyi kamar ta kuntatamin saboda ta turamin yaran bazan iya daukar dawainiyarsu duka ba, amma abunda bata saniba shine naji dadin hakan matuka domin kuwa sun dawo gidan mahaifinsu kenan dawowa tahar Abada, kuma a yanda na lura sunajin dadin zama da mamee sosai Alkhairai dayawa idan zasu faru dani ta dalilin mamee ne inaji ajikina itace silar yayewar duk wata damuwarmu." Cikeda damuwa Mama tace.
"Toh amma yaya zaka iya daukaan dawainiyar karatunsu duka? Ko Mameen zata hakura fadeelah tunda itace Babba tafara a