Header Ads
Showing 51001 words to 54000 words out of 171869 words

Chapter 18 - BIBIYATA YAKE YI COMPLT Document by Zainab Bawa.txt

Ads the beginning of article before Image

05 Jun 2024

1071

Ads at the middle of Article

haɗuwa ba.
Ummi tace.


"Ga maryam nan sai haƙuri min haɗaku da aiki"
Mama tace.


"Ko menene abin aiki?" aida Marmeeyy da Maryam Duk ɗaya suke" Ummi tayita godiya. A haife ta girmi Mama sosai amma dayake macece mai gyara bazaka taɓa cewa takai shekarunta ba. Ummi tace.


"Abbansu yana mota wai yanaso su gaisa da Babansu daga nan Abuja zamu wuce anan zamu tashi" Mama tace"


"Toh bari ayi masa magana kishigo dashi. Dukansu suka miƙe Mama taje ta sanarwa Baba sannan aka buɗe masa ƙofa suka shigo shida Hamma da Ƙofar Babban falonsa"


" Sun daɗe aciki suna hira ashe sunsan juna tun suna samari amma dai bawani sanayya can ba sai gashi kuma zumunci ya ƙullu yanzu. kusan 1hour Abba yana wajan Baba har Hamma yakoma mota yabarsu dan shi zai kaisu. Ummi ma na wajan Mama amma batayi zaton Abba zai jima haka wajan Baba ba.


"Kinga dai ta dalilin yara zumunci ya ƙullu" cewar Ummi. Mama tace.


"Gashinan sai dai muyi fatan Allah ya rayasu zumunci yacigaba ko bayan ranmu. Duka suka amsa da Amin.


Bayan Abba yafito muka rakasu har waje danyi musu Sallama sai alokacin naga Hamma. A kunyace na gaisheshi na fisge. Yanata kallona nikuma Allah. Allah nakeyi kar wani ya lurada irin kallonda yake yimin dan duk rashin fahimtar mutum idan yaga kallonda yake yimin saiya fahimci wani abun. Kamar baisanda mutane a wajanba yaketa aikamin da kallo daga ƙarshe na ɓuya a bayan Maryam har aka gama sallama akayi addu'a suka tada mota a zatona babu wanda ya lurada kallonda yake yimin Ashe bansaniba duk abunda yakeyi akan idon Abbansu. Muna kallonsu har motarsu tatashi ta kaucewa ganin idonmu sannan muka koma ciki."






ZAYNAB ALABURA


Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya.


A ɗakin Mama Maryam tasauƙa dan kayanta ma anan aka zubasu. Shikenan mukabar karatu muka shiga sharholiya. Maimakon musamu karatu kamar yanda muke tunani sai kuma wasa saida Mama taci ƙaniyarmu kafinnan muka Cigaba da karatu.



Koda yaushe da rana muna palour ko cikin gida kokuma ɗakinmu na daa da dare muke rabuwa ita tashige ɗakin Mama mukuma mushiga ɗakinmu. Ƙwana biyu Hamma yayi acan yadawo. Amma bayan 3days yasake komawa.




sai ana gobe za'a fara exam kafin nasake samun saƙo daga wancan numbern anamin addu'ar farawa a sa'a. Tun daga ranar kusan kullum ne ƙwana duniya sai nasamu saƙon addu'a daga wannan number dake gabaki ɗaya ma yanzu wayar ba damuna tayi ba yasanya nafita harkarta tunda ko data bana buɗewa.


Wancan wayarne take kullum atare dani dannasan Hammana yakan kirani idan yasamu sarari a aikin daya jeyi.


Maryam kuwa wata shaƙuwace na lura tashiga tsakaninsu da Yaya Habib abun har mamaki yake bani shiba mai zaman gida bane amma musamman yake zuwa yimata hira.


Ban Fahimci abunda yake faruwa ba saida ranar muka fito daga exam lokacin mun rubuta Exam na biyu kenan. ita tafara fitowa sai tazauna tajirani. Da nafito maimakon mutafi sai na bita muka zauna muna ɗan hutawa kafin mutashi muwuce gida tace.


"Babe duk gidanku Yaya Habib yafiku kyai shine yayi kamada Baba sakk" Na harareta nace.




" Saboda kinsan duka ƴan gidanmu koh?"


"Yaa Ahmad kaɗai bansaniba kuma shima zan ganshi soon kum bana tunanin yafi Yaya Habibu kyau."


"Aysha fa?" na jeho mata tambaya.


"Dama-Dama ita amma dukda haka batakai Yaya Habib ba kamanni kawai suke" na taɓe baki danna gama gane yanda ta dosa. Tacigaba da faɗin.


"Babe wallhi Yaya Habib koh. Hmmm ya haɗu he's so caring" na ɓata rai nace.


" ke wai me kike nufi ne?"


"Oh baki gane abunda nake nufi ba? Toh mun faɗawa juna ne"


"mtsww" naja tski.


"Bangane ba crushing kike akansa kenan?"


"Ta wani fannin Yes in other side kuma no soyayya ce"


"Lallai Babe bantaɓa sanin bakida hankaliba sai yau Yaya Habibun? Ƙwata-ƙwata shekara nawa yabaki? Asunyi atata sukai 2years shine zakice kin wani faɗa masa? wai soyayya Banason shirme" maryam ta wangale baki da mamaki tace.


"Me kike nufi?"


"Abunda nake nufi shine kuba sa'an soyayyar juna bane idan zaki farka amafarki ki farka ki rungumi dahir wanda kike dashi a hannu"


"Iyyeh wato babe ni kika maida maras wayo koh?" ni Na goyi bayan soyayyarku da Hamma kece bazaki goyi bayan tawa soyayyar ba?"


"Shekaruna dana Hamma akwak tazara soyayyarmu ba ɓatawa juna lokaci bace amma taku yaudarar kaice. Kumama tayaya zaki haɗa soyayyata da Hamma da taki soyayyar? wai shirin film akeyi ko littafin hausa ne da idan na auri yayanki kema dole saikin auri nawa?" kuma Mafa kin tsofewa Yaya Habibu har indai maganar aurene Haba babe. Yaya Habibunda yanzune yake shiga 22years sai kace almara" ranta yakai ƙolokuwa wajan ɓaci dan haka bata kulani ba fuuu ttashi tatafi nima nabi bayanta. Keke napep ɗaya muka shiga amma babu wanda yake yiwa wani magana. Muna isa kowacce acikinmu ta ɗauko kuɗi ta miƙawa Me keke.napep ɗin ya kallemu da Mamaki yace.


"Ba tafiyarku ɗaya bane sai aɗauka acikin ɗaya kawai' har muna haɗa baki wajan faɗin.


"kowa da tafiyarsa" haka ya karɓa yaciro canjinmu yabamu. Muka shiga gida rai ɓace kowa da tafiyarsa tana gaba ina biyeda ita abaya Yaya habibu na ciki canopy ga dukkan alamu yana hutawa ne. Ganin yanayinda muka shigo yace.


"kai kuzo nan. Kun sake yin faɗane naganku tsuru-tsuru? Muduka muka fara zare ido ya dubi Maryam saida ya saisaita murya sannan yace.


"Meya faru ke faɗamin inajinki dan kinfita hankali" saida na marairaice itama sannan tafaɗa masa abunda nafaɗa ya ɓata rai sosai ganin irin kallonda yakemin nasam ransa yaɓaci da gudu na juya zan shige gida ya cafkoni haɗeda kafamin ranƙwashi yace.


"Munafuka idan ke zaki mana auren saiki Hana. Kuma waLlh naji zancenann bakin wani saina takaki" wajan sai zafi yakemin ina sosawa Idona yacika da hawaye najuya nadubi maryam tataɓe baki haɗeda yatsina fuska. Ni harga Allah bnsan sunrigada sun ƙulla soyayyarsu ba na ɗauka suna shirin yine hakan yasaka nayi kasassaɓa. Amma Na ƙudirci rama abunda tayimina najuya nashige ciki.
Nashiga da Sallama nawuce ciki fuuu Mama tace.


"Yauma ansake wani rikicin kenan yara sai azabar rikici kamar masu ganin hanjin juna" anty tayi dariya tace.


"Nifa rikicin nasu ma dariya yake bani ba jimawa anyi faɗa ba jimawa an shirya" Ana haka Maryam tashigo itama a murtuke tayi musu sannu da aiki tawuce. Akwance nasamu anty fadeelah a cikin ɗaki dake ita diploma tayi tagama aysha ce take degree yanzu take ajina biyi. Ganin yanda nashigo yasa tace.


"A'a marmeey jarabawarce duk haka? Na yi nodding kaina batareda nayi maganaba kawai na danna kiran Hamma" yana ɗauka nasaka kuka. Lokaci ɗaya ya rikice ya dibirbirce yana tambayana abunda yafaru daƙayr na tsagaidata cikeda shagwaɓa mai haɗe da taɓara na faɗa masa abunda yafaru. Tun daga can ina iya jiyo hucinsa ya katse kiran kawai. Yana datsewa yakira Maryam yayi mata tass-tass kuma yace karta yarda su haɗu ido biyu saiya wanke fuskarta da mari. Bayan ya kashe yakirani yayita lallashina har nayi shiru nasake mukaci gaba da Hira. Saida mukayi sallama sannan anty fadeelah ta dubeni tace.


"Lallai Marmeey kincika ƴar rainin hankali ke kina soyayya da yayanta ke kice bazatayi da naki ba? Wallhy Hamman nema dayake biye miki yabi ya sakaltaki da yawa ya fifitaki akan ƴar uwarsa. Saida naturo baki sannan nace.


"nima ai nawa ɗan uwan ya fifitata akaina ranƙwashinafa yayi harda cemin munafuka"


"Oh yanzu ranƙwashi kike yiwa wannan kukan taɓaran? Wani sai yace ai dorina yasaka ya zane miki jiki. Mijinki ya shiga magana da sakalci"


"Naga Hamma ne mijin? Kuma shine ya sakaltani koh? Babu damuwa ai" ta jijjiga kai haɗeda faɗin


"lallai Marmeey bakida kunya" muna cikin haka maryam tashigo ranta a ɓace sosai ta zauna gefe sannan ta dubeni kamar bazatayi magana ba sai kuma tace.




ZAYNAB ALABURA




Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya.








"Wai haushi kikaji? Ashe babu daɗi zafi kikaji? Kinmanta abunda kike saka Hamma yakemin? Ai wallh tsaf zan rama ɗaya bayan ɗaya saina rama abunda kikayimin da kin ɗauka ke kaɗai kika iya soyayya koh? Toh nima na'iya kuma Yaya habibu yana sona bake kaɗai bane wacce akeyi miki soyayyar. yanzu zai ɓaɓɓalaki akaina. Wai har kinkira kin faɗawa Hamma har yana cewa zai maremim fuska a'ina zai ganni? Aiko yadawo bazan yarda mu haɗuba har sai su Ummi sun dawo. Itakuma bazata bari ya dakeni ba" naƙi na kulata dan haushinta nakeji sosai Anty fadeela da muke bata takaici da dariya tace.




"Wai shin maryam da Marmeey yaushe zakuyi hankali? Yarinta fa ke damunku kuna juya yayyyunku yanda ranku yakeso sukuma dake Allah yayi sokaye sunata biye muku kuna rashin hankali. Na turo baki ina ƙunƙuni nace.


"Anty fadeeala idanfa kin girmi Yaya habib baki girmi Hamma ba kidaina ce masa soko"


"Wai dama kingirmi Yaya Habib" cewar Maryam sai alokacin na tankata nace.




"Sosai ma kuwa aiko aysha ta bashi watanni" na faɗa cikeda gatse. dasauri ta miƙe zata fita anty fadeelah tace.


"dawonan" sumu-sumu ta dawo ta zauna. Anty fadeelah tacigaba da faɗin.


"Ina zakije? Kuyiwa kanku faɗa kutsaya kuyi exam ɗinku cikkn lafiya kugama lafiya amma kunfi bawa soyayya muhimmanci fiyeda karatu banaji agida duka ansan abunda kuke shukawa ku faɗa musu subarku kuyi karatu idan bazaku iyaba ni saina kirasu dukansu nace su ƙyalesu kugama exam tukunna"
Dasauri nace.


"A'a ni wallh a'a Ina karatu karki kirashi bakiga yanzu ko waya bamayi da dare ba? Shi yacemin natsaya nayi karatu a nutse"


"Kefa" tafaɗa tana kallon maryam.


"Nima zanyi tabata amsa" toh gara ai tafaɗa sannan ta maida hankalinta kan wayarta. Ahaka Aysha tadawo daga school ta samemu muna zaune jefi-jefi muke harara juna. Idon Aysha na kanmu ta ajiye jakarta tana faɗin.


"Ayagis yauma ansake wani rikicin kenan?"


"Keda kikasan halinsu cewar Anty fadeelah" kafin mubar ɗakin saida muka shirya tukunna."






Wasa gaske soyayya tanata ƙarfi tsakanin Yaya Habibu da Maryam. Da ɗai-ɗai da ɗai-ɗai saita mutanen gidan suka fara ganewa. Abun kamar wasa har barazana nayi mata nace saina faɗawa saurayinta. Tace.


"Kinga dakin hutasar dani dan inata masa kora da hali sai yanzu yafara ganewa kinga kina faɗa masa zai fita hanyata. Nasamu Yaya habib maikuma zanyi dashi? Ko wayarsa bana ɗagawa sainaga dama amma haka zai nace saiya kirani. Ni karma wata rana yaje yakira gaban Yaya Habib yazo ya kashemin aure"
Sake baki nayi ina mamaki nace.


"Wai kekam nake ke cemin ba'a gwadawa namiji so ba? Koduk munafunci ne?" bata kulani ba dan tasan tafaɗa."


Mama tana fahimta takirashi ta zaunar dashi. Dafarko tafara tambayarsa Habibu wai shin Soyayya kukeyi da maryam ne? Saida ya sunkuyarda kai sannan yace.


"Eh mama dama inataso na faɗa miki" ashe kin sani"




"Wanann rawar kan badole kowa yasani ba Habibu? Amana batace haka ba an bani amanarta bazan bar wannan abin yacigaba da faruwa ba yarda damu yasa iyayenta suka batta a wajanmu kubar wannan rashin hankalin dan Allah" yayi ƙasa dakai alokacin yayi dai-dai da shigowarmu daga makaranta kenan muka tsinki maganar. Dasauri mayam ta ƙarasa ciki sai ganinta kawai sukayi fim. Tazauna gaban mama sai haki take tafara faɗin.


"Mama bansam zancenda kukeyi ba amma kaman akanmu ne dan Allah mama karki rabamu wallh inasonsa nicema nafara sonsa kafin yafara sona" Daga yaya habib har mama baki buɗe suke kallonta shi kansa namiji bazai iya wannan kasassaɓar ba. Nikam bani na aikataba amma inaji mata nauyi dan haka naja ƙafata nayi ɗakinmu na daa. Babu kowa aciki nazauna gabana sai faɗuwa yakeyi sai inaji kamarn nice soyayyata ta bayyanawa duniya aka santa. Ko har indai zanji haka akan soyayyar aminiyata da Yayana. Yaya kenan aranarda aka gano nice mai soyayyar? Bazanma iya imagine ba dan haka na fiske. Banfito aɗakin ba saida naji fitowar Yaya Habibu sannan nashiga ɗakin Mama. Bansamu kowa a palour ba sumu-sumu kamar munafuka nawuce ɗakinmu dan banaso ma mama taji shigowata. Ina shiga na sameta ƙwance akan bed ta rufe har Kanta" zama nayi bakin bed ɗin na janye bargonda ta ruhu dasauri ta buɗe ido ganin nice ya sanya ta sauƙe ajiyar zuciya. Nace.


" me kikeyi anan?"


"Babe ki ƙyaleni bazan iya haɗa ido da mama ba kinsan kasarsaɓar danayi? Wallh tsorone ya kamani sai naji kamar wanda za'a rabamu shine fa nakasa controlling kaina" Tausayi tabani sosai cikin Sigar ƙwantarda hankali nace.


"Ki ƙwantarda hankalinki har indai mamanda nasani ne bazata rabaku ba sannan zata nuna miki kamar babu abunda yafaru. Mama nasonki dan haka zata asheki hanni bibbiyu"


"Allah babe?"


"Allah kuwa ke kinsan mama batada matsala ai"


"Nasani sosai amma nayi rashin kunya fa. Wallh saida nayi nace anya nice kuwa? Kamar ba bafulatana ba"


"Share kawai Babe kina dani ai babu wani abunda zai faru" tayi dariya tace.


"Nasamu gwarin guiwa."


Tunda tana raɓe-raɓe taga mama ko kaɗan bata canja ba saima wata kulawa data ƙara bata saita saki jikinta.


Ahaka muka kawo ƙarshen exam ɗinmu sauran guda ɗaya amma ita anbada interval atsakani. Yayinda auren ya Ahmad sai ƙaratowa yakeyi. Maryam ma tace itama zai taje bikin amma har lokacin bamu tambayi baba ba. Koda yaushe munada exam Hamma ke zuwa yakaimu amma bashi yake dawo damu ba. Yanzu bamucika samun lokaci tareda shi ba shidai haƙuri kawai yakeyi yana jiran agama wannan exam ɗin yasako mahaifa acikin lamarin.
Ana gobe Zamu rubuta exam ɗin ƙarshe Maryam tace na rakata gidansu ta ɗebo wasu kaya ta canja kayayyakinda tayi amfani dasu. Tunda immediately
ana gama exam zamu tafi bikin Yaa Ahmad.


Da rana muka shirya muka tafi munsamu ƙofarda zai kaimu cikin gidan a buɗe hakan ya nuna Hamma yana gida tunda dama tun kafin mu fito na kirashi na gaya masa.


Har muka kusan gama abunda mukaje yi Hamma bai fitoba sai ga kiran wayarsa na ɗaga yacemin.


"Baby har yanzu baku iso bane?"


"Mun iso muna ɗakin Maryam" nabashi amsa.






ZAYNAB ALABURA


Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya.






"Okay toh kizo ɗakina ki sameni Ina jiranki yafaɗa sannan ya kashe wayar" maryam tace.


"Muje koh babe?" nace.


"Hamma nakirana bari nadawo saimu tafi"


"Ohh toh shikenwn jeki kinga shaff na manta ma ban ɗebi jewelries ɗina ba barina ɗeba you can go" saida na tsaya ganan madubi nadubi fuskata daƙyau sannan na fice nabarta tana ɗeban jewlries ɗin.
Saida na ratsa har nakai ƙofar palournda nataɓa samunsa aciki sannan nayi knocking dakansa yataso ya buɗemin ƙofar idanuwana suka sauƙa akan fuskarsa ya sakarmin murmushi nima na mayar masa sannan nayida kaina ƙasa. Ciki yayi nabishi a baya ya isa ya zauna akan kujera naje kujerarda take gefe ta zauna.


Nasake gaisheshi ya amsa sannan yace"


"Babyna kinyi kyau sosai. Nadaɗe banganki da kayanda ba uniform ba sai yau. Tunda nace ina sonki kika ƙauracewa gidannan" nayi murmushi kawai yacigaba da faɗin.


"finally gobe zaki gama exam kina gamawa Su Abba kawai zamu jira su dawo ayi magana. Amma inaso ki sanarwa mama kafin su dawo"Na zaro idanuwa nace.


"Hamma yaushe zan iya? Kabari kawai idan sun dawo ka faɗa musu" ya harereni yace"


"Wato ni maras kunya koh?" dasauri na girgiza kai nace.


"A'a Hamma ni bahaka nake nufi ba" Ya jijjiga kai alamun bai yarda ba nace.


"Allah kuwa Hamma" yayi murmushi sannan yace shikenan nayarda. Amma gaskiya kiyi yanda zakiyi mama tasani" na gyaɗa kai alamun nayarda amma bawai dan zan iya faɗa matan ba?. Najiyo muryarsa yana faɗin.


"Ina tunaninma Abba ya fahimci wani abun amma dai baice komaiba sai dai yanayinsa alokacinda muke tafiya abuja ya nunamin" nan da nan cikina ya ɗurk ruwa jikina har wani ɗan bari yakeyi kaɗan nace.


"Hamma yayi wani reaction akai koh? Kaine randa zasu tafi kanata kallona kuma kasanfa da mutane a wajan na faɗa muryata tana rawa" saida yayi ƴar dariya sannan ya Matsao ƙarshen kujerarsa yayi kusanci da tawa kujerar. sosai turarenda nasaka yake fisgarsa yana sauƙar masa da kasala. A sanyaye ya miƙa tausasan hannunsa ya kamo nawa hannun yace.


"Calm down baby bawani abun bane fa alamu ma ya nuna yayi farin ciki da hakan sosai dukda bai fito ya nunamin cewa yagane wani abunba" na sauƙe ajiyar zUciya haɗeda zame hannuna daga cikin nasa ka kunshesu a jikina bance komaiba" Mun ɗauki samada 1hour muna hira a palourn nayi tunanin Maryam zata nemeni amma batayi hakanba.

"Baby kicemin kina sona yau da ya kasance babu kowa a wajan dagani saike kunnena kaɗai zai saurara" na sunkuyarda kaina ina wasa da zobben hannuna wanda shima zoben yake kallo nakasa magana saima shine yasake faɗin.


"Please Baby ko bakyasona ne" nayi saurin girgiza kai yace.


"Okay tell me inajinki ya lumshe idanuwansa yace na rufe idanuwa kinga bana kallonki harna fara ƙoƙarin faɗa sai kuma na miƙe nace.


"Maryam na jirana barina tafi ya buɗe idanuwansa a lokacin" bafara tafiya ina faɗin basai ka kaimu ba kayi zamanka kawai zamuyi waya" har nakai kusan ƙofa ya miƙe taku ɗaya biyu uku yazo yanda nake saiji nayi ya kamo hannuna ta baya yace.


"Baby wani irin turare kika saka?"


"Humarne da kulaccam nabashi amsa" ya sauƙe ajiyar zuciya ya ƙarasa takowa dai-dai yada nake batareda yasake hannun ba nikuma damuwata ya sakemin hannunta dan ƙirjina sai bugawa yakeyi.


"Baby waya faɗa miki humra da kulaccam turaren ƴan mata ne? Na mamane kika saka koh?" na gyaɗa masa kai a tsorace dan ganin yanayinsa ya canja. Nasake ƙoƙarin ƙwace hannuna ya kamashi gam-gam ganin yana shirin haɗa jikina da nasa yasa nafarayin baya ahaka har saida muka isa ƙofar dake a tufe take gm naji na bugeta ya iso yamun rumfa ya haɗe jikina danasa sannan yafara

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads